Thursday, 29 June 2017

ZUCIYA.....kowa da irin tasa 35

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*Wattpad As_AyusherMohd*

{ *35*}

   Yanda yake kallanta yasa ta had'e rai tare da maida kallanta wajen window,  itakam batasan me zata cemai ba, ana san kashe ka? Kuma 'yan uwanka?? Itakam kalaman nan sun mata tsauri.

  Ga mamakinta jitai yace " tunda karyar ciwo kikai yanzu ai sai ki koma gida."

  Nafi ta kalleshi a tsorace tace " Sauka zanyi a haka??"
Kai ya d'aga mata alamar yes, idanunta ne sukai rau rau ta kalleshi sannan tace " taya zan iya fita ahaka komayafi fa babu a jikina, sannan bani da kud'in da zan tafi da kaina."

   Ya d'aga mata kafad'a alamar wannan kuma ruwanta ne, Nafi ranta ya b'aci a zuciye ta matsa da niyyar bud'e kofa, har ta zura kafa d'aya zata fita sai taji yace " shigo in ajiyeki ba dan halinki ba inada abinyi."

  Ta koma ta zauna kamar ba taso sai dai ko kallan inda yake batai ba, Ashraf ya tada mota zuciyarsa fal da tunani, har suka isa gida ba wanda ya sake magana, yana parking ta bud'e kofa zata fita sai kuma ta juyo tace " Yaya ina zaka?"

  Kallanta yai yace " banaji wannan yana d'aya daga cikin damuwarki tunda dai baki fad'amin me kike nufi da kar inje aiki ba, kin kuma san halina ba a sani abu."

  Nafi ta kalleshi cikin kulawa tace " Yaya tunda kaga na furta hakan ai kasan da dalili, in ba haka ba meye nawa da zance karkaje aikinka?ni ba matarka ba?"

  Juyowa yai ya kalleta kalamanta na karshe sun tsayamai a wuya, sai dai ya share yace " ke nake jira zan fita ko?"

  Nafi batasan sanda wani takaici ya kamata ba ta kafeshi da ido na takaici, kallanta yai sannan ya juya ya d'au wayarsa, bakin ciki ya hanata d'auke idanunsa daga kansa jitai ya tada mota, alamar zan tafi, takaici yasata ta fito daga motar a zuciye tana kallo yaja motarsa ya tafi, tabi motar da kallan takaici.

  Wannan wani irin mutum ne, duk yanda na damu da rayuwarsa amma shi ko a jikinsa?? Sai ma rashin mutunci ne zai biyo baya?.
  Sam ta kasa d'auke idanunta daga hanyar daya wuce, jitai an dafa ta a firgice ta juyo, Mumy ta gani tsaye itada Little.

   Nafi tai saurin share kwallarta sannan ta kakaro murmushi tace " Mumy ina kwana???" tafad'a tare da risinawa, mumy ta amsa sannan tace " Nafi me kike yi anan? Little duk ta damu tanata nemanki?"

  Nafi ta kalli Little sannan tai murmushi tace " Ayya My Sisto tuba nake."

Little ta harareta sannan ta juya tai b'angarensu, Mumy ta kalli Nafi databi bayan Little da kallo tace " Nafisa ina kika je???"
  Nafi tai kasa dakai, Mumy tai murmushi sannan tace " shikenan, kije gun 'yar uwar taki dan hankalinta ya tashi."

  Nafi ta d'aga kai sannan tai bayan Little da sauri.

A tsaye ta ga Little ta cire kaya daga ita sai towel da alama wanka zata shiga, Nafi ta karasa gunta ta zauna akan gado tana kallan Little wacce ta had'e rai.
  Nafi tai murmushi tace " Little bazaki kulani ba?"
Little ta juya tai hanyar toilet, tanaji Nafi ta kara cewa " My Sisto tuba nake kinji kiyi hakuri."

   Little ta wuce toilet ba tare da ta amsa mata ba, nan Nafi ta mik'e ta gyara d'akinsu ta gama shara kenan Little ta fito, Nafi ta kalleta zatai magana taji Little tace " ki je kiyi wanka Yusra tun d'azu take kira wai dan Allah muje yanzu."

  Nafi ta mike ta karaso gun Little ta rungumeta tare da cewa " Little wlh wani abu ne ya taso min dayai gaba da duk tunanina."
  Little tace " Shikenan Feena ni kin barni anan cikin tsoro tunda na tashi naga banganki ba na kuma fita kaf na zaga ban ganki ba."

  Nafi tace " Sry nayi laifi."
Murmushi sukama junansu, nan Nafi ta saketa sannan itama tasa nata towel d'in ta nufi toilet, har taje zata bud'e kofar ta juyo tace " Little nikam a iya sanina ba wata matsala dake tsakanin Mumy da Umma ko?"

  Little ta kalli Nafi tace " Feena kenan, a haka dai kamar babu, sai dai inaji a jikina kamar da wani abu."

  Nafi ta kalleta tace " kamar me??"

  Little ta d'an tab'e baki tace " kinsan a duniya in har akace kud'i to fa an gama komai, kud'i da kike ganinsu sune matsalolin komai na rayuwar duniyar nan, duk wata matsala inka dubashi daga kasa to fa lalai zakiga kud'i shine silar komai."

  Nafi ta shiru tana mamaki, can tace " Amma dai nan banaji za'ai fad'a akan kud'i ko? tunda dai naga kowa yanada shi."

  Little ta furzar da iska sannan tace " Feena kenan ai a gidan da ake da kud'in anfi samun matsala akan kud'in tun balle in dukiyar da mai ita."

   Nafi ta mata kallan mamaki, Little tai murmushi sannan tace " share kawai."

  Jiki a sanyaye Nafi ta shiga wanka, sam wanka take amma tanata nanata kalaman Little dukiyar da mai ita? Kawu kenan? To in shine meye na neman kashe Ya Ashraf?"

  Ta dad'e kafin ta fito, tana fitowa taga Little ta ciro musu dinkin Less anko ne shima, Nafi ta zauna itama ta fara shafe shafe.

   A b'angaren Ashraf kuwa yana fita daga gidan ya nufi gidan abokin babansa ko ince lawyer d'in babansa, bayan sun gaisa yace " dama so yake ya d'auki mota d'aya daga cikin motocinsa dake gidan.

  Nan ya d'auko masa keys d'in Ashraf ya d'au d'aya sannan sukai sallama ya fita.

   Hanyar Company d'insu ya nufa, yasha kwanar karshe ya hango wasu mutane kusan su goma a cikin wata katuwar mota baka kirin sai dai sun sauke glass d'in motar sannan wasu sun zuro kansu suna duba hanya, bakaken kaya garesu haka kuma baza'a ganesu ba saboda tabarau baki dake fuskarsu.

   Ashraf ya rage gudu dayazo kusa dasu, sam sukam sun d'auke kai daga kallan motarsa ganin ba irin ta bace wanda aka basu umarni.
Hakan ya bashi damar ganin yawan mutanen dake ciki, sannan ya wuce, lalai ya tabbatar shi suke nema saboda yazo giftawa yaji wani yace "wai ya haryanxu banga mota kirar Marcedes_Benz C300, wai ya tabbatar nan zai biyo??"

  Ashraf ya giftasu zuciyarsa fal da mamaki, meke faruwa? Me Nafeesa ta sani? Me taji????

   Ya karasa gun aikinsu nan ya tadda 'yan team d'insa sun dad'e da zuwa, nan ya zauns suka fara abinda ya kawo su.

   Su Nafi ansha  kwalliya, suna fitowa Habib na yin parking, tundaga nesa Little ta hangoshi ta saki wani lalausan murmushi na farinciki, Nafi ta kalleta sannn ta kalli inda take kallo ganin Ya Habib yasa tai murmushi itama tace " Little a dinga kokarin dannewa irin wannan nuna soyayya kirikiri haka??"

  Little ta harareta sannan tace " haka nace miki?"
Nafi ta d'an rangwad'a kai tace " Little kenan."

   Juyowa yai shima ya hangosu, nan ya tsaya tare da kurawa Nafi ido, gaskiya yarinyar nan type d'insa ce ba karya, har suka iso gun yana kallanta, Nafi ta d'an had'e fuska tare da kawar dakai ge.

   Little ta matsa gunsa tace " Ya Habib daga ina haka?"

  Idanunsa nakan Nafi yace " wlh wucewa nazo yi shine na shigo."

   Little ta kalli Nafi dan taga yanda yake kallanta, sai dai bata kawo wani abu ba tace" Nafi tayi kyau ko yaya?"

  Habib yai murmushi yace " Sosai ma kuwa."

  Nafi ta matsa daga saitinsa sannan tace " inafa wani kyau dan kowa yaganki yasan kece kikai kyau."

  Ta fad'a tare da cewa " Ya Habib ko ba haka ba?"
Ya kalli Little kunya tad'an kamashi yai wani murmushin burin kunya yace " dama ai Princess daban ce."

  Little ta saki murmushin farin ciki.

   Little ta kaleshi cikin kauna tace " Ya Habib yaushe zaka tafi?" yace " zuwa la'assar dan inasan ganin Ashraf."

  Kai little ta d'aga tace "Allah yasa mu dawo mu sameka."

   Yace Ameen tare da satar kallan Nafi.

  Nan sukamai sallama suka shiga motar Little sukai gaba.

Su Umma kam da Asim suna zaune a falo suna jiran good news tunda sunga fitarsa daga gidan da motar mercedes wanda hakan yasa Asim ya sanar dasu sunan motar da number ta, sai dai jin shiru har shad'aya ba labari yasa Asim ya kira, sun sanar dashi har yanzu motar bata wuce ba, nan suka kara jinkirtawa zuwa azahar, nan ma akace motar bata wuce ba, cikin takaici Asim ya kira wani ma'aikacinsu na company ya tambayeshi Ashraf yazo? Ga mamakinsa jiyai ance tun d'azu yana nan.

  Haushi da takaici suka turnukeshi ya kirasu ya hau su da fad'a sannan yace " su tafi daga gun kafin ma a zargi wani abun.?"




   *THE INNOCENT TEAM*

Wednesday, 28 June 2017

Zuciya....kowa da irin tasa 34

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

*na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*Wattpad As_AyusherMohd*
*Dukan Godiya ta tabbata ga Allah Subhanahu Wata'ala, muna kara godiya gareshi da ya nuna mana watan Ramadan lafiya yasa mukai ibadun mu lafiya, sai fatan Allah ubangiji ya karbi ibadun mu...(Ameen)*
    *Inama dukan d'okacin masoyana barka da sallah da kuma fatan alkairi a ko ina suke...*
  Allah Ubangiji ya Maimaita mana Ameen..

{ *34*}

Umma ta juya cikin takaici da niyyar lalai sai ta sa a kori yarinyar nan kafin ta zamar musu masifa.

  Nafi kam har tayi gaba ta tsaya tare da juyowa tabi Umma da kallo, kai ta girgiza ta juya zata wuce ta hango Asim ya nufo Umma da sauri kamar zai fad'i da kasa, kallan yanda yake baza sauri take da alama akwai magana da yake san isarwa cikin gaggawa shi yasa yake wannan saurin.
  Umma tana hangoshi da ganin yanayinsa yasa tai hanyar b'angarenta da sauri itama, Nafi har ta juya zata koma d'aki taji sam hankalinta ya kasa kwanciya, a hankali ta tako tazo wajen b'angaren Umma sai dai ta rasa tayayya zatai karyar da zata shiga?
   Shiru tai ganin ba halin shigan yasa ta juya da niyyar komawa, Asabe mai aiki a kitchen ta hango ta nufo gun rike da tire babba da kuloli akai, Nafi ta karasa gunta da sauri tace " Asabe ina zuwa?"
  Asabe tace " Umma zan kaima kumallon ta."
Nafi ta amshi tiren tace " Barshi ni bari na kaimata dama ciki zan shiga."

  Cikin rashin damuwa Asabe ta bata tare da kad'a kanta ta koma inda ta fito, Nafi kam da sauri ta nufi kofar Umma, gabanta kam sai dukan uku uku yake saboda tsoro sai dai ta rasa dalilin dayasa zuciyarta keta tunzurata akan lalai ta shiga.

   Murd'a kofar tai a hankali ta shiga da sallaha itama ciki ciki tayi ta.
Batai mamaki ba dan dama batasa a ranta za ta gansu a falo ba, nan ta wuce cikin tsoro ta ajiye tiren akan dinning sannan ta kalli d'akunan dake falon guda biyu, a ina suke???abinda ta fad'a kenan a ranta.

   Lalab'awa tai ta karasa d'akin farko,tare da sa kanta a jikin kofar kamar munafuka, jin alamun rashin mutum yasa ta karasa d'ayan, zuciyarta sai kara tsananta take da fad'uwa wannan karan bata sa kanta a kofa ba tana zuwa jikin kofar d'akin taji cikin fad'a wanda yasa ta tsorata taji Muryar Asim yace " Umma nikam bakin ciki kasheni zai yi dan nikam indai har na cigaba da ganin Ashraf to fa lalai inaji ni zan bar gidan nan."

  Gaban Nafi ne ya yanke ya fad'i me kenan? Ta fad'a a ranta.
Kafin ta nemo amsar tambayarta taji Umma tace " ni d'in ce maka akai farin ciki nake in na ganshi? To amma ya zakayi....???"
Cikin fad'a Asim ya katse Umma da cewa " Yanzu sam 'yan gun aikinmu basa karramani magana ma ba yimin suke ba, sannan yanzun nan abokina na gun aiki ya sanar dani cewa shareholders na company d'in sun yi meeting akan a dawo da Ashraf matsayina inyaso ni sai a ragemin matsayi, nifa wlh in bakuyi wasa ba zanyi aika aika."

  Umma ta gyara zama tace "Asim kayi hakuri abi maaganar nan a hankali."

  Cikin zafin rai yace. " a hankalin me? Ni wlh har yan daba na kira kafin nazo nan na sanar dasu  inya fito aiki anjima su tareshi su kawar mun da numfashinsa."

   Jikin Nafi kam rawa kawai yakeyi, har tsuma takeyi saboda tsananin tsoro da fargabar abinda yau kunenta yake jiye mata.
  A tsorace ta juya cikin tsananin tsoro da firgici tai waje har kafarta na hard'ewa ta fad'i kasa.
  A d'aki kam Umma ta kalli Asim tace " Asim yau lahadi naga ba aiki?"

  Asim yai wani murmushi yace " ai shi zai je saboda akwai wani project da sukeyi shi da 'yan team d'insa."

  Umma tai ajiyar zuciya sannan tace " baka ganin anyi gaggawa in aka mai illa tun yanzu? Asim yai tsaki yace " Illar me? Shima Abban ai yafi kowa san Ashraf ya mutu."

  Umma ta jinjina kai sannan tace " Aneesa fa?"
  Asim ya kara jan tsaki yace " kyale wannan in ya mutu taji ta cafki dukiyaa a hannu kina ganin zata damu?"

  Umma tai murmushi sannan tace " duk da Neesa na tsananin san Ashraf banaji tana sansa kamar yanda takesan kudinsa dan na tabbata da bashida komai duk sanda takemai bazata tab'a aurensa ba."

  Asim yai kwafa yace " Ni wlh na tsani ma na gansu tare, nifa inaji duk duniyarnan ba wanda na tsana kamar yaran nan."

Umma ma tai tsaki tace " ai nima dashi da uwarsa sune mutanen dana tsana kaf duniyar nan."

  Nan suka zauna suka cigaba da sake sakensu.

  Nafi kam dakyar takai kanta falon b'angarensu, ta zauna akan kujera har yanzu jikinta rawa yake, sam kwakwalwarta ta kasa d'aukan abinda ta jiyoma kanta.

  Dif taji kwakwalwarta ta d'auke sam bata tunanin komai sai da wasu dakiku suka shud'e sannan taja wani dogon numfashi sannan ta mike a zabure tace " Ya Ashraf????"
  Jitai idanunta sun kawo kwalla ace d'an uwanka na jini???wannan wace irin rayuwace???? Sanar dashi zatai?? Zai yarda da abinda zata fad'a??ko Little zata fad'ama??kai ta girgiza tace"kar itama in tada mata hankali..."

  Wata zuciyar tace Mumy fa???kai ta girgiza da sauri tace " Mumy kuma da wani idan zata zauna dasu??"

  Kanta ta dafa dataji ya sara, can tace " Kawu fa???"

  Hucci ta saki cikin damuwa tace " shikuma matarsa ce da d'ansa."

  Kan kujera ta fad'a wasu hawayen suka sake zubo mata, Ya Ashraf me kai ake neman halakamin kai???ta fad'a cikin wata irin murya mai ban tausayi.

  Agoggon  bango ta kalla karfe tara, karfa Ya Ashraf ya fita??? Da sauri ta mike kawai ta nufi b'angarensa, hankalinta bai tsaya ba sai da ta isa kofar b'angarensa, me zata cemai??? Shiru tai ta tsaya agun kamar abu mara motsi, dan batada amsar tambayar nan.

  Tana tsaye ba mafita har dakika goma suka shud'e, motsin bud'e kofa ne yasa ta dawo hayyacinta, idanunta ne suka firfito cikin tsoro, ta kalli kofar.

  Ashraf ne ya fito, jitai gabanta ya fad'i cikin mamaki ya kalleta, sai dai kafin yai magana sai ga Aneesa ta fito rike da jakarsa, fuskarnan tata a had'e da alama ranta a b'ace yake.

  Cikin mamaki itama ta kalli Nafi, "Malama wacce ce ke? Me kuma kike anan?"
 
  Nafi ta had'iye yawo cikin tsoro ta kalli Ashraf, shima kallan mamaki yake mata, Aneesa ta kara kallantaa yanzu kam kallan rashin mutunci ta mata.
Tace " Ke malama wacece ke? A wani dalilin kikazo min kofar miji??"

Nafi kam jira take Ashraf yai magana sai dai abin haushi gani tai ya d'auke kansa, tare da amsar Jakarsa zaiyi gaba, jitai idanunta sun fara cikowa ita gani take ai ya kamara Ashraf ya sanar da Aneesa, ganin ya fara tafiya ga tana so ta tsaidashi daga fita waje, sannan ga Aneesa ta tsareta da ido yasa duk ta rikice.

  Shikam Ashraf haushin abinda tai jiya da daddare ne yasa yaki kulata, Aneesa ta bud'e baki zatai magana kawai Nafi tai baya luuu jikake ta zube a kasa, wannan ita kadai ce mafita a gareta abinda ta fad'a kenan a ranta tare da runtse ido.

  Aneesa ta d'anyi kara tare dayin baya cikin tsoro, hakan yasa Ashraf ya juyo da sauri, cikin rud'ewa yasa ya karaso inda take, sannan ya d'agota tare da cewa " Nafeesa!!Nafeessa!!."

   Sai a lokacin Aneesa ta gane waccece, kallan Ashraf tai duk ya wani rud'e haushi da kishi suka kamata a zuciye ta matso tace " Aljanu ne da ita??"

  Ran Ashraf ya b'aci ganin yanda tai maganar cikin rashin kulawa, yace " bishiyar kuka ce a kanta..."
Ya mike a zuciye ya d'agata ya nufi mota da ita, Nafi kam haryanzu gabanta bai bar fad'uwa ba tanaji ya bud'e bayan mota ya sata a ciki.

  Tanaji ya bud'e gaban mota ya shiga, ya tadata tad'anyi zafi sannan yaja motar suka fita, suna fita daga gate d'in gidan sai taji yace " Will u get up now?"

  Idanunta ta kara runtsewa a ranta tace " badai dani yake ba?"
Ashraf ya kalleta ta madubi sannan yace " abinda kika koyo a makarantar kenan? Pretending??"

  Nafi kunya da takaici duk suka kamata ta kara danna kanta kujera, gefen titi ya gangara yai parking sannan ya juyo ya kalleta yace " Kin tashi ko sai na fitar dake waje da kaina?"

  Nafi ta mike zaune tare da zunburo baki gaba kanta na kasa, ya kura mata ido yace " me kike san fad'amin?"

  Kallan mamaki tamai, tace " ya akai kasan abu nake san fad'a?"
  Kallanta yai sannan ya kalli window yace " inba abu kikesan fad'amin ba me zai sa kizo b'angarena kinsan inada mata kizo ki tsaya a waje?"

  Baki ta tab'e a ranta tace " da cewa nai bakada mata?"

  Ya kalleta sannan taji yace " da alama kin manta inada mata inba haka ba mezai sa kije b'angaren? Ai sai ki kirani a wayar Little ko ta saurayinki."

  Nafi ta saki baki tana kallan sa tace " to ni menace?"

  Ya juya kai sannan yace " Ki tambayi abinda kika ce a zuciyarki."

  Nafi tai shiru rai b'ace.
Ashraf yace " to fad'amin? Menene?"

  Nafi tai shiru tare da maida kanta kasa.
Ashraf ya kara had'e rai yace "zan saukeki fa inja motata inyi gaba ko ce miki akai banda abinyi??"

  Nafi ta kalleshi jiki a sanyaye, cikin wani irin murya tace "banifa da lafiya, xaka saukeni."

  Wani murmushi ya saki na rainin hankali yace " harda karya kika koyo a makarantar? "

  Ta kalleshi sannan ta d'an shagwab'e murya tace " nifa Yaya ba karyar dana koyo."

  Har cikin ransa sai dayaji wani abu, sai dai ya sake dakewa yace " ke jiranki nakeyi ko?"

  Nafi ta kalleshi tace " Yaya dan Allah kar kaje gun aiki yau."

  Kallan mamaki ya mata yace " bangane ba? Ke harkinkai matsayin da zaki hanani abu?to ko Aneesa bata samu wannan matsayin ba."

  Nafi ta kalleshi cikin wani yanayi tace " Na sani Yaya banida wannan matsayin kuma ban kai kaina wannan gun ba, sai dai ba dan nibaaa ba kuma dan halina ba sai dai ka duba darajar Allah ka hakura da zuwa aikin nan yau."

Ta karasa magana tare da kawar da kanta alamar idanunta nasan kawo kwalla, kallan mamaki yake mata, sai dai yanzu yasan tabbas da wani abun.......




*THE INNOCENT TEAM*
🏌🏻‍♀