Saturday, 4 March 2017

JALALUDEEN 78

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com

   *LAST PAGE*

   No. 7⃣8⃣

      Can gida kuwa wasu abin nan ya basu haushin gani suke Dad bai kyauta ba, wasu kuwa harda habaici na dama yarinyar da batada mahaifi me zaisa ya had'ata da d'ansa?"

     Zahra kam taji ba dadi dasu Junaid sai dai ya za'ai tunda dai an riga da angama, Ammar ko gidan baije ba, sun riga sun shirya yin dinner sai dai Zahra ce da Junaid kawai zasu.

    Jalal kam suna kwance, sai can Seemah ta farka, tana ganin Jalal idanunsa biyu da sauri ta mik'e tsaye tare da wayancewa da hmm ina toilet din ne? Tafad'a tana dubawa da gudu tai nufi kofa ta bud'e ta shige.
Jalal ya bita da dariya ganin yanda ta rikice.

  Tunanin wayarsa ce tazomai yasa ya jawo wayar Seemah ya kira Abbansa.
Abba ya daga, Jalal ya gaidashi.
Cikin zumud'i Abba yace " Jalal kaji abin alheri ko? Bansan mezancema Ammar da Isma'il ba."
  Jalal yadanyi murmushi yace " Zainab fa?"
  Abba yai shiru, Jalal ya danyi murmushi kad'an nasan bazatai farinciki ba.
Abba yace " Jalal kayi tunanin inda Seemah zata zauna?"
" hmm ina tunanin tambayarta ko nan kaduna  ko kuma nan, ni abin ne banbarakwai nake jinsa."

  Abba yai dariya yace " ba wani banbarakwai Allah ya riga ya tsara Seemah matarka ce."
  Jalal ya kalli kofa inda yaji motsin Seemah, yace " Abba sai anjima wayar Seemah ce."
Nan sukai sallama tare da kashewa, Seemah ta harareshi kad'an tare da cewa " wa yace a d'aumin waya?"

  Jalal ya dan yi murmushi yace " yayarki na kira."

  A zabure ta karaso kusa dashi tace " wacce yayata?"
Kallanta yai yace " haka ake jinyar baza'a bani abinci ba? Yunwa nakeji."
  Ranta a b'ace ta bud'e kular da ta gani a d'akin fatan dankali ne yaji kifi sosai, ta zubamai  a plate sannan ta mikamai, tace " wacce yayata?"
  Jalal yadan rik'e ciki  kadan yace " haka ake kula da miji ko abincin baza'abarshi yaci ba?"
  Juya kai tai aranta tace " su miji manya."

  Yana gama ci ta kalleshi tace " wacce yayata? "
Hannu yasa ya riko ta tare da zaunar da ita kusa dashi yace " Meemah bamuyi tunanin inda zaki zauna ba?"
  Ta turo baki tace " inafa zan zauna?"
Ya kalleta yace " inda zamu zauna nida ke a kaduna ko anan."

  Ta mik'e tare da cewa " ni yazanyi iyi sallah ko mayafi ban fito dashi ba, kallanta yai yace " ai kuwa sai dai kiyi waya a kawo miki dan bazaki fita a haka ba......"

  Kusa dashi ta matso tace" to ya kakeso inyi?"

  Yace " bana fadamiki ki sa a kawo miki ba nidai matata bazata fita a haka ba mutane su kalleta."

   Ta sa dariya sai data tsagaita ta kalleshi tace " lalai mai mata."
Lumshe ido yai yace " sosai ma, Ammar ne ya bani matar da nakeso wacce ji nake duk numfashina tana tattare dani."
   Dariya ta sakeyi tace " Kai Deen yaushe ka zama haka?"
Jawota yai jikinsa yace " ke kika maidani haka, mu zauna a abuja ko? Kinga kusa da Dad d'inki."

  Ta turo baki tace " bayan bani kad'ai bace matar ka?"
  Yai ajiyar zuciya yace " Meemah amma kinsan ai...."
  Saurin cusa kanta tai a kirjinsa alamar kunya tace   " na sani amma a da dan rannan tafiya kai ka barni."

  Ajiyar zuciya yai yace " Meemah banasan zama a asibitin nan mu roke likitan ya sallamemu please kinji?"

   Tace " naki wayan baka warke ba ta ina zamu tafi? Kuma ni banshirya tarewa yanzu ba."

   Hararta yai yace " a ina? Ai kafata kafar matata Amnar yamin abinda ban taba zatoba ta ina nikuwa zan barki kije wani gida? Mu tafi gidana inyaso sai insa a nemarmana gida."

  Baki ta turo tace " an fa kai min kayana can gidan Ya Ammar kuma kwasowa za'ai ko me?"
  Jalal ya rungumeta yace " bakomai sai musai wani."
Ta mik'e tace naki wayan.

  Washe gari kuwa sai da Jalal ya matsa aka sallameshi duk lokacin abinci ana aikowa daga gidan su Dad.

  Ammar kam hotel ya koma kawai ya tare, su Dad basu sani ba ashe yayi booking d'in jirgi, washe gari da safe yazo ya sanar da Dad zai koma England amma ba dadewa zaiyi ba, ba musu Dad ya amince saboda yasan halin da Ammar din ke ciki.


 
   Bayan Jalal ya warke da kanshi ya kaita gun Abdul, nan ya nemi yafiyarta tare da alkawarin canza halayensa, sunyi ziyara har garin iyayenta nan sukaje taga 'yan uwanta.

     Jalal ya kama gida a Abuja inda suka zauna shida Seemah, kulawa kaunar dake tsakaninsu ta wuce duk yanda zan kwatanta muku, Yau yakama wata tara kenan da auren su, duk karshen mako yake tafiya kaduna Seemah ita ta tsara mai hakan saboda tana ganin yanda yake rashin damuwa da Zainab hakan bazai mata dadi ba, shikanshi yanzu yana daidai kokarin kwatanta adalci a tsakaninsu, sam Zainab bata jin haushin Seemah ita gani take ma auren da Jalal d'in yai shine sanadiyyar kulata da Jalal yake, Seema na d'auke da tsohon ciki, itakuma Zainab laulayi takeyi.

  Jalal ya shigo gidan ganin yanata sallama ba'a amsa ba, a rude ya shigo gidan ya fara neman inda Seemah take, har daki ya shiga batanan, d'akinshi ya nufa, yana budewa yaga ta fesheshi da wani farin abu, baya yai yana mamaki, nan ta matsamai ya kalli d'akin, candle ne kanana an jera shi a kasa anyi kwalliyar I♡U dashi kwaliyar tayi kyau, ya kalleta cikin mamaki, kayan bacci ne a jikinta shara shara ya sakar mata wani sansanyar murmushi tareda karasowa ya rungumeta, murmushi itama tai tace " My Deen kardai a manta da babynmu."
  Sassauta rikon yai sannan ya d'ago a hankali ya kai bakinshi cikin nata, wani irin salon kauna sukema junansu, jitai kafarta naneman kasa d'aukanta, Jalal ya riko kugunta nan suka cigaba da aikama juna sakwanni, a hankali Jalal ya jata kan gado sannan ya tare neck tie d'insa ya cigaba da sumbatarta, cikin salo a kuma hankali ya bakinshi na nata ya zare mata 'yar rigar dake jikinta, itama mab'allin rigarsa ta dinga cirewa har ta cire su duka, sumbatar kirjinsa ta fara nan fa suka shiga cikin wani yanayi wanda su kadai sukasan halin da suka shiga.

   Sai da suka gama sannan ta kwanta akan kirjinsa, shikuma yana shafa kanta, yace " Meemah wannan gyaran fa? Decoration d'in yayi kyau, kara kwanciya tai a kirjinsa tace " a internet na dubo yanda akeyi."
  Yai ajiyar zuciya yace " Meemah in miki wani alkawari?" Ta d'aga kai, tare da juya fuskarta saitinshi, yace " indai mace kika haifa sunan Mahaifiyarki zamusa mata Fatima, in kuma namiji ne to sunan  Ammar ko Dad sai kizab'a a ciki."

  Murmushi tai tace" nagode sosai Deen, amma ya maganar Ya Ammar?"
  Yace " yace next week zai dawo."

  Tai ajiyar zuciya tace " kaii nayi missing d'in yaya."

   Mikewa yai ya sunkuceta sukai toilet, kafin suyi wanka sai daya wanke mata kai da kanshi, dan tace bata iya sunkuyawa, nan sukai wanka suka fito a tare, shi ya shafa mata mai sannan itama ta shafa mai tana shafamai tana tambayar yasu Ya Zainab?" Yace suna lafiya.......



  Ammar ya zaune a cikin jirgi yana karanta jarida watace a zaune a kusa dashi ta zake sai bacci take, haushi ya kama Ammar ya juya kansa jikin window, tana gama baccin ta mik'e tare da yin mika, ta kalli Ammar tace " dan Allah awa nawa mukai?"
  Kallanta yai yace  " ke agoggonki tsayawa yai?"
  Agoggon hannunta ta kalla ashe da agoggo a hannunta da sauri ta juya fuskarta, yai murmushi sannan ya juya, mai service ce ta karaso ta kallesu tace " mai kukeso a kawo muku? Tea ko coffee? "
  A tare sukace " Coffee."
Kallan juna sukai sai sukai dariya, matar tai dariya itama tace " da alama ku couples ne kunyi matching sosai."
  A tare suka kara cewa " a'a."
Tai sake dariya sannan ta tafi, tana tafiya  Ammar ya kalleta kadan kyakyawa ce sosai, juyawa yai jiyai tace " A Abuja kake?"
Yace " eh kefa?"
Tace nima...........
Murmushi sukama juna a tare.



  Zahra ma ankusa haihuwa, Dad da Abban Jalal aminta ta dawo sosai, yanzu Abban Jalal yananan yana kasuwancinsa a babban shagon da Jalal ya bud'e mai.

  Zaid ma saura wata d'aya ya auri Zaheeda wacce ta warke sumul, har malami Jalal ya d'aukar mata yana koya mata karatu.

  Abdul kuma an sakeshi yana zaune a dan karamin gidansa shida matar sa 'yar uwar Sagir, Ya canza kamar bashi ba.

   Jalal da Seemah masha Allah kauna kam suna san junansu sosai........nace To Allah yasauketa lafiya

  Nima nace mu had'u a wani littafin nawa in Allah ya yarda.......



GODIYA TA MUSAMMAN GAREKU
Yan Group d'ina
THE QUEEN BEE
AYUSHER FAN CLUB
Sannan ina godiya gareku 'yan
*NAGARTA*
BEELY BADARU GROUP
'YAN SAUYI NA KCK
EXCELLENT HAUSA WRITERS
MU SAN JUNA
TALENTED HAUSA WRITERS
MARYAM MAI DALA
HAUSA NOVEL
MY BLOG FANS
HAUSA NOVELLA
BE A LADY WITH FASHION
Da kuma ragowar group d'in da duk nake ciki ina godiya gareku.



   Ina alfahari daku
MY BEELY BADARU
SIS PHARTY
ASY KHALEEL
MAMAN SHAHEEDA
MUNAY
SADNAS
AUNTY KYADY
FATTY

   Ahh gaisuwa gareki babbar Aminiya AISHA M.UMAR....
NI AYUSHER MUHD ke muku fatan alkairi��������

JALALUDEEN 77

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com

  
*Luv u oll my fans.......*

   No.7⃣7⃣


   Seemah na zaune tayi wanka tana jira agama ma Zahra kwalliya sannan a mata, rigace doguwa ta atamfa a jikinta aiki ne a jikin rigar har wajen ciki d'inkin yayi masifar kyau, a zaune kawai take amma gaba daya batajin jikinta daidai, jitai an fara kud'a hakan yasa gabanta ya sake fad'uwa, suka shigo d'akin sukace an d'aura, Seemah kasa tai da kanta ganin wayarta tai kara yasa ta daga, Zaid ne da sauri tace   " Ya Zaid ina ya Ammar? Jinake kamar wani abu ya sameshi."
  Zaid yace " Seemah ki fito ina waje mijinki ba lafiya."
" Naam? Me kake nufi?"
  Kashe wayar yai dan jiyai baisan me zai ce mata ba,  A zabure Seemah ta mik'e ko hijab bata dauka ba d'ankwalin data yafa akanta kawai ta sura tai waje ko takalmi batasaba.

  A waje taga mutane sun taro anacewa " waye kuma Jalal?"
Tsayawa tai turus, can kuma sai tai tunanin ko ba Jalal d'in ta suke nufi ba, waje tai da sauri ta fada mota Zaid ya kalleta sannan ya ja motar, duk ta rikice tace " Ya Ammar meya samu Ya Ammar d'in?"
Kallanta yai jiki a sanyaye yace " Kunyi magana da dad?"
Ta girgiza kai tace " a'a yadai kirani da safe yacemin, ko mai na rayuwa mukaddarine, haka kawai yacemin."

   Suna isa asibitin suka fito, duk Seemah ta rikice, harsunje shiga d'akin wayar Zaid tai kara, ya kalleta yace " nan ne ki shiga."

  Ko kula shi batai ba ta fada dakin, daga nesa tafara ganin kamar ba Ammar ba, jiki a sanyaye ta karasa kusa da gadon, turus tai ganin Jalal a kwance duk ya rame sai bacci kawai yake.

   Hawayene suka fara zubo mata a hankali takai hannu gefen fuskarsa hawayenta ne suka shiga d'iga kan kuncinsa, sai zubowa sukeyi ta kasa magana sai hawaye kawai take.

