Sunday, 25 December 2016

JALALUDEEN 26

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*

   *To u My Beely Badaru, Happy Birthday Sis, wish you long life and Prosperity.* ........���������� *Have fun it's ur day Beely.*��������������


   No. 2⃣6⃣

   Mikewa Seemah tai tare da zama a kasan gun shima Jalal ya zauna kusa da ita kallan nesa da gun tai daji ne a gun, sannan tace " Deen Inama zan iya tsayar da lokaci?" Kallanta yau sannan shima ya kalli gun yace in kika tsayar da lokaci muna nan yaushe zamuyi aure kenan?

  Murmushi tai sannan ta juyo takurama ido tace " kana ganin za'a amince dani a gidanku?" Kai ya d'aga mata yace " karki damu da wannan ni nasan me zanyi akai."
   Ta d'auke idonta daga kanshi sannan tace " Ban tab'a tunanin zanji ina bukatar kasancewa da wani har inji inasan inyi aure ba."

  Ajiyar zuciya yai ya kura mata ido ji yake kamar ya d'auketa su gudu, Juyowa Seemah tai itama ta kalleshi idanuwansu ya had'u da juna, jitai ta kasa d'auke ido daga kanshi, wani irin kallo sukema juna mai ciki da ma'anoni daban-daban a hankali Jalal yakai hannu gefen fuskarta yace " Meemah I promise you this,  I will always love you."

  Idanu ta lumshe sai ga hawaye sun zubo mata, Jalal ya kalleta yace menene? A hankali ta bud'e ido tace " Deen akwai time d'in da hawaye ke bani mamaki, suna zuwa a lokacin bakin ciki, sai dai akwai lokacin da in farin ciki yama yawa sai kaji hawaye."

   
    Sauke hannunsa yai daga fuskarta sannan ya mik'e yace " Okay tunda haka ne mu gudu mubar garin." Mik'e wa itama tai tana dariya tace " what? Mu gudu muje ina?"
   Juyowa yai ya d'ana mata hannunsa a goshi ta rik'e gun cikin shagwab'a tace ka sake ko? Yace wasa nake miki so nake insaki dariya ke kuma naga kina neman d'aukan abin serious.

  Juyawa tai tana kokarin haurawa sai dai ganin abin da wuya yasa ta juyo ta kalleshi tace na kasa, Murmushi yai sannan ya matso tare da mik'a mata hannu yace " kina da ni shine kike cewa kin kasa?" Hannu ta bashi nan suka fara hawa, suna isa suka shiga mota suka juya zuwa gari, sun tsaya a traffic light sai ga wani ya kawo agoggon hannu, guda 2 ne a kwallin iri d'aya sai dai d'aya na mace ne d'aya kuma na namiji komai na agoggon iri d'aya ne, Seemah ta kalli me agoggon tace bani wannan, nan ta siya yana tafiya Jalal ya kalleta yace dama kina siyan abin kan hanya? Hannunsa ta kalla dake jikim sitiyarin mota bata tankamai ba kawai ta fara sa mai agoggo, kallanta yai da mamaki yace me kikeyi hakan?

  Bata tankamai ba sai data gama sannan itama tasa nata ta jira hannunta kusa da nashi kallan agoggunan yai komai nasu iri d'aya murmushi yai yace anko kikeso muyi ko me?

  Hannu ta buga a goshinta tace "Oh God ya zanyi da Deen? Baisan komai a harkar soyayya ba."

  Jalal ya had'e rai yace " to in ba anko ba menene wannan?" Ta kalleshi tace " Couple watch ne baka sani ba?"

  Had'e rai yai ganin an basu hannu yaja motar, Seemah ta kalleshi tace kasan meye ma'anar abindq mukasa? Bai amsa mata ba ta cigaba da cewa " it will always bring us together, haka ake cewa a England magic d'in abin kenan, sannan daga yanzu karka tab'a cirewa daga hannunka in ba haka ba........"

   Sai kuma tai shiru  kai ya girgiza yace " in ba yarinta ba mezai sa kiyi believing akan wannan shirman in na shire kuma sai me? Sai mu rabu ko........"

   Da sauri tace "please kai shiru, kasan me? Mu acan in tsakanin saurayi da budurwa wani ya cire nashi to yana nufin wanda ya cire d'in bayaso a cigaba da relation ship d'in."

   Jalal yace " inkuma ya tsage ko wani abun fa?"

" worse scenario kenan, alamar akwai bad abu dazai faru tsakanin masoyan."

  Hararta Jalal yai yace " Kuma ke kina fad'amin kin yadda da wannan shirman?"

  Tace " ba hadda bane mu acan munyi believing da haka ne."

  Kai Jalal ya kara girgizawa yace " na manta ashe 'yar 20 yrs ce."

  Harara ta makamai batace komai ba ta juya kai tana kallan titi.


   Sunje daidai shiga kwanar gidansu motar Habib na fitowa daga layin, clashing sukai Habib yabi motar da kallo, tabbas motarsa ce, Kallan na ciki yai baidai gane ba saboda suna tafiya yadai ga namiji sannan a kwai mace a gefensa kamar Seemah.

    Har sun hau titi hankalinsa ya kasa kwanciya ya kalli Driver d'insa yace mu koma gida, Seemah kam Jalal na ajiyeta a waje yace bari na wuce zan d'an tsaya a company kafin na wuce, ta kalleshi tace dagaske gobe zaka Birnin gwarin? Kai ya d'aga mata yace " dole insan abinda zanyi kafin sukai kud'i." Kai ta d'aga tace " I will miss you." Shima yace mee too.

  Fitowa yai ya fara tafiya yana kallan motar ta wuce sai dai Habib bai ga fuskarsa ba sai bayansa daya gani, Suna zuwa kofar gida Seemah na fitowa,  tana ganin motar Habib ta karasa kusa da motar, Habin ya zuge glass yace" Kanwata daga ina kike?" Ta kalleshi tace guri mai dad'i yaya.

  Gaban Habib ne ya fad'i guri mai dad'i? Ya fad'a yana kallanta, tace " yaya kaje ka dawo yau da daddare sai muje gun Dad inada abinda zan fad'a muku, tafad'a tana kallan agoggon hannunta.

  Habin ya gyad'a kai yace shikenan ba dad'ewa zanyu ba, amma wanda ya kawoki kamar ba Bala bane? Murmushi tai tace Some One Special ne yaya, ka bari zancen dazamuyi dakai kenan da daddare.

  "Okay bari inje, Amma Some.........."

Katseshi tai tare da cewa bye yaya, tafad'a tare da shiga ciki,  key kawai ta ba Bala ta shiga gidan fuskarta d'auke da tsantsar farin ciki.





  Dad sai jeka ka dawo yakeyi a d'aki, yarasa daga inda zai fara tufko zaren sam komai ya cud'e mai, Ammar shine kad'ai solution d'insa,  waya ya d'aga ya kira Ammar, yace Ammar ka taho Nigeria gobe, inyaso kabar Junaid akan harkokin aikin shi kad'ai, wani farin ciki ne ya kama Ammar yace amma Dad step mom fa? Shi Dad sam yama manta da harkarta, yace kabarta acan ai ba wani abu bane, kuma za'abar gida ba kowa ne? Ammar yace " Dad na gode kamar kasan hankalina nakan Kanwata wlh, Dad yai murmushi yace kaje kai booking flight,  nan sukai Sallama.

   Ammar wani sanyin farin ciki ne ya kamashi ashe zai ga kanwarsa kafin 1month? Kaiii shi harya kosa goben tayima.


  Hmmmm

© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*


��‍♀
.

No comments:

Post a Comment