*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
1⃣1⃣
Ashraf ne ya kalleta kadan yace "Aneesah tailorn ki kuwa yana nan? "
Fuska ta kara daurewa tamau tace " menene? "
"kayan Nafisa nake tunanin muje akai mai can naga ba laifi ya iya d'inki sosai. "
Jitai zuciyarta na neman tsagewa saboda takaici, rasa ma mai zata cemai tai, kawai sai ido ta bishi dashi, ganin kamar bai ma fahimci ranta a b'ace yake ba yasa tace " Yaya d'anyi parking."
Cikin mamaki ya kalleta yace " parking kuma? "
Kai ta d'aga hakan yasa ya gangara gefen titi, ta bud'e kofar ta sannan ta kalleshi tace " randa zaka fita domin ni ka d'aukoni amma bazan zauna kusa da kai domin wata ba. " tana kai nan tai waje, ya bita da kallo cikin mamaki, me take nufi domin wata?
Yana kallanta ta tari adaidaita, ga magrib ta kawo kai,shima ya ja mota yai gaba.
Aneesa na shiga mota ta fara matsar kwalla dan tsabar takaici ita zai d'auka su zaboma wannan kucakar kaya?
Tana isa gida ta wuce gun ummanta da gudu nan ta sanar da Ummanta duk abinda ya faru sannan ta d'ora da cewa " Umma kinga lesukan dana zab'a kuwa? Na d'auka nawa ne? Ina wannan kucakar ina sa kayan dubu talatin? "
Umma ma da ranta yakai kololuwar tashi tace " kwantar da hankalinki ita d'in banza? Har ta isa tasaki kuka? Bare har ta had'aku fad'a da Ashraf?"
Aneesa ta goge kwallarta tace " Umma me Ashraf yake cemin? "
"Neesah mana, tun kina karama yake fad'a miki haka shi yasa wasu ma haka suke ce miki."
Aneesa tai kwafa tace " to Umma tunda na cemai wannan yarinyar ta d'auka ita ya kira d'azu bai sake cemin Neesah ba har yanzu. "
Umma ta kanne ido cikin b'acin rai tace " Aneesa kada ki kuskura ki kara yadda Ashraf yasan bakyasan yarinyar nan, sannan karki kara yimai musu akanta."
Aneesa ta mata kallan mamaki, Umma tace " tabayan gida zamu b'ulo mata, ni na fad'a miki bazata cika sati a gidan nan ba zata d'auki tsuman kafafuwanta tayi gaba. "
Aneesa ta jinjina kai alamar gasuwa tace " Umma ni ko ganinta ma bana sanyi wlh. "
Umma tai murmushi tace " d'aure kinji 'yata, sati d'aya yayi yawa. "
Nan sukai murmushin mugunta su dukansu.
Nafi kam tana zaune a d'aki ita kad'ai mahaifinta ne ya fad'o mata a ranta tace " ko baffa yana me? "
Jitai an kwankwasa kofa hakan yasa ta mike tare da yafa d'an kwalinta ta bud'e kofar, Matar data gani d'azu itace ta gani yanzu, ko ba'a fad'a ba tasan Mahaifiyar Ashraf ce, murmushi ta mata sannan tace "fito falo muyi magana."
Tai gaba Nafi ta bita a baya, akan kujera ta zauna hakan yasa Nafi ta zauna daga nesa kadan a kasa, Mumy ta kalleta tace " ya sunan? "
"Nafi. " ta fad'a kanta a kasa.
Mumy tace " Nafisa kenan ai."
Nafi tace " Eh." tai maganar cikin sanyin murya.
Mumy ta kalleta da gani batafi sa'ar Little ba tace " kinsan ko ni wacce? "
Nafi tad'an kalleta kad'an sannan tace " Mamar Dan Binni ko? "
Mumy tai dariya tace " Ashraf kenan? "
Kai ta d'aga itama tana murmushi, Mumy tace " Nafi iyayenki fa? "
Kallan Mumy tai jiki a sanyaye batace komai ba, Mumy tace " Nafi karkiji komai ki sanar dani duk abinda ya faru babu wani abu, ni mahaifiyar Ashraf ce."
Nafi tai shiru me zatace? Me zatace?
Jitai Mumy tace " Nafi!! "
A hankali Nafi tace " Mahaifiyata ta koma saudiyya da zama, mahaifina shine yake kokarin aurar dani ga babban mutum shine Dan binni ya taho dani. "
Mumy tai shiru ba shakka yarinyar abin tausayi ce amma ita tasan Ashraf sarai shi ba mai shiga abinda bai shafeshi bane bare har ya d'auko yarinya daga gaban mahaifinta.
Ta kalli Nafi tace " Kidinga kirana Mumy kamar yanda kowa yake cemin, sannan ki saki jikinki kamar nan ma gidanku ne. "
Nafi ