Sunday, 30 July 2017

Zucia...Kowa da irin tasa 58

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

  *Where am i going to started? Ayeesh! U really left me without word, Thanks alot for the dedication of the whole book "Jini D'aya", I really appreciate ur love....May almighty Allah help and guide u through the right path...Ameen*

   58

   Bayan ya gama ne ya sa mata karamin towel ya sa mata akai sannan ya kalleta yace " zaki fita in watsa ruwa ko zaki zo mu watsa......"

  Ai bata jira ya karasa bama tao waje da sauri, murmushi yai sannan ya tura kofar.

  Nafi kam kofar tabi da kallo tace "wato yaya sam bashida kunya ko?"

  Zama tai a bakin gado littafin nan na diary ta gani a hankali ta zaro shi ta bud'e shafin farko "To My dearest Son Ashraf."

  Abinda ke rubuce kenan tai murmushi ganin wani d'an karamin hoto ba sai an tambaya bama Ashraf ne, passport ne da alama yana nursery aka d'auka tai murmushi sannan ta bud'e shafi na biyu.

  _Ashraf Allah baiyi zanga girmanka ba sai dai inaji ajikina ko bani zaka zama yaro na gari, mai san 'yan uwansa da na kasa dashi._

  Nafi ta sake murmushi tace "Abba ai d'an naka ne ba a gane cikinsa."
  Tana bud'e d'ayan page rubutu ne sosai, tana kokarin karantawa taji motsin alama na bud'e kofa, da sauri ta maida littafin sannan ta mike.

  Ashraf ya kalleta sannan ya karaso inda take, yace "matsoraciya."

  Kanta ta kawar gefe batace komai ba.

  Toilet ta wuce da sauri, yabi bayanta da kallo zuwa cinyoyinta da suke a waje, kansa ya shafa sannan ya zura riga doguwa ya fita falo.

  Nafi kam bayan ta watsa ruwa ta fito tare da tsayawa a d'akin to me ma zatasa? Ina kuma yayan yaje? Rigarsa ta gani t-shirt irin mai dogon hannun nan kawai ta zura sai ta sauke towel din kasa ta d'aurashi kamar zani.

  Tana d'aura kanta da ribbon Ashraf ya shigo, kallanta yai yadanyi dariya yace " da har ina tunanin d'auko miki kayan yayarki?"

  Da sauri tace " wacce yayar?"

  Ya d'an bata rai kadan yace "wace yayar kike da ita a gidan nan?"

Baki ta tabe tace " bansa kayanta bama an jikani ina kuma ga ta ganni da kayanta?ai inaji kanazir zata zubamin ta kyasta ashana."

  Ashraf ya danne dariyarsa yace " ke dai tsoronta kawai kikeji da alama, ko da yake baki da laifi Anisa ai akwai zuciya, ga kwarjini kuma bata da tsoro kamar o'o."

  Nafi ta d'an harareshi kadan tace " nima ai inada zuciyar kuma ba tsoro garen ba kawai dai raga mata nake nima."

  Ashraf baisan sanda yasa dariya ba, sai dayai sosai sannan ya kalleta ta wani ci magani yace " ayya bansan raga mata kike ba ai, ashe karamar matar tawa ba tsoro."

  Nafi ta kara had'e rai tace " ai in aka bi ta gaskiya ma nice babba dan nice uwargida."

  Baki Ashraf ya bud'e sannan yai dariya yace "Uwar gida?"

Ta turo baki tace" to wacce in ba ni ba?"

  Dariya yasa zai yi magana yaji ana knocking, nan yai waje yana dariya, lalai yarinyar nan, uwar gida??? Ha ha ha ni kaina sai da na sa dariya.

  Dan liti ne bayan ya shigo ne Ashraf ya kalleshi yace " ya? Ina da ina yaje?"

  Nan Dam litti yashiga mai bayani, Ashraf yai shiru can yace " shikenan sai zuwa gobe."

  Dan litti yamai sallama ya fita, Nafi bayan taji rufa kofa ne ta fito, a falo ta ganshi ya zauna tare da sa hannunsa duka biyu akan hancinsa zuwa bakinsa, Nafi ta zauna kusa dashi tace "Lafiya?"

Kallanta yai tare da girgiza mata kai alamar ba komai, ya mata murmushi.

  Itama murmushin tai sannan tace " nikam kun hadu da babansu Ferry ko?"

  Kallanta yai yace " Inda kikai yaji?"

  Tai murmushi tace " ka ganshi?"

  Kai ya d'aga alamar eh, sannan yace " ya akai?"

  Tace " baka sanshi ba ko?"

Kai ya d'aga mata cikin rashin kulawa yace " yeh."

  Shiru tai hakan yasa yace "ya akai?ya kamata in sanshi ne?"

  Tai shiru kafin tace " a company din Abba yai aiki da."

  Kallan mamaki ya mata yace " what?"

Tace " kuma da alama abokin Abba ne, dan bayan rasuwarshi ya ajiye aikinsa na company din."

  Ashraf yace " ko abokinsa ne mai zai sa ya ajiye aikinsa dan Abba ya rasu?"

  Shiru tai hakan yasa ya dafata yace "Nafisa!"

  Nafi tace " wlh bansan dalili ba sai dai kamar yana zargin mutuwar Abba ne."
  Shiru yai hakan yasa tace " menene?"

Ya kalleta yace " sunansa Isma'il?"

  Kallan mamaki tamai tace kasan sunan ne?"

  Da sauri ya mike yace " zan turo Little ta kawo miki kayanki."

Ta mike tace " ina zaka?"

  Bai amsa mata ba sai makulli daya zara yai waje da sauri.

Bayansa tabi da kallo, sannan ta kalli ledar daya bata d'azu, mam ta bud'e ganin kwalin waya yasa wani farin ciki ya kamata, irin wayar hannunsa ce har kalar sai dai ita bata kai waccen ba, wani murmushin farin ciki tai tace "Yaya na gode."

  Nan ta bud'e wayar ta shiga ta tabata.

********

  Ashraf direct a kofar gidan su Ferry yai parking, ya karasa suka kaisa da mai gadi sannan ya tambayeshi ko mai gidan na nan, mai gadi yace " eh yana gida, wa za'ace mai?"

  Ashraf yace kace " Dan marigayi Abbas ne."

  Nan mai gadi yai cikin gida, baifi minti 3 ba sai gashi ya dawo wai ya shiga.

  Nan ya rakashi falon baki, Nabil na zaune kusa da mahaifinsa yana ganin Ashraf ya mike suka gaisa sannan cikin muryar rada yace " rannan ya aka kare kai da budurwata Feena?"

  Ashraf ya makamai harara sannan shima cikin rada yace " kai saurin gyara bakinka,wacce budurwar taka?"

  Yana kainan yai gaba, a gaban mahaifinsu Ferry ya zauna, tare da gaidashi cikin ladabi.
Dad ya amsa sannan ya kalli Ashraf cikin tsoron abinda yazo dashi yace "Ashraf ya akai?"

   Ashraf ya d'ago yace " Tun ranar da na fara zuqa gidan nan ka san ni ko?"

  Dad ya kalleshi bai amsa mai ba, Ashraf yai murmushi yace " Na dade ina nemanka sai dai bansan ta inda zan soma cigiya ba, shiyasa nabarma kaina saninka."

  Kallansa Dad yai yace " nema na?"

  Ashraf yai murmushi yace "kasan lawyer din Abbana?Uncle Salim?"

  Dad yace " Salim?"

Ashraf ya d'aga kai yace " ya sanar dani kai da amintar dake tsakaninka da mahaifina sai dai kowa na mamakin barinka company daga sanda Abba ya rasu."

  Ashraf yad'an tsaya sannan ya cigaba, " sai dai ni ina tunanin ba aminta bace tasa kabar company din sai dai cikin d'ayan biyu, ko dai kasan abinda ya faru da mahaifina? Ko kuma da kai akai abinda akai, sai dai a koda yaushe in zuciyata ta rayamin na biyun ina saurin neman sauki gun Allah daya sa hakan karya zama gaskiya."

  Dad ya kalli Ashraf ga mamakin Ashraf sai jiyai yace " Ya Mansir?"

  Ashraf yace " kawu? Yana nan." ya fada yana mai kallan mamaki.

Dad yai murmushi yace " me kake tunani gama da Mansir?"

  Ashraf ya d'an rage idanunsa yace "naam?"

  Dad ya sake murmushi yace " u are smart, nasan kasan me nake nufi."

  Ashraf ya kalli Dad yace " nagane me kake san tambayata sai dai bansan meyasa nakeji a jikina ba Kawu bane kadai."

  Dad yai murmushi yace " As i expected nasan dan Abbas bazai bani kunya ba, u are right sai dai bazakaji komai a bakina ba, sai dai zan baka suna guda d'aya kaje kai amfani da wannan sunan ka gano shi da su waye suka had'u sukama Abbas haka."

  Ashraf yai shiru yana kallan Dad, dad yace " Auwal max."

  Kaje kai tunani ka kuma yi amfani da wannan sunan mutumin ka gano su waye ragowar, in ka gano sai ka dawo ni zan sanar da kai abinda na sani saboda a lokacin ne zan gane lalai zaka iya komai."

   Ashraf ya maimaita sunan "Auwal Max!"

  Sannan yai godiya ya mike ya fito, a wajen falon ya tsaya yana kallan kofar falon, lalai mutumin nan ya iya d'aure magana, ya maimaita sunan Auwal Max!

  Sannan ya fito daga gidan yayi sa'a bai ga Nabil ba da sauri ya fada mota yai gaba.....

  *GODIYA MARA ADADI AKAN ADDU'OINKU.*
_Nagode kwarai, insha Allah zaku cigaba da jina kullum._

  _Tnx for ur love and support💞_

  *ASHRAFEENAH TEAM*
  *LET'S GO👩🏻‍✈*

Thursday, 27 July 2017

Zuciya....Kowa da irin tasa 54

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

  *ASMY I Sincerely dedicated this page to u may Allah help and guide u through the right path always....(Ameen)......*😍😍😍

{54}

   Ashraf ya fita daga gun taron rai a b'ace, Dan litti ya kalla wanda ke waje yace " muje inkaika b'angaren baki ka huta ina da gun zuwa."

  Duk da Dan litti bakinsa tam yake da tambaya ganin yanda Ashraf yai yasa ya kasa tambayarsa, nan Ashraf ya kaishi sannan ya aiko da kaya a kawo mai shi kuma yai waje a mota da gudu.

   Ta ina zai soma nemanta???
Yayi yawo iya yawo ga magrib ta kawo kai, gaba daya hankalinsa ya gama tashi, ina Nafinsansa?

  Little ce ta kirashi a waya wanda ita kanta ta kasa zama daidai saboda rashin Nafi, bayan Ashraf ya d'auka yace "ta dawo ne?" yai maganar cikin zumud'i.

  A hankali tace "a'a yaya."

  Yai tsaki sannan yace " to meye?"

  Cikin sanyin jiki tace " yaya ina tunanin gidan kawarta ta tafi."

Da sauri yace "kawa?dama tanada wata kawa ne?"

  Little tace "Ferry wannan kawartata ta makaranta, ai a nan kano suke."

  Ferry??? Tai saurin cewa kanwar Ya Nabil.

  Duk da yaji haushin inda akace take dan shi ya dauka saurayinta ne, amma yanzu ganin Nafi shine a gabansa yace "ina ne gidan?"

  Tace "wlh bansani ba amma bari na turo maka number ferryn."
Yace "turon to."
Ya kashe wayar tare da dafa sityarin mota yace " lalai Nafisa zan gamu dake."

  Little ce ta turo number da sauri yai dialing sai data kusa katsewa Ferry ta d'auka cikin salon iyayi tace " HELLO!"

  Ashraf yace "Farida ce?"
Tace "nice, wanene?"
"yayan Nafisa ne, tana nan kuwa?"

  Ta kalli Nafi da suke hira da Ummansu tace "tananan amma...."
Da sauri ya katseta yace " a wacce unguwa kuke?"

  "kabuga ta fada."
Nan tamai kwatance ya katse layin, tabi wayar da kallo tare da cewa " kai wannan guy din Feenan sai a slow."

Mikewa tai ta koma gunsu Nafi, Nafi kam Umma ta kalla tace " Umma ashe Baba acan yai aiki?"

  Umma tace " Nabil je ya fada miki ko?"
Daya dawo ai yacemin a gidan Marigayi Abbas kike.

  Nafi tai murmushi tace " ba yar gidan bace bafa."

  Umma ta kalleta a nutse tace "kiyi a hankali da wannan gidan."

  Kallan mamaki Nafi ta mata tace "Umma meya sa?"

  Umma ta girgiza kai sannan tace " nidai abinda zance miki kenan, har yau in na tuno da mutumin nan sai naji zuciyata ta karye."

  Nafi ta kalleta cikin damuwa tace "Umma wai wani abun ne ya faru da Marigayin?"

  Shiru Umma tai sannan ta mike tace "bari in je kitchen Babanku ya kusa dawowa."

  Nafi ta bita da kallo cikin kulawa.

  Tana fita Ferry ta kalleta tace "tashi kiyi wanka."

  Nafi tace "ke nifa yanzu zan tafi, duk kece kikasa nai dare haka."

  Ferry ta jata ta turata toilet, Nafi tai dariya dama batasan komawa, da saninta tai dare dan Umma ta hanata tafiya, wanka tai sannan tai alwalar magrib ta fito, wata had'adiyar doguwar riga taga Ferry ta fito dashi, ta mata kallan tambaya sannan tace "zance zaki ko?"

  Ferry ta matso tace "Feenah gwada rigarnan, Baba ne ya siyomin dayaje umara to kuma abin haushi tamin kadan."

  Nafi ta ture hannunta tace "naki na gwada din."

  Ferry tace "shikenan bari na fada ma umma ta saki ki gwada." jin haka yasa Nafi ta amsa sannan ta gwada.

  Ta mata daidai, gashi kamar dan ita akai doguwar rigar, light pink ce sai dai daga gaban rigar ta sama anye jere da manyan duwatsu har kusan cikinta, ta mata kyau sosai, rigar tanada mayafinta sai dai mayafin plain ne.

  Nan Ferry ta sata a gaban madubi tace yi kwalliya.

  Nafi tace "wai ina zamu?"
Ferry tai dariya tace "sirri ne."

  Kai Nafi ta girgiza sannan ta fara kwalliya, tayi kwalliya sosai, ta kuma yi kyau sosai, nan ta mike tai sallah, tana idarwa wayar Ferry nayin kuka, da sauri Ferry ta d'au wayar tai waje.

  Nafi ta tabe baki tace "ferry kenan uwar soyayya."

Shigowa Ferry tai rike da wani turare a hannunta mai masifar kamshi, sanyin kamshi gareshi, nan tazo ta fesa ma Nafi.

  Nafi tai dariya tace "lalai  to ke yaushe zaki shirya?"

  Tace kedai ki sauka kuyi sallama da Umma.

  Nafi tace "Au bari na mike na tafi, amma meye ma sani kwalliya haka?"

  Ferry tai dariya tace "sauko."

Nafi wacce batasan tafiya kuma bazata iya fad'aba ta mike a hankali suka sauko.

  Umma tama sallama nan umma ta bata ledar dauke da turare da kayan kwalliya.

Nafi tai godiya suka sauko.

  Ashraf yana tsaye a jikin mota sai ga motar mai gidan ta iso, ya tsaya kusa da Ashraf dan ganin waye a kofar gidansa.

  Ganin ya tsaya yasa Ashraf ya karasa tare da gaidashi, gaban Baba ne ya fadi ganin ko wanene, cikin sanyin murya yace "Me kakeyi anan?"

   Ashraf yai murmushi zai yi magana yaji Baba wanda ya dauka gunsa yazo yace " Ba Ashraf bane?"

  Kallan mamaki Ashraf yamai yace "nine...Amma???"

  Baba yace " me kake anan?"

  Ashraf ya kalleshi yace "a ina kasan ni amma?"

   Gaban Baba ne ya fadi ya dauka gunsa yazo ai, cikin dan rawar murya yace "na ganka a magazine ne."
Yana kainan ya ja motarsa yai cikin gida.

Kallan mamaki Ashraf ya bishi dashi, yanda ya kira sunansa da yanda yamai tambayar bai yi kama da wanda aka gani a magazine ba, kallan gate din gidan yai yana mamaki, fitowar yarinyarce yasa ya katse mai komai.

  Kallanta kawai yakeyi, tunda ta fito, ganin mutum a tsaye yasa ta tsaya  itama, ferry tace "muje mana sanyin ranki ne."

  Nafi ta kalleta tace "ya akai yasan gidan nan?"

  Ferry ta nuna kanta da hannu, tace "kina wasa dani ko?"

Nafi ta harareta, Ferry ta dafata sannan suka cigaba da tafiya, kallanta yake ya kasa d'auke idanunsa, yaushe na zama haka? Meyasa bana iya jure abinda zuciya ta take fadamin akan wannan yarinyar?"

  Nafi kam kasa kawai take kallo, har suka karaso kusa da gun, Nafi ta tsaya itama a hankali ta d'ago ta kalleshi, idanunsa na kanta tad'an shagwab'e fuska.

  Ferry ce ta katsesu dayin gyaran murya tace "yaya ni zan koma."

  Ashraf ya kalleta yace "Farida nagode kwarai amma dole na bada tukuici."

  Dariya tai tace " ba wani tukuici yaya indai ka kula damu to komai ya biya."

  Hannu yasa a aljihu, yaji ba komai, ba dai bai d'auko wallet dinsa ba?"

  Farida ya kalla wacce take mai dariya, Nafi ma dariyar ta guntse, Ashraf yace "karki damu zan kawo tukuicin daga baya."

  Tace "ba komai yaya."

  Nan ta dafa Nafi ta rada mata a kunne, "ki tabbatar kin gama kwace zuciyarshi a yau din nan."

Tana kaiwa nan ta juya ta tafi, kallan Nafi yai yace "muje ko?"

  Tad'an turo baki sannan ta karasa ta shiga ta zauna, ya shiga tare da maida kallansa kanta yace " bansan ina fadan da zan miki ya tafi ba."

  Ta kalleshi fuska a shagwab'e tace " me nai da za'amin fada?"

  Kasa jurewa yai ya jawota ya rungumeta, a hankali yace mata " Nafeesa ni kaina ina mamakin kaina."

  Itama a hankali tace "Name fa?"

Yace "nakasa controlling din kaina a kanki, ni na san ba haka nake ba, ban kuma san ya akai na koma hakan ba."

  Idanu ta lumshe sannan tace " nifa ba yau naso komawa ba."

D'agota yai yace " kinsan zunubin dake kan matar data fita ba sanin mijinta kuwa?"

  Kallansa tai tace " ni kam ban saba da zancen miji ba."

  Ya matso da bakinsa kuncinta yace " ya? Ko kinaso in tabbatar miki ne a yau d'in nan?"

Idanu ta zaro da sauri tace " a'a bance ba."

Yai murmushi sannan ya tada mota, hannunta ya kamo ya rike d'ayan kuna yana tuki dashi, kamshin turarensa ne ya hadu da nashi sai ya bada wani sansanyan dadi, ga Ac din daya kunna, Nafi kam har wani lumshe ido takeyi, a zuciyarta tace "Allah ka d'auki raina a lokacin da nake irin wannan farin cikin."

  Har suka isa gida hannunsu na cikin juna yai parking sannan ya kalleta yace " b'angarena zamuje."

Idanu ta zaro tace "muyi me?"

  Hannu yasa ya ja kumatunta kadan yace "uwar tsoro abu kawai zan baki."

  Tai murmushi batace komai ba.

  Ya fito sannan ta fito shima, yana gaba tana binsa har suka isa b'angarensa yace "ta zauna, sannan shi kuma ya shiga d'aki."

  Kayan jikinsa ya cire ya saka doguwar jalabiya.

  Itakam hotonsu wanda sukai da Anisa kawai take kallo, baki ta tabe, sam bataji zuwansa ba sai ganinsa tai ya zauna kusa da ita.

  Kallansa tai ta saki murmushi, shima maida mata yai sannan ya nuna mata cinyarsa yace "kwanta."

  Kallan tsoro tamai, ya kafeta da ido, a hankali ta kwanta a cinyarsa tare da lumshe idanta, ya zame d'an kwalin kanta sannan ya fara shafar kanta a hankali, idanunta a lumshe suke sai dai Allah ne kadai yasan me takeji a wannan lokacin.

  Ashraf fuskarta yake kallo yace " gobe zamuje musai waya, daga yanzu karki sake fita ba sanina, kinji?"

  Kai ta d'agamai fuskarta d'auke da murmushi.

  Idanu ta bud'e a hankali tace " na d'agama hankali da baka gan ni ba?"

  "Hmm, ban taba zatan zanji haka ba."
  Tai murmushi tace " I can't help dole ne in sake guduwa wani gun."

  Harararta yai ya had'e rai yace " in kika sake gwadawa zakiga b'acin raina da baki taba gani ba kuwa."

  Ta turo baki tace " sai in sake shirya yanda bazaka iya min fada ba."

  Hararata yai yace " ahh i am dead, abinda banaso ya afko a kaina."

  Tace "mekenan?"
Yai furzar da iska yace "bazan iya fada ba."

  Murmushi tai sannan ta kara lumshe ido, ji take lalai in abu ya rabasu da Ashraf lalai to kuwa ba tantama mutuwa zatai sai dai wani iko na Allah.

A hankali yakai bakinsa ya sumbashi goshinta, ta bud'e ido a hankali suka kura ma juna ido, idansa ne taga ya d'an canza kala, batasan ya akai ba taji tsoro karfa su wuce gona da iri, su biyi a bangare.

  Da sauri tace " Yaya."

A hankali yace "Uhmm."

Tace "Abba hatsarin mota yai ko?"

  Kallanta yai yace "eh."
Tace "kaima hatsari kai harkaje garin mu ko?"
Yace eh.
Tace " Motar Abba alokacin an duba meya jawo hatsarin?"

  Kallan ta yai gaba d'aya hankalinsa na kanta, idanunsa taga ya kada sosai, ta mike zaune, tace" yahkuri in na ba....."

  Jawota yai ya rungumeta tsam a jikinsa, yace " me kike tunani?"

  Kai ta girgiza alamar ba komai.

  Ya dago ya kalleta hannayensa na kan kafadarta, yace " Nasani Nafisa sai dai banasan ki cigaba da binciken abinda bai shafeki ba."

  Hawaye ne ya zubo mata na tsananin tausayin Ashraf, idanunta na kansa tace " Na dauka duk abinda ya shafeka ya shafeni?"

  Hannu yakai a hankali ya share mata hawayenta yace " ba haka nake nufi ba....."

  Tacigaba da zubar da hawaye tace " Y are u enduring everything by ur self? Can't u share it with me?"

  Kallanta kawai yakeyi, tacigaba da cewa " kwanaki kasheka ya Asim yaso yi, amma ba wanda ka fadama, abubuwa nawa ka sani wanda baka fadama kowa ba? Kana tunanin in kabar mutanen da sukeyin evil deeds saboda 'yan uwane kana tunanin zasu daina?"

  Yauce rana ta farko dayakeji har cikin jinin jikinsa lalai yarinyar nan ta damu dashi lalai tana sanshi saboda Allah, lalai zata iya komai domin shi.

  Jawota yai a hankali yakai bakinsa cikin nata...  Wata duniyar suka shiga kiss suke deeply wanda gaba d'ayansu wani feelings sukeji wanda su kadai ne sukasan abinda sukeji tundaga kansu har kafafuwansu.........

  Ni dai nace to fa ayi a hankali kar a gangara🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣.

  *#ASHRAFEENAH*
💞

Zuciya....Kowa da irin tasa 56

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

  *56*

    Ashraf yacema dan litti akan su tsaya a wani babban shago na wayoyi, nan suka fita tare.

   Waya ya d'auka kirar Samsung S7+ karamar ta hannunsa, sannan ya kalli Dan litti yace"kaifa wanne kakeso?"

  Kai Dan litti ya sosa, Ashraf yace "shikenan in ba ka so."
Da sauri yace " ni kowacce ma ina so."

Ashraf yai murmushi yace "a d'auko mai Iphone 5."

  Wani ihu da dan litti ya sake sai dayasa mai wayar ya kwashe da dariya, nan suka sai sim sannan ya kara siyan wani extra sim sannan suka fito.

  Suna shiga mota ya d'auko wata yar karamar waya daga cikin jakarsa, yasa wannan d'ayan sim d'in a ciki sannan ya maidata jakar.

  Sun isa gun aiki Ashraf ya fito d'an litti yabi bayansa, Asim ne wanda yake tsaye yake jiran isowar Ashraf ya taso da sauri, ya taho gun Ashraf fuskarnan a had'e.

  Dan karamin tsaki Ashraf yaja a ransa yace "The fool is here."

  Asim na karasowa ya kalli Ashraf yace " Kai bakaji kashedena ba ko? Akan kaba yarinyar nan takardarta ta bar gidan nan ba ko?"

  Dan litti ya matso yace " Malam meye hakan?"

Murmushi Ashraf yai yace " barshi magana zamuyi."

Nan Dan litti ya matsa tare da had'e fuska kamar irin shi akama abun nan.

Kallo Ashraf ya maida kan Asim yace " Mahaifinka yace zai bani matsayinka, mai kake tunani?"

  Idanu Asim ya zaro tare da kumburo baki yace "matsayina? What do u mean?"

  Ashraf ya dafashi yace " what do i mean? Da alama sai ka tambayi mahaifinka da ya dage akan bani matsayinka, mayb kuma ya kula ne u are useless."

  Yana kaiwa nan yai gaba, Dan litti yabi bayansa rike da jakarsa yana hararar Asim.

  Ashraf ya kalleshi yace " Dan litti kasan kanin mahaifina?"

Kai ya girgiza alamar a'a yace "jiya dai na ganshi sai dai banaji zan iya gane shi."

  Ashraf yace "zan nuna maka shi inaso ka dinga kulamin dashi akan abubuwan da yakeyi da kuma wadanda yake gani, sai dai karka bari kowa ya ganka kar kuma asan abinda kakeyi."

  Dan litti ya mai salute da hannunsa yace "yes sir."

Hannunsa Ashraf ya ture yace " sorry ba a military muke ba."

   Nan sukai dariya sannan suka shiga.
Jakarsa Ashraf ya kaimai sannan ya juyo ya fita.

Asim kam yana gama magana da Ashraf yai office dinsa kamar zai fadi saboda sauri, yana zuwa ya ture takardun kan desk dinsa da hannayensa biyu, ciki hucci yace " ni zakama haka Abba?"

  Kawu kam yana zuwa office yasa aka rubuta takardar ragema Asim matsayi aka aika mai.

  Asim yai shiru yana kallan takardar, can cikin takaici ya yaga takardar sannan ya mike cikin fishi yai office d'in kawu.

  A zaune ya ganshi shi da  manager  suna magana, nan ya tsaya suka gama, manager din ya fita sannan ya shiga.

  Tsayawa yai a kan mahaifinsa yace "ban yarda da ragemin matsayin nan ba."

  Kawu yace " kasan complain din da ake kawomin naka kuwa?in ban rage ma matsayi ba mai kake tunani mutane zasu daukeni?"

  Mamaki ya kama Asim yace " wa zaka ba matsayina? Ashraf?"

Kawu ya juya kai yace " haka shareholders da director's suka yanke."

Dariya Asim yasa yace " ko kuma ka tsara ba?"
Kawu ya had'e rai yace "kai ni kake fadama haka?"

Asim cikin hucci yace " ni dai na fada kar a kuskura a ragemin matsayina in ba haka ba zan iya tona abubuwan da na sani."

  Mikewa kawu yai tare da dukan desk dinsa da hannu yace " me zaka tona?"
Yai dariya yace "abubuwan da kai, kana tunanin in Ashraf yaji zai barka?wato yanzu tunda kaga Anisa batada matsayi a gunsa shine kake neman juya mana baya ka koma gunsa ko?"

  Kawu a zuciye ya d'aga hannu ya kai mai mari, Kallansa Asim yai sannan yai waje rai a b'ace."

  Kawu ya bi bayansa da kallo sannan ya zauna tare da rike kansa.

  Asim sama yahau cikin takaici yahau hucci tare da kara, ko aure bai taba kawowa ba saboda yanasan ya gaji Company din nan, shine yanzu mahaifinsa zai fara juyamai baya??"

   ************

  Nafi kam bayan ta gama aikin gyara musu d'aki ta zauna tare da daukan qur'ani tana karatu.

   Mumy ce ta aiko a kirata, nan ta mike gabanta na faduwa tai waje.

  B'angaren Mumy ta nufa ta zauna tare da zama a kasa.

  Mumy ta kalleta tace " jiya ina kika je?"

  Nafi kanta na kasa tace " Gidan wata kawata da mukai makaranta."

  Mumy ta kalleta tace " ina sanki a natsayinki na yarinyar da aka taimaka amma ba wai a matsayinki na matar Ashraf ba."

Nafi ta d'ago a hankali ta kalli Mumy.

  Mumy ta cigaba "Ashraf bai samu kulawa daga gareni ba sai bakin ciki dana dinga kunsa mai, mahaifinsa ya rasu hankali bai gama shigarsa ba."

Idanun Nafi suka ciciko, Mumy tace " sai dai hakan ba yana nufin zan yarda ya auri mara ilimi ba alhalin aiki babba yana gabansa, yana bukatar matar datasan gari sannam takeda ilimi at least degree, shine wanda zai gaji mahaifinsa."

   Nafi tai kasa da kai hawaye suka zubo mata, Mumy tace " kije kiyi tunani in har kina san Ashraf to kiyi tunanin menene abinda zaifi amfanarsa a rayuwar nan."

  Nafi ta mike a hankali tana share hawayenta, b'angarensu ta nufa, da gudu mai gadi ya karaso yace " yallabai yace wai ki mai abincin rana zai dawo da anyi la'asar."

  Kai ta d'aga sannan ta koma ciki.

Ana azahar ta fito tai kitchen ta fara mai girke girken Asabe na tayata.

   *********

  Umma da Anisa kam suna zaune abin duniya ya damesu, Anisa can ta nisa tace " duk laifinku ne Umma, meyasa kuka hanani haihuwa dashi?"

  Umma tace "mene?"

  Anisa ta cigaba" da yanzu akwai zuri'a a tsakaninmu ko baya sona ai nasan halin Ashraf bazai wulakantani ba."

  Umma ta mike tsaye tace " Anisa meke damunki?"

  Anisa cikin dan fada tace " wlh ni duk ku kuka cuceni, da ace na haihu dashi ai da d'ana shine zai zama yanada gadon dukiyar Ashraf amma dayake ba ni kukeso na gaji dukiyar ba shi yasa ba wanda yai wannan tunanin."

  Tana gama fadar haka ta mike tai cikin d'aki tare da bugo kofa da karfi, Umma ta bita da kallan mamaki.

  *******

  Karfe hud'u da rabi Ashraf ya dawo, b'angarensa ya nufa, shima dan littibya wuce nasa.

  Zama yai tare da d'aukan waya ya kira Little, yace "kin dawo?"
Tace eh yaya.

Yace "ki turomin Nafi."

Ta amsa sannan ya kashe.

Nafi ta kalla wacce tai wanka tai kwalliya cikin atamfa riga da siket, bata d'aura d'an kwalli ba kanta ba kisto sai dai ta tifkeshi da ribon.

  Kan nan yayi gwanin sha'awa.

Little ta kalleta tace " Yaya na kiranki, da alama dama shi kike jira."

Nafi ta harareta tace " ni wai ina mutumin ki? Naji shi shiru kwana biyu.

  Little tace "tafiya yai wlh amma gobe zai dawo."

Nafi ta zari d'an kwalinta tai waje.

  Kitchen ta nufa ta d'auko tiren data jera mai abincinsa sannan tai b'angarensa fuskarnan fal take da farin ciki, dukda dai kalaman Mumy suna kara yimata yawo a zuciyarta.

  A bud'e taga kofar hakan yasa tasa kai tare da sallama, Ashraf wanda ke zaune akan kujera ya kalleta fuskarnan d'auke da murmushi, dinning ta wuce ta ajiye sannan ta tsaya daga gun tace "ka taso."

  Hannu ya mata alamar tazo nan tad'an yi kasa dakai sannan ta make kafada tace " naki ni dai ka taso."

  Murmushi yai ga mamakinta sai taga ya taso ya nufota, jingina tai da jikin dinning din tana kallansa fuskar nan d'auke da murmushi.

  Ya karaso kusa da ita batai zata ba sai jitai ya rungumeta.

  Murmushi tai sannan tace " Yaya ka dawo lafiya?"

  " Hmm lafiya lau, jiya yaushe kika tafi?"

  D'agowa tai ta kalleshi tad'an mai hararar wasa tace " ba bacci kai ka shareni ba."

  Idanu ya zaro yace garin yaya?"

Ta turo baki tace "Allah yaya indai ina zuwa gunka kana min bacci ko?"

  Bakin data turo ya d'an sumbata hakan yasa ta maida shi da sauri, yace " me za amin?"

  Kallansa tai tace " kazo kaci abinci."

  Murmushi yai sannan ya saketa ya ja kujera ya zauna tare da nuna mata kujerar kusa dashi.

Nan ta zauna ta zuba mai, kallanta yai yace " muci."

  Tace " am full."
Idanu ya kafeta dashi hakan yasa ta mike ta d'auko wani spoon din ta zauna.

  A hankali suke ci sai dai ya kamo hannunta na hagu ya rike.

  Bayan sun gama ne ta zubamai juice ya sha sannan suka mike.

  Hannu yasa a kugunta ta kalleshi tai murmushi a haka suka karasa ya zauna akan kujara tare da jawota kan cinyarsa.

Kallansa tai tace " yaya inada nauyi fa."

Dariya yai yace " indai kinada nauyi to lalai Afra ma tanada nauyi."

  Cikin shagwab'a tace " Afran?""

Ya d'aga mata kai sannan ya d'auko ledar dake gefensa yace " Gift."

  Kallansa tai ta amsa zata bud'e yace " ba anan ba sai kin tafi kya bud'e, yanzu dai tukuicina zaki bani."

  Yai maganar yana mata wani kallo, itakam in Yaya na mata irin wannan abun mamaki takeyi dan a iya saninta da gani take mutum ne wanda bashida sakin fuska, sai dai ferry dama ta fada mata maza duk daya suke indai a harkar so ne, kenan shi yana santa da gaske."

  D'an kwalin kanta ne ya zame, kanta ya kurama ido, a hankali yakai hannu ya shafa yace " i like this."

  Murmushi tamai sannan tai kasa da kanta tace " tukuicin me kake so?"

  Nesa dashi ya nuna mata yace zauna, nan ta tashi ta zauna a gun, zatai magana taji ya kwantar da kansa kan cinyarta yace " a gajiye nake, so nake inji ya bacci yake a kan cinyar matata."

  Kallansa tai tare da sa hannunta kan fuskarsa tace " amma ai kana kwanciya akan cinyar yaya Nisa."

  Yai murmushi bai ce komai ba sai idanunsa daya rufe.

  Murmushi tai sannan tasa hannu ta fara shafar kansa.

  Ta ina zata iya rabuwa da Ashraf?

  Bataji zata iya, in kuwa tai to gaskiya rayuwarta ta gama karewa.

*#ASHRAFEENAH*
💋

Tuesday, 25 July 2017

Zuciya....Kowa da irin tasa 55

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

  *Someone!!!*
      *Somewhere!!!*
        *Is Made For U*

  {55}

   Sun yi nisa sosai, Ashraf ya saketa a hankali, da sauri ya shiga d'akinsa, itakam kafafunta ta had'e dan jitai har su rawa suke, tun da take bata taba jin abinda taji yau ba, wani irin feeling ne wannan???"

  Ashraf kam kwanciya yai rufda ciki akan gado, wata muguwar sha'awa ce take tasomai sai dai bazai taba kusantarta ba har sai ta aminta dashi a matsayin miji, juyi ya shiga yi.

  Nafi kam ta dade itama a zaune kafin tabi kofar d'akinsa da kallo, ya kamata ta tafi kafin dari yayi sosai, a hankali ta mike tai d'akin.

   Sallama tai jin shiru yasa ta murd'a kofar d'akin, Ashraf najin haka yai saurin rufe idanunsa, kallansa tai a hankali ta tako tazo inda yake.

  Zama tai a gefensa takai hannu kan sumar kansa, ta kurama fuskarsa ido, a hankali tace "bacci?"

  Jin shiru yasa tad'an turo baki tace "shine ka barni a zaune kai ka taho ka kwanta?"

   Shiru tai tare da cigaba da kallansa a hankali takwantar da kanta saitin fuskarsa suka zama fuskokinsu na fuskantar juna, ta sa hannu a kan kuncinsa sannan tace " please let me be the first person whom you can trust."

   Murmushi tai sannan ta kai bakinta a hankali kan leb'ensa ta sumbata, sannan tace "Goodnight."

  Ta mike tare da jamai bargo tai waje, b'angarensu ta nufa a zaune taga little a falo ta matso da sauri zata mata magana taga Little ta mike tayi ciki, Nafi tabi bayanta.

  Toilet ta wuce direct dan da alama tanajin jikinta ba yanda yake ba, a gun tsarki ta gano lalai abinda ya zubo na sha'awa ne, nan ta wanke wandon ta ta gyara jikinta tasa wani sannan ta fito.

  A kwance taga Little ta kalleta tace "Little yanzu haka zamuyi ta zama bakya kulani?"

  Little bata tanka taba, Nafi tace " ban taba tunanin zaki iya kin kulani ba saboda kinji ance ni yar kauye matar yayanki bace, ni kaina nasan ban kai wannan matsayin ba, sai dai........"

  Little ce ta katseta da cewa " kin dauka saboda matsayinki a gun yaya nake miki haka?"

  Nafi ta kalleta tace "to menene in ba shiba?"

  Little ta mike zaune tace " shekararmu nawa tare?nikenan da miki zancen saurayi akan ki kula wane ki kula wane, bansani ba ashe mahaukaciya kika mai dani."

  Nafi cikin mamaki tace "mahaukaciya kuma?"

  Cikin zafi Little tace "mahaukaciya mana, inba haka ba da igiyar auran yayana a gunki amma nake neman had'aki da wani?"

  Nafi ta matso tare da rike hannun Little tace "Little kiyi hakuri wlh ni kaina mantawa nake akwai abu a tsakanin mu."

  Nan dai Nafi tai ta bata baki har ta hakura, sun dan yi hira kadan kafin Nafi ta kalli Little tace " nikam Little wani abu na damuna."

Kallan mamaki Little ta mata tace name kenan?"

Nafi tai shiru can tace " Abban Ashraf na ga shine ya fara zancen had'in auren Yaya da Ya Nisa, to menene dalilinsa na ajiye wasiya yace a ba matar Ashraf ta farko bayan yasan ko ince Yaya Nisa yakesan ya fara aura?"

  Shiru Little tai can ta girgiza kai tace "ban sani ba, ni banma taba kawo abin a raina ba, amma kina ganin da wani abun ne?"

  Kai Nafi ta girgiza tace "ba komai, bari nai sallah."

  Ta mike tana tunani tabbas da wani abun, sai dai menene?????

*************

A b'angaren Ashraf kuwa tana fita yabi bayanta da kallo yanaji kamar ya jawota ya rungumeta sai dai ina bazai iya hakan ba, bayan yayi sallah ya d'aga katifarsa ya d'auko wani karamin makulli sannan ya zugi wardrobe dinsa ya ture kayan, nan wata yar karamar kofa ta bayana, nan yasa makuli ya bud'e ya zaro wasu takardu a ciki sannan ya koma ya kulle kofar d'akinsa da makulli ya zauna tare da baje takardun nan, bayan ya gama bincikensa da 'yan rubuce rubucensa ya maida ya rufe sannan ya juye fuskarnan a murtuke kamar mai tafiya yaki yace " Mu zuba mu gani."

  Kan gado ya kwanta ya sa diary d'in mahaifinsa, wani shafi ya bud'e an rubuta _Someone! Somewhere is made for u my dearest son_"

  Murmushi yai da ya tuna abinda nafi tace da kiss din data mai, hannu yakai kan leb'ensa yace " yarinyar nan kamar ba ruwanta ashe itama killer?"

  A haka har bacci yai gaba dashi.

  Da safe ya tashi tare da sawa a kiramai dan litti, sunyi breakfast kafin Ashraf ya kalli Dan litti yace "yanzu me kakeyi?"

" Achaba."

  Ashraf ya jinjina kai yace "mota fa ka iya?"

  Dan litti ya d'aga mai gira yace "ka sanni ai akwai karambani ai zamana a kachako sai da na koya."

  Ashraf yace "gaskiya nafa sanka."
Dariya sukai kafin Ashraf yace " zaka koma kauyene?"

  Da sauri yace "a ina?ai ni yanzu i am big for them."

  Ashraf ya sa dariya yace "u are big?wato baka daina bako?"

  Ashraf ya mai alamun zip a bakinsa yace "na daina kai kawai nake san ma."

  Ashraf yace "to in ba matsala nafisan ka zama driver d'ina, saboda nafisan wanda zan yarda da shi."

  Zaro ido dan litti yai yace " Ashaf kana kasheni in nazama driver dinka ai na zama dan gomna."

  Dariya sosai Ashraf yai yace " whoa! Dan litti kai kadai ke sani dariya akai akai."

  Dam litti ya mike tare da yima Ashraf salute yace "yes sir!"
Ashraf yai murmushi yace " kaii ban taba ganin mutum irinka ba."

Dan litti ya zauna yace "Ashaf karka damu zan zama mutum mai rike ma amana, dama tunda muka hadu nake sanka bazan taba bari wani abu ya cuceka ba."

Ashraf yai murmushi sannan ya dafashi yace "thanks, amma kanaso kacemin wai baka iya fadar Ashraf bane ko ya?"

  Dan litti yai dariya yace "in na cema Ashraf ai mantawa zakai nine d'an littin gayu."

  Dariya suka sakeyi kafin su mike su fita.

  Makullin motarsa yaba Dan litti shikuma ya wuce b'angaren kawu.

  A tsaye ya ganshi shima zai fito, mumy na kusa dashi, wani takaici ya kara kamashi ya matso kusa da kawu ya gaisheshi fuska dauke da murmushi sannan ya gaida mumy.

  Bayan sun amsa ne kawu yace "Ashraf ya akai?"

Kallan mumy yai yace "magana nakeso muyi."

Mumy ta kalleshi jiki a sanyaye tai waje, ya matso kusa da kawu fuskarnan a sake yace "naji shiru ne, jiya banga takardar appointment ba."

  Kawu ya kalleshi yace "wai da gaske kake?kasan fa matsayin Asim ne ya kakeso inyi."

  Wani murmushin rainin hankali yai tare da jinjina kai yace "ahhhh! Na manta ko da yake ba matsala ka barshi a matsayinsa kai sai ka bani naka, dama ai can nawa ne ko ba haka ba???"

  Ya fada yana kallan kawu.

  Kawu ya shiga hucci, Ashraf yai murmushi sannan ya dan girgiza d'an yatsansa yace "No no no, kawu how can u get angry? Bayan a sama kaga komai?wanda ya sha wahalar yana karkashin kasa?"
  Kawu ya kalleshi sannan yai yake yace "ce maka akai raina ya b'aci?" 

  Ashraf ya d'an kanne idanuwansa yace " why?kunya kake na gano hakan? Hmm ko da yake ba matsala yi zamanka a kujerarka nizansa ka sauka da kanka in har baka ajiye da hannunka ba."
Yana kai nan yai waje,yana fita kawu ya shiga hucci, jakarsa ya cillar can gefe sannan ya zauna a kujera yana maida numfashi kamar wanda yai gudu......

  Ashraf ya fitowa ya harari d'akin sannan ya juya, jiyai ance "Ya Ashraf."

Juyowa yai ya kalli Anisa wace duk ta dan fada a kwana biyu, ya matso yace" ya akai?"

  Kallansa tai tace " yaushe zaka zo ka maidani b'angare na?"

  Kafada ya d'aga yace "da nina kawoki nan?"

  Kallansa tai tace "yaya ni bazan koma bane harsai ka saki wannan yar kauyen dan pride dina bazai bari in iya kallanta ba, kace ta koma kauyensu."

  Hannu yasa ya dafata yace " a maysayinki na wa kenan?"

Tace "yaya!"
Yai murmushi yace " karki damu kiyi ta zamanki a gun mahaifiyarki gani nake zatafijin dadin hakan, nima kuma zan samu saukin bincike min d'aki da akemin."

Yana kainan yai gaba, kallo ta bishi dashi yasan komai meyasa bai taba magana ba????

  Mota ya wuce, dan litti ya bud'e mai baya nan ya shiga ya rufe shikuma ya shiga mazaunin driver.

  *#ASHRAFEENAH TEAM*

👩🏻‍✈

Zuciya....Kowa da irin tasa 54

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

  *ASMY I Sincerely dedicated this page to u may Allah help and guide u through the right path always....(Ameen)......*😍😍😍

{54}

   Ashraf ya fita daga gun taron rai a b'ace, Dan litti ya kalla wanda ke waje yace " muje inkaika b'angaren baki ka huta ina da gun zuwa."

  Duk da Dan litti bakinsa tam yake da tambaya ganin yanda Ashraf yai yasa ya kasa tambayarsa, nan Ashraf ya kaishi sannan ya aiko da kaya a kawo mai shi kuma yai waje a mota da gudu.

   Ta ina zai soma nemanta???
Yayi yawo iya yawo ga magrib ta kawo kai, gaba daya hankalinsa ya gama tashi, ina Nafinsansa?

  Little ce ta kirashi a waya wanda ita kanta ta kasa zama daidai saboda rashin Nafi, bayan Ashraf ya d'auka yace "ta dawo ne?" yai maganar cikin zumud'i.

  A hankali tace "a'a yaya."

  Yai tsaki sannan yace " to meye?"

  Cikin sanyin jiki tace " yaya ina tunanin gidan kawarta ta tafi."

Da sauri yace "kawa?dama tanada wata kawa ne?"

  Little tace "Ferry wannan kawartata ta makaranta, ai a nan kano suke."

  Ferry??? Tai saurin cewa kanwar Ya Nabil.

  Duk da yaji haushin inda akace take dan shi ya dauka saurayinta ne, amma yanzu ganin Nafi shine a gabansa yace "ina ne gidan?"

  Tace "wlh bansani ba amma bari na turo maka number ferryn."
Yace "turon to."
Ya kashe wayar tare da dafa sityarin mota yace " lalai Nafisa zan gamu dake."

  Little ce ta turo number da sauri yai dialing sai data kusa katsewa Ferry ta d'auka cikin salon iyayi tace " HELLO!"

  Ashraf yace "Farida ce?"
Tace "nice, wanene?"
"yayan Nafisa ne, tana nan kuwa?"

  Ta kalli Nafi da suke hira da Ummansu tace "tananan amma...."
Da sauri ya katseta yace " a wacce unguwa kuke?"

  "kabuga ta fada."
Nan tamai kwatance ya katse layin, tabi wayar da kallo tare da cewa " kai wannan guy din Feenan sai a slow."

Mikewa tai ta koma gunsu Nafi, Nafi kam Umma ta kalla tace " Umma ashe Baba acan yai aiki?"

  Umma tace " Nabil je ya fada miki ko?"
Daya dawo ai yacemin a gidan Marigayi Abbas kike.

  Nafi tai murmushi tace " ba yar gidan bace bafa."

  Umma ta kalleta a nutse tace "kiyi a hankali da wannan gidan."

  Kallan mamaki Nafi ta mata tace "Umma meya sa?"

  Umma ta girgiza kai sannan tace " nidai abinda zance miki kenan, har yau in na tuno da mutumin nan sai naji zuciyata ta karye."

  Nafi ta kalleta cikin damuwa tace "Umma wai wani abun ne ya faru da Marigayin?"

  Shiru Umma tai sannan ta mike tace "bari in je kitchen Babanku ya kusa dawowa."

  Nafi ta bita da kallo cikin kulawa.

  Tana fita Ferry ta kalleta tace "tashi kiyi wanka."

  Nafi tace "ke nifa yanzu zan tafi, duk kece kikasa nai dare haka."

  Ferry ta jata ta turata toilet, Nafi tai dariya dama batasan komawa, da saninta tai dare dan Umma ta hanata tafiya, wanka tai sannan tai alwalar magrib ta fito, wata had'adiyar doguwar riga taga Ferry ta fito dashi, ta mata kallan tambaya sannan tace "zance zaki ko?"

  Ferry ta matso tace "Feenah gwada rigarnan, Baba ne ya siyomin dayaje umara to kuma abin haushi tamin kadan."

  Nafi ta ture hannunta tace "naki na gwada din."

  Ferry tace "shikenan bari na fada ma umma ta saki ki gwada." jin haka yasa Nafi ta amsa sannan ta gwada.

  Ta mata daidai, gashi kamar dan ita akai doguwar rigar, light pink ce sai dai daga gaban rigar ta sama anye jere da manyan duwatsu har kusan cikinta, ta mata kyau sosai, rigar tanada mayafinta sai dai mayafin plain ne.

  Nan Ferry ta sata a gaban madubi tace yi kwalliya.

  Nafi tace "wai ina zamu?"
Ferry tai dariya tace "sirri ne."

  Kai Nafi ta girgiza sannan ta fara kwalliya, tayi kwalliya sosai, ta kuma yi kyau sosai, nan ta mike tai sallah, tana idarwa wayar Ferry nayin kuka, da sauri Ferry ta d'au wayar tai waje.

  Nafi ta tabe baki tace "ferry kenan uwar soyayya."

Shigowa Ferry tai rike da wani turare a hannunta mai masifar kamshi, sanyin kamshi gareshi, nan tazo ta fesa ma Nafi.

  Nafi tai dariya tace "lalai  to ke yaushe zaki shirya?"

  Tace kedai ki sauka kuyi sallama da Umma.

  Nafi tace "Au bari na mike na tafi, amma meye ma sani kwalliya haka?"

  Ferry tai dariya tace "sauko."

Nafi wacce batasan tafiya kuma bazata iya fad'aba ta mike a hankali suka sauko.

  Umma tama sallama nan umma ta bata ledar dauke da turare da kayan kwalliya.

Nafi tai godiya suka sauko.

  Ashraf yana tsaye a jikin mota sai ga motar mai gidan ta iso, ya tsaya kusa da Ashraf dan ganin waye a kofar gidansa.

  Ganin ya tsaya yasa Ashraf ya karasa tare da gaidashi, gaban Baba ne ya fadi ganin ko wanene, cikin sanyin murya yace "Me kakeyi anan?"

   Ashraf yai murmushi zai yi magana yaji Baba wanda ya dauka gunsa yazo yace " Ba Ashraf bane?"

  Kallan mamaki Ashraf yamai yace "nine...Amma???"

  Baba yace " me kake anan?"

  Ashraf ya kalleshi yace "a ina kasan ni amma?"

   Gaban Baba ne ya fadi ya dauka gunsa yazo ai, cikin dan rawar murya yace "na ganka a magazine ne."
Yana kainan ya ja motarsa yai cikin gida.

Kallan mamaki Ashraf ya bishi dashi, yanda ya kira sunansa da yanda yamai tambayar bai yi kama da wanda aka gani a magazine ba, kallan gate din gidan yai yana mamaki, fitowar yarinyarce yasa ya katse mai komai.

  Kallanta kawai yakeyi, tunda ta fito, ganin mutum a tsaye yasa ta tsaya  itama, ferry tace "muje mana sanyin ranki ne."

  Nafi ta kalleta tace "ya akai yasan gidan nan?"

  Ferry ta nuna kanta da hannu, tace "kina wasa dani ko?"

Nafi ta harareta, Ferry ta dafata sannan suka cigaba da tafiya, kallanta yake ya kasa d'auke idanunsa, yaushe na zama haka? Meyasa bana iya jure abinda zuciya ta take fadamin akan wannan yarinyar?"

  Nafi kam kasa kawai take kallo, har suka karaso kusa da gun, Nafi ta tsaya itama a hankali ta d'ago ta kalleshi, idanunsa na kanta tad'an shagwab'e fuska.

  Ferry ce ta katsesu dayin gyaran murya tace "yaya ni zan koma."

  Ashraf ya kalleta yace "Farida nagode kwarai amma dole na bada tukuici."

  Dariya tai tace " ba wani tukuici yaya indai ka kula damu to komai ya biya."

  Hannu yasa a aljihu, yaji ba komai, ba dai bai d'auko wallet dinsa ba?"

  Farida ya kalla wacce take mai dariya, Nafi ma dariyar ta guntse, Ashraf yace "karki damu zan kawo tukuicin daga baya."

  Tace "ba komai yaya."

  Nan ta dafa Nafi ta rada mata a kunne, "ki tabbatar kin gama kwace zuciyarshi a yau din nan."

Tana kaiwa nan ta juya ta tafi, kallan Nafi yai yace "muje ko?"

  Tad'an turo baki sannan ta karasa ta shiga ta zauna, ya shiga tare da maida kallansa kanta yace " bansan ina fadan da zan miki ya tafi ba."

  Ta kalleshi fuska a shagwab'e tace " me nai da za'amin fada?"

  Kasa jurewa yai ya jawota ya rungumeta, a hankali yace mata " Nafeesa ni kaina ina mamakin kaina."

  Itama a hankali tace "Name fa?"

Yace "nakasa controlling din kaina a kanki, ni na san ba haka nake ba, ban kuma san ya akai na koma hakan ba."

  Idanu ta lumshe sannan tace " nifa ba yau naso komawa ba."

D'agota yai yace " kinsan zunubin dake kan matar data fita ba sanin mijinta kuwa?"

  Kallansa tai tace " ni kam ban saba da zancen miji ba."

  Ya matso da bakinsa kuncinta yace " ya? Ko kinaso in tabbatar miki ne a yau d'in nan?"

Idanu ta zaro da sauri tace " a'a bance ba."

Yai murmushi sannan ya tada mota, hannunta ya kamo ya rike d'ayan kuna yana tuki dashi, kamshin turarensa ne ya hadu da nashi sai ya bada wani sansanyan dadi, ga Ac din daya kunna, Nafi kam har wani lumshe ido takeyi, a zuciyarta tace "Allah ka d'auki raina a lokacin da nake irin wannan farin cikin."

  Har suka isa gida hannunsu na cikin juna yai parking sannan ya kalleta yace " b'angarena zamuje."

Idanu ta zaro tace "muyi me?"

  Hannu yasa ya ja kumatunta kadan yace "uwar tsoro abu kawai zan baki."

  Tai murmushi batace komai ba.

  Ya fito sannan ta fito shima, yana gaba tana binsa har suka isa b'angarensa yace "ta zauna, sannan shi kuma ya shiga d'aki."

  Kayan jikinsa ya cire ya saka doguwar jalabiya.

  Itakam hotonsu wanda sukai da Anisa kawai take kallo, baki ta tabe, sam bataji zuwansa ba sai ganinsa tai ya zauna kusa da ita.

  Kallansa tai ta saki murmushi, shima maida mata yai sannan ya nuna mata cinyarsa yace "kwanta."

  Kallan tsoro tamai, ya kafeta da ido, a hankali ta kwanta a cinyarsa tare da lumshe idanta, ya zame d'an kwalin kanta sannan ya fara shafar kanta a hankali, idanunta a lumshe suke sai dai Allah ne kadai yasan me takeji a wannan lokacin.

  Ashraf fuskarta yake kallo yace " gobe zamuje musai waya, daga yanzu karki sake fita ba sanina, kinji?"

  Kai ta d'agamai fuskarta d'auke da murmushi.

  Idanu ta bud'e a hankali tace " na d'agama hankali da baka gan ni ba?"

  "Hmm, ban taba zatan zanji haka ba."
  Tai murmushi tace " I can't help dole ne in sake guduwa wani gun."

  Harararta yai ya had'e rai yace " in kika sake gwadawa zakiga b'acin raina da baki taba gani ba kuwa."

  Ta turo baki tace " sai in sake shirya yanda bazaka iya min fada ba."

  Hararata yai yace " ahh i am dead, abinda banaso ya afko a kaina."

  Tace "mekenan?"
Yai furzar da iska yace "bazan iya fada ba."

  Murmushi tai sannan ta kara lumshe ido, ji take lalai in abu ya rabasu da Ashraf lalai to kuwa ba tantama mutuwa zatai sai dai wani iko na Allah.

A hankali yakai bakinsa ya sumbashi goshinta, ta bud'e ido a hankali suka kura ma juna ido, idansa ne taga ya d'an canza kala, batasan ya akai ba taji tsoro karfa su wuce gona da iri, su biyi a bangare.

  Da sauri tace " Yaya."

A hankali yace "Uhmm."

Tace "Abba hatsarin mota yai ko?"

  Kallanta yai yace "eh."
Tace "kaima hatsari kai harkaje garin mu ko?"
Yace eh.
Tace " Motar Abba alokacin an duba meya jawo hatsarin?"

  Kallan ta yai gaba d'aya hankalinsa na kanta, idanunsa taga ya kada sosai, ta mike zaune, tace" yahkuri in na ba....."

  Jawota yai ya rungumeta tsam a jikinsa, yace " me kike tunani?"

  Kai ta girgiza alamar ba komai.

  Ya dago ya kalleta hannayensa na kan kafadarta, yace " Nasani Nafisa sai dai banasan ki cigaba da binciken abinda bai shafeki ba."

  Hawaye ne ya zubo mata na tsananin tausayin Ashraf, idanunta na kansa tace " Na dauka duk abinda ya shafeka ya shafeni?"

  Hannu yakai a hankali ya share mata hawayenta yace " ba haka nake nufi ba....."

  Tacigaba da zubar da hawaye tace " Y are u enduring everything by ur self? Can't u share it with me?"

  Kallanta kawai yakeyi, tacigaba da cewa " kwanaki kasheka ya Asim yaso yi, amma ba wanda ka fadama, abubuwa nawa ka sani wanda baka fadama kowa ba? Kana tunanin in kabar mutanen da sukeyin evil deeds saboda 'yan uwane kana tunanin zasu daina?"

  Yauce rana ta farko dayakeji har cikin jinin jikinsa lalai yarinyar nan ta damu dashi lalai tana sanshi saboda Allah, lalai zata iya komai domin shi.

  Jawota yai a hankali yakai bakinsa cikin nata...  Wata duniyar suka shiga kiss suke deeply wanda gaba d'ayansu wani feelings sukeji wanda su kadai ne sukasan abinda sukeji tundaga kansu har kafafuwansu.........

  Ni dai nace to fa ayi a hankali kar a gangara🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣.

  *#ASHRAFEENAH*
💞

Zuciya...Kowa da irin tasa 53

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

  *53*

  *Wannan shafin naki ne Billy Galadanci*......😍😍😍

    Idanu Ashraf ya zaro cikin mamaki ya nunashi yace "Dan Littin Gayu?"

Keya d'an Litti ya sosa yace " Ashaf nine dai kam." yai maganar yana washe  baki.

  Dariya sukama juna ganin za'a bada hannu yasa Ashraf yace, shiga muje.

    Da sauri dan litti ya shige bakin nan yaki rufuwa.

  Gefen titi suka gangara Ashraf yai parking tare da kallan guy din wanda sai washema Ashraf baki yake, Ashraf yai murmushi yace "Dan Littin Gayu."

  Dan Litti yai dariya yace "inafa gayu? Gayun daya kusan kaini prison."

  Ashraf bai san sanda dariya ta kwacemai ba yace " Ah haba? Ni ai bantaba tsammanin ganinka a nan ba."

  Nan D'an litti ya shiga bashi labarin zuwansu da su Datti da kulleshin da akai, da zamansa a kachako, har zuwa komawarsa kauyensu da abinda Datti yai.

  Ashraf yai murmushi yace " Gaskiya kasha wahala gun nemana, ko da yake alheri ya zamarma tunda gashi nan ai ka canza."

  Dan litti yai dariya, Ashraf ya cigaba " Shi kuma wannan mahaifin Nafin....."
Sai kuma yai shiru.

Dan litti yace " Ai datti ni har yau Allah bai hadani da mutum irinsa ba."

   Shiru Ashraf yai, tausayin Nafi na kara ratsashi.

  Ya juyo ya kalli Dan Litti yace " yanzu ina zaka?"

  Dan Litti yace "mun shigo kano ne dama kawai yawo, nida abokaina."

  Ashraf yai murmushi yace " Dan Litti kenan, kace yanzu an daina sakar mana turanci."

  Kansa ya kara sosa wa yace " inafa?inasanyi ina tsoron abinda zai jamin."

  Sukai dariya a tare, Ashraf yace "ba matsala mu tafi gidan mu."

  Dadi ya kama Dan Litti shi dama burinsa ya gansa da Ashaf.

     Nafi kam yau gidan duk ya isheta, ga Little bata kulata ba tai wanka tai tafiyarta makaranta, gashi bata isa ko fita tai ba, yunwa ma takeji amma saboda gudun rigima ta kasa fita.

Mikewa tai ta shirya ta duba jakarta taga d'ari biyar ta fito ta hau adaidaita tamai kwatancen gidansu Ferry.

   Tai sa'a suna nan aikam suna haduwa hira ta barke, anan taci abinci suka cigaba da hirarsu.

   Duk yanda sukai akan ta fada musu meya sameta a fuska taki fada cewa kawai tai faduwa tai, sai dai su sunsan ba faduwa bace Sai dai ba yanda zasuyi.

*********

  Ashraf sun isa gida yai parking din motarsa sannan ya kalli Dan litti wanda ya saki baki, hanci, ido duk yana kallab tangamemen gidan dai bai taba gani ba a tsawon rayuwarsa.

  Ashraf ya sa hannu ya zunguroshi, Dan Litti yai firgigitbya kalleshi.

  Fito mu shiga ko?"

   A hankali Ashraf ya fito sai kara kallan gidan yakeyi, Ashraf yai gaba, nan yabi bayansa yana tafe yana kalle kalle.

  Bangaren Ashraf suka nufa, bayan ya bud'e ya kalli Dan Litti yace 'shiga muje ko?"

  Kai dan litti ya girgiza yace "a'a kadai fara shiga."

  Ashraf yai murmushi sannan ya shiga, nan Dan Litti ya dan dosana kafarsa a hankali sannan ya shiga, kallan Ashraf yai yace " Ashaf lalai kana bawa gayu kunya, wannan duk haduwarsu suka ganka ko motarka ko gidanka ai dole su shiga hankalinsu kunya ta kamasu."

  Ashraf bai san Sanda dariya ta zo mai ba yace " Lalai Dan Litti, kai dai baka rabuwa da shirme, shigo insa a kawo ma abinci."

  Nan ya zauna a tare da kara kallan falon, Ashraf kuma yai ciki.

  Dariya kawai dan litti ya shiha yi ba kakautawa wanda yasa Ashraf ya fito da sauri, a kasa yaganshi yana dariya, cikin mamaki yace " ya akai?"

  Dan litti ba tare da ya daina dariya ba yace "lalai Datti zai ci Kw*******"

  Ya karasa yana dariya, kai Ashraf ya girgiza sannan ya koma ciki, bayan dan litti ya gama dariyarsa ne idanunsa suka fada kan hoton Ashraf da Anisa, nan yace "KAI! Kai jama'a." da karfi yai maganar wanda yasa Ashraf ya sake fitowa ya kalleshi yace " ya akai?"

  Dan litti yace " Tab, Ashaf amma wannan matar taka tayi, da alama wannan yarinya mai wanke wanke ta koma, yo dama ina kai ina ita?."

  Ashraf ya dan daure fuska zaiyi magana yaji Dan litti ya sake cewa " lalai Datti zai suma duk randa ya shigo gidan nan." ya kara kwashewa da dariya.

  Kai Ashraf ya girgiza sannan ya koma ciki, waya ya daga ya kira Little yace " ki sa Nafisa ta kawo min abinci."

  Little wacce tun dazu take neman Nafi tace "yaya wlh nima nemanta nakeyi."

  Cikin rashin fahimta yace "kamar ya kenan?"

   Tace "wlh na dawo daga makaranta naga batannan."

  Cikin fada yace "to ija taje?"

  A tsorace Little tace "wlh bansani ba yaya "

  Tsaki yaja sannan ya kashe wayar, ya zauna a bakin gado, haushinsa da takaicinsa d'aya da ko waya bai sai mata ba, ya rufe ido cikin takaicin kansa yace " why?"

  Yanzu tayaya zai soma nemanta?to inama ta sani da zata? Kansa ya dafe cikin takaici.

  Yana fitowa sai ga Little ta shigo da tire ta kalli dan litti mamaki ya kamata bayan Habib ba wanda yaya yake kawowa bangarensa,ina kuma ya samo wannan?"

  Ashraf ne ya katseta da cewa " ko wa ya dawo?"
Kai ta daga alamar eh, fuskan nan tasa a daure yace " ki buga taro."

  Ta amsa da to sannan ta fita, kallan Dan Litti yai yace " zo ka ci abinci Gayu."

  Nan ya kaishi dinning ya turamai tiren gabansa sannan shi ya fita.

  Tunda ake taro agidan yauce rana ta farko da Ashraf ya fara zuwa gun taron da wuri, zuwa yai ya zauna fuskarsa a murtuke.

  A hankali kowa ya fara shigowa duk wanda ya shigo sai yayi mamakin zuwan Ashraf da wuri.

  Bayan kowa ya hallara ne Ashraf ya mike yace " bayan fitata waye ya kira matata Nafisa?"

   Cikin mamaki kowa ya kalleshi, Kawu yace " dalilin taramun da kai kenan?"

Ashraf yadan motsa baki sannan yai murmushi yace " matata bayan fitatavna tabbata wani ya kirata, in kuwa ba'a kirata ba anje har inda take anci zarafinta, dan a yanzu haka bata gidan nan, ban kuma san inda ta shiga ba."

  Umma tace " to menene namu a ciki? Banaji wannan damuwar mu ce, kila ta tafi yawon karuwancinta ne."

  Ashraf yq shafa goshinsa yace " menene naku a ciki? Ina tunatarwa ne da in ban ganta ba ni kaina bansan me zan aikata ba."

   Asim ya mike rai a bace yace " kai! Kayi kadan ka taramu akan wata banzar yarinyar da mu bamu san matsayinta ma a gunka ba, wanda babu shaidar ita matarka ce."

  Ashraf yadan yi murmuhsin da har hakoransa suka fito yace " Little kiramin bakon nan."

  Nan ta mike tai waje, Ashraf ya cigaba " wlh in har wani abu ya samu Nafisa bani da guarantee din abinda zan iya aikatawa."

  Mumy ta kalleshi zatai magana kawu yai saurin cewa "nina kiranta bayan ni kuma banaji akwai wanda ya kirata, inka tashi hukuncin sai kamin, tunda yanzu idanka ya rufe akan karamar yarinya sam baka tunanin kowa."
  
   Ashraf ya kalleshi sai dai baiyi magana ba, ya gane Mumy ce ta kirata kenan, tunda yasan ai kawu suna tare gun aiki.

  Kallan Mumy ya shigayi, ta had'e fuska tace "eh nice na kirata, Ashraf wai meke damunka ne kwana biyi?"

  Idanunsa ne suka fara canza kala, a hankali ya ke fitar da wani hucci dan kar a gane ransa yakai kololuwa gun tashi.

  Shigowar Dan Litti ne ya taimakeshi da yayi barna dan tibiren dake gabansa mai dauke da cups na tangaran kawai yake kallo.

  Dan litti ya tsaya daga nesa cikin tsoro ganin duk an zubomai ido, kuma kallan tsana ake mai.

  Ashraf ya kalleshi yace " karka damu mutumina gani nan anan."

  Kallan Ashraf yai sannan hankalinsa yadan kwanta, Ashraf ya kalli Kawu yace "to ga shaida na nan na sanda aka daura auren, banaji daga wannan shaidar kuma kuna bukatar wata."

  Kawu ya Mike ya kalli Dan Litti yace " daga ina kake?"

  Dan litti yace " kauyen gwaram."

  Kawu yace " menene hadinka da Nafisa?"

  Kauyensu na kusa da tamu."

  Menene ita kuma tsakaninta da Ashraf?
Matarsa ce.

   Wannan kalma ta rikita kowa, Ashraf yama Dan litti alama akan ya koma.

  Yana fita Ashraf yace " zan nemo matata da kaina, sai dai bazan yafema wanda ya kuskura ya kara shiga harkarta ba."