   A hankali Jalal yad'an bud'e ido jin ruwa na d'igarmai, kallan Seemah yadauka mafarkine yasa ya kara lumshe ido, hawaye kawai takeyi, can ya sake bud'e ido daidainan ta kalleshi, idanu suka had'a yad'an motsa bakinshi kad'an yace " Meemah?"

  Hawayene ya cigaba  da zubo mata tace " Deen? Me ya sameka haka?"

   Sai a lokacin ya tabbatar ba mafarki yake ba kallanta yai tare da cewa " me kike anan?"
  " Naam?"
Tafad'a tare da kallan d'akin sai a lokacin ta tuna kamarfa Ammar ne yakamata ta gani ba shi ba, ta d'an juya tace " Ni cemin akai inzo in duba mijina na d'auka ya Ammar ne bashida lafiya."

  Jalal ya d'an juya ido yace " meya sami Ammar d'in?"

  Ta d'aga wayarta ta kira Zaid ga mamakinta Ammar ne ya d'aga.
Cikin tsanin damuwa tace " Ya Ammar kana ina?"
  Yace " Seemah?"
   Yanda ya kira sunanta yasa jikinta yai sanyi ta kasa amsawa.

  Cikin wata murya yace " ki kula da mijinki, ke yake bukata a wannan lokacin."
Da mamaki tace " ban gane ba? Kana ina?"
  Yai shiru can ya daure yace " An daura muku aure da Jalal karki damu dani ko kiyi tunanin wani abun, kawai ki kulada lafiyar mijinki."

   Jitai kalaman sun shigar mata kunne banbarakwai sai dai kafin ta sake magana Ammar ya kashe wayar.

  Kallan Jalal tai sai dai ganin yanasan tashi ya kasa saboda cikin dake bayansa, yasa ta daure matsowa tai zata taimaka mai, kallanta Jalal yai yace " bashi kawai, ki nemomin likita."

   Bata kulashi ba kawai ta shiga taimaka mai, tana gamawa ta duba ga kayan shayinan da abinci hakan yasa ta hadamai shayi ta mikamai tace " ina zuwa."
Kallanta yai yace " kina zuwa ina? Me zaki dawo yi anan? So kike ran Ammar ya sake b'aci?"
  Kallan yanda ya rame tai ta kauda kai tare da cewa ni kaina ban fahimci abinda ya Ammar d'in yake nufu da an d'aura mana aure dakai bane shiyasa nakesan ganinsa.

   Bata jira mai zaice ba tai waje, Jalal ya kara maimaita kalamanta.

   Seemah na fita taga Dad yana tahowa shida Abba, da sauri takarasa gunsa yace   " Seemah muje ciki."

Kallan mamaki tamai sai dai ba zata iya musu ba.
D'akin Jalal suka koma bayan sun zauna shiru, nan Dad ya warware musu duk abinda ya faru jiya zuwa yau.

  Seemah kuka take sosai, yana gama maganar yace " dan haka ki zauna anan ki kula da mijinki ki bar sha'anin biki su Zahra sayi."
  Ta kasa magana haka ma Jalal wanda yakejin maganar kamar ta tsuniya, ganin halin da suka shiga yasa Dad ya mik'e shida Abba sukai waje.

  Seemah ganin sun fita yasa ta mike da gudu ta bi bayan Dad ta baya ta rungumeshi tana wani irin kuka, Dad ya daure ya juyo da ita setinsa yace " Seemah?"

  Cikin tsananin kuka tace " Dad meyasa ka bar Ya Ammar yai haka? Kamanta nace na hakura? Sannan babban burinka ne fa?"

  Dad yad'an shafa kanta sannan ya kalli kafarta da ko takalmi babu yace "  a haka kika fito ba ko takalmi?"

   Hawayenta ne ya karo tace " Dad ina Ya Ammar d'in? I have to meet him. "

Dad yai murmushi yace " karki damu yayanki yace ki kulada Jalal."

  Yad'an zareta daga jikinsa yace " karkiyi tunanin komai sai mijinki."
Yana kainan ya juya ya fara tafiya.

   Tsugunnawa tai a gun ta shiga kuka, ta dade agun sosai mutane sai wucewa suke suna kallanta dakyar ta daure ta mike tai cikin d'akin ga mamakinta Jalal ta gani ya mik'e yana sa rigarsa, da sauri ta karasa inda yake? Idanunta duk sun canza tace " Ina kuma zaka?"

  Kallanta yai yace " me Ammar yake tunani? Ni zanje in mai magana."

  Cikin kuka tace " ni ina zansan me yake tunani, amma kaidai bazan barka ka fitaba bayan ba lafiya gareka ba."

  Kallanta yai cikin wani yanayi yace   " Meemah tunanin halin da Ammar yake ciki nake."

  Ta goge hawayenta tace " naji wannan amma ka koma ka kwanta sai inkira Ya Ammar d'in."

  Jiki a sanyaye Jalal ya zauna, ta mikamaj wayarta tareda dialling d'in number Zaid.

  Ammar ya d'auka, Jalal yace " Ammar meke faruwa?"

  Ammar yad'anyi murmushi kad'an yace  " meke faruwa dame? D'an na bar maka Seemah ko dan kana tare da ita?"

  A zuciye Jalal yace " Ammar meke damunka ne? How can u joke now."

  Ammar yai ajiyar zuciya yace " kai dai dakake lovesick yanzu sai ka ware."

  Jalal yace  " Ammar ban aminta da...."
Katseshi yai da cewa " ka saketa to."
Yanakai nan ya kashe wayar, shiru Jalal yai yana maimaita kalmar saki.

  Seemah ta zauna kusa dashi kadan tace " me Ya Ammar d'in yace? Wasa yake ko?"

  Jalal ya kalleta cikin mamaki yace " da alama dagaske yake tunda haryake cemin wai in sakeki ."

  Ta kalleshi da mamaki, mik'ewa tai da sauri tace " Me Ya Ammar yake tunani?" Tafad'a tare da hura iska.

  Jalal ya daure yace " taimaka min in kwanta please. "
  Harararsa tad'anyi tace " akan me?"
Kallanta yai sannan ya daure yace  " hmm kiramin ko nurse ne."
Ta d'an tab'e baki tace " nurse d'in ai kala biyu ne, maza da mata wacce kakeso a kira ma?"

  Jalal ya kalleta tunowa yai da masifarta ta da yace " auu kiramin koma waye ai ni patient ne."
Ta makamai harara tare da turashi gado da d'an karfi, zafi yasa sai daya saki kara yace " me kuma nai kinsan dai ba lafiya ce dani ba, irin wannan tureni?"
  Ta harareshi tare da komawa gefe ta zauna, Jalal ya juya kai kamar mai bacci dan jin abin yake banbarakwai.

  Text tama Ammar kamar haka.
_Ya Ammar na sani sarai kayi haka ne dan farin ciki na sai dai Ya Ammar aikin gama ya gama bani da abincewa a wannan lokacin, kalma daya zan iya fadama shine Allah ya sakama da mafificin gidan aljanna ya kuma baka matar data fini._

   Tana turawa ta kwantar da kanta jikin kujera tana kallan Jalal dake kwance kamar mai bacci, jitai yace   " Kallan fa?" Ya fad'a a hankali tare da bud'e idanunsa."

   Bata d'auke idanunta daga kansa ba tace " wai me ya sameka?"
  Ya kalleta shima yace " Ni kaina bansan me ya sameni ba, kawai ganina nai a asibiti." 

   Ta lumshe ido sannan tace " ban tab'a tunanin zan ganka haka ba."
  Shiru yai can ya daure yace " Meemah ina farinciki a raina kuma ina bakin ciki."
  Name fa?

  Kallanta yai yace " ina farincikin kasancewa dake sai dai ina tausayama Ammar danasan yana sanki kamar ransa."

  Seemah jitai idanunta sun ciciko tad'an daga kanta tare da sasu a jikin cinyarta tana hawaye.

  Jalal yace " tunda nake ban taba tunanin zan aureki ba ko a mafarki shiyasa nakejin abin kamar ba gaske ba."

  Seemah kam hawaye kawai takeyi, Jalal ya daure yace " Meemah zo nan."
A hankali ta d'ago ta kalleshi idanunta duk sun kumbura, hannu ya miko mata yace " please! "
  A hankali ta mik'e kamar wacce kwai ya fashema ta karasa kusa dashi, hannu yasa ya jawota jikinsa ya rungumeta, idanunsa sunyi jaa yace a hankali cikin kunnenta " Meemah dagaske ke matata ce? In mafarki ne banasan na farka in kuwa gaskene to lallai zan baki farincikin da zaisa hankalin Ammar ya kwanta ya kuma ji dadin had'in dayai."

  Kanta ta kara cusawa cikin kirjinsa mamaki take yanda wata zuciyar ke neman sanyata cikin wani shaukin dabai kamata tai ba a wannan lokacin.

  Sun dad'e sosai a haka, har Jalal bacci ya fara d'aukansa.

  Seemah dataji haka yasa ta barshi sai da barcin ya kamashi sannan ta zare jikinta a hankali, kallansa ta tsaya yi, a hankali takai hannu gefen fuskarsa ta shafa.

  Kasa d'auke hannunta tai daga fuskarsa, zuciyarta sai bugawa takeyi lalai tanasan Jalal itakanta ta sani to amma ya zatai? Haka zata amshi auren nan ta manta da hallacin Dad? Shiru tai tana tunani kala kala.

    

     Ta dad'e a haka ta fara kokarin mek'ewa taga ashe Jalal na rik'e da d'ayan hannunta.
   Kwantar da kanta tai saitin inda Jalal yake kwance, bata sani ba itama sai gani tai bacci ya d'auke ta.


   Can Jalal ya bud'e ido a hankali ya kalli Seemah dake kwance a saitinsa, kura mata ido yai yanajin wani shaukin santa na d'ebarsa.


   Murmushi yai sannan yace " Ammar anya ya kamata inbi abinda zuciyata ke raya min?  "

Bakinsa yakai saitin goshinta a hankali ya sumbata tare da lumshe idanunsa.

 





   © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*

JALALUDEEN 76

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com

   No. 7⃣6⃣


      Ammar na tura kofar yaga Jalal a kwance a kasa cikin kid'ima shida Zaid sukai mota dashi, asibiti suka wuce dashi hankalin Ammar yayi dubu gun tashi gani yake kamar shine sanadiyar wannan ciwon, suna zuwa asibiti akai emergency dashi,  Ammar ya tsaya a wajen dakin jiyake kamar yai ihu, Zaid ya kalleshi yace   " kazo likita nasan ganinka."

Ammar jiki a sanyaye ya karasa ciki, likitan yace " kaine Guardian dinsa?"
" eh, wani abun ne?"

Likitan yace " me kukeyi har jikinsa yakai haka? Ga bigewar dayai abayansa baizo anyi treating dinsa ba sannan ga rashin cin abinci dan da alama rabonsa da abinci tun jiya da rana, ga damuwa mai karfi dake ransa, so kuke ku kasheshi ko me?."

  Yai ajiyar zuciya sannan ya kalli Ammar wanda gaba daya abinduniya ya dameshi likitan ya daure ya dafashi, yace " ba komai zamu dubashi dakyai."

   Ammar ya kurama Jalal ido, nan likitan yasa akaja gadon Jalal akai wani dakin dashi, Ammar ya kalli Zaid yace " ka fito da wayarka?"
Mikamai Ammar yai yana cewa ya kamata asanar da su Zahee ko?
Ammar bai amsa mai ba ya danna number Dad.
" Ammar kana ina ne kawu na nemanka?"
Ammar cikin sanyin murya yace " Dad ina asibiti."

A zabure Dad ya mike yace   " kana asibiti kamar ya? Me a sameka? Ciwo kaji?"

Ammar ya girgiza kai kamar yana ganinshi yace " Dad kazo please, Jalal na kwace ba lafiya sosai."

Mamaki ne karara ya bayyana a fuskar Dad yace " inalilihi wa ina ilaihi raji'un, Ammar meya sami Jalal din?"

  Ammar dake kallan Jalal yace " Dad nidai kazo please. "
Dad yai ajiyar zuciya yace bari na zo.
Jiyai Ammar yace " kazo kai kadai please Dad."
Dad ya amsa tare da fitowa.

   Sunyi shiru, a inda Jalal ke kwance, Dad ya kalli Zaid yace " tsaya anan Ammar ina da magana dakai."

  Sun fita waje can gun da ba mutane sosai, Dad ya kalli Ammar yace " meya sameshi haka? Duk ya canza?"

  Hawaye ne suka dan gangaroma Ammar yasa hannu ya cire yace " Dad ya zanyi? It's all my fault. "

  Dad yai shiru yace   " Ammar!"
" Dad."
Yai maganar cikin wata murya, Dad yasan halin Ammar da tausayi dafashi kawai yai yace " kaje gida nizan tsaya anan."

  Kai Ammar ya girgiza yace " bazan iya tafiya ba Dad sai naga Jalal ya ware."
Kai Dad ya jinjina yace " to Ammar amma kaga dare yayi ga gobe karfe 10 za'a daura auren nan baka tunanin ya kamata kaje gida?"

  Ammar yai shiru, can yqce " Dad in Seemah tasan Jalal bashi da lafiya ya zatai? Balle intasan ciwon a dalilinta ne?"

  Dad ya kalleshi batare da yace komai ba, Ammar ya cigaba " Dad ya zatai?"
Kai dad ya juya yace " Ai ba fada mata za'ai ba."

  Ammar ya runtse ido sannan ya bud'esu idanunsa sun cika taf yace " Dad baka gani muna shiga hakkin ta?"
Da mamaki Dad yace " Ammar me kake nufi haka?"

   Ammar ya had'iyi wannan abun yace " Dad babban bakin cikina aduniyar nan bai wuce inga Seemah cikin damuwar da harzai kaita gayin kuka, amma Dad kasan kukan da nasa Seemah ta dalilin yaron nan? Sau nawa ina ganinta tana kuka akan abinda baifi karfina ba ko ince akan abinda nine xan iya daidaitashi, amma haka nake ganinta tana kukanta bana iya tab'uka komai saboda wani buri na zuciyata."

  Hawaye ne suka gangaro kumatunsa, ya kalli Dad yace " Dad nan!!!!"
  Dukan inda zuciyarsa yake yai, da karfi yace " nan gun Dad ni kadai nasan ya nakeji inaga Seemah na hawaye, sannan ina tuna Sadaukar da rayuwarsa da Jalal yai saboda Seemah, kanwarsa batada lafiya amma baije gunta ba......"

   Dad ya dafashi yace " Amma ai ita Seemah itama ta zab'eka."

  Ammar ya girgiza kai yace " tadai zabi farin cikin ka ne Dad, yarinyar nan bataso ko kadan taji tama abinda bazai faranta maka rai ba ciki kuwa harda sadaukarwa da farincikin rayuwarta, na sani zan kula da ita, ina santa kamar raina sai dai nasan inda zuciyarta take  , Seemah na bala'in sona amma son 'yan uwantaka takemin."

  Dad yai shiru sai dai jikinsa yayi mugun sanyi yakasa furta komai.
  Ammar yacigaba tare da share hawayensa yace " Dad duk farincikin da Seemah takeso nima inasan shi sai dai ina bakin cikin zuciyata tana neman canza min tunani na."

  Dad ya kalleshi, Ammar ya tsaida hawayensa yace " Dad na tsaida solution gobe auren nan da Jalal za'a daura bazan iya ganin abokina da kanwata danafiso a duniya cikin damuwa ba nikuma ina farin ciki ba."

  Kallan tsananin mamaki dad yamai yace " Ammar kasan me kake fada kuwa?"
  Murmushi Ammar yai wanda kana ganinsa kasan na bakin ciki ne yace " Dad ka taimaketa ne saboda son da kake ma mahaifiyarta da kaunar da kake ma yarinyar ko?"
Dad ya daga kai tare da cewa " hakane amma...."
Ammar yace " ka taimakesu ne saboda Allah na sani Dad."

  Dad yai shiru, Ammar ya cigaba " in har munaso ladanmu ya karfafa agun Allah mu bawa Jalal Seemah sai kaga Allah yakara daukaka mu ya kuma biya mana da mafificin gidan Aljanna."

   Dad ya kalli Ammar cikin tsananin kulawa yace " Ammar kaifa? Ni gani nake kamar sai kafi Jalal shiga wani hali in aka rabaku da Seemah."
  Kai ua girgiza yace " a'a dacan a matsayin kanwata take yanzu ma a haka zata zauna, na sani sanda nake mata ya wuce duk yanda kowa ke tunani amma tunda ni kadai nake santa haka banaji wani abun zai sameni."

    Dad kam kalaman Ammar sun ratsa jinin jikinsa, yace " shikenan Ammar."

  Murmushi Ammar yai yace " Dad dan Allah karmu fadawa kowa sai Abba kowa yaji a gidan bayan an daura in ba haka ba wani sai ya nemi canzama ra'ayinka."

   Dad ya dafa Ammar yace   " Ammar ka tabbata ba komai?"
Kai Ammar yadaga yace " marainiyar Allah itace first ni daga baya, sannan sai kamin addu'a Allah yabani wata."

   Rungumeshi Dad yai yace " Ina Alfahari dakai d'ana ka fahimtar dani abinda ban yi tunani ba, Jalal yaron kirki ne tun yana karami, naji dadi sosai da kaunar da kukema juna kuna yara ta dawo muku yanzu."

   Sun dade agun suna hira kafin su koma ciki, dad da Zaid suka koma gida.

   Washegari kowa ya tashi anata hidima, Seemah ta rasa dalilin dayasa gabanta keta faduwa, Ammar ta kira sai dai taji Junaid ya d'aga, tace " yaya Ammar fa?".

  Junaid ya kalli Zaid wanda yace Ammar yace kar afad'a mata inda yake, yace " yad'an fitane."

  Ta kashe wayar tare da d'an had'e rai.
 
Zaune suke a massallaci an fara add'uoi za'a daura aure.
  Abba zaune yayi shiru yana tunanin kalaman Dad, na jiya daddare, ajiyar zuciya yai alokacin da akace waliyin Jalal yaji dad yace " ganinan."

  Dad ya riga ya sanarda mahaifin Jalal wato Amadu nan yai farin cikin da hakan har kuka sai dayai.

   An dauren auren Junaid da Zahra,  Jalal da Seemah akan sadaki dubu d'ari wanda da kudin da za'a bada na Ammar ne.

  Mamakine ya kama 'yan uwan mahaifin Dad dana mahaifiyarsa, Habib ya kalli Dad cikin mamaki sai dai aikin gama ya gama.

    Zaid ne ya kira Ammar dake asibiti gun Jalal yace " Ammar an d'aura."

  Runtse idanunsa yai jiyake kamar yasa ihu, dakyar ya daure yace " ka fad'awa Seemah mijinta na asibiti ba lafiya."


   Zaid yace " Ammar inzo in daukeka?"
Ammar ya d'aga kai, Zaid ya daga kai tare da cewa " Jalal din ya farka?"

  Ammar ya girgiza kai yace   " a'a ko ido ya bud'e sai dai inga ya maidasu, sai dai likita yace abarshi ya huta stress sunmai yawa ga damuwa."

  Zaid ya d'aga kai.



  © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*

JALALUDEEN 75

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com

   _Ina kara godiya da jinjina gareku 'yan group d'ina na *Queen Bee* da kuma *Ayusher Fan Club* na gode kwarai da kaunar ku.......Allah yabarmu tare Ameen_

   No. 7⃣5⃣

     Jalal na tsaye jikin window yaji kiran Ammar daga wa yai yana tsokanarsa Ango da kanka?
Ammar ya kalli Seemah dake zaune a gefensa tayi shiru yace " ka fito ina wajen gidanka."
  Jalal yace " ok ganinan dama ina so muce wani guri dakai."
Ammar yana kashe wayar ya kalli Seemah datai shiru, yace " zaki kai minti nawa?"
  Kallansa tai idanunta suka dan canza kala tace  " ni kati kawai zan bashi sai sallama da godiya daxan mai sannan in bashi hakur....."

  Ammar jiyai zuciyarshi takasa jure wa ya kalleta hakan yasa tadan juya fuska tace   " kajirani anan yana fitowa zan fita minti 10 ma ya isa."

  Ammar baice komai ba ya juya ya kalli hanyar kofar da Jalal zai b'ulo, itama shiru tai tana tunanin anya ta kyautama Ya Ammar?
  Kallan inda Ammar yake kallo tai daga nesa ta hango Jalal ya fito, Jallabiya ce a jikinsa fara sai dai tamai kyau, ido ta kuramai gani tai kamar yanzu yafi da kyau jitai zuciyarta ta shiga bugawa ta kasa dauke idonta daga kanshi, Ammar daya juyo dan yi mata magana yaga yanda take kallan jalal jiyai wani kishi ya taso mai, haushin kanshi ya fara ji menene dalilinsa na barinta taga Jalal? Anya yasan me yakeyi kuwa?

Har Jalal ya kusa isowa motar, Ammar ya kalleta tare da daurewa yace " Ki sauka kije kinga cema Dad nai xamu anso dinkinki, kallan Ammar tayi tace  " yaya mu tafi kawai."

Da mamaki ya kalleta yace " kin fasa sallamar daban hakurin?"
Kallansa tai idanunta sun ciciko tace " Yaya banaji zan iya......"
Ammar zai yi magana kawai Jalal shikuma zuciya daya ya bud'e kofar inda Seemah take da tunanin zama a gun dan suje inda yace, glass d'in motar irin wace na ciki yana ganin na waje ne amma na waje baya ganin na ciki, ga mamakinsa Seemah ya gani zaune da sauri ya maida kofar ya rufe jikinshi a sanyaye, zuciyarshi ce ta fara bugawa da sauri.

  Juyawa yai kawai maimakon ya koma gida kawai ya kama tafiya, Ammar ne yabishi da kallon tausayi sannan yace " Seemah bazakije ba?"

  Jiki a sanyaye ta bud'e kofar, dan tunda suka hada ido da Jalal taji gaba daya jikinsa ya kama rawa ta fita tare da kallan Jalal daya tsallaka titi kamar ta kula kawai tafiya yake hakan yasa ko Ammar bata sakema magana ba balle ta rufe kofar tai gunsa da sauri.

  Sam hankalinta nakan Jalal, So take ta tsayar dashi gashi batasan ya zatai ba, Ammar na jingine a mota yana kallanta, tazo tsallaka titi wani mai babur ya taho a guje, karar da Ammar yai na kiran sunanta yasa Jalal juyowa, da gudu ya taho gunta, itakam sam hankalinta nakan Jalal ganin ya nufota da gudu yasa ta tsaya cak, ta manta sam a titi take.

  Saura kiris mai babur yai gaba da ita Jalal ya fuzgota, yai baka tim, Tsoro ne ya kamata, ta dago cikin firgice, tare da fara jijiga Jalal, hawaye sai malala suke tana kuja tana kiran Deen! Deen.

  Ammar ma daya taho da gudu yai turus ganin Jalal a kasa, ganin yanda Seemah take kuka yasa hankalinsa ya dawo, matsowa yai tare da cewa " Jalal!"
Ido Jalal ya bud'e tare da kallan Ammar yace " Ammar dan  taimaka ka tayani na mik'e."

  Seemah ce ta kalleshi cikin mamaki au dama yana jinta? Mik'ewa tai tare da fara goge hawayenta, tace " Ya Ammar kacemai mu tafi asibiti a dubashi."
Mamaki ne ya kama Jalal, bai kalleta ba shima ya kalli Ammar daya mikamai hannu ya kama sannan yace " Ammar kacema matarka basai naje asibiti ba."

  Ammar ya karasa dagashi tare da kallan Seema sannan ya kalli jalal yace " ni ba sakon wanda zan isar, Amma Jalal ka tabbata zaka iya tafiya?"
Jalal ya dan cizi leb'ensa kadan yace " karka damu z......"
Seemah ce ta katseshi da kallan Ammar tace " Yaya a'a mu kaishi asibiti please kaga saboda nine."

  Jalal bai kalleta ba yace " nace bazani ba, gida zan koma."

  Seemah kam daurewa tai ta matso daf da Jalal sun kusa isa mota, tace "kalleni."

Jalal yaki kallanta,  ta kalli Ammar sannan ta kara cema Jalal " Deen please. ..."
    Jin yanda tai maganar yasa Jalal ya kalleta a sanyaye tace " Deen muje asibiti please. "

Ammar kam da tundaga faduwar Jalal yasa duk jikinsa yai sanyi, ya kalli Jalal yace  " Jalal muje asibiti a dubaka inba sokake hankalinmu yaki kwanciya ba."

  Jalal bai magana ba har suka karasa motar, Seemah da sauri ta bud'emai gaba, ya kalli Ammar yace " A baya zan zauna."

Jiki a sanyaye Seemah ta maida kofar ta rufe tare da bud'ema Jalal baya, Ammar ne yataimaka mai ya shiga, gyambon dayake fatan ya warke shine ya mik'e shikadai yasan meyakeji ganin Seemah a kusa dashi kuma wai ankusa bikinta, jiyai kamar ya dauketa su gudu,  hakan yasa bayasan kallanta bare yimata magana saboda shikadai yasan meke ranshi.

  Sun fara tafiya Seemah dai a zaune kawaj take sai dai akai akai tana goge hawayenta, Ammar yai shiru a mota kawai tuki yake, sai taimakon Seemah da Jalal yai shi kuma ya buge, ga Seemah tun dataga Jalal ya buge take kukan nan , wani irin so Jalal kema Seemah?

Tambayar dayake nanatawa a zuciyar sa kenan har suka isa asibitin, bayan yaga likita nan akasa a mai X ray.

  Seemah tai shiru a wajen dakin daya shiga tana tuno yanda Jalal ya buge,  Ammar kam yana gurin likita, Jalal na fitowa ya dan tsaya a jikin kofa yana kallan Seemah batare data sani ba, jin kamar ana kallanta yasa ta juya, da sauri Jalal ya dauke idansa tare da cewa " Ammar fa?"

Seemah ta mik'e tsaye  tace " ba dai wani abun ko? Ba dai wani abun ko?"

Kallanta Jalal yai zuciyarshi ta kara karyewa, a hankali yace " kar ki damu ba wani abun."
Ta matso kusa dashi tace " Deen meyasa d'azu zaka taimakamin? Kana tunanin zanfi farin ciki ne in ni banji ciwo ba kaikuma ka ji?"

Kallanta Jalal kawai yake cikin wani yanayi, ta share hawayenta tace " me yasa baka barni ba? Kasan yanda nakeji kuwa ganinka cikin wannan yanayi a maimakona?"

  Jalal ya d'auke idansa tare da daurewa yace " ko waye ma naganshi cikin wannan yanayi zan taimaka mai, ya wuceta zai wuce, sai dai tsayawa yai cak ganin Ammar ya juya baya, da alama ya gansu tarene yasa ya juya baya, Jalal na kallansa ya gangara yai wata hanyar.

Tausayin kansu ne ya kamashi, me yasa zuciyarsu zataso mutum daya? Why?

Muryar Seemah yaji kamar tasan me yake cewa tace " Deen ka taba tunanin ya nakeji a cikin raina? How can u walk away from me bayan kana ganin waye ya kawoni dan inma sallama? Meyasa zuciyarka bata tunanin halin danake ciki?"

   A hankali Jalal ya juyo idanunsa sunyi jaa sosai kamar masu shirin kawo ruwa cikin raunanniyar murya yace " Meemah I am okay! Kije gun Ammar I think shine yake bukatarki."

  Kallansa tai jiki a sanyaye tace " bam gane ba."

  Ya kalleta da raunannan idanunsa yace " ta ya ma zakisa Ammar ya kawoki nan? Me yasa bakya duba halin dazai shiga? "

  Jiki a sanyaye ta kalleshi,  Jalal ya juya kamar zai tafi da sauri tace " I am Scared."
Cak ya tsaya batare da ya juyaba, ta cigaba " zuciyata na tsoron kar inyi aure ba tare da na ganka ba."

  Jalal ya juyo ya kasa kuma danne abinda ke ransa, cikin wata irin murya yace " what about me?"
  Cikin tsananin mamaki ta kalleshi, yace " kinsan halin da nake ciki me zai sa kizo gurina ki nemi tada min hankali dayawa? Meemah kin dauka ni basan ganinki nake ba?"

Yai ajiyar zuciya tare da girgiza kai yace " noo."
Kawai banaso ran mutane dayawa ya b'acine ta sana diyyar mu."

  Ya danyi hucci kadan sannan ya juya ya fara tafiya, kuka Seenah ta cigaba dayi, tun tana kallansa har ya bace mata.

  Jalal kam gate kawai ya wuce ya tari babur yahau.

Sai text yama Ammar akan yaje ya dauki Seemah shi ya wuce gida, karya damu buguwar batai karfi ba.

  Ammar na ganin sakon ya taho gun da sauri, a tsugunne yaga Seemah tana kuka wiwi, tsayawa yai daga nesa kawai yana kallanta zuciyarsa sai kuna take, ba abinda ya tsana irin hawayen Seemah.

Sai data gama sannan yaje ya mikar da ita suka wuce gida.

  Jalal kam da yamma yaje gun Abdul, rokansa Abdul yai akan yana san ganin Seemah.

Jalal ya fadamai zai sa Ammar ya kawota duk da yasan ba lalai tazo ba.
Jalal duk ya canza da ya dade bai ga Seemah ba amma yanzu tunda ya ganta yaji hankalinsa yaki kwanciya jiyake kamar yafi santa yanzu ma.

Haka Seemah tun bayan sun rabu da Jalal ta zama maman shiru,  tsakaninta da kowa a gidan bai wuce gaisuwa sai eh da a'a.

  Ammar kam shima ya shiga wani yanayi balle tunda yaga Seemah ta canza gaba daya, Jalal ya sanar dashi Abdul na nemanta amma daya sanar da Dad yace " ya bari sai andaura aure sai suje tare."


   Duk abinda akasama rana tofa lalai zaizo da sauri, yau gashi ta kama ranar alhamis ranar kamu kenan, hidima kam sai yinta akeyi, kowa ka kalla yana cikin farin ciki yake.

Jalal kam yau da zazzabi ma yatashi a jikinsa, a kwance yake tun dare gashi ba kowa a gidan shikuma baisan kiran ko Sagir ne, Seemah ma kawai yake takeyi dan batasan Dad da Ammar su gane.
Sai dai Ammar tun da suka bargun Jalal yasan halin datake ciki.

  Anyi kamu na gani na fada a gidan Abba, Amarya Zahra da Seemah ansha kyau, haka aka gama taru lafiya sai kuma washe gari daurin aure.

  Ammar na kwance a d'aki yana kallan number  Jalal ya dade kafin ya daure da kirashi, sai dai duk yanda ya kira Jalal bai daga ba ya kalli agoggon bango na dakin karfe takwas na dare, yasan tabbas baiyi bacci yanzu ba.

  Ya dade yana kiran Jalal sai dai duk da haka bai daga ba, kallan Zaid yai dake faman waya da Zaheeda yai dan bugemai kafada yace " tashi muje gun Jalal."

Zaid ya cema Zahi yana zuwa sannan ya kalli Ammar yace   " ban gane ba."
  Ammar yace  Jalal yaki daukan waya inaji ba lafiya ba.

  Nan yai waje tare da cewa " Zaid ka biyoni muje."

  Sunje gida  sukaita kwankwasawa, Jalal dakyar ya mik'e dan tun dafe ba abinda yaci ga zazzabi mai zafi dake damunsa......

  Yana bude kofar ya fadi kasa.......





©    *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*

��‍♀

Wednesday, 1 March 2017

JALALUDEEN 74

JÅĹÀĹÙĎĚĚN




Na AYUSHER MUHD

ayushermohd.blogspot.com

  _Ina bawa masoyana hakuri najina shiru da kukai, kuyi hakuri amma insha Allahu zanyi kokarin ganin na kammala littafinan acikin satinnan, nagode kwarai da san da kukema littafin nan....Luv U Ol ❤_

   No.7⃣4⃣


      Abdul zaune yana kallan uwargidansa kallan tsananin mamaki yace  " Rabi kinsan me kike fada kuwa? Ban gani in sakeki ba ina cikin wannan yanayin ba?"

  Wata dariyar rainin hankali tamai tace " me? Kana tunanin soyayya ce tasa na aureka?"
Tai wata dariyar rainin hankali tace " are you naive or fool? Kai kana tunanin duk mutanen dake kusa dakai saboda suna sanka ne ko suna san kudinka? "

  Abdul cikin mamaki ta kalleta yace " Rabi da kikazo na dauka abu na farko da zaki fara tambaya shine meya faru a shekara 20 din? Da gaskene? Sannan ki tambayeni halin da nake ciki a gidan yarin nan amma......"
Katseshi tai cikin fada tace " so kake inzauna ka fadamin wani shirme dakai a baya? Ko ce maka akai na damu da halin da kake ciki? Takardata nake bukata dumin inasan barin kasar nan cikin gaggawa kafin laifinka ya fara kokarin shafata."

  Abdul ya kalleta cikin tsananin mamaki yace " me ne? 'Ya'yan mu fa? Ko kin manta da 'ya'ya a tsakanin mu?"

    Rabi ta saki wata dariya taban haushin mai sauraro tace " 'ya'ya? Ahh haka ne ashefa kai baka sani ba ko? Amma ina mamakin ina hankalinka yake, sai dai kayi hakuri 'ya 'ya nawa ne ba ka da hadi dasu."

  Abdul cikin mamaki yace " me kike nufi nufi da kalamanki? "
Tai tsaki tace " malam inka ga dama ka saken in bakaga dama ba kai ta ajiye da sakinka zan koma dubai da abokinka Marfuz wato uban 'ya'yana inka ga dama ka aiko mana da takardar saki can." Tana kainan ta mike, cikin zafin rai ya riko hannunta yace " marfuz? Abokina? Me kike nufi?"

Hannu tasa ta fizge hannunta da karfin gaske tace " matsalarkace, tana kaiwa nan tai waje."

  Kai ya shiga girgizawa ya tuna shine sanadiyar arzikin marfuz kuma shine abokinsa da ya dinga zigashi akan abubuwa marasa kyau ciki kuwa harda fyad'en dayama fatima.
Ihu yasa cikin tsananin takaici ya rike zuciyarsa dake kuna tare da tsugunnawa a kasa, lalai kuka ma rahama ne, jiyai sam ya kasa kuka, sai wani irin zafi da zuciyarsa keyi.

  Guard din dake bakin kofa ya kalla yace " dan Allah......."
Ai bai karasa ba yaji numfashinsa ya rike, nan guard din ya matso da sauri ya shiga danna mai baya, dakyar numfashinsa ya dawo.

  Abdul sam ya kasa cin komai, a zaune kawai yake shikadai yasan me yakeji.

   Jalal kam ya zama celebrity a gari ko ina ka duba kaga hutunshi a magazine ko a jarida ansa Jarumin da baya tsoron hukuma sai gaskiya, duk shirin dayace zaiyi kuwa a gidan tv to lalai zakaga mutane sun zako akan ganin me jarumi kuma matashi zak gabatar.

  Biki ya matso, sai dai Zahra ce kadai take shirin bikin amma sam Seemah batasa baki a harkar in Zahra tazo mata da xancen ya zasuyi kaza, kya kacinta kawai tace to, dama ba fita take ba inba gidan Ya Habib taje ba, yau saura sati daya biki, gida ya fara cika, hakan yasa yau Seemah ta tattara kayanta kamar yanda Dad yace akan ta koma gidansa saboda matarsa tazo itama, ta gana cikin gada kayantane ta ci karo da agoggon ta kurama agoggon ido tai nan fa ta fara tunano rayuwarsu ita da Jalal, kallan agoggon take ta kuma zarfafa cikin tunani, Ammar dake tsaye a jikin kofa ya taho da saurinsa zai nuna mata katin biki na dinner daya amso, ganinta a zaune tasa a goggo tana kallo yasa ya tsaya, hannu a harde tare da jingina da jikin kofar, basai Seemah ta fadamai ba yasan agoggon da take kallo me yake nufi dan kuwa agoggon dake hannun Jalal kenan kullum, ya kuma gansu iri daya sak, jiki a sanyaye ya juya harzai fita sai kuma ya fasa ya koma ya tsaya tare da cewa " Kanwata ko in juya ne?"
  Kallansa tai da sauri tare da juyawa ta goge hawayenta ta mike tace " yaya yaushe kazo?"

Ammar yadan hade rai kadan yace " nafi awa biyu fa anan."
Cikin tsananin mamaki ta kalleshi tace " da gaske? "
  Dariya yai yace " lalai taya za'ai ki yarda?"

Harararsa tai tace " Yaya wato dai kai na kula inba tsokanata kaiba sam bakajin dadi ko? "

  Shiga ciki yai kusa da ita ya tsugunna kasa ya dauko agoggon data yar tana saurin mikewa, kallan agoggon yai sannan ya mike tare da mika mata, kallansa tai batare da ta amsa ba, kallanta ya sakeyi yace " amsa mana nasan abune mai mahimmanci a gunki."

  Kallansa tai tareda shan jinin jikinta tace " Yaya ba......"
Murmushi ya mata yace " ansa mana."
Hannu tasa cikin sanyin jiki ta amsa, yace " me? Kinaso ki mai sallama ne kafin biki?"

  Kallansa tai cikin tsananin mamaki, da sauri ta juyamai baya tace " bafa haka bane yaya, kawai ganin agoggon nai."

  Ya dawo gabanta tare da daga kai yace " nasani Seemah nasan komai hakan ne yasa banaso kidinga boyemin komai, nine na tambaye ki bawai ke kika tambayeni ba."

  Idannunta ne suka ciciko ta girgiza kai tare da cewa " how can I......?"

" I am okay!" Ya fad'a yana kallanta, tai kasa dakai, yace " banaso ki dinga tunanin bakimai sallama ba..."
   Ganin tayi kasa dakai ya juya tare da cewa " in bakyaso shikenan."
Yana fada ya juya kamar zai wuce, jiyai ta riko hannunsa ta baya, ya tsaya batare da ya juya ba, duk da kishin dake damunsa amma bayaso yaganta cikin wannan halin saboda shi.
  A hankali  Seemah tace " Yaya zan iya?"
  Bai juyo ba ya daga mata kai tare da daurewa yace " banine na ce ba?"
Ta goge hawayen ta da d'aya hannun tace " yaya zan mai sallama tare da ajiye duk wani ragowar abu dake zuciyata, bazan sake tunaninsa ba bare insa ka kaji ba dadi ba."

  Ammar ya daure ya juyo ya kalleta tare da mata Murmushi yace " karki damu Kanwata farincikina bai wuce naganki kina farinciki karki damu dani farincikina na tattare dake."

  Yai ajiyar zuciya tare da cewa " in har kinaso ki ganni ina farinciki to ke zan jira kiyi farinciki kafin ni."

  Seemah ta share kwallarta jikinta yai mugun sanyin, tausayin Ammar ya kara shigar mata zuciya, zare hannunsa yai yace " kishirya in ajiyeki, in yaso sai ya dawo dake."

Yana kainan ya fita, kallon tsananin tausayi ta bishi dashi, zama tai a gun tare da runtse ido tace " Seemah meke damunki? Taya zakice zakije bayan kinsan koyace kije dolene yaji haushi?"

  Ta dade a zaune kafin Ammar ya kirata yace tafito yana jiranta.

   Jalal kam zauje yake a dan karamin gidan daya kama, saboda ya sai gida babba yanzu a kaduna inda Umma da kuma matarsa Zainab suke zaune acan, Zahida kam itama jiki ya fara sauki sosai Zaid kam kusan duk karshen sati sai yaje, tun  Zaheeda na wase wa harta fara saki gashi ba laifi yanzu tana iya takawa kadan kadan inta rike sanda.

  Takardu ya gama dubawa sannan ya mike danjin yunwa ta fara kamashi, kallan calendar dakinsa yai ya zagaye wata number da jan biro, karasawa yai jikin calender yace " saura 7 days?"
  Ajiyar zuciya yai sannan ya kalli wayarsa dayaji tayi kara alamar text, dagata yai yaga sako ne ga mamakinsa daga police station ne, wai Abdul na nemansa, yataimaka ya ziyarceshi."

Wata iska ya furzar yace a fili " Allah yasa ya daidaita tunaninsa akan 'yarsa."

  Window ya zuge ya kurama titi ido, yaushe rabansa da Seemah?
Kai ya girgiza tare da cewa " Ahhhh...."




© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*



��‍♀