Sunday, 16 October 2016

ILHAM 13

🏵🏵🏵🏵🏵
             ILHAM😪
          🏵🏵🏵🏵🏵



Na Ayusher Mohd✍🏼

1⃣3⃣

Gun zamanta tai hawaye yafara zubowa khalil ya karaso yanasan mata magana amma yakasa hkn yasa ya zauna kusa da ita kawai


Tun daga wannan rana iman itace assignment din meenal hk classwork in akaga sunyi iri daya wani sa'in meenal sai tace ai ilham ce ta satar mata littafi a gida ta kwafa hkn yasa ilham kullum sai dai tai na meenal daidai nata kuma ta cancanza



Hk yauma an basu assignment din math ilham kawai tai nata ta kwanta  ganin meenal bata kawo mata littafintaba yanda tasaba meenal bata tashi tunawa da assignment ba sai da safe aikuwa ilham nashiga wanka ta kwafe assignment din suna isa class sukai submitting sai dai ba'afi 1hr ba malamin yasa aka kirasu ya kallesu yace acikin ku waye ya kwafi assignment din dan uwansa da sauri meenal tace ilham ce dama tasabamin ilham ta kalleta tace malam ba hk bane yace to ya ya ne?tace bandau littafintaba Allah meenal tai sauri tace ina kallan yaya ya dauko yabaki ai  Zatayi bayani ta tuna fadan umma tace yahkuri sir ran malamin ya baci yace meenal ta tafi sannan yasa ilham kneel down takusa  1hr sannan yace go an call ur brother ai ba kekadai yakamata inyi punishing ba ilham ta taho tana kuka Allah sarki yaya me yasani dazatasa a hukuntashi data isa class din khalil naganinta ya fito yace ilham lafiya? Takalleshi yabata tausayi tace yaya bilal aka aiko in kira yace bilal kuma? Tace eh cewa akai in kira monitor yace auho yakoma ya kira bilal nan yafito yana wani cin magani aranta tace dama kaiya kamata ahukunta ba yaya ba


Ahanya ko kulata baiyi ba tace yaya bilal dan Allah in an tanbayeka kai yaya nane kace eh dan Allah yace a wani dalili? Ko lefi kikai? Tace a'a


Suna isa staff room malamin math yace class rep. kaini yayanta? bilal yai shiru malamin yakara tambaya bilal ya daure yace eh tare da kallam ilham baiyi auni ba yaji saukan ruler akansa dasauri ya juyo yace sir yana sosa gun ilham dariya ta kamata amma tsoran malam ya hanata malamin yace kneel down bilal ya kalli malamin sannan ya kalli ilham yace sir menayi malamin yace hk ma xakace? Yakara rankwalamai ruler bilal daganan yai shiru can kuma malamin yace kanada kokari amma ace  baxaka dinga taimakawa kanwarka da karatu ba hb bilal yaxa'ayi kadinga satar answer wani kana bata? wannan is a bad habit sai yanzu bilal yagane wato ta saci littafin meenal shine ta kalamai malamin yace plz karka sake kanaji bilal ya daure yace ok sir sannan malamin yace ya koma class kafin ya mike ilham tayi class da gudu


Aranshi yace wlh sai kin gane shayi ruwa ne yai kwafa yai class rai  a bace


Ilham kam sun shiga wasar buya da bilal ko gidansu yazo sai ta gudu baya ko ta shige bandaki bilal duk yana sane da ita kuma yayi alkawarin hukuntata


Yau mai aikinsu batannan gashi yau weekend hkn yasa tun safe ilham ke aiki dan ko wanka batai ba shara wanke wanke duk ita tai ba kunya yarinya karama kamar zata mutu tana gama wanke wanke ta zube a kitchen tana hutawa bilal ne ya shigo shida khalil mumy naganin bilal ta taso tana maraba da dan mu bilal yace mumy ina wuni tace ya gd? Ya Abbanka? Yace baya gari yaje dubai tace lalai yace dady fa? Tace yana asibitin nemanshi kake? Yace a'a dama mun kwana 2 bamu hadu ba yana magana yana waigen ilham dake zube a kitchen yai murmushin keta ganin ba aiki😏yace mumy nikam akwai wani kosai da kika tabayi mai dadi da wancan azumin haryau bana manta dadinshi tace koyi maka zanyi? Yace kardai in takura miki tace hb dai bilal gudin kar meenal ta taya ilham atunaninshi yasa yace ina meenal? Mumy tace bari insa a surfa waken yace to sannan tace khalil kiramai meenal ya mike yana kallan ilham



Ilham na zaune ganin bilal yasa tafara tunanin dukanta zaiyi sai taga ya wuceta jin muryar mumy tayi tace ilham tashi ki surfa mana wake tace mumy wlh nagaji bakiji bayana ba mumy tace kin tashi ko sai na daka ki ta mike  tadebo wanke ta fita waje hk ta wanke waken sannan mumy tace kikai nika ko? Jiki a sanyaye tai waje bilal yai murmushi 😏 sai dai khalil tuni ya mike yace jeki huta bari inkai tace a'a yaya yace ilham barshi nace ta saki tana kallan hadiza


Hadiza haushi yasa ta juya kai dan tanajin haushin yanda khalil ke ma yarinyar nan khalil yace bilal bari inje indawo yace to itakam ilham daki ta shiga ta fada gado


By Ayusher Mohd📚

ILHAM 12

🏵🏵🏵🏵🏵
           iLHAM😪
           🏵🏵🏵🏵🏵


Na Ayusher Mohd✍🏼


1⃣2⃣
Ilham ta share hawayenta tare da mikewa tsaye tace yaya dazan shiga makaranta mafa maimakon Fatima Ashiru sai mumy tasa akasamin Fatima mahmud yai shiru shikanshi yasan akwai wani abu kuma kwakwalwarshi nasan tuno mai wani abu daya faru yana yaro sai dai hkn ya faskara suna cikin hk meenal takara zuwa da gudu tace yaya kazo yaya bilal yazo dasauri ya mike yace ilham zo mu shiga ciki tace tab ni ai banasan ganin wannan abokin naka mara mutunci ina nan khalil yai murmushi sannan yai cikin gida itakam nan ta zauna tana hango wannan ginin da aka kewaye kuma umma ta musu gargadi karsu kuskura suje gun mutum daya ne yake zuwa wani likita tai ajiyar zuciya tare da mikewa


Sam ta manta bilal nannan tai cikin gida shikuma ya mike zai tafi khalil na bayanshi zuciya daya ta shigo shima yazo fita ai kuwa sukai gware yana dagowa a zuciye ya hankadata yace dama nasani ai bazaki taba ganina ki wuce ba sai kim batamin rai jiyadda kikamin da kaya ya shiga duba rigarshi ba wani abu yai ba amma bilal da fitina khalil yace hb bilal kamata ahankali yarinyace kuma daga gani tafika jin jiki ya fita ya dagata yana kade mata jiki


Ilham ta kafeshi da kallan tsana idanta yai jaa bilal yace kin dauke idan daga kaina kosai na tsokaleshi tace wai ni mena maka ka tsaneni yace kinfi kowa sani ya fito ya bigeta takusa faduwa khalil ya tareta ta mike tai cikin gida


Khalil ya biyo bilal yace wai abokina mai kanwata ta maka? Yace kai kake ganin yarinyar nan salaha batada kunya rannan bakaga dukan da sukawa meenal ba yarinyarnan duk yanda nai tabata hakuri sai tace ita batai laifin komai ba shiyasa nisam ta fita daga raina khalil yace kaii ban yarda ba ina ilham ina dukan meenal? Bilal yace kaika sani ya wuce ya shiga mota driver din gidansu yajashi sukai gida



Ilham ce da safe bayan sun tashi daga barcita gyara dakinsu yanda ta saba sannan ta shiga dakin mumy ta gyara ta share sannan tai wanka tasa uniform din makaranta dakarfi taji meenal na kiranta ta fito rike da safa tace menene? Tace kije inji mumy tace to tare da karasawa falom a zaune taga dadynsu ta tsugunna tace dady ina kwana yace ilham kim tashi lafiya tace eh yace good tace mumy fa yace tana daki hkn yasa tai cikin dakin ashiru yabita da kallo zuciyar shi na tunomai fatimarsa


Tana shiga hadiza tace zo nan takarasa tace kira nai intuna miki karfa kimanta meenal yayarkice duk abinda tafada amakaranta kiyi hkri  tace mumy amma meyasa zata dinga cewa mutane ni mai aikinsu ce? Ran hadiza yafara baci amma tadaure tace to meye dan ta fada basai ki share ba? In sun yarda kansu in basu yarda ba su suka sani Tace shikenan tace yauwa kidinga yi mata class work kuma sannan intace kimata abu kidingayi kece karama dole kiyi tace to sannan ta mike tafito tai gun umma tagaisheta sukayi breakfast suka tafi skul



Sam ilham batada kawaye dan makarantar masu kudice da a wata makaranta take sai dady yamaidata tasu meenal da khalil yanzu batafi 2 month a makarantar ba


Meenal bataso ba dan tun tana karama mumy ke nuna mata ba matsayensu daya ba hkn yasa tafadawa yan ajinsu ilham yar masu aikinsu ce

Ilham na sauka daga mota taiwa khalil sallama tai class dan bangarensu ba daya ba su suna primary 2 ne itada meenal


Suna shiga malamin english ya shigo ba raba musu takardar test din daya musu jiya kaf class din ilham ce highest dan malamin sai dayasa a tafamata haushi gun meenal kuwa kamar me. ALLAH yabawa ilham baiwar mahaifinta duk abinda takaranta ko ta saurara ya zauna

Lokacin break nayi da gudu tai bangaren su khalil dan ta nunamai paper dinta taga wani class mate dinsa tace dan Allah inka shiga ka kiramin yayana kace mai ina baya yace to tai bayan class din da gudu ta juya baya tana jiran tawa khalil surprise shikuma dan aiken dayaje yace bilal ina khalil?  Yace yaje shop yace eyya dama kanwarshi ce ke nemanshi tana bayan class shikam yadauka meenal ce yai baya yana zuws yaga ta juya baya yace ya akai? Ilham ta juyo dadan tsallanta yace yaya suprise tare da ware takardar sai dai ganin bilal yasa ta sauke takardar tare da turo baki yadan yi karamin tsaki bilal ya matso daf da ita ya kama kunanta da karfi ta fizge tace da zafifa yace matsonan ni kikawa tsaki? Tace nifa ba tsaki nai ba yace ko tace eh ya kamo hannunta da karfi ya matse yace wato dan ba khalil bane ga marainin wayon ki ko tadan kwala kara tace hannuna yace sai kim fadan mekikai ta juyakai tafara cin lebenta hk take in taurin kan ya motsa ya saketa ganin tafara abin ya rankwasheta akai ya wuce ta bishi da harara tai hanyar class jitai an rufe mata ido tace waye kuma? Khalil ya juyo ta gabanta yace oh god waya tabamin sister ta kafin tabashi amsa yaga lebenta na jini dasauri ya ciro handkerchief ya goge mata yace muje ki kuskure baki waya tabaki? Tace bakomai sannan ta mikamai takardar ta yagani yace wow good girl kai wannan kanwartawa tana jaa tace menake jaa yai dariya yace kanki na jaa tace niban gane ba yai murmushi yace no hausa hk sukai tayi harta manta abinda bilal yamata



suna komawa gida taga meenal tayi gun mumy da gudu batasan meta cemata ba itadai taga mumy taxo a zuciye tace ina paper dinki da aka rabamuku ta mika mata taga taci 10/10 tace amma kinji jiki dan bakin ciki meenal taci 5 ke kice 10  shine dan kinsan abu bazaki fada mata taci ba? Tace mumy ba hk bane umma dake zaune tace zo nan ilham ta mike taje tace daga yanzu karki kuskura ki kara wuce meenal kota menene kuwa ilham ta kallesu dukansu sannan tai waje da gudu khalil ya bita



By Ayusher Mohd📚

ILHAM 11

🏵🏵🏵🏵🏵
             ILHAM😪
         🏵🏵🏵🏵🏵



By Ayusher Mohd✍🏼



1⃣1⃣

Cikin mota ta shiga sannan ta sauko ilhamm ta rike jitai har tashar an iso ana nemanta hkn yasa tai kasa da kanta ga Cikinta dake ciwo kamar me? Sai dataga sun tafi sannan ta dago motar lagos ta cika hkn yasa driver shigowa ya ja motar fatima tai ajiyar zuciya sai dai ana fara tafiya cikinta kamar an zigashi ya shiga murdawa ba sassauci haryakai ta dukursa a kasa wacce kezaune kusa da ita tace lfy? Fatima ta kasa magana matar da karfi ta fadawa driver yace yanzu yaza'ayi? Wani a motar yace akaita asibiti? nan wani yace akwai asibiti anan kusa sukace ya musu kwatance jin ana kwatancen asibitin yasa fatima tafara tsoro dan tanaji kamar asibitin mahmud nada ake kwatantawa sai dai lokacin tagama fita hayyacinta batasan komai ba suna isa asibitin akai ciki da ita yanzu har amai takeyi nurses din suka kira wani doctor yai emergency da ita sannan suka kira Ashiru sukace matar oga ba lafiya gata a asibiti cikin kidima yace ganinan a fara dubata sukace to

Sannan wata nurse ta anshi ilham da jakar fatima ta musu bayani asibitin ma na mijintane sannan suka wuce suka tafi


Likitoci uku ne akan fatima ga nurses sai dai inaa abin yaci tura ashiru ya shigo a birkice daidai lokacin da fatima ta daina numfashin da gudu yazo yaga wani doctor na danna mata kirji doctor ya dago yana girgiza kai ai ashiru naganin haka yakarasa da gudu ya shiga jijigata amma ina kuka wiwi yakeyi.



Duk asibitin yayi tsit sai can ilham tasa kuka hkn ne ya dawo dasu daga tunanin rashin fatima sannan wata nurse ta daurw tace akira gida asanar ko? Ashiru ya dau waya dakyar yakira waya



Su umma sunji mutuwar mahmud kam jiyai kamar shima ya mutu ga bakin cikin bai isa ya mike ba wannan rana ta kasance ranar bakin ciki ga mahmud da Ashiru dakuma yan uwanta.



Mahaifiyar fatima taso daukan ilham sai dai umma harda hawaye wai abarta anan ko mahaifinta zaidinga ganinta yaji dadi dawannan shawara suka amince sai dai bayan 40 suka sai da gidan suka koma wani gidan da ba wanda ya sani acewar umma ta gaji daganin yan uwan mahmud da fatima na zuwa itakuma hadiza da Ashiru so suke subar gidan yanda inya bude asibintin mahmud kowa zai dauka nashine agidan da suka siya sunsa an gina musu daki daya da toilet a can cikin gidan sun katange nan sukasa mahmud suka daukarmai mai anki namiji na kula dashi duk takardun filayensa sun siyar bakincikinsu daya wai duk yanda sukaso suga kudin mahmud ya faskara ance musu mahmud yace dole ilham ce kawai zata iya ansar kudi wannan abu ya kona musu rai ga kuma asibitin ya hada da banki dolene duk wata kudin da mahmud ya cike sai ya shiga account din mahmud wannan abu ya bata musu rai shiyasa suka saida shagon fatima kudin hadiza ta bude wani boutique a unguwar da suka koma.

Lokacin kuma labarin rayuwar ilham ya fara😪


Bayan shekara 8

Ilham ce zaune a bayan gidansu inda tasaba zama sai hucci takeyi muryar meenal ce ta daki kunnanta ke ilham mumy tace in bakizo ba wlh sai ranki ya baci ta mike ko kallan meenal batai ba tai cikin gida tana isa taga hadiza rike da bulala hadiza tace dan iskanci ina tambayarki abu dazu shine kika shareni? Tace ni banina dau miki dari biyar ba mari taji an saukar mata ta juyo ta kalli hadiza sannan tai kasa dakai tace yau zanga inda taurin kan nan naki ya tsaya nanta shiga zane ilham sai dai ilham taki bata hakuri ran hadiza ya bacci kwarai yarinya sai dan banzan taurin kai tuntana karama indai tace xatai abu ko batai niyar yin abuba duk abinda xakamata tofa baxatai ba meenal dake tsaye tana murmushin mugunta ganin yanda jikin ilham yafara fashewa da gudu khalil yakaraso ya rike hannun hadiza yace mumy meye hakan? Tace khalil barni da yarinyarnan yace meta miki hb mumy yaza'ayi ki kama jikin 'yarki kidinga jibga tace wacce......saurin hadiye maganarta tai tunawa datai ashefa umma da ashiru sun gargadeta karta kuskura tace ba 'yarta bace dasauri ta wayance tace ko 'yatace intai sata dole in hukuntata yace sata kuma? Tace dari 5 dina tadauka yace indai wannan ne nizaki daka dan nina dauka dazu nazo ansar kudi zan sai littafi naga kina toilet nadauka na fita hadiza ranta ya baci tai faki fuu itakuma ilham ta mike da gudu ta koma gun xamanta khalil yazo yace ilham kiyi hakuri laifinane? Tasa kuka tace yaya anya kuwa mumy ce ta haifeni? Yace hb ilham wace irin tambaya ce wannan?



By Ayusher Mohd📚.

ILHAM 10

🏵🏵🏵🏵🏵
            ILHAM😪
         🏵🏵🏵🏵🏵




Na Ayusher Mohd✍🏼


1⃣0⃣
Sanda fatima ta usa asibiti tagama firgita tana zuwa tai emergency tai musu bayani sukace ita ake jira tai signing a shiga dashi operation ai tanajin hk tafara baya baya sai da wata nurse ta rike ta ta mika mata takardar hannunta na rawa hk tai signing taso ganin mahmud amma hk kawai taji tana tsoron ganinshi sun dade a emergency kafin taga an turo gadonshi da gudu ta karasa daidai lokacin su umma suka karaso itada Ashiru da hadiza

Ganin fatima a wannan yanayin yasa tasan da matsala da gudu fatima tabisu dakin da sukai dashi tana zuwa likitan yace ke kadai kikazo tace eh ni matarshi ce ka fadamin keya sameshi? Ashiru ne ya shigo yace doctor ya akai? Doctor din yace biyoni office


Fatima kam kuka take sosai duk abin umma da hadiza sai da suka tausayawa mahmud ba ayi minti 20 ashiru ya dawo jiki asanyaye idanshi yayi jaa dana sani duk ya isheshi umma tace me sukace? Ashiru ya nisa sannan yace kafafuwanshi sun halaka dan shikanshi zaiji kamar ba'a jikinsa suke ba sannan magana baxai iyataba fatima tace wani irin zancene wannan? Ashiru yace fatima ki nutsu plz dasauri takoma kusa da mahmud tafara wani irin kuka hadiza tazo ta rungumeta tana bata hakuri ita kanta ilham dake baya sai kuka takeyi umma tasa hannu ta amsheta sai dai taji jikinta zafi hkn yasq suka tafi gun nurse
Yan uwan mahmud sunzo dubashi hk ba na fatima

Sabi'u driver yayi kuka yace sai dana rubuta nabashi fa nasanar dashi karya hau motar cike da mamaki fatima ta kalli Ashiru tasan tabbas batada hujjar zargi dan agabanta yabada takardar sai dai bata yarda mahmud yaga ance karya hau motar ba dan tasan ba dalilin dazaisa ya hau motar dabatada lfy

Sai da mahmud ya kwanta ciwo ne sannan yasan halin da fatima ke ciki a gidan dan yanzu a gaban idansa ake mata rashin mutunci gashi rashin mutincin da sukema yan uwanshi yasa sun rage zuwa kuma ashiru ko kunya yafadamai san fatima yake sai dai fatima batasan yasani ba.



Wannan shine abinda ya faru a baya.....yanzu sai mu cigaba😉

Asitin mahmud daxa'a bude sai dakatarwa akai Ashiru ke kula da karamin dama can

Fatima kamar yadda tasaba ta shirya mijinta da yarta zama tai tana karanta mai wani litafin taki "Kudin Tsatsuba" sai murmushi yakeyi  yasa hannu ya mata alama ta matso ta karaso kusa dashi ta kwanta tsakaninsu yanzu ba wani abu dan yanzu shi bazai iya wani abuba....


Kwankwasa kofa taji ta mike tare da cewa inaji an kawon kayan miyar bari inje inyi lunch ya daga mata kai tadau ilham suka fita ganitai gidan ba kowa mamaki ya kamata ina sukaje? Ta tabe baki ta ajiye ilham a kasa tana wasanta itakuma ta fara girki jitai an sakalo hannu ta baya an rungumeta cikin tsoro ta fara kokarin kwacewa sai dai an matseta sosai tace meye hakan? Wani salon hauka ne kuma wannan? Kansa yasa a bayanta ya saki wani nannauyan ajiyar zuciya a zuciye tadau wukar dake hannunta tace wlh ko ka matsa ko na caka ma dajin haka ya saketa ta juyo ta daga hannu zata mareshi ya rike hannun yace karki karamin hk fatima ke ai ba dutse bace kina bukatar namiji nasani basai kin fada ba tai wani murmushin mugunta tace lalai nayarda kanada matsala a kanka ya matso sosai kusa da ita hkn yasa tafara jaa da baya hartaje bango ta tsaya ganin ya daga hannu ta dauka marinta zai yi ta runtse ido da karfi



Salati sukaji anayi a bayansu cikin salon yaudara fatima kawai taji ashiru ya sauke hannun afuskarta ta bude ido tare da rike kuncin tace ni ka mara? Yace an mareki kuma Wlh tau takasance rana ta karshe dazaki nemi shigamin daki hadiza ta karaso tace daki? Yace ina bacci kawai nadanji motsi nadauka kece ganinai anzo kusa dani nikuma ina tunanin kece yasa na jawota nace kin dawo? Jin shiru yasa na farka nace ta fitarmin a daki gashi ba komai a jikina sai gajeran wando shina nasa riga nafito in mata magana


Fatima kam dariya yama bata tace lalai yanzu sharrin daga gun mata yakoma gun maza? Ankan ta rufe baki ta farajin duka hadixa ta ajiye meenal ta shiga dukan fatima kamar zata kasheta dakyar ashiru ya janyeta


Umma takaraso rai a bace tace wato mijinki ya nakasa shine dan zalama kike neman mijin wani? Lalai fatima na yarda ke tantiriyace wuce muje taja hannun fatima dakarfi tai gun mahmud da ita suna isa ta fara zayyanewa mahmud abinda yafaru shidai sai kada kai yakeyi alamar ba hk bane yana nuna musu su bashi littafinshi yai rubutu amma ba wanda ya kula da hkn sai fatima


Sai da suka gama fadan sannan umma tace ki dau kayanki kibar gidan nan dan bazamu iya zama dake ba kina neman mijin hadiza



Fatima kam akwai taurin kai dan duk abin nan ko kuka batai ba tace umma nida gidan mijina zakice inta....marin da aka saukar mata ne yasa ta dago ta kalli umma idanta yai jaa umma tacigaba nabaki yau zuwa gobe ki tattara ki tafi kibar kuma ilham anan suka juya suka fita




Suna fita ta bisu suka ce lfy? Tace 'yata zan dauko dake falo ta wucesu tana zuwa ta tadda khalil na Mata wasa ta dauketa azuciya takoma ciki hadiza tace kai wannan fatima shakiyiyace ji idanta ko hawaye umma tace kinsan taurin kanta ai




Tana shiga ta tadda mahmud na kuka sosai ta karasa ta rungumeshi sai a lokacin hawaye yafara zubo mata ta dago a zuciye tace doctor zan dau mataki a daren nan ya dago alamar bai ganeba tace yau da daddare zamubar gidan da ilham zantafi lagos a daren nan inaje zan sa dady yataho dakanshi ko ya daukeka ku taho tare ko yasa su umma subar gidan ya daga kai alamar yayi ta kara rungumeshi


Mahmud ya mata alama data duba safe dinsa ta duba taga takardu dayawa ta kwaso tazo kusa dashi ya cire guda daya sannan yasa a maida sauran sannan ya mika mata takardar takarba ta duba takardar asibitin shine tace meza'ayi? Ta mika mai littafin rubutunshi yasa ki kira lawyer na ki bashi tace to yace sannan kice mai karya bawa ilham takardar asibitin ko kuma kudaden dana bar mata harsai takai 20yrs ko tazo kafin nan karya bata kifadamai date din da aka haifeta tace to doctor daga hk bata kara cewa komai ba sai dai ya kula tanadan rike ciki tun dazu ya mata alama da hannnu menene? Tace bakomai ciki nane kedan ciwo ya tambayeta kuma ahk zatai tafiya tace ba wani abu ai ba serious bane.




Tun magrib tadau karamar jaka tasa karanta kala 2 dana ilham sannan tadau kudi a safe dinsu ta hada komai takarasa gun mahmud ta rungumeshi tsam tace doctor sai jibi kenan? Dan nasan gobe in Abba yazo bazaku zo goben ba yadaga mata kai yana murmushi jiyake kamar bazai sake ganinta ba ganin sallamar nadaukan lokaci yasa ta mike ya riko hannunta sun dan jima a hk sannan ta zare tace bari in fita dan nasan da magrib suna daki ya daga kaii tadau ilham tasa a baya ta fita cikin sanda tana murda kofa khalil na. Fitowa daga kitchen hannunshi rike da biscuit yace Aunty fita zakiyi? Ta daga kaii tare dayin waje da sauri ta fita taga mai gadi batace mai komaii ba tai waje



Khalil na shiga yacewa  hadiza umma yanzu Aunty tafita da jaka ina zata? Dasauri hadiza ta fito tai gun umma tafada mata umma tace dama ai hk mukeso ko? Hadiza tace wayasan meta shirya yi a wajen harda ilham fa ta fita umma tace hk ne sa Ashiru ya nemota nan suka fadama Ashiru dake asibiti azauce yai waje ya shiga nemanta layi layi


Gudu fatima take duk yanda cikinta ke ciwo batabar gudu ba fatanta taga mota tahau sai dai duk wacce tazo wucewa da mutane hakan yasa ta kira lawyer ta fada mai inda take ya karaso dasauri sannan tamai bayanin sakon mahmud tace kuma yakaita tasha dan ta kula tafara ganin mutane na nemanta



Ba musu ya kaita airport sannan yace karki damu duk yanda sukaso suci kudin sabon asibitin mahmud bazasu iyaba dan nina bashi shawara ya hada asibitin da banki yanda duk kudin da aka samu dolene su shiga banki tace mungode yace amma kamar baki da lfy? Tace ba komai sannan tasauka tai tasha





By Ayusher Mohd📚

NI DA PRINCE 18

☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄




*NA AYUSHER MOHD*



NO.1⃣8⃣

Salman yai ajiyar zuciya yace ke karki kuskura kib'atamin rai a daren nan dan zakisha mamaki, salma tad'an juyakai batare datayi magana ba, salman yace kwanta!in so kike mu kwana tare😏 dasauri ta juyo tace na'am? Yace eh ba haka kike son jiba? Ta mike daga kan gadon tace yaza'ayi mukwana tare😳? Salman ya matso inda take yasa hannunshi a kugunta ya janyota jikinshi, da sauri ta runtse ido, yai wani murmushin mugunta yace ba haka kike so ba? Ta d'aure tazare jikinta tace a'a ka kwanta😞.

Salman yace a'a mukwana taren ko? Dasauri ta girgiza kai tace a'a nabarma bargon da pillow d'in yaI kwafa aranshi yace kin d'aukan bansan burga zakimin ba? .


Kwanciya yai tare da jefo maya pillow din, ta amsa tarr da kallanshi☹, sunyi shiru dukansu kowa da abinda yake sakawa,can tad'aure tace sorry cikin sanyin murya, shima cikin magana mai sanyi yace 4 what? Tace maganar dana fad'a dazu I think bai kamata nafad'a ba, salman yad'anyi juyi yace at least kinsani, tace eh amma kaima u overreacted yace so kike nima in baki hakuri? Tace in mutum yai abinda bai daceba hakuri yake badawa ai, yace in hakane I can't zatai magana yace karki damen bacci nakeji🤔 aranta tace kamar nadamu muyi maganar😒.


Karfe 4 ta tashi tai alwala ta fara nafila batai minti goma da tashi ba salman ya mike ganin tana sallah kwarai yaji dadi aransa, mikewa yai yashiga toilet shima yad'auro alwala ya fita, harya dawo tana zaune tana karatun qur'ani sai dai a zuciyarta takeyi.

Wucewa yai ya hau gado sai dai ba bacci yai ba waya ya d'auko yana dannawa.


Wajen 7 ta kwanta yana kallanta sannan shima ya kwanta, basu tashiba sai da hanne tai musu knocking, salma ta mike tare da bude kofar, hanne tace ranki ya dade ku shirya zaku gaisuwa gun matan gidan, tace to nagode, hanne tace aikin nane ai.


Salma takoma ciki tare da kallan salman tace zamu gaisuwa, yai tsaki tare da juya mata baya ta makamai harara aranta tace so rude.

Kaya ta d'auka ta wuce toilet tai wanka ta goge jikinta tasa kayan, tana fitowa ya shiga ta kalleshi tace mutum sai isa🤔? Yace I can hear u dasauri ta rufe bakinta, ta shafa mai tare da murza hoda, ta zura kwalli tayi kyau dan dama mai kyan ce.


Mayafi tad'auka tare da cewa dole insa akawomin Abba yad'inkon hijabai ko biyu ne ta yafa mayafin tai falo, shayi ta had'a ko kulolin bata budeba, ta kurba ruwan tea din jin daxafi yasa ta ajiye tashiga tunani, ko ina yaya kamal? Wai ahaka zata kare rayuwarta a gidan nan? Kwakwalwarta ta cunkushe da wannan tunanin da basu da amsa, batasan salman harya fito ya zauna a kujerar gefenta ta d'ayan bangaren, jin motsin bude kula ne yasata ta d'ago wata baiwa ce ke bude kwanukan tana tambayarshi abinda yakeso? Salma takalleshi ta tabe baki, a ranta tace abincin ma sai an budema? Ko kallanta baiyiba itama tad'auke kai tashanye shayinta ta mike da sauri hanne ta karaso tace ranki ya dade bakici abinciba ai😞? Salma tace banajin ci ne hanne karki damu, hanne tace jiyamafa bakice na safe ba, salma tace nakoshi ne, hanne zatai magana salman yace kin min shiru ko kuwa? Batace ta koshi ba? Hanne tai kasa tace yahkri ranka ya dade, salma ta kalleshi ranta in yayi dubu ya b'aci ta koma falo ta zauna a kujera batare datace komai ba.

Salman harya gama sannan, ya mike tare da kallanta dasauri hanne takarasa gunta tace ki taso, salma ta d'ago ganin salman na kalleta ta harareshi tare da d'auke kai, ya ce taso mana? Ta mike fuskarnan a hade suka fito a jere ya matso yace kin manta abinda nace miki ko? Karki bari wasu susan halin da muke ciki ta kalleshi tace kaikuma fa? Yace ni me? Tace shikenan.

Ya juya kai nan suka wuce bayi nata gaisuwa, salma na amsawa ya matso yace kidaina amsawa ki wuce kawai tace amm...yace bansan musu tad'an turo baki batarr datayI magana ba haka suka karasa bangaren hajiya karama tana zaune a kilisarta sun shiga sun gaisheta ta amsa tare da tambayar salma yazaman bakunta, daganan bata sake magana ba shima salman haka, nan suka taso sukai hanyar bangaren hajiya babba itama sun gaisa tad'an tambayi salma koda abinda takeso? Tace a'a nan ma taga sunyi shiru har suka taso, mamaki ya isheta haka ake rayuwa a gidan bad'an hirar rayuwa da shakuwa?


Sun isa bangaren fulani zasu shiha ishaq ya taho shida mannir tundaga nesa ishaq kebin salma da kallo har karkata kai yake, suna isowa kofa ya kura mata ido sam yamanta da salman, sai da mannir ya kula yadan tabashi sannan, itakam salma duk ta tsargu ganin irin kallan dayake mata, ishaq ya had'eyi yawo tare da cewa Ango kasha kanshi😁 salman yaI murmushi tare da cewa muje ciki ishaq ya kalli salma yace Amarya muje😁, takalleshi tareda yin murmushi ai jiyai kamar ya fad'I har salma ta shige ciki itada salman ishaq bai kula ba sai da mannir ya matso yace yaya me kake kitsimawa? Ishaq yace mannir waccen yarinyarce matar salman? Mannir yace eh mana dan ma baka ganta agun dinner ba🤔 ishaq yai ajiyar zuciya yace amma na cuci kaina ai dani ta dace gaskiya da sake😠.

Mannir yace sai hakuri dan tazama matar kanninka, haushi ya ishi ishaq yace bazan yarda ba kasan irin wannan matar nake dreaming arayuwata? Najib yace yaya mai kake shirin yi? Yace I have to think amma bazan bari ta kubcemin ba😕






ishaq😳




By Ayusher Mohd📚

ILJAM 8

🏵🏵🏵🏵🏵
            ILHAM😪
            🏵🏵🏵🏵🏵



8⃣
Haka umma tai ta masifa sai dai fatima ko ajikinta yazasuyi da ita? Ganin takicewa komai yasa umma da hadiza suka kara kufula hadiza ta matso tace amma bakida mutunci in mahaifiyarki ce zaki shareta fatima tace to mexance? Haushi yakama hadiza ta daga hannu zata mareta fatima ta rike hannun tace nizaki mara? Sannan tadan tureta kadan tsautsayi yasa ta fadi tadan bige ciki kan kace me tafara ihu tana rike ciki tsoro yakama fatima lokacin kuma mahmud yakaraso ganin wannan yanayi ga fatima a tsaye ko ta taimaka musu yasa yaji ba dadi dasauri ya dauketa suka koma mota yai asibitinsu da ita yana shiga ya cire coat dinshi yai labour room da ita batafi minti 30 ba ta haifi yarta mace mahmud yafito yana goge gumin dake fuskarsa



Nurses ne suka gyarata sannan suka turo gadonta sukai daki da ita umma takalluli mahmud tace sannu dan nan Ramatu datana duniya bansan wani irin farin ciki zatai ba yace umma kije gun hadiza tace to


Gida ya wuce yana shiga yaga fatima a falo tana waya dagaji da Mamanta take waya yaji tana cewa yanzu yaushe zaku koma lagos din? Baisan me akaceba yaji tace saura 1 month 😳? Dan Allah ku kara wata daya kafin ku tafi dan lokacin ne edd dina mahmud yakarasa ciki ganin yanda take murmushi yasan abin farin ciki aka fada mata daki ya wuce ya cire kaya ya shiga wanka yana fitowa yaganta a bakin kofar toilet tace sannu doctor ya jikin hadizan? Yace ta sauka tace Alhamdulila inanan ina tunani yace dakin damu ai ba a haka yakamata inganki ba tace mekake nufi? Yace yarinyarnan a gabanki ta fara nakuda amma ko kitaimaka musu tai shiru jikinta yafara rawa can tace doctor kaima kasan da dalili hk kawai bazanyi hk ba jawo hannunshi tai tazaunar dashi akan gado tafara shafa mai mai daga nan kuma ya huce..... nan ta sanar da shi mahaifinta zasu koma lagos yace meyasa? Tace nadaiji umma tace uban gidansa ne dake can yace ya koma dan ya dinga taimaka mai mahmud yace to Allah ya taimaka


Sai magrib  su umma suka dawo lokacin fatima tasa ansiyo mata kaji tayi farfesu ta dau kular tai cikin gida a falo taga Ashiru tace ina wuni ya mike da sauri yace fatima kawo in daukar miki tace me? Yace kular ta kalleshi kawai ta cigaba da tafiyarta ga mamakinta taji an riko mayafinta tana juyowa taji Ashiru yace ciki ne dake😠? Tace eh bacin ran nameye ran Ashiru yakara bacci yace amma fatima kinci amanata yai waje fuuu kallo tabishi dashi me wannan mutumin yake nufi? Ganin batada lokacin wannan shirman yasa tai cikin dakin azaune taga umma da zulaiha sai hadiza dake kwance ita da baby khalil na kusa da babyn yana mata wasa fatima ta karasa da sallama suka amsa amma kowa ya juya mata fuska tace sannu hadiza Allah yaraya mana hadiza tace Amin inma ba har zuciyarki kika fada ba tace hmmm


Sannan ta ajiye kular tace umma sannu naso binku asibiti sai dai ganin ba kowa a gidan yasa na hakura tace wannan kuma ke ya dama sai kije ki dauko mana katinki muje mu siyo kayan yara dan dama bamuyi siyaya ba fatima tace Ashirun bashida kudi ne? Hadiza tace kefa nakula yanzu bakida mutunci cemiki nai bashida kudi? Kawai dai shi kudinshi muna tarawa ne za'ayi abu dashi tace gaskiya ne ku tara naku ku karar dana wani umma tace nakula yau rashin mutunci kike ji tace bari inje in fadawa mahmud ke kika ture hadiza sai muga ko ba abinda zai ce ko kuma mu shiga mudauki abubuwa masu tsada mu siyar fatima tace hmm zulaiha muje ki anso ta juya ta fita ranta a bace



Anyi suna sai dai fatima bataji dadin sunan ba dan duk kawayen hadiza da zulaiha ne yan duniya sai yada mata magana suke dan dama tuni umma ta daina neman yan uwanta na makarfi ko zuwa sukai korarsu take tun bayan mutuwar mai unguwa mahaifinta, taro ya tashi yarinya taci sunan mahaifiyar Ashiru Amina sai suke cemata Meenal



Wata 2 da haihuwar hadiza itama fatima ta haifi yarta mace farin ciki agun mahmud da fatima ba'a cewa komai har fatima tafara tunanin mahmud yafita farin ciki shine ta tsokaneshi tace dama namiji nahaifa wanda zai gajeka ya xama likita yai murmushi yace ai wani sa'in mace tafi dadi ta gaji mutum bare irin aikina da muke neman mata masu ilimin sai dai karki sa rai in 'yata tace batasan tazama likita bamai takura mata sukai murmushi



Ana gobe suna fatima tai ta damun mahmud yafada mata sunan dayama yarinyar huduba dashi amma yaki fada hkn yasa tafara tunanin Ramatu yasa sunan mahaifiyarsa aikuwa ran suna ga mamakinta taji wai sunan yarinya Fatima dasauri tadaga waya ta kira mahmud tace doctor yace hmm kinji dadi ko? To nafiki jin dadi dan inaso inga nasawa 'yata sunanki tace nagode doctor nan tace sai mudinga cemata ilham gudun karkasa mu rasa wa kake kira inkace fatima nan yai murmushi sukai sallama



Suna kam ansha shi dan mahmud ya barar da kudi hk yan uwan mahaifinshi da mahaaifiyarshi sunzo daga makarfi sai dai fatima ce kawai ta karbesu su umma kam kamar su koresu suke ji




By Ayusher Mohd📚

ILHAM 7

🏵🏵🏵🏵🏵
             ILHAM😪
           🏵🏵🏵🏵🏵



Na Ayusher Mohd✍🏼

7⃣

yanzu cikin hadiza yakai wata 3 sai wani salo datake tsira agidan komai tace bataso bata tashi yin salon sai fatima nanan, yau fatima tare suka fita da mahmud yakaita shopping tunda suka fita takejin ba dadi jikinta kwanakin nan haka takeji bayan sun sauka daga mota mahmud ya anshi ledojin yace fatima naga tunda muka fita kamar bakyajin dadi muje ciki in dubaki tai murmushi tare da ansar leda daya tace ba waninan ni lafiyata kalau dama so nake ka daukan min ledojin kaga sai in rike daya karkace nayi sankai yace hmm fatima nasanki fa mudai je indubaki dan na kula sam bakyasan kiganni cikin damuwa shiyasa duk sanda kike ciwo sai dai inya cikine kike nunawa to nima yanzu nagane dan hk daga yanzu nizan dinga kula dake tace da aiki zakaji ko da kula dani doctor?  Zaiyi magana sai ga zulaiha tashigo tace yaya ina wuni yace ina kika je? Tace Bashir ne yasaukeni munje gaida iyayensa ne yace auho ai gwara dai ayi auren nan kar lokaci ya kure ta karasa tace Aunty fati ina wuni? Fatima ta amsa ba yabo ba falasa zulaiha tasa hannu ta karbi ledojin tace yaya bari inshiga dasu yace to fatima ta kaudakai aranta tana mamakin kinibibin mutanen nan


Suna shiga gida sukaga umma da hadiza zaune a dan tsakar gidansu sunashan farfesun kayan ciki umma tana ganinsu ta mike lale maraba da dan albarka yace umma ya gida? Tace lafiya lau zo ka zauna a zuboma farfesu yace to tare da kallen fatima umma tace fatima taho mana sai kace wata bakuwa kefa dama bakida saurin sabo fatima ta kalleta sannan tai wani murmushi😏 tace banajin ci ne umma dakafin kifada ma xan zauna inci hadiza tace yaya yau tunda natashi naji farfesu nakesan ci kasan yanayin yace hmm balaifi sannan yace muje ciki tare da kallan fatima haushi yakama umma ta riko hannun fati tare da cewa nikam mahmud banajin dadi muna tare amma baxamu dinga komai tareba? Fatima ta raba girki yanzu kuma batacin abincinmu kaima ta hanaka? Yace ah hb umma ba hk bane fatima dake tsaye jiri kawai ke dibanta ta zare hannunta daga gun umma batare datayi maganaba tafara tafiya tana tangadi mahmud yatsaya basu hkri yaji fatima ta zube a kasa dasauri yakarasa yana jijigata duk ya rude lokacin kuma ashiru yashigo ganin fatima shima ya karasa gun dasauri yana jijigata ga mamakin mahmud yaga ashiru kwalla ta zubomai amma tunda bashida lokacin tambayarshi kawai yasuri fatima sai part dinsu su umma kuwa dan munafirci  harda hawaye yana isa ya shiga dubata sai dai tsananin mamakin abinda yake gani yasa shi yin shiru dasauri yadaga wayarsa yaduba kwanan wata yakamata fatima tai aladarta kwana 14 da suka wuce amma gudin kar zumudi yasa ya yanke hukunci yasa yadan sa hannunsa ya danna kasan cikinta ahankali tace doctor zafi  yace fatima zaki iya zuwa toilet? Tace sai dai ka rikeni amma mexanyi acan yace mudai je haka sukaje yamiko mata roba tai fitsari batai musu batai dan so take kawai takoma ta kwanta yana kwantar da ita yace fatima bari inje asibiti indawo tace da yamman nan?yace asibitin mu zani kinga ai kusa yake tunda bayan layi ne yanzu zandawo tace to sannan ya fita



Su umma ya gani a bakin kofarsu dukansu har khalil a ashiru wai so suke suji ya jikin fatima yace dasauki magani zan samo mata sukace to sannan umma tace zulaiha jeki zauna agunta ko zata nemi wani abun yace yauwa umma nagode sannan yai waje



Direct yai asibiti yashiga yin gwaji lalai abinda yake zargine fatima cikine da ita wani mugun farin ciki ne ya rufeshi haka ya fito duk wanda yagani a asibitin sai ya bashi kudi daya iso gida kuwa yai sa'a bakowa direct part dinsu yai yana isa yaga fatima ita kadai dan dama karyar umma ne ba wata zulaiha data shiga shikam yama manta fatima kawai yaje ya daga sama yana juyata tace doctor lafiya? Yace kaaii wannan matar tawa sai ahankali tayi batan wata amma bata sani ba? Tace batan wata? Yace ba tsakiyar wata kike period ba tace eh amma ninaga baizo ba kasan wani sa'in yana juyawa ya sauketa tare a dungure mata kai yace oh ace mutum yanada juna 2 amma bai sani ba? Tace me😳 ? Yace yes tare da manna mata kiss yace munkusa yin baby fatima Allah ya anshi addu'ar mu ai tashi tai ta daka tsalle dasauri ya rungumeta yace fatima rufamin asiri tai murmushi ya rike hannunta tare da zaunar da ita yasa hannunshi a kan cikinta yace fatima bansan wani irin farin ciki nake ciki ba tace doctor inrokeka wani abu? Yace menene? Tace plz karka fadawa kowa xancen cikin nan yace ban ganeba? Tace kawai so nake abun yazama suprise kasan yafi dadi ya lakuci kumatunta yace wato daban sani ba nima suprise din za'amin? Tace ina na isa inyiwa doctor suprise yace shikenan amma adinga kulamin da baby ko insa zulaiha tadinga yin aikin part din mu? Tace a'a karka damu zan iya yace toh fatima na😘







Babu wanda yasan fatima nada ciki dan tarage shiga gunsu sai dai su in suna nemann kudi dan ba kunya suke cewa tabasu katinta bayan mahmud duk sati yake ajiye musu kudi shiyasa itama tai dabara ta bude sabon account sai take raba kudin 2


Cikin hadiza yana wata 9 ita kuma fatima wata 7 lokacin ne umma tafara zargin akwai wani abu ganin yanda fatima kullum cikin dogowar riga da hijab gashi bata fita waje kuma duk sanda suka shiga gidan tana zaune wannan yasa yau umma tashirya sai taga fatima


Fatima yau da ciwon baya ta tashi jin kwankwasa kofa yasa ta zira hijab ta bude tana budewa kawai taji anja hijab dinta cike da mamaki ta dago umma ce da hadiza suka yaye mata hijab tace umma sannu da zuwa ai umma tashiga salati lalai fatima ciki ne dake shine dan baki daukeni abakin komai ba kikaki fadamin ko? Wannan yarinya anyi mara mutunci nan suka cigaba da tijara fatima kam ko ajikinta dan bazata taba manta sanda tajisu suna cewa basaxu bari fatima tasamu ciki ba bare ma mahmud yasamu magaji




By Ayusher Mohd📚

ILHAM 6

🏵🏵🏵🏵🏵
             ILHAM😪
            🏵🏵🏵🏵🏵



Na Ayusher Mohd✍🏼



6⃣

Rashin haihuwar fatima yadameta duk gwajin da akai ance lafiyarta kalau ga kuma wani habaici dayan gida suka tsiri yi mata tana mamaki wannan alamari ita da gidan mijinta amma azo ana ci mata mutunci bayan ita bata taba gorantawa hadiza ba sanda akai auren hadiza mijinta ashiru ya ziga hadiza ta dinga kuka wai ita tafisan zama agidan tana tsoro tana marainiya mara uba tayi nesa da mahaifiyarta to dama ba hk sukabar mahmud ba fatima tayi tunanin zai hana amma ga mamakinta yace tazaune gida da mutane ai yafi dadi kuma Ashiru yadinga taimakamai gun kula da asibitinshi sai dai azahiri ashiruya ziga hadiza ne dan yadinga ganin fatima.



Wannan abun yabakanta mata rai yama za'ayi mahmud yamata haka? Datamai magana sai yace tayi hakuri shine ita bata musu gorin zama a gidan ba sai sune zasu mata gori?



Yau weekend kamar yanda fatima da mahmud suka saba suna dadewa suna bacci sai dai cikin baccinsu suka dingajin guda sai yi akeyi haushi yakama fatima tafito azuciye ta zira hijjab tai cikin gida hadiza tagani da zulaiha sunata guda gakuma hauwa da khalil tare da mahaifinsa azaune fatima cikin bacin rai takarasa tace haba umma yaza'ayi kina kallo sudinga yimana guda kamar gidan biki? Hadiza tayo kanta kewai meyasa bakida mutuncine in mahaifiyar mahmud ce zaki fadamata hk? Fatima tace in itace ai nasan kafin ta karasa hadiza tace oho dai koma meye muna cikin farin cikine kuma dole mu nunama makiya



Fatima tace abin farin ciki? Zulaiha tace hadiza ciki ne da ita dajin haka sai da gaban fatima ya fadi amma da yake tanada dauriya tace hb kai amma naji dadi Allah yaraba lafiya hadiza tace to amma dai yakamata yaya yasake aure dan zama da juya bashida amfani wannan kalma taba  fatima haushi hakama ashiru azuciye yace hadiza meye hakan? Umma tace barta ai gaskiya tafada ashiru yai waje a zuciye dan bakin cikinshi yaji anayiwa fatima haka mahmud kam ganin fatima bata dawo ba yasa ya fito dan ya duba



Sunajin motsinshi umma ta wayance fatima kinga jiya dana fita naga wasu mayafai masu masifar kyau shiyasa na daukar miki ta mika mata mayafi fatima ta tsaya tana kallanta tace umma meye kuma hakan? Mahmud ya karaso tare da rike hannun fatima yace haba fatima ba asan adinga maida hannun kyauta baya jin muryar mahmud yasa ta juyo sannan takalli umma tai murmushi sai yanzu ta fahimceta wato sunji mahmud zasu raina mata hankali ta ansa tare da sakala hannunta jikin mahmud tace nima gani nai anbani nikadai umma batasaiwa su hadiza ba ☹ yai murmushi sannan yace kyallesu ita ai umman tasan zaifi miki kyau shiyasa umma tace ah to wake ta wadannan yaran? Hadiza da zulaiha sukai shiru fatima takalli umma sannann ta maida kallanta gun mahmud tace doctor khalil fa yakusa yai kani ko kanwa? Cike da murna mahmud yamusu Allah yasanya alkairi sukai part dinsu



Suna shiga fatima tace doctor nikam ina tsoro? Yace name? Tace kar inje nice bana....dasauri yarufe mata baki sannan ya rungumeta yace fatima inaji ajikina rabon mu yakusa zuwa dan hk mu roki Allah amma kidaina fadar haka kara kankameshi tai tana hawaye.


Hadiza kuwa suna shiga daki taja tsaki sannan tace umma yama za'ayi ki bada mayafina tace dallacan daya gane ya koremu fa wake ta wanu banzan mayafi kina ganin nikaina in na fita bina ake da kallo dan ansan nafito daga gidan manya muje muyiwa kanmu saki na dafe? Wayasan yaran nan gaba mezai zama? Gwara mu kwashi rabonmu in bai haihu ba mu kwashe dukiyar suka tafa nace Allah yashirya ni Aysha




By Ayusher Mohd📚

ILHAM 5

🏵🏵🏵🏵🏵
            ILHAM😪
           🏵🏵🏵🏵🏵




Na Ayusher Mohd✍🏼

5⃣

Sanda akai rabon gado gidan saleh yakasance na mahmud sai dai hauwa ta fito da wani salo agaban mutane tai ta kuka wai yama za'ayi tabar gidan bayan ga danta aciki? In ta tafi wazai dinga kula dashi wannan dalilin yasa mutane sukai ta jinjinawa kokarinta mahmud ma yace ba matsala, haka mahaifinta ma ya aminta da zabinta sai dai yace mata inhar mahmud yai aure tofa dole ta dawo gida da wannan shawara hauwa tacigaba da zama a gidan



Lokacin da mahmud yasamu aiki da taimakon mahaifin fatima zo kaga murna agun hauwa mutane kam suna yaba mata sai dai acikin zuciyarta bakin ciki ne fall gashi mahmud dole zai bar gidan yakoma kaduna wannan dalili yasa tai gun malami akan arufe bakin mahmud yakasa cewa badasu zai koma kaduna ba.


Lokacin da mahmud yafara aiki jeka ka dawo yakeyi haryai wata 6 ganin anasamun alheri sosai yasa yakama gida dan yanaso ya auri fatima sukoma can da zama, gidan falo daya ne sai dakuna guda 3 ko wannne da toilet dinsa bai fadawa kowa ya kama gida ba sai fatima itakam murna agunta kamar me ba dadewa akasanya rana tunda yan uwan mahaifinshi sunanan wata 2 akasa lokacin ne kuma ya sanar da hauwa tsarin dayai zai barsu anan acikin gidanshi su cigaba da zama shikuma zai koma cikin garin kaduna ran hauwa yabaci dan gaskiya bazata yarda yabarta anan ba hakan na nufin bazatasan meyake samu ba ita kuma tafisan komai ai da ita sai dai alokacin tacemai ba komai dan tagane aikin malamin nan bai ci ba



Bayan auren mahmud da fatima suka koma kaduna lokacin kuma abubuwan alheri sukai ta faruwa mahmud tsantsan gwazanshi yasa wani babban likita dake da asibiti private yanemi yadinga zuwa suna aiki tare lokacin dayake free sannan fatima mahaifinta yabata jari tafara business wannan yasa kudi yafara shigo kusu sosai har fatima taba mahmud shawarar yasai fili


Hauwa kam sai shiga malamai take akan ajuyo da hankalin mahmud yaji dole sai ya zauna dasu harta samu nasara wata rana mahmud yana tashi daga bacci yaji duk duniya babu wani buri dayake dashi daya wuce yazauna dasu hauwa hakan yasa yafadawa fatima itakam bataso ba tace doctor duk abinda kake fadamin suna maka yau da kanka kakeso kuzauna tare? Yace fatima wannan ai duk ya wuce nidai ki amincemin itakam batasan hakan sai dai bayadda zatai tunda abinda mijinta yakeso ne tace shikenan doctor amma yazamu zauna ku 6 a wannan gidan?yace karki damu kafin muyi gidan kanmu ne sai su hadiza da zulaiha su zauna a daki daya ummansu ma haka muma daki daya tace hmm shikenan ga mamakinta alokacin yashirya wai makarfi zaije



Ai sanda yasanar da hauwa wannan shawara farin ciki ya cikata tace to tunda kaga hakan ne yadace sai muje din dama mai unguwa yace inkoma gida yace a'a zan mai magana tace to su hadiza murna kamar me dama suma so suke su koma kaduna a fasa dasu dan yanzu mahmud yasai mota honda


Wannan shine mafarin dawowarsu hadiza gidan basu nuna komai ba dan fatima ma najin dadin zama dasu sau tari hadiza na taimaka mata ta hanyar kasuwanci dama aikin gida sun dauke mata


Shekarar auren Mahmud 5 kenan sai dai haryau Allah bai basu haihuwa ba sai dai yanzun arzikin mahmud ya bunkasa dan yanzu har asibintin kanshi ne dashi kuma sun hada gwiwa da fatima suka bude shago suka zuba kaya Alhamdulila kudi kam Allah yabasu sai dai yanzu su hadiza ta aure wani abokin mahmud ashiru da suke aiki guri daya sai dai ashiru nurse ne ba likita bane sanda yaga hadiza yazo lokacin yazo tarun bude asibitin mahmud ne



Hadiza ce tace tana sanshi danshikam ganin matar mahmud yasa yaji duk duniya ba wacce yakeso irinta auren ma ya amincene ko zai dinga ganinta yanzu hadiza danta daya khalil dan Shekara 3

Rayuwar gidan tafarawa fatima zafi dan in mahmud bayannan hadiza da hauwa basa raga mata haka zasuzo suce sai ta basu kudi intaki suce zasu dau kayanta su siyar gashi kallan da Ashiru yake mata ya fara isarta wannan dalilin yasa bata shiga part dinsu sosai a part dinta take girki da mahmud yatambayeta tace kawai sunga yafi saukine ganin har part dinta suke biyota yasa ta fara zama a shagonta gun kanin mamanta dake rike da shagon.




By Ayusher Mohd📚

ILHAM 4

🏵🏵🏵🏵🏵
            ILHAM😪
         🏵🏵🏵🏵🏵


Na Ayusher Mohd✍🏼

4⃣
Haka mahmud yatafi makarantar Abu cike da farin ciki gashi course din dayakeso yasamu wato Medicine mahmud yafara karatu a sa'a bayan wata 1 yake zuwa ganin gida

Yauma kamar yadda yasaba yazo hutu makarfi, yazo wucewa ta gidan chairman yaga yarinyar nan tadawo daga makarantar islamiya sanye da uniform brown da dogon hijab duk da bamai san magana bane ganin bataganshi ba yasa yace kee parrot ta fara waige kozataga parrot din yace ke dake nake tace nice partot😳?yace eh mana yau yan maganar basa nan takaraso kusa dashi tace laa ashe kaine kasan da bangane ba yace hmm lalai tace amma ni mutum ce mai ya hadani da aku? Yace inye lalai nayarda kan nan yana jaa tace hmm daga ina kake naganka da jaka? yace daga makaranta nake tace wacce? Yace zariya tace uhm wai a garin nan kake naga bana ganinka yace to da cemiki akai sai kinga kowa a garin ko garin karami ne?


Tace hm amma ai natambayi Abba yacemin gidan malam saleh ne  gidanku kuma rannan naje akace bakanan mahmud yasa dariya yace nikikaje nema? Tace uhm rannan zaiyi magana wata mata ta fito daga gani mai aikinsu ce ta fito nemanta dasauri tace natafi kar aga na dade ta juya tai gun matar ya juya yana murmushi tun sanda yafara ganinta yake yawan tunaninta yarinyar tana burgeshi


Bayan ya karasa gida yataradda abin bakin ciki mahaifiyarshi yagani tana kuka akofar dakinta yakarasa gunta yace umma meya faru bai rufe baki ba yaji an jikesu da ruwa cike da mamaki ya mike? Yace lafiya? Meye hakan? Hauwa ta cigaba da bala'i ni wato anhana 'yayana cigaba da karatu ke sarauniya danki na makaranta amma ko kunya bakiji ba zakicewa saleh wai yama su hadiza fada akan zancen da suke😠ke zaki aurar mun  dasu in basuyi zance ba shi kuma harzaizo ya rufemin 'ya'ya da fada to wlh kunyi kadan dukanku mahmud da ranshi yagama bacci yace amma ai kome tayi hakkin tane tunda 'yayan mijinta ne dasauri Ramatu tajashi sukai daki ta rufo kafar haka hauwa tai ta masifa

Mahmud kam bayasan zaman gidan hakan yasa washegari yakoma dama sunkusa fara jarabawa yafito babanshi yacemai chairman na nemanshi hakan yasa ya wuce gidan a tsakar gida yaga fatima zaune a kujerun rubar da aka ajiye a gun rike da waya a hannunta karasawa yai dauke da murmushi a fuskarsa harya karasa batasan ya iso ba ya leka wayar yaga game take yace parrot nan kika gudu da sauri ta mike tace laaa yaushe kazo?; yace yanzu tace yaya mahmud makaranta zaka koma nakara ganinka da jaka? Yace ya akai kikasan sunana? Tace dadyna na tambaya yace hmm

Haka shakuwa mai karfi ta shiga tsakanin mahmud da fatima dan duk sanda yadawo hutu sai sun hadu harya fahimci santa yakeyi har mahaifansu sun sani

Alhamdulila karatun mahmud yazo karshe kuma tunda yashiga first class yake fita dashi lokacin daya zana jarabawar karshenshi fatima tagama secondary ta zama yan mata lokacin kuma mahaifinta bayakan kujerar chairman yabar siyasa sai dai yakoma kasuwanci kuma Allah ya budamai sosai

Yau ake ceremony na gama makarantar su mahmud a makaranta fatima da dadynta sun taho saleh ma yadauko Ramatu a yar karamar motarsu civic sunzo zariya cikin tsautsayi wata mita tashigo basu sani ba tai gaba dasu agun kafin akarasa asibiti Allah yadauki ransu wannan rana maimakon ranar farin ciki takoma ranar bakin ciki kuka kam yashashi haka yazama marayan sai dai cikin ikon Allah jarabawar su tana fitowa yasamu aiki a asibitin cikin garin kaduna




By Ayusher Mohd📚




By Ayusher Mohd📚

ILHAM 3

🏵🏵🏵🏵🏵
            ILHAM😪
        🏵🏵🏵🏵🏵



3⃣

Bayan ta shirta ne takalli mahmud tace doctor akwai abinda kakeso ne? Yamata nuni da littafinshi ba musu tadauko ta mikamai da biro dan tasan magana yakesan yi hk ya ansa ya fara rubutu sannan ya miko mata
"Fatima yazanyi da rayuwata? Bana zaluntarki kuwa? Inaji ajikina kamar bana kyautawa"bayan tagama karantawa ta karaso kusa dashi ta zauna tare da rike hannunsa tace doctor plz kadaina irin wannan maganar kamanta so ne yasa na aureka?

Ya girgiza kai alamar bai mantaba tace toka gani plz doctor kadaina irin wannan zancen fatana kamin addu'a ya daga kai hawaye ne yazubo mai ta mike tace doctor mace kakesan zama?ina jarumtarka take? Asanina ban taba ganinka kana kuka ba amma yanxu abu kadan ne kesaka kuka? Nikuma kukan nan yafi komai bakantamin dan hakan na nunamin har cikin zuciyarka ka karaya tana gama fadar haka tadau ilham tai falo ta rungume ilham ta zube akasa tana kuka tace doctor plz be strong in kana hk ban san ni kuma yazanyi ba.....


 Mahmud Saleh shine sunan mahaifin ilham sunan mahaifinshi Saleh wanda yake malami na almajirai dake makarfi a garin kaduna saleh nada mata 2 Ramatu wacce take uwar gida sai Hauwa dake amarya, saleh ya aure Ramatu tun saurayi da budurwa soyayya ta hadasu har sukai aure bayan aurensu da shekara 1 ta haifi danta akasamai Mahmud bayan haihuwar Ramatu mai unguwarsu yabashi auren yarsa Hauwa duk da bayaso bayadda zaiyi hk ya aure hauwa


Tunda Ramatu ta haifi mahmud Allah bai kara bata haihuwa ba sai dai hauwa data haifi hadiza daga baya ta kara haifar mace zulaiha

Sam hadiza batasan Ramla da mahmud dan tana bakin cikin ita batada namiji gashi malam saleh kullum suna tare da mahmud har ya isa zuwa makaranta yasashi a makarantar primary mahmud nada baiwa dan indai yakaranta abu sau daya to yazauna a kwakwalwarshi hakan yasa shugaban makarantarsu ke sanshi dakuma alfahari dashi malamaibma kiranshi genius suke


Bayan mahmud yagama primary makarantar ya shiga secondary lokacin ne hankali yazomai kuma yakara gane baiwar da Allah yamai mahmud bashida magana gashi hakan yasa duk wata bakar magana da hauwa zata fada baya kulata.


Lokacin daya gama secondary chairman din garin dakanshi yace yadau nauyin karatun mahmud dan duk garin bawanda yakaishi cin jarabawa dankuwa sai da akai bincike ko satar ansa yayi


Chairman yaneman mai Abu zaria wannan alamari yayiwa saleh dadi farinciki agunsa da Ramatu ba'a magana haka mahmud ya hada kayanshi yaje gidan chairman dan tare zasu tafi lokacin dayaje akace yajirashi a falo yana wanka yana zaune wata kyakyawar yarinya tashigo sanye da uniform din makaranta ta kalleshi tace ina wuni yace ina gajiya tace wakake jira? Yace anan gidan kike?tace ai ni nafara tambayarka😗 yai murmushi yace chairman nake nema tace to yace nibaki ban amsata ba tace eh sunana fatima yace nice name tai murmushi yace amma ba lokacin tashi bane ya akai kika dawo gida? Tace laa🙊 namanta kagan ni da shirme malamin mu nefa yabani ajiya books dinsa namanta dashi akaban pass inje indauko natsaya surutu yai murmushi yace aji nawa kike? Tace jss 2 yace hmm yanzu kuma me kikeyi dabaki je kin dauko ba tace ahh tare dadan dungure kanta kai nima sokuwa ce ko? Yace nibance ba tace hmm wayasan mekace aranka yace to yaushe zakije ki dauko books din ai da gudu tai ciki yasa dariya yace she is cute


Jiyai an bude kofa dasauri yadaga kai chairman ne ya fito rike da yarinyar dazu yace mahmud mutafi ko? Yace ina kwana yace lfy lau sannan yakalli yar tasa yace fatima ba gaisuwa?; tace mun gaisa dady yace wai haka tare da kallan mahmud yai murmushi yace mun gaisa tace Abba natafi yace to sai kin dawo ta kalli mahmud tace sai anjima yace to



By Ayusher Mohd📚

ILHAM 2

🏵🏵🏵🏵🏵
        ILHAM😪
        🏵🏵🏵🏵🏵

Na Ayusher Mohd✍🏼


2⃣
Tana isa taga ya fado kasa takarasa da sauri takarasa tafara kokarin dagashi dakyar ta samu tamaidashi sai numfashi take alamar wahala tace nadauka kayi bacci doctor ya kalleta yamata alama da hannu waye? Tace bafa kuwa umma ce taxo taji ya jikinka yake ya kalleta alamar ina? Baxai yiwu ba tace kwanta nima wanka zanyi inzo inkwanta yadaga mata kai tayi hanyar toilet ilham tasa kuka ta juyo ta karasa gunta tashiga jijigata ganin kamar yunwa takeji ta fara shayar da ita mahmud kurii yai da ido yana kallanta yana tuno tsantsan soyayyar dasuka nunawa juna ya lumshe ido kamar yana bacci ita kam fatima ganin ilham takoma bacci yasa ta kwantar da ita tai toilet.....



Washe gari da sassafe ta tashi tai cikin gida tafara girki dan wannan aikintane inji umma daga sanda mahmud yakwanta ciwo tace girkin gidan yatashi daga gun matsu aiki ya koma kanta haka take aikin ilham nabayanta sai data gama komai ta jera a dinning sannan hadiza tafito rike da yarta  a hannu taba ilham wata 2 tayiwa fatima wani mugun kallo sannan tace umma tace kije inkin gama aikin ko kulata fatima batai ba haushi yakama hadiza tai cikin daki

  fatima ta rike kugunta jin bayanta ya amsa sannan takalli agoggo karfe 8:00 tasan lokacin tashin mahmud yayi gashi umma nakiranta hk tayi part din umma jiki a sanyaye


Tana shiga tatarad da umma a kishingide takarasa tace umma ina kwana ta kalleta a wulakance tace dan iskanci kwashe kudin account dinki kikai? Tace umma ban gane ba umma tace zan haska miki mari wato kina bakin ciki dan hadiza na amfani da kudin ko? Kudinkine ? Ko guminki ne? Fatima tace a'a amma ni umma inama nake zuwa bare in cire kudi tace to kina nufin hadiza ce ta cinye?tace banceba umma tace to kisan yadda zakiyi mahmud yatura miki kudi ko kuma in saki kisaida filin dayasai miki fatima tace umma😳 ai kamar jira take tahauta da fada fatima kuwa ko gezau batai ba tana gamaji tamike batare datace komai ba tana fita tasauke ilham ta rungumeta tace ilham yazanyi?itakam ilham batasan ma me ake ba sai murmushi take



Tayi part dinsu taji anrikota ta juyo ciki da mamaki Ashiru tagani dasauri ta kwace hannunta tace malam meye hakan? Ashiru yace fatima dakin yarda dani da duk wannan abun bazai faru ba ta kaleshi shekeke tace ko😏? Yace Allah fatima ni nasan meyakamata tace Ashiru kasan Allah idan baka fita daga idona ba xakasha mamaki ta wuce tai part dinsu tana isa tai gun mahmud idanshi 2 yasa laptop agaba yana abu dasauri ta ajiye ilham tai kusa dashi tace doctor am sorry ya girgiza mata kai alamar ba komai ta dauko kujerar guragunsa tasashi sannan ta turashi toilet har wanka ta taimakamai yai sannan tadawo tadau ilham itama tamata

Saii datagama shiryasu sannan tai cikin gida dan dole sai sun gama break fast zatazo tadau ragowar gashidai mijinta ne mai kudin gidan da kudinshi ake komai amma bayadda xatai 😪

Wannan rayuwa tana bata wahala sai dai fatanta Allah yashige mata gaba hk tadau abincin takaima mahmud yagama ci sannan taci tai wanka
  Wannan kenan.....




By Ayusher Mohd📚

ILHAM 1

🏵🏵🏵🏵🏵
        ILHAM😪
           🏵🏵🏵🏵🏵


"Dasunan Allah mai Rahama mai jin kai....Dafatan kowa yayi sallah lfy Allah ubangiji yamaimaita mana Ameen"


1⃣

   Zaune take a kasa takurawa yarta yar wata 6 ido dake bacci yarinya kyakyawar gaske ta ce aranta ilham yazanyi? idanta ya ciko da kwalla, sannan tajuya takalli falonta kaya more rayuwa dai acikin falon ba'a magana sai dai babu abinda ke birgeta yanzu lafiyar mijinta ya fiye mata duk wadannan  daga cikin daki taji kararrawar dasauri ta mike dan tasan mijintane ke magana takarasa dakin dasauri tana isa taje kusa dashi tace Doctor ya akai?

 Yamata alama da hannu ta taimakamai zaiyi fitsari dasauri ta miki ta taimaka mai sannan tace sai me? Yamata alama da ruwa ta tsiyayomai a cup sannan tace kasha maganinka kawai sai ka kwanta gaba daya yamata alama da kai yana mata murmushi ta miko mai magani ya yasha tashafa fuskarshi tace yauwa Doctor na dama ku likitoci in baku sha magani ba waye zaisha ya riko hannunta tare da sumbata tadan sunkuyo tare da rungumeshi  kwankwasa kofa taji anyi  ta kalleshi tace doctor bari in duba ingani ya daga mata kai ta juya tana murmushi  tai kofar falon tace waye taji ba'ai magana ba sai tai tunanin ko matar baban mahmud ce dasauri ta bude gudun laifi da mamaki taga Ashiru mijin hadiza kanwar mahmud ta uba tadaure tace mekazo yi? Yace fatima plz kitsaya muyi magana tace wai Ashiru meke damunka ne? Yace kezancewa meke damunki mezakiyi danamiji dayanzu ya nakasa? Tace Allah ne ya jarrabceshi kuma shi zai yaye mai yace fatima wlh ninasan yanda nake sanki mahmud baya miki wannan soyayyar



 Cike da mamaki ta kalleshi tace Ashiru kanada hankali kuwa? Da aurena kazo kanamin wannan maganar? Yace nima ai da aurena kuma mijinki shiba kafa ba ba baki ba mezakiyi dashi? Ran Fatima ya baci tace nikuma ahaka nake sanshi ba yace ke dutse ce? Yaza'ayi kice ba kya sha'awa.....marin data tsinkamai ne yasashi rike kumatsunsa tace wlh kabala'in shiga hankalinka kuma wannan yazama rana takarshe dazaka kara zuwa kamin zance banza kuma karka kuskura kakara cin mutuncin mijina


Jitai ance awani mijin naki? Dasauri suka juya hadiza ce kanwar mahmud takaraso rike da hannun danta khalil dan shekara 4 tace Abban Khalil me kakeyi anan? Ya fara inda inda yace dama zuwa nai inji ya jikin mahmud tace saka nai? Ko cewa akai munada hadi dashi? Yace ba hk bane kema kinsan bai dameni ba kawai...jisukai fatima ta banko kofa da karfin tsiya hkn yasa suka tsorata khalil kuwa yasa kuka ran hadiza yabaci aikuwa tai gun mahaifiyarta tana munafikin kuka



Fatima kuwa tana shiga tadau ilham tai cikin daki da ita ta tadda mahmud a jingine yana hawayen bakin ciki dasauri takarasa tace menene doctor? Yasa hannu yagoge hawayen ya girgiza kai alamar bakomai ta sukunyo ta rungumeshi tana hawaye tace Allah yabaka lafiya doctor yadaga mata kai jitai ana kwankwasa kofa again aranta tace sai kuyi tayi jin yanda ake buga kofar yayi yawa yasa ta taho da niyar yimusu rashin mutunci sai dai tana bude kofar taga umma mahaifiyar hadiza kafin tai magana umma ta wanka mata mari sau 3 a jere tace wlh ba'a hallici dan dazai dakarmin 'ya ba fatima tace ni?😳 hadiza tace duka nawa kikamin dazu fatima tai kasa dakai tace yahkuri umma tace jeki daukon ATM dinki fatima tace umma kudin ciki duk kin karar..wani  marin takara sauke mata tace kin wuce ko kuwa? Tai cikin gida abin tausayi tadauko tamika kata suka juya suna yar mita😏 a bakin kofa fatima tazube tana hawaye wannan wacce irin rayuwa ce? Ko mijin zata dauke su gudu da yarta? To tayyaya zata dauki namijin dabashida kafa baya magana jin kararrawar da ake dannawa tayi yawa yasa ta tashi dasauri tai gun mahmud😕



By Ayusher Mohd📚

NI DA PRINCE 17

☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄




*NA AYUSHER MOHD*



NO.1⃣7⃣

Salman yana fita mota ya fad'a yai hanyar Buk, tafiya yake amma ransa duk a b'ace, inda najib yake ya nufa, a kusa da makarantar Buk yake da zama, najib bad'an kano bane daga bauchi yake,  karatune yakawoshi nan.

Salman yai parking din mota ya fito ya nufi d'akin najib, knocking yai najib dake zaune yana kallo yataso ya budemai, cike da mamaki yake kallan salman sai dai kafin ya firta wata kalma salman ya ture hannunsa dake jikin kofa ya wuce cikin d'akin, najib yakalleshi yace Ango? Ya haka? Salman ya fad'a gado tare da d'aukar remote yace waye angon? Najib ya rufe kofar tare da karasowa yace salman bai kamatafa aganka a wajeba yau🤔salman yace tunda kaine ubana ba? Najib yace Allah yabaka hakuri dagaji ranka a b'ace yake, salman yai tsaki tare da canza tasha yace nifa banajin zan iya sati 1 da waccen 'yar rainin hankalin a d'aki d'aya😏 najib yace haba salman meyasa kake hakane? Kasani sarai su ishaq dasaninsu suka tinguno zancen auren nan, plz ka jure mubasu kunya.

Salman yace yarinyarce kanta na rawa tagama rainani, sai kace ni din sa'an tane😠.

Najib yace salman yarinyar nan fa batada laifi ina ganin yanda kake mata, ni naji dad.....salman yakatseshi yace kasan wacece ma wai? Najib yace naji dai Amir yace 'yar skul din mu ce, salman yace kyale banza shi baisan me ake ciki ba sai yaje yana yad'a maganarsu mannir, wannan 'yar rainin hankalin nan cefa mai *Ninja*😏najib yace ninja? Salman yace  kaifa banza ne ninja mana basune suke rufe fuskarsu da wani bakin kyalleba? Najib ya kwashe da dariya yace amma prince sai a hankali nikaf din ne ninja? Yace to yarinyar cefa? Najib yace badai wacce nakusan bigewa ina koyon nan ba? Salman ya juya kai yakalli gefe sannan ya ceji baki yace ita fa, najib yace ita😳? To dama ka santa ne? Salman yace dalla malam inazansan wannan kucakar?nifa an cucenI wlh, najib yace amma ta hadu akwai kyau😁.

Ran salman ya b'aci yad'au pillow ya makamai yace cemaka akai kyai shine komai?nan dai sukaita musunsu nikam naja jiki nabar gun😒.


Salma kam ta dade kafin tadawo normal nan ta gyara d'akin dan taga falon har an gyara kafin su fito ankuma sa turaren wuta, bayan tagamane 'yan uwa sukaita zuwa yi mata sallama sai azahar tasamu nutsuwa tai alwala tai sallah, so take ta zaga taga gidan sai dai kunyar hakan takeyi, hakan yasa kawai tazauna a d'aki ganin qur'anI yasa tad'auka tafara karantawa, jitai cikinta na kara tasanI yunwace amma fitina irinta salma taki fita taci.


sai karfe 2;30 hanne ta kwankwasa salma ta bude, tace ranki ya dade ankawo abincin rana tace to tare da mikewa nan tazauna a dinning ganin abinci kala_kala yasa tace hanne abincin ai yai yawa🤔 hanne tacs haka ake kawowa sai dai inkungama sai akwashe, salma ta girgiza kai tace oh nan tafara cin abinci, taci sosai sannan tasha lemo ta koma d'aki.



Hartai isha'I salman bai dawoba hakan yasa ta kwanta a gado ta shige bargo, dan sanyi akeyi, jiya data kwanta a kasa sanyi ya ratsata ga ba bargo, da ciwon jiki ta tash.
Jinta mike akan had'aden gadon d'akin yasa tasaki ajiyar zuciya, takwanta tashiha tunanin masoyinta, da ace tanada waya dako Abba takira taji lafiyar kamal😞 tana tunani bacci mai karfi yai gaba da ita.

Salman sai 11 ya dawo ya shigo, ganin d'akin dulim ba wuta yasa ya kunna, mamaki ne yakamashi ganin salma tai dai_dai akan gadonshi, yakarasa cikin bacin rai yad'au sandarshi ya zunguro ta ta farka cikin razana tare da rike gun, ganin salman yasa ta hade rai tace malam banasan haka, nafad'ama kadaina zungurata salman yai murmurshI 😏yace kinfisan in tab'aki? Dasauri tace karka kuskura ehe😗 yace to mike mai guri yazo ai kin mori gadon, salma kam taji dadin bacci akan gado tace ina zani? Yace inazaki? Inda kike kwana mana🤔tace tab aikam yau bazan yarda ba sai dai kanani pillow da bargo😕salman yace bakya ganewa ko? Yafad'a yana nuna kansa, tace oho ko mezakace baxan yadda insake  kwana a kasa ba😠.

Salma  yace matsalarkice wannan sannan yad'au rigar dayake bacci da ita ya wuce toilet ta murguda baki tace ai naga alama sai nima nadinga zakewa😠.

Ai naga yanada d'an manner nasan yanda zanyi yaban bargo,
Hijab din sallarta tad'auko tasa a tsakiyar gadon, yana fitowa ya kalleta yace baki sauka ba? Tace oho gashinan na raba mana ni nan bangaren kai nan, salman yai wata dariya yace what? Gadon nawa kika raba harda wani ni nan ke nan? Tace eh sannan kar wanda ya kuskura ya gangaro bangaren d'an uwansa😏 salman yace lalai kin girma dayawa tace da nid'in yarinya ce? Yace kin cire hijab dinnan kin sauko ko kuwa? Tace kazabi d'ayan uku, ko in koma falo na kwanta, ko kaban bargo ko kuma mu kwana a haka😏 salman yakalleta yace in zaba? Tace eh u have to choose a'a bama haka ba u most choose😎....







😳🙊nace lalai salma an zake😜



By Ayusher Mohd📚

NI DA PRINCE 16

☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄




*NA AYUSHER MOHD*



NO.1⃣6⃣

Mayafin kalar kayan tad'auko sannan tasa takalmi flat ta fito falon, salman na zaune a dinning kuyangi na tsaye a bayansa, ta karasa gun cikin nutsuwa.


Kuyangin ne suka gaisheta a tare ta amsa tare da zama a falon, salman yai gyaran murya da alama magana yakesan yi salma ta mannamai, yasake yi hakan yasa tad'an dago yamata alama da fuska akan tazo taci abinci, ta juya kai tace nakoshi in ka gama mu wuce, ya d'aga kafad'a alamar ruwanta sannan ya kammala tare da mikewa yai hanyar waje, salma ta mike tare dayin tsaki tace mutum sai girman kai ai yacemin in taso😠, ta mike hanne da wata baiwar nabinta a baya salman tagani tsaye a waje takarasa nan bayi maza suka rufo musu baya, salman yad'aga kai sama mutane na gaisheshi amma ga mamaki salma ko amsawa bayayi.


Sai da suka kusa isa fadar sarki, salman ya matso daf da ita yace u have to be careful dan karki kuskura ki bari wani a cikin gidan nan yasan irin zaman da muke, mark my word.

Salma ta d'ago ta kalleshi gabanta ne ke  fad'uwa tadaure tace sai ka fad'amin😗? Bai bata amsa ba ya cigaba da tafiya, sun isa fadar nan aka musu iso, bayan sun shiga salman ya tsuguna itama ta tsugunna nan suka gaida sarki ya amsa cikin farin ciki, nan 'yan fada suka fita suka barsu, sarki yakalli salma yai murmushi lalai yama d'anshi zabi mai kyau dan yarinyar ta kwantamai, yamaida idansa kan salman yace salman ina tsananin farin cikin wannan auran dan Allah ka rike yarinyarnan amana, kaji? Salman yai kasa dakai yace insha Allahu Abba, salma ta kalleshi ta gefen ido tace sai kace gaske ji yanda yakoma innocent😏.


Sarki yace jeka waje salman inasan magana da sirikata salman ya d'ago tare da kallan salma sannan ya mike yai waje, sarki ya kalli salma yace 'yata matso, cikin kunya salma ta matsa kad'an sarki yace salma agaskiya ba yaba da yanda kike Allah yasa abinda nagani hakan yake, tai kasa dakai batare datace komai ba, yace salma dan Allah ki rike yaron can da mutunci ki kula dashi, yaro ne maraya he is so lonely, salma tad'an dago idanta maraya? Ta maimaita aranta yace eh salma maraya ne mamaki ya kamata ya akai yasan abinda ke ranta? Sarki yakatse tunaninta dacewa Allah yabaku zaman lafiya tai kasa da kai batace komai ba, yace jeki salma ta mike tare damai sallama.


Tana fita ta saki ajiyar zuciya tare da dubawa ko zataga salman, sai dai ba alamarsa, hannece ta karaso tace ranki ya dade muje inkin gama, salma har zatai magana sai kuma ta fasa tace muje.


Part dinta suka koma hanne tace sai gobe zaku gaidasu fulani tace to tare da shiga ciki, daki ta koma ga mamakinta salman taganI zaune yasa earphone a kunnensa haushi yakamata ko kallansa batai ba ta karasa kan karamar kujerar d'akin ta zauna tare da kifa kanta ajikin kujerar, tunanin rayuwarsu da kamal tafara, yanda yasota yakuma kula da ita, dashi ta aura tasan da sunanan suna diga luv💖 amma gata yau ta auri wanda kallansa batasan yi shima haka.


Tunaninta yayi zurfi batasan sanda hawaye yafara zubo mata ba, muryar salman taji da alama waya yake, jitai yace kai fa dan iska ne najib ni kakema zancen wata amarya? Bataji mai akaceba sai jiganI tai yad'an kalleta sannan yace kai har kana tunanin akwai wata 'ya mace daxanyi lokacin ta? Ni ai a tarihin rayuwata ba mace kaima kasani, ganin yanda salman yai shiru daga ji magana ake sai jitai yace  banda lokacinka sannan zancen lokaci kuma mu zuba mugani, yana kainan ya katse wayar sannan yakalli salma yace ke kuma meye na kallona ina magana? Tace mezan kalla? Yace banasan kallo gwara ki sani, haushi ya isheta dama a wuya take tace malam nifa nagaji da bakaken maganganunka salman nifa nasan nafika san rashin auren nan dan ni inada wanda nake so kaifa? Bana tunanin kasan me kalmar so take nufi, sannan.....dasauri ya katseta yace kinada magana ne? Tace ai maganar nakeyi yanzu😡 yace banjiba ko zaki maimaita😏? Bakin ciki ne yazoma salma wuya tarasa mema zatace kawai ta harareshi tare da cewa haka maraya yake?I thought mara uwa ba haka suke ba? Cikin hanzari taga salman ya sauko idanunsa ya kad'a yai jaa yakaraso inda take ya fizgota daga kan kujera sannan ya matseta a jikin bango, idanta ta runtse da karfi, ko miyau takasa yad'iya salman cikin zafin rai da wata irin murya yace *WHAT DO U KNOW*? Jikin salma yafara rawa, salman ya kara matse mata hannu har saidatai karamin kara yace *HOW DARE U TALK TO ME LIKE THAT?* I can tolerate anything but don't u dare to say something like that😡..
Salma kam jikinta rawa kawai yake yana gama fad'ar haka ya saketa tare da d'aukan makullin mota yabar dakin, idanta na rufe sai dataji ya bugo kofa da karfi sannan ta bude ido a hankali jikinta har a lokacin bai daina rawa ba ta kalli hannunta dake mata zafi, ganin guntai yayi jaa dakyar ta furzar da wata iska sannan ta tsugunna tare da rike kanta, tace me nace da ranshi ya b'aci haka? Ahankali hawaye yafara zubo mata tace yaya kamal yazanyi?




Nima kaina jikina rawa yake ganin salma acikin wannan yanayin📚

NI DA PRINCE 15

☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄




*NA AYUSHER MOHD*



NO.1⃣5⃣

Salma kam tsaye tai a band'aki kara karema bandaki kallo tai, aranta tace band'aki shine akama wannan kwalliyar oh, sai kuma tai tsaki tace wlh nikam an cuceni mezanyi da salman?fuskarta ta shiga wankewa a sink dan bazata iya wanka a gidan da batasan kanshi ba, tad'an dade kafin ta fito, salman tagani kwance ya rungume pillow yana narkar bacci...

Haushi ya isheta ganin ko bargon baiyi karar ajiyewa ba takai hannu kamar zata dakeshi,  tad'an daki iska sannan tace d'an rainin wayau ni da wannan ai gwara abarni ko shekara 10 zanyi a barni na jira kamal ko a had'ani da d'an garuwa😏.


Ta koma kan sallaya ta tada sallah, ta dade tana nafila sannan ta d'aga hannu tashiga jero adduo'I tanayi tana hawaye, sai wajen 2 sannan ta mike dan kashe wutar dakin, ta kashe ta juya zata zauna taji ance I can't sleep while light is off, dariya ma abin yabata a hankali tace dayake nepar a gidanku take😏 salman yace I can hear u, kuma ki kunnan wuta,tace gaskiya ni ban iya bacci da haske ba, yace wannan kuma matsalarki ne.

Salman yace ki kunna min wuta ko? Dasauri ta matsa daga gun takaraso inda yake ta kunna yar karamar fitila ta dum light dakd side bed dinshi, zaiyi magana tai saurin juyawa zata koma kan sallayarta  hijab dinta ya kamo ta baya yace ke! Ta juyo tace waye ke? Yace ke wannan hasken yamin kad'an,nida d'akina fa baki isa ki takuran ba😠 ta fizge hijab dinta tace sai kai hakuri da wannan inba hakaba ka bani makulli na fita🤔 tana kainan ta karasa kan sallaya ya kalleta taredayin kwafa.

Itakam salma nan ta kwanta tare da takure jikinta, kan kaceme? Bacci yayi awon gaba da ita.

Kamal kam tunda ya tsugunna a wajen nan bai tashi ba mahaifinsa yace kar wanda  ya kulashi nan kowa ya watse aka barshi, sai wajen karfe 10 Abba yakasa jurewa yazo dakanshi ya d'agashi suka shiga ciki, sai dai kamal sam yakasa ko magana kawai idansa zaka kalla kasan yana cikin matsanancin bakin ciki.


Da Asuba karfe 4:30am salman ya tashi,ya sauko yaga yanda salma ta takure dariya tabashi yace kad'an kika gani tunda ke kika ce ni kikeso, harzai samata bargonshi sai kuma yafasa yai toilet.
Alwala yayi sannan ya fita, salma kam gajuya da rashin baccin wuri ga jikinta ba karfi saboda zazzaben datai agida yasa bacci mai karfi yai gaba da ita, sam bata farka ba lokacin sallah.

Salman na dawowa ya kalleta tananan ayarda ya barta yai tsaki yace a waje kamar ustaziyar gaske amma ace mutum ko sallar asuba bai farkawa? Daga gani ba yau tasaba makara ba🤔 karasa wa yai inda take ya d'au sandar dake ajiye a d'akin yad'an zungureta dashi,  cikin bacci tace Abba kafito? Salman ya tabe baki sannan ya kara zungura mata da karfi, cikin razana ta mike, sai dai me? Saman tagani ya harde hannunsa biyu.
Haushi ya isheta tace wani sabon cin mutunci ne wannan? Bai mata magana ba ya juya ya hau kan gado takara cewa haka ake tashin mutum daga bacci?yace ke ni da sanyin safiyarnan bansan magana meye dan an zungureki?tace what? Kwanciya yai tare da juya mata baya, tai toilet batare data mai magana ba.

Alwala tai sannan ta fito ta tada sallah, bayan ta idar ne ta kwanta wani baccin ne yasake d'auketa.



Wajen karfe 9 sukaji anan knocking, salma ta mike da sauri ta bude kofar, wata baiwa ce tace ranki ya dade dafatan kin tashi lafiya? Salma tace lafiya, baiwar tace sunana Hanne baiwarki, salma tace baiwa? Tace eh zuwa nai nasanar dake karfe 10 zakuje gaida sarki, sannan karfe 12 baki zasu fara yimuku sallama.
Salma tace toh😳 hanne takara kasa dakai tace karfe 9:30 zan kawo abinci, salma tace hmm to, nan hanne ta juya salma takoma ciki sannan tace nizan iya zuwa gun sarki kuwa? Tai maganar a fili, salman yace I can hear u, salma tad'an murguda baki tace mutum sai kunne kamar maciji? Yace inajinki fa? Tace oh ni😱 ta shiga duba drawer ko zataga kayanta sai dai kayan salman ne a jere tace oh wai nI ina akasamin nawa? Salman najinta amma ya shareta ya mike ya shiga wanka tabishi da harara.

Tana zaune ya fito sanye da kayan daya shiga dasu yazo yad'au kaya a drawer yakoma toilet, tace ba laifi he has manner🙄
ta mike takara duba kayanta, sai dai bata gansu ba, salman ne ya fito sanye da wata dakakiyar shadda ya kalleta sannan cikin magana kamar bayaso yace ki duba akwatina, yanakai nan yaI waje ta bishi da harara wato yasan inda suke shine ya shareta, ta mike ta hau kujera ta janyo akwatin dake kusa aranta tace wad'annan akwatin masu kyau sune na lefen kenan? Cikin hanzari ta duba tarr da d'auko wani swiss less mai masifar kyau tace amma kayan sunyi kyau nan tashiga neman hijab dazata sa, sai dai babu da alama wanda tai sallah dashi shi kad'aine gashI na sallar irin burum din nan ne, kawai ta wuce tai wanka, tasa kaya sannan tazo ta shafa mai ta murza huda, nan taji an murda kofa ta juyo salman yace malama ki fito ga abincin anan, ta kalleshi shima kallan ta yai she is natural beauty haka yaji zuciyarshi tafad'a ya kauda zancen yace mekike shirin yi hakan? Ganin ta d'auko hijab din ta zura, tace me nake kuwa? Yace ki tambattar kin cire hijab din nan kinsa mayafi kalar kayan, yarinya sai kace a rigar fulani😏

Ta kalleshi tace waya sani? Ya juya batare daya amsa mata ba tai raurau da ido tace da ace mutumincan karami ne da sai na mai dukan tsiya💪🏼👊🏻



Nace hmm 😜



By Ayusher Mohd📚

NI DA PRINCE 14

☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄




*NA AYUSHER MOHD*



NO.1⃣4⃣



Takarasa ta zauna a kujera fuskarnan a hade, najib ya kalleta ya kalli salman yaga shima fuskarnan a hade, yace oh god yad'an matso yace hb prince kad'an saki ranka mana 'yan jarida na kallo fa? Salman ya kakaro murmushin yake, sannan najib yakalli salma itama tad'an kakaro murmushi.


Angama shagali nan aka fara d'aukan hutuna kana ganin salma da salman sai kasan murmushin yake suke a hutunan, bayan an gama 'yan uwanta suka mata sallama suka shiga mota, idanta ne ya ciciko ganin Asabe ta sata a motar da aka kawota sannan takalleta, tace salma kiyi hakuri, ki manta da kamal a ranki, yanzu ke matar wani ce dan haka ki kula da hakkinsa.



Salma ta kalleta hawaye ya fara zubo mata tace Aunty meyasa kuka had'ani da salman? Cike da mamaki Asabe tace me salman din yai? Tace shikenan Aunty a bar maganar, Asabe tace koma dai menene ki rike mijinki, karki kuskura ki wulakantashi.


Salma kam hawaye take ta rike hannun Asabe tace Aunty kicema yaya kamal......dasauri ta katseta tace salma me kike shirin yi? An fa d'aura miki aure, salma tai kasa dakai Asabe tace mun tafi sai munzo, Allah yabaku zaman lafiya.


Salma ta bita da kallo hawaye na tsiyaya a idannunta,salman kam yanacan suna sallama da mutane sai can ya shigo shida kamal, lokacin salma kam ta hade kai da gwiwa tana zuba kuka, jin motsin bude kofa yasa tad'an sai_saita kukan salman yashigo ya zauna.

Nan suka fara tafiya salma kam sai kuka take.
Salman ne ya Kalli salma  ta gefen ido dataketa shesheka tsaki yai yace malama dalla kimana shiru kin cikamana kunne, salma tad'ago ta makamai harara, ya juyo yakalleta tare dayin kwafa, najib ya ce salman hakuri zaka bata ba fad'aba.

Salman ya kalleshi ta glass sannan yace ni? Yafad'a tare da nuna kansa, yacigaba ni wai kake nufi? Najib yace eh mana, salman yace over my dead body.
Salma ta d'ago jajjayen idanunta tace kwantar da hankalinka nima I won't let that happen.

Daga nan kowa ya d'auke kai ita ta jingina kanta da window, shikuma yad'au waya.

Najib yace oh god.......


Sun isa gida sai dai a bakin gun sukaga su zeena a tsaye nan suka kama salma sukai ciki da ita, dakinta suka kaita su ka sata a gaba wai sai taci abinci, nan ta daure tad'anci kadan sannan suka mata sallama suka tafi.

Mikewa tai tacire gwagwaron tai alwala tazo tai sallar ish'ai tana zaune agun ta zuba uban tagumi , salman ne ya shigo dakin tare da sallama ta amsa kamar bataso ya shigo ko kallan inda take baiyi ba ya bude drawer yad'au kayan baccinsa yashiga toilet din dakin.

Ruwa ya watsa sannan yasa kayan yana fitowa ya fad'a gadonsa, salma ta kalleshi da mamaki tace malam meye hakan? Ya d'ago yace mefa? Tace anan zaka kwana? Yace da dakinki ne? Tace ba haka nake nufi ba amma tunda nazo nan aka kawoni, yace wannan matsalarkice sai kinemi inda zaki kwana ko ki kwana a kasa, tace what? Yace oho kardai ki kuskura kibar dakin nan dan bayi suna falo in baki kwana anan ba zasu fad'ama fulani dan haka dolene ki dinga kwana a kasa, tace dole? Yace yes kinada jaa ne? Tace mikomin bargo inshimfida a kasan? Yace bargo? Nikuma fa? Tace sai ka yaye bedsheet din ka rufa dashi.

Salman yace kin ma rainan hankali ana sanyin zakice inkwanta na bargo? Ko in ja bedsheet? Ce miki akai zan iya bacci akan katifa zalla? Ran salma ya b'aci tace to ya kakeso inyi? Yace oho miki amma bazanyi abinda kikeso ba salma ta cika tai taf sannan tad'aure tace miko pillow, yace I can't do that dan ni haka nake bacci in kwanta a d'aya in kuma rungume d'aya salma tai tsaki tace u are so selfish tana gama fad'ar haka ta mike tai hanyar kofa, dasauri salman yai dungure ya damko hannunta yace are u crazy? Tace mayb yace naga alama to ina zaki? Tace falo inje in kwana yace baki fahimci abinda nake nufiba kenan😡 tace ina zan fahimta? Yace go back yafad'a yana nuna mata cikin d'akin tace I can't🤔 da karfi yasa hannu ya fincikota yai ciki da ita yasa makulli ya cire makullim yasa a aljihu. Salma ta fizge hannunta tace karka kara tab'ani😠yace ina kika ga jikin daza'a tab'a? Haushi ya isheta kawai tashige toilet, salman yai tsaki yace kawai za'azo a takuramin nida dakina😏 wannan aure ne ko takura🙄?




Nace ba ka tambayeni ba salman katambayi kanka😏.




By Ayusher Mohd📚

NI DA PRINCE 13

☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄




*NA AYUSHER MOHD*



NO.1⃣3⃣

Tafe suke yana gaba tana baya, har suka isa kusa da motar najib ya fito da sauri yanacewa Amarya ansha kanshi, salma ta hade rai dan tagane shi, najib yace hmm salman Amaryarmu bata magana ne? Salman yai tsaki yace kaifa banza ne kamar bakasan munafircin wasu matan ba, najib yai saurin kauda maganar tare da cewa bismillah Ango ya budema Amarya kofa dan gimbiya ce😊

Salman yace wa? Nizan bude mata? Salma tace nima ban nema ba😏 ta zagaya ta d'aya bangaren ta bude ta shiga tare da rufo kofar da karfi.

Salman ya kalli najib yace zakasha mamaki inkasan wacece najib yace naga itama ba sauki🤔 daga haduwa harkun fara fad'a? Da alama dai kunsan juna.


Salman yace abar maganar shiga mutafi yafara kokarin bude gidan gaba najib yace yada haka? Ai a kusa da ita zaka zauna salman yace dalili? Najib yace naga an d'aura auran? Salman ganin baisan doguwar magana yasa kawai ya bude baya ya shiga, salma ta juyo ta makamai harara, yace ke wa kike harara? Tace wanda ya tsargu tafada tare da juyawa tana kallan window.


Salman yad'auko waya yana dannawa, najib kam sai lekensu yake ta glass yana mamaki koda ace salman baisan yarinyar amma kyanta ai ya isa yasa yasota, shi jiyake inama za'amai auran dolen indai zai sami irin salma😜.


Ba wanda yasake magana acikinsu sai najib dakebin wakar Aashiqui dake tashi a cikin motar, salma kam tunanin duniya ya d'auru akanta jitake kamar duk duniya ba wanda aka tsana kamar ita.


A hankali najib yai parking, salman yace nifa natsani irin wannan gun na hayaniya😏najib yace haba salman ka hana ayi komai yanzu d'an dinner din ma bazaka bari ayi lafiya ba?salman Ya kalli salma dake cikin duniyar tunani yace ke tamai shiru yakara cewa ke limamiya! Ta juyo cikin bacin rai ta bugamai wani kallo kuma taki d'auke idanta, mamaki yakama salma yace ke who are u staring at? Tace in baxaka kirani da sunan da aka rad'amin ba kabarshi ya matso daf da ita har tanajin saukar numfashinsa akan fuskarta ya kai bakinsa saitin kunnenta dasauri najib yafita, salma kam numfashinta ne ya tsaya cak!! Salman yai wani murmushi yace how dare u talk to me like that? Dakyar numfashin salma yad'awo tad'aure tad'an turashi tace meye hakan? Yai murmushi yace u have to be careful bakomai nake d'auke ba.


Yana fad'ar haka yai waje ta sauke wani numfashi tace wannan wani irin mutum ne? Najib ne ya kwankwasa mata glass a hankali ta zuru kafa ta fito, najib yace salman ku tafi atare plz?  Yace kace ta matso, najib yace kid'an matsa ta matsa kusa dashi, najib yace dan Allah ku tafi a tare, salma ta kalli najib tace kacemai karyai sauri, salman yai wani murmushi wato tafi karfin tamai magana, itama aranta tace kaji ko da dadi.


Ahankali suka fara tafiya sunje shiga aka ce su tsaya nan 'yan yara da akama anko suka zo suka tsaya a gabansu kuyangi kuma suka fara zuba flower ahankali suke tafiya har suka isa masaukinsu.


Abin ya kayatar da mutane ganin shima salman light blue din shadda, mutane sun yaba kyan salma sosai,ga salman ma ba bayaba abun nasu chakwas😜

Sukansu 'yan uwanta dabadan sunsan itace Amarya ba da bazasu yadda salma bace ganin kyan datai.


Anfara gudanar da shirye_shiryen da aka tanadar anyi gada, anyi kid'an gwarya sannan yan busa da kalangu, sai kuma DJ.

DJ ya kira Amarya da Ango tsakiyar fili, sai dai duk maganar dayakeyi daga salma har salman ba wanda yake kokarin tashi, ganin haka yasa najib yazo kusa da salman yace hb salman so kake ka bamu kunya? Yai tsaki yace toshi Dj din cemai akai yakirani? Najib yace kayi hakuri plz, salman yace to kace ta taso, najib yakalli salma dake daf dashi yai murmushi shikanshi yasan ma'auratan kowa ba sauki amma yazaiyI? Haka ya juya yace Amarya kitashi kuje, salma tace kacemai yafara mikewa ai shine namiji😗 Salman yakalleta tad'auke kanta ganin mutane na kallansu ga dj ya saki murya sai kiransu yake yasa ya mike, ahankali itama ta mike suka nufi tsakiyar fili.


Suna tsaye mutane sai barnar kudi suke suna musu liki, salma kam mamaki take sai kace takarda? Suna tsaye har dj yace su koma gunsu, ahankali suka fara tafiya zasu koma, tsautsayi yasa takalmin salma ya turgude tai baya luu zata fadi, da sauri salman yasa hannu ya tarota, nan suka kalli juna salman yace Will u stop pretending?dasauri ta mike tare da matsawa kad'an, ranta duk a b'ace.


Nan mutane auka shiga tafi abin ya burgesu......


Nace hmmm


By Ayusher Mohd📚

NI DA PRINCE 12

☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄




*NA AYUSHER MOHD*



NO.1⃣2⃣



Asabe kam da sauri ta juya tai d'akin Abba dan sanar me.

Kamal yakaraso da sauri ya rungumeta kuka take sosai yace salma bazai yiwu ba, u are mine, muje gunsu Abban susan yanda......jin muryar mustafa sukai cikin zafin rai yace wani irin sabon iskanci ne wannan kamal😡? Dasauri salma ta janye jikinta, ya cigaba baka da hankaline? Matar wani kake rungumewa? Kamal yace Dady wai me kake fad'a haka? Yaza'ayi salma tazama matar wani bayan ni?dai_dai nan su Abba da goggo da Asabe suka karaso gun, mustafa yace bayan kai? Kai wa? Cike da mamaki kamal yakalli dadynsa zaiyi magana mustafa ya katse shi dacewa, kad'auka mudun shashashu ne? Tun yaushe ka gama karatu? Kamal yakalli salma sannan ya kalli Abban salma ya maida idanshi kan dady yace dady amma......

Mustafa yace banasan iskancin banza, dan kaga yarinya nasanka shine kadinga raina mata hankali daga kace saura 3wks ku gama sai ka kara cemata 2wks itakuma saboda shirme da yarda dakai yasa take d'auka, to bari kaji nasani sarai kafi 8month dagama makaranta dan wa'inda kwankwaso ya biya muku tare tuni suka dawo, ko sai kai kad'ane karage?


Kamal yakalli salma zaiyi magana, tsugunawa tai da sauri tace wayyo ni😭 Mustafa yakalleta sannan yakalli Abba yace Amadu dagata dakanka ka kaita mota dan 'yan daukarta sun gaji da jira yakalli kamal sannan yace to yaya, tare da karasowa ya d'agata.

Idanta ya rufe da kuka kawai sa kafa takeyi, dasauri kamal ya karaso kusa da ita yai kneel down yace salma please😥 mustafa yace Amadu ku wuce nace, cikin sanyin jiki da tausayin kamal Abba ya wuce da salma mota.


Motocine guda 20 tata tana tsakiya nan akasata mutane harda makota ganin motar bilis yasa suka shiga😜.

Salma kam zaune take a cikin mota tai kasa dakai banda kuka ba abinda takeyi zee ma kukan take dan tasan yanda salma kesan kamal, Asabe kam rungume salma tai tafara lallashi sai dai kamar zigata take.




Sun isa gidan sarki salma batamasan ina sukeyi ba tadai ji sun yi parking.
'Yan uwa na gidan sarki sun fito taryarsu, nan aka yan Rakiyar bangaren salma, ita kuma su zainab suka riketa sukai bangaren fulani da ita, zee da Asabe na biye dasu.


Sai da suka kaita duka bangaren matan sannan suka maidata bangarenta, yan rakiya sun rikice da kallo ganin irin dukiyar da aka zuba a bangaren, falone kato da kofofi uku, d'aya daki ne a cikinsa da bandaki a d'akin nan ne master bedroom, sai kuma dayar kofar da kuma daki ne da toilet aciki, sai d'ayan kitchen ne kato duk da bawani girki sukeyi ba amma anyishi ko akwai abinda zaisa ai girki aciki.



Baban dakin aka kaita tanaji mutane nata wasa kayan gidan amma ita ko kallan dakin ma batai ba bare, hawaye sai gudu suke a fuskarta, wata baiwa ce ta shigo tace wai ance duk ku fito za'a wuce, sukace amarya bata shirya ba ai, baiwar tace eh ita yanzu za'a shirya ta zasu taho dashi.


Nan suka fara fita, akabar salma ita kad'ai, kifa kanta tai tana kuka yanzu shikenan an rabata da yaya kamal? Wacce irin rayuwa zatai?jin sallama tai dasauri ta zauna tare da gyara mayafinta zeena ce da wasu mutane guda 2, zeena ta yaye mata mayafi aranta tace masha Allah sannan tace salma yanaga idanki a haka? Wani irin kuka kikai haka? Salma ta kakaro murmushi tare dayin kasa dakai.
wata daga cikin matan tace hb Amarya yanzu ai an daina irin wannan kukan, zeena ta kalli d'ayar tace Meema Yaza'ayi? Tace gata so cute I wish bata b'ata fuskarta haka ba amma ba matsala zeena tace tnx.


Nan meema ta matso ta yaye ma salma mayafin gaba daya ta zare d'ankwalin kanta, itakanta zeena sai datai mamakin gashin kanta, ahankali meema tashiga yima salma kwalliya sun d'au lokaci kafin su gama sai dai me? Duk wanda yaga salma to ba karya sai ya kara kallanta tayi kyau na garari....

Zeena ta shiga fasama meema kai, nan suka d'auko wani ratsatsen kaya wanda kyansa ya wuce tunanin mutum, dark blue ne sai kwalliyar jikinta da akai da golden rigar doguwa ce, ta baya jan kasa takeyi, nan aka d'aura mata gwagwaronta dark blue sannan aka yafa mata wani shara_sharan net golden, aka miko mata takalmi mai d'an tsini golden.
Salma tayi kyau na karshe sai dai bata farin ciki sam.


Zeena tace kai Amaryarmu karfa kisa kanina ya fad'I garin kallanki nan sukai murmushi salma kam ta juya kai.


Nan suka ce mu mun wuce yanzu salman Zai zo ku tafi, nan suka fita suna murmushi.



Salma na zaune tana tunanin rayuwa ita dake tunanin auranta da kamal sai gata a gidan wani can da bata sani ba, sannan tace a fili wai ahaka suke nufi  zanje? Da wannan net din? Tasaki tsaki daidai nan salman yashigo ko salama baiba dan duk ranshi a b'ace yake da akace wai shi zaizo ya d'auketa.


A bakin kofa yatsaya yace ke! Salma taki d'agowa yakaracewa ke! Takara kim d'agowa haushi ya isheshi yakaraso kusa da ita tana kallan kafarsa na tahowa duk da a tsorace take amma bazata yarda yace mata ke ba jitai ansa sanda a tabo mata kafad'a da mamaki tad'ago dan ganin wannan rainin hankalin.

 *tofah*🙄

Nan idanun ma'auratan ya hadu cikin tsananin mamaki mara misaltuwa salma ta mike tace *YOU?* salman yakalleta ba laifi kyanta ya wuce misali sai dai kamar yasanta, jikin salma ya shiga bari? Tad'aure tace me kake anan Prince? Yace oh kinsani dama? Tace ohhh baka ganeni ba? Wace ka cima mutunci a Buk? Me kazoyi nan? Ko nan din ma biyoni kai? Salman yai wata dariya mai karfi wacce tasa zuciyar salma tagama tsinkewa, sai daya gama sannan yace *SALMA*?

Da mamaki ta kalleshi tace eh meye? Yakara dariya sannan kuma ya hade rai kamar zaki yace kina nufin kece matar? Ta kalleshi batare data amsa ba yace yar gidan Amadu u are really something, wato sai da kikasan yanda kikai kika aureni ko? Sai dai kuma I really pity you dan tun daga yau zaki fara regretting yar gidan masu gini.

Salma tunda taji yace wai auranshi jikinta yafara rawa, zama tai a gadon dabas tace kai ne mijin😳? Yace ke banasan pretending din banza, zatai magana ringing din wayarshi ya katseta yad'aga.
Najib ne yace to ango wato anga mata shine aka ahanyani a mota ko? Salman yakalli salma yace u will be really surprise inka ganta, najib yace to please kazo mutafI yaya zainab sai waya take, salman yace ok gamunan.


Salma yakalla yace ke taso muje tace amma....ya katseta banasan wani munafirci taso muje, tace munafirci kuma? Yashareta tace wai da wannan mayafin zani? Yai tsaki yace ke bansan iskanci inkinga dama ki fito, yanakai nan yafara tafiya, itama tsakin tai tare da binshi, ya kalleta kawai yai kwafa yaga alama sai ya mata service😜😜😜😜





By Ayusher Mohd📚

NI DA PRINCE 11

☄☄☄☄☄☄☄
💥 *NI DA PRINCE*💥
☄☄☄☄☄☄☄

*NA AYUSHER MOHD*

NO.1⃣1⃣

Haka salman yashirya cikin dakakun kayan sarauta da Mai martaba ya aikomai dashi, shi kanshi yasan yayi kyau najib sai kodashi yake, yai dan karamin tsaki yace I wish wannan auran da budurwar danakeso akeyi,amma meye amfanin kwalliyar? Najib yace zaka fara ko? Dan Allah kazo mu wuce, turarensa ya fesa sannan yasa hula da takalmi ya fito cikin kasaitarsa.

Tunda ya fito bayi da 'yan uwa kemai sannu da Allah yasanya alkairi amma kasaita da jin kai irin na salman ba wanda ya amsawa sai najib ne yashiga amsawa.

Yana zuwa hanyar fada wasu bayi sukazo suka kewayeshi yace kun fara ko? Najib yace wad'annan fa? Salman yace ai aiki yaganka dan hakannan zasuyi tabinmu har agama, najib yace lalai kace alamace ta ango ya taho, salman ya juya kai ba tare dayai magana ba.

Guri yacika sosai su Abba kam suna wani guri da aka ware musu, tsoro ya fara kama Abba shikanshi yafara tunanin kodai saida 'yarsa yai?.

Salman haka yai ta ratsawa cikin manyan mutane suna gaisawa, basu dade ba aka shiga huduba ta sallar juma'a, bayan anyi sallah ne aka d'aura auran *SALMAN DA SALMA* akan sadaki dubu hamsin, dan Abba yace sadaki kad'an yafi daraja a aure duk yanda sukaso ko dari abada amma yaki yace hamsin ya isa hakan yasa aka hakura aka bada hamsin.

Salman kam baimasan an d'aura auran ba yana waje suna hira da Amir da Najib sai dayaji masu busa da kirari sun matso kusa dashi sunayi nan fa mutane suka zagayeshi, haushi duk ya isheshi jin wai sunan matar salma, wato salman da salma kenan😡? Inama ace wacce yakeso ne take da wannan sunan kuma sukai aure? Da baisan irin kyautar dazaiyi ba yau.

Najib ne yaja hannun salman yakaishi gunsu Abba, har kasa salman ya tsugunna yagaidasu, Mustafa yace ikon Allah sai yau mukaga sirikin namu, salman yai kasa dakai, Abba yadaure yace salman ko? Nan prince yace eh, Abba yace kada kamanta amana muka baka😊 salman aranshi yace amana🤔? Amma afili sai ya d'aga kai Abba yakaraji yaran ya birgeshi yace Allah yabaku aman lafiya, Najib cikin murna yace Amin.

Salma na tsugunne tana alwala dan baccine ya d'auketa sai da aka tasheta, jin busa a waje da kid'an kalangu yasa mutanen gidan suka shiga sa mayafi suna fita kallo, salma kam abin dake faruwa a gidan sam haushi yake bata, da gudu taga mutane sun shigo suna guda sun tsaya akanta, takarasa d'auraye kafa ta d'ago jitai sunce Alhamdulila an d'aura auran *SALMAH DA SALMAN* jitai gabanta ya yenke ya fad'I cikin rawar murya tace ma naau gud'ar kud'an matsa in wuce, jitai an rungumeta idanta ta rufe kwalla ta zubo mata Asabe tace Alhamdulila salma naji dadi, Allah yakareki daga sharrin makiya.

Ahankali hawaye suka shiga zubo mata ta d'aure tace Aunty sallah zanyi, Asabe tace muje in kaiki nan gida ya kara kaurewa da murna zee ma ta iso, sai dai ganin kawarta a wannan hali yasa jikinta yai sanyi.

Wajen karfe 6 na yamma Asabe da goggo sun zauna sai gyara amarya sukeyi, dakyar suka lalabata tai shiru har zee tasamu damar yi mata kwalliya, motocin d'aukar amarya suna waje, dan wasu yan zumudin harsun shige.

Lifaya ce aka nad'a mata wacce Matar mustafa dakanta  ta siyo mata mai tsadar gaske tayi kyau sosai acikin orange din lifayar, ga zee ta mata kwalliya, tasha sarka da d'ankunne silver hakama takalmin kafarta.
Sai kamshin humra da turaren wuta takeyi.

Bayan sun gamane suka kaita d'akin Abba Tana zaune kusa dashi, Abba yace salma? Tace naam yace kiyi hakuri kinji? Tace Abba kadaina bani hakuri, yace naga salman a gaskiya ya kwantamin tai murmushin yake yace kuje mutane na jira gashi naji ance jarfe 8 akwaI abinda za'ayi acan tace umm...

Nan suka mike ta kalli umma datai kasa dakai, kusa da ita taje tare da cewa Umma natafi d'agowa umma tai idanta yai jaa tace Allah yabada zaman lafiya salma bata amsa ba tai waje da sauri jin kuka zai kubce mata.

Zee ce a gefenta sai Asabe dake kusa da ita sunzo fita kofa salma tasa kai shima yasa kai aikam suka gwari juna, zee tace sannu sannan ta d'ago tace malam la.......cikin wata irin murya salma taji ance mekuke nufi da nad'e mata kai? Dasauri ta yaye mayafin da aka rufeta tad'ago jikinta ne yashiga rawa ahankali tafara ja da baya tana girgiza kai wasu hawayen bakin ciki na zubo mata.

Asabe ta d'aure tace meye hakan kuma? Tafad'a tana kallan mai maganar? Yace Aunty ni...
Asabe ta katseshi bamu hanya nace?
Yace Aunty..
Takara katseshi
tace ka bamu hanya ko?

Ahankali ya matsa idanshi taf kwalla Asabe ta fizgo hannun salma da karfi tafara janta sun zo fita kawai ya kama d'ayan hannun salma yace salma haka alkawari yace? Dama akwai ranar dazaki wuce gidan wani namiji bani ba? Takalleshi a zabure hawaye yakeyi shima runtse idanta tai dakarfe batasan sanda kuka ya kufce mata ba, yace isowata kenan ko gidan banjeba nace dan taxi yakawoni infara ganinki amma me? Sai infara ganin motoci, sannan in ganki kinfito da sufar amarya wacce za'a kai gidan wani? Salma mekeke shirin aikatawa rayuwar mu? Girgiza kai kawai take cikin matsanancin kuka tace Yaya *KAMAL* na shiga uku........yaxanyi?

Hmmmmmmm babar magana inji kawata koxali🤔

By Ayusher Mohd📚