  Yana kai nan yai waje......

_Ina mika ta'aziyata ga Aisha Y. Kura na rashin mahaifinta datai, Allah ubangiji ya jikansa, yasa aljanna ce makomarsa ya kuma kai haske kabarinsa (Ameen)_

*#ASHRAFEENAH TEAM*

Zuciya...Kowa da irin tasa

Friday, 21 July 2017

Zuciya....Kowa da irin tasa 50

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

_Godiya gareku 'yan Nice Hausa Novel musamman hajiya admin Aisha Sabi'u Mohd....ILYSM😍_

{ *50*}

     Nafi kam a falo ta zauna ta dafa kanta itakam Allah ya yaye mata wannan abun dan bata ganin akwai riba a cikin wannan san da takema Ashraf.

   Kwanciya tai daga nan bacci yai gaba da ita akan kujerar.

   Sai la'asar ta tashi tana shiga taga Little ma bacci take nan tai sallah sannan ta tasheta itama tai, kitchen ta nufa dan kara samun fasaha akan girki.

  Sai 6 ta fito tana shiga bayan sunyi magrib aka aiko wai ana sallama da ita, mamaki ya kamata ta tsare Little da ido, Little tace " ba Alamin bane Allah dan shi baima san kin dawo ba."

  Nafi tace "to waye??"
Little tai murmushi tace "ki shirya sai ki dubo mana."

  Harararta Nafi tai tace "wani shiri kuma? Bansan waye ba kawai sai in hau kwalliya sai kace mai neman saurayi?"

  Little ta sa dariya tace " to da mecece?ai duk budurwa nema take har sai ta samu tsayaye."

  Nafi ta tabe baki ta zari mayafi tai gaba Little na tsokanarta.

  Waje ta fita mota d'aya ce a gun hakan yasa ta tsaya daga dan nesa tana tunanin karasawa, fitowa yai tare da zama a saman motar yace "My Feena ko sai na zo da kaina?"

  Jin muryar Nabil yasa tai murmushi sannan ta karasa, kallansa tai cikin zolaya tace " da alama rashina ya hanaka sukuni?"

  Ya dafa kai yace "Feenah taba kiji inaji zazzabi ne ke neman kamani saboda missng dinki."

  Tai dariya tace "Ya Nabil to ya? Nayi mamakin ganinka a daren nan."
Ya kalli agogo yace " ko isha'i batai ba shine dare?"
Tai dariya sannan tace "Ina Aminiya?"

  "Tana gida nima wucewa nazo yi nace bari na tsaya mu gaisa."
Murmushi ta sakeyi tace "aikam na gode."

  Ya kalli gidan yace "dama a gidan Marigayi Abbas kike?"
Kallan mamaki tamai tace "kasanshi ne?"

  Dariya yai yace "ina fa mutumin daya rasu kafin muyi wayau."
Tace "then?"
Yace " A company dinsa dai Dad yai aiki."

  Cikin mamaki tace haba?
Ya daga mata kai sannan yace "Amma tun bayan rasuwarsa shima ya ajiye aikin."

  Nafi tace "me yasa?"
Iska ya dan tara a bakinsa sannan ya furzar yace "bansan dalili ba."

  Kallo ta tsareshi dashi tace " Kace wallahi."
Yai murmushi yace " me nene matsayinki a gidan?"
Ta kalli gidan sannan tace "nima bansani ba ganinan ne dai kawai."

  Dariya yasa yace "ban gane ba."
Tace Wallahi dagaske."

  Kallan mamaki ya mata yace " kiyi a hankali to da irin wannan gidan manakisa da sharrinsu yawa gareshi, dan mutuwar Abbas din........"

  Bakinsa ya guntse jin yana shirin yin baran barama, Nafi ta kalleshi fuska dauke da mamaki tace " Me? Akwai sa hannu ko me?"

   Juyar dakai yai yace " Hmm yaushe zakizo gida?"
Tace "Ya Nabil?"

  Kallan gate yai yace "ga wani can ya fito da mota."
Nafi ta kalli gun,  motar Ashraf ce idanunta ta kaida kan Nabil tace " Ya Nabil dan Allah me ka sani??"

   Kifta ido yai yace "bazai miki fada ba?"
Hade rai tai tace " akan me kenan?"

  Zaiyi magana yaga an dallesu da fitilar mota wanda sai da Nafi ta juya,  ta tabbata so yake yaga waye, shiyasa tana juyawa ta maida kanta gun Nabil.

  Ashraf kam wanda suka fito shida Anisa.
Ya tsaida mota batare da ya kashe fitilar ba, Anisa ta kalleshi ya had'e rai tare da kafe Nafi da ido, mamaki ya kamata.

  Shikam Nabil kallan Nafi yai yace " Feenah da alama ke ake jira kar inja a miki fada bari na tafi."

   Da sauri tace a'a yaya taimakamin karka tafi please.
 Yace "Ba kya tsoro?"
 Kallansa tai fuska dauke da murmushi tace " mu shiga motarka mudanyi gaba please, sannan banaji zan barka ka tafi baka karasa fadar abinda zaka fada dazu ba."

  Kallan mamaki ya mata, ta shagwabe fuska tace "please "

  Sauka yai sannan ya zagaya ya bud'e mata mota ta shiga sannan shima ya shiga tare da tada mota.

  Anisa ta kalli Ashraf tace "wai me mukeyi anan ne?"

  Bai ma san tanayi ba dan wani irin abu ne ya tasomai yana ganin sun hau kan titi ai kuwa shima ya taho da gudu da mota ya sha gabansu saura kiris motoci biyun su bigi juna, Nafi kam da Anisa duk sun runtse ido kowa na tsoron abinda zai faru shikanshi Nabil ya tsorata, Ashraf a zuciye ya kashe mota sannan ya fito ko kofa bai rufe ba yazo Kofar da Nafi take ya bud'e da karfinsa.

   D'agowa tai cikin tsoro tana kallan idanunsa da suka kada sukai ja sai hucci kawai da yakeyi, hannu yasa ya fizgota da karfi, Anisa ganin haka yasa ta fito tare da shan gabansu tace "Ya Ashraf me kakeyi hakan? Ina zaka bayan kasan unguwa zamu?"

  Kallanta yai cikin idanunsa da sukai ja bai bata amsa ba kawai ya zagaya ta gefe ya sa Nafi a bayan motarsa ya shiga ba tare da ya kuma kallan Anisa ba yai reverse sannan ya ja motar a zuciye.

  Nabil kam wannan abu ya d'aure mai kai shima a hankali yaja tasa motar yai gaba yabar Anisa wacce ta tsaya kamar gunki.

  Ta dade agun kafin ta koma gida, gun Umma ta nufa tai sa'a Asim nanan nan ta zayyane musu abinda akai tare da fashewa da wani irin kuka.

  Umma ta mike tsaye tace " Asim dole ne musan abinyi dan nikam na gaji da wulakancin wannan dan marasa tarbiyar."

  Asim a zuciye yai waje ya nufi bangaren mahaifinsa......

  Shikam Ashraf gudu kawau yakeyi, Nafi kam tayi shiru a baya sai dai har yanzu tsoron abinda Ashraf yai takeyi, gashi sai gudu yakeyi ga dare.

  Addu'a kawai take a ranta, can karshen titin Naibawa ya tsaya, wajen fly over sannan yai parking ya fito tare da bud'e kofar Nafi.

 Ta kalleshi cikin tsoro.
"Fito!"
Abinda taji yace kenan, ta danne tsoro sannan tace "in fito inyi me??"

  "What?" ya fada yana kara kallanta.

  Ta murguda bakinta tace " Haka kawai ka jawoni ka kawoni nan sannan in fito inyi me?"

  Kallan mamaki ya mata tai saurin kallan gefe, shiga yai kusa da ita tai saurin matsawa tare da harde  hannayenta ta maida kallanta gefe.

   "Waye waccan d'in?"
Tace wa kenan?
"tambaya ma kike? Wanda yake neman sa ki a mota ku tafi wani guri a daren nan."

  Baki ta turo tace "Wani ne."

  Yace "wani? Bakida hankaline bakisan mutum ba kike neman shga motarsa? In ya lalataki fa?"

  Dariyar da ta nemi taho mata ta guntse tace " to meye a ciki? Tunda so na yake?"

  Me? Bakida hankali ne?" ya fada a zuciye, ta kalleshi tace " ni so nake ma in aureshi dan na gaji da zama a inda na sona ake ba."

  " who said that?" shikansa baisan sanda ya fadi hakan ba.

Kallan sa tai fuskarta da alamar tambaya, ya juya kai sannan yace " karki kuskura inkara ganinki da wani namijin balle har ki samu mai dariya ko shiga motarsa."

  Tace" Akan me?"

  Yace " Tambaya ma kike? So kike wani abu ya sameki ace nine?"

  Haushi ya kamata ba haka taso ji ba, ta juya kanta tace " bazan iya rabuwa da shi ba."

   Hannu yasa ya rike kafadarta da karfi tare da juyo da ita saitinsa, yace " ni kike fadawa haka?"

  Baki ta turo batace komai ba, kallanta ya tsaya yi, batai auni ba taji bakinta cikin nasa, nan ta fara kokarin kwacewa sai dai ya riketa da kyau tun tana kokarin kwacewa har tai la'asar....Wani sakon ni suke ba juna wanda su kadai suka san ma'a narsa, sun dade sosai a haka sannan a hankali suka saki juna, idanuwansu dake lumshe suka bud'e a hankali.

   Idanunta suka ciciko cikin sanyin murya tace " Yaya why are u doing this to me?"

  Jawota yai jikinsa ya rungume ta yace " Nafeesa ni kaina bansan me nakeyi ba."

  Tace " ba so na kake ba me yasa kakeyin hakan to?"
Ya kara kankameta yace " Na rasa me ke damuna, ni kaina abin na damuna."

  Ta dago da jikinta tace " karka sake tabani har sai ka san abinda ke damunka."

  Kallan mamaki ya mata yace " Ke halal dina ce bawai haram dina ba."

  Wani murmushin takaici tai tace " Halal? Since when did i became your halal?"

   Yace " What?"

  Ta rufe ido sannan ta bud'e tace " Halal din da ba wanda ya sani? Halal din da ni kaina ban san halal bane? Halal din da kake tsoron kar mutane su sani? Halal din da kai kanka baka tabbatar dashi ba?"

   Kallanta yai sai dai kalamanta sunsa jikinsa yai sanyi, ta sake murmushin takaici tace " ko ma meke damunka nidai karka kara tabani sai ka tabbatar dashi sannan sai na yarda da hakan."

  Tana kai nan ta juya kanta tare da share kwallar da ta zubo mata.

  Jiki a sanyaye ya bud'e motar yai waje ya koma mazauninsa ya zauna a hankali ya tashi motar sukai gaba.

  Yana kallanta ta madubi jefi jefi tana share hawayenta, ya sani sarai shine silar kukan ta, me yasa yake zama dalilin hawayen ta? Why did he always cause her pain?"

  Jiyai gaba daya jikinsa yai sanyi jiyake kamar ya jawota jikinsa ya lallasheta, bayaso ko kadan yaga tana kuka dan har zuciyarshi abin ke tabawa.......

*#ASHRAFEENAH TEAM*

Zuciya.....Kowa da irin tasa 52

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡

  *52*

   _Ga masu min korafi akan yin da nake sau d'aya, kuyi hakuri inada uzuri ne, ni kaina inaso inga nayi dayawa dan in kamalla littafin, sai dai ina kara baku hakuri, dan Allah kuyi hakuri da page d'ayan da nakeyi, in har na samu dama nima zan yi sama da page d'aya......Nagode da kauna, Allah yasa ku fahimceni._

Sun dawo gida aka bar Umma kadai acan, Mumy ta kalli agoggon jikin mota karfe 12, lalai dole ta hakura sai zuwa gobe ta samu yin magana da Ashraf in ma wasa yake to lalai kar ya sake mata irin wannan wasan.

   Shikam Ashraf hankalinsa a kwance yai baccinsa, itakam Nafi akan sallaya tai bacci tana jiran Little.

  Little ta shigo taga Nafi na bacci, shiru tai ta tsaya tana kallanta har ta kai hannu zata tasheta ta koma kan gado ko me ta tuna? Sai naga ta fasa, kayanta ta cire tai kwanciyarta.

   Mumy tana shiga b'angarensu taga Kawu a tsaye sai zirga zirga yake, yanzu in har da gaske Nafi matar Ashraf ce kenan ko sun kawar da Ashraf itama tanada gadonsa? Gadan me? Bayan ba wanda yasan da auren iya kaci su karyata hakan.

  Ya zarfafa a tunani sam baiji sallamar Mumy ba sai jiyai ta dafashi, kallanra yai sannan ya zare hannunta ya koma kan kujera ya zauna tare da daure fuska, Mumy ta karasa gunsa tace " Me ya faru?"

  Ya kalleta yace " Abinda yaran nan yai yana matukar damuna, nasan Ashraf bai daukeni a matsayin uba ba sai dai ban taba tunanin zai wulakantani haka ba."

  Mumy tai ajiyar zuciya tace " nikaina abin nan ya tabani, sai dai ina gani ya fadane kawai, gobe zanje in mai magana ai aure ba hauka bane."

  Washegari da sasafe su Nafi na bacci sukaji buga kofa kamar za'a b'ala kofar, a razane suka tashi, Little ta bud'e kofar da sauri.

   Anisa ce a gefenta kuma Umma ce fuskarnan kamar me? Banko kofar sukai tare da shigowa ciki suka gifta Little tare da wucewa gurin Nafi wacce ta mike zaune sai dai kana ganinta kasan a tsorace take, Anisa ta karaso a zuciye ta d'aga hannu zata kifa ma Nafi mari, da sauri Nafi ta rike hannunta duk da tana tsananin tsoron yanda taga fuskokinsu sai dai bazata yarda da duka ba kuma.

   Anisa ta kalleta cikin tsananin kishi tace " ke har kin......."
Umma ce tai saurin kifa ma Nafi wani wawan mari ba tare da ta zata ba, Nafi ta sake hannun Anisa tare da rike kuncinta ta kafe Umma da ido, Umma cikin mamaki tace " ni kike ma wannan kallan?"

   Nafi ta dauke idanta jitai Anisa ta rufe ta da duka gaba daya hannayenta, Little ta karaso zata tare, Umma ce ta riketa tace "meye naki a ciki? Ke bakya kishin cin mutuncin da akama 'yar uwarki?"

  Little ta tsaya jiki a sanyaye, Anisa kam ta dage sai sauken takaicin ta take akan Nafi, can Nafi ta mike ta rike hannun Anisa, tace "Yaya Nisa inaji yanzu kin huce ai ko?"

   Anisa tai sototo tana kallanta, Umma tace " mene?"
 Nafi wacce taji zafin dukan iya zafi ta daure tace " gani nai dukan ya isa haka inkuma ba kasheni takesan yi ba."

  Umma a zuciye ta fizgo wayar charger dake jikin socket tai kan Nafi zata daketa, Nafi ganin ba sarki aikam ta sake hannun Anisa tai hanyar waje da gudu, jitai ta bugi mutum, ta tsaya tare da d'agowa ta kalleshi, Umma kuma wacce suka taho itada Anisa rike da bulala zata daketa itama ta tsaya cak.

  Ashraf ya kallesu, yace " me kuke tunani kuke aikatawa?"

   Umma ta fara hucci, Anisa kuma kallan yanda Nafi ke tsaye a jikinsa take, Ashraf ya kallesu yace "Umma me kukeyi?"

  Umma tace " Kai dan marasa tarbiya,kayi kadan ka wulakantamin 'yata akan wata banza yar daji, kuma wlh kaji na fada maka ko ba yau ba sai na mata dukan da sai an kwantar da ita a asibiti kamar yanda aka kwantar da tawa 'yar."

   Murmushi ya sakar mata wanda ya bata tsoro, yace "Umma kenan banaji ranar da zakiyi hakan 'yarki ma zata kwana a gida."

  Anisa ta matso cikin takaici tace "Yaya mai kake nufi? In umma ta daketa kana nufin nima dukana zakai ko me?"

  Hannu yasa ya shafi gefen fuskar Anisa yace " No no no, kinfi kowa sanin banasan harkar duka sai dai ina nufin a ranar zamana dake ya kare."

   Baya baya ta fara ja, tana girgiza kai, wannan ba Ashraf dinta bane, Ashraf ya kalli Umma wacce ta saki baki tana mai kallan mamaki yace " i tried really hard inga na boye abinda ke raina, sai dai naga alamar bakusan wannan ba, dan haka daga yanzu i won't tolerate anyone ko da kuwa Little ce."

  Yana kai nan ya kalli Nafi yace " koma ciki ki kwanta zanga wanda zai kara gigin tabaki."

  Nafi kam yau ta zama kurma, a hankali ta koma ciki, Umma ta kalleta cikin takaici, Ashraf ya kalli Little yace "kin bani kunya." ya juya zai fita jiyai Anisa tace "Yaya karka fita."

  Juyowa yai ya mata wani kallo yace " a matsayinki na wa?"
 Tace "ni ai matarka ce."
 Murmushi yai sannan ya tako a hankali har inda take ya rungumota jikinsa sannan yakai bakinsa kunnenta yace " mata wace take shan maganin hana daukan ciki? Wacce take binciken dukiyar mijinta? Wacce take jiran mijinta ya rasu ta samu gadon sa?"

  Kallan tsoro tamai, ya matso da fuskarta wajen kuncinta yace " why? Kin dauka duk ban sani ba?"

   Ya kara mata murmushi sannan ya juya yai gaba, zubewa tai a kasa tama kasa kukan sam, Umma ta matso tace "ke ya ce miki?"

  Kai kawai take girgizawa, ganin haka yasa umma ta cicibeta sukai waje.

  Little kam da sauri tabi yayanta.

  Nafi kam ita kanta a d'aki zaka tai dabas tana mamakin abinda Ashraf yakeyi tun jiya, ita kanta shakkarsa take taya za'ai ya dinga fadar bakar magana hankalinsa a kwance? Bata taba ganinsa a haka ba lalai kenan akwai wani hali nashi da ya boyema 'yan gidan.
 
   Ashraf na fita bangarensa ya nufa, yau kam gidan kamar ba safiya ba kowa ya tashi, a bakin kofarsa yaga Mumy hakan yasa ya gaidata kai tsaye ya bud'e kofarsa ya shiga.

 Shigowa tai itama, guri ya samu ya zauna itama ta zauna a kujerar da ke kallansa, Little ce ta shigo ganinsu tare yasa ta koma gun dinning ta zauna.
 
   Sunyi shiru kafin Mumy tace " Ashraf!"
 Kallanta yai batare da ya amsa ba.
 Tacigaba "me kake nufi da kalamanka na jiya?"
 Cikin rashin kulawa yace "me nake nufi kuwa?abinda kikaji shine gaskiya."

  Ido ta kuramai can tace " kasan me kake fada kuwa? Kasan me ake nufi da aure?"

 Dariya yai ya kalleta yace "Mumy kenan, na dauka ko dan shekara 18 yasan me ake nufi da aure, sannan banyi tunanin zaki damu ba in nayi aure ba tare da saninki be tunda kika sake aure ba tare da sanina ba sannan kika fita daga harkata tun ina karami."

  Idanunta ne ya ciciko tace " Nasani i am a bad mother to you, sai dai Ashraf kai kanka kasan ba inda uwa zataki danta."

  Idanu ya rufe yace "gashi kuwa na gani? Tunda nake dake kin taba tambayata yaya nake?meke damuna?menene matsalata? Banaji tun mutuwar mahaifina kin kara zama dani zama na uwa da danta."

  Mumy tai shiru, sai idannunta da suka ciciko, Ashraf ya dan rufe bakinsa sannan ya dan sa hannu ya shafi kansa yace " inaji a jikina ba san mahaifina dani kike ba."

  Yana kai nan ya mike zai shiga ciki, sunansa ta kira "Muhammad!"
 Tsayawa yai cak jikinsa yai sanyi, tacigaba " bazaka fahimci dalilina na yin hakan ba, sai dai na sani banida wani uzuri da zan kare kaina tunda komai da nai is due to ky selfishness and greed."

  Bai amsa ba ya shige d'akinsa, Mumy tabi bayan dakin da kallo tare da share kwalla.

  Shima yana shiga ya zauna a bakin gado tare da rufe fuskarsa da hannayensa biyu.

  Mikewa yai tare da yin wanka yasa kaya ya dau jakarsa yai waje ganin lokacin aiki yayi.

  Little ya gani a zaune bai kulata ba yai waje, itama kasa binsa tai dan jikinta duk ya mutu.

  Ashraf a gun ajiye motoci yaga kawu shima zai fita, da saurinsa ya karasa gun kawun wanda har abin yaba kawu mamaki, Ashraf ya karasa tare da cewa "dama gunka zan fara isa in naje Company."

  Kawu ya kalleshi yace "me? Ka bada hakurin laifin daka aikata?"

  Ashraf yadan yi dariya yace " laifi? Basan na aikata laifi ba, sannan magana ce ta inasan kai appointing dina a matsayin chief director a company."

  Kallan mamaki kawu yamai yace " Ashraf meke damunka?"

  Baki yadan motsa yace " meke damuna kuwa? So nake inyi sauri in amshi abinda yake a matsayin nawa, me? Laifi ne yin haka?"

  Kawu ya saki baki yana kallan Ashraf, Ashraf yace "sai naga takarda." yana kai nan ya shiga mota yai gaba.

   Nafi kam yau wunin daki tai da azahar Mumy ta aiko akan taje, bayan sun gaisa Mumy fuska a hade tace " Nafisa so nake ki fadamin gaskiyar meke faruwa."

  Shiru Nafi tai, Mumy tace "ki fadamin ko?"
 Nafi ta kalleta tace "mumy kiyi hakuri."

  Mumy ta runtse ido tace "kina nufin da gaske ya aureki kenan? Tun kafin kuzo garin nan?"

  Kasa Nafi tai dakai, Mumy ranta ya b'aci ta mike tai ciki, Nafi jiki a sanyaye tai waje.

********

  Ashraf ya taso daga aiki yana cikin mota a gun traffic light, an tsayar dasu, shikuma yana kan mashin ta saitin gun da Ashraf yake.
 Ashraf ya leko kansa ganin mai saida ruwan faro ya amsa tare da mikamai dari biyar, yaron yace bari na nemo cangi, kai Ashraf ya girgiza mai yamai alama da hannu akan yaje kawai.

  Yaran ya juya yana murna, shikuma dake kan mashin ya leko dan ganin me wannan abin arzikin.

 Kallan mamaki yamai da sauri ya sauka daga kan mashin din ya matso inda Ashraf yake yace " Wazob main ba kai bane Ashaf?"

  Ashraf yamai kallan mamaki yace " Kamar nasan......"
 Dariya yasa yace " bari nama inkiya ta, Do you went?🤔"

*#ASHRAFEENAH TEAM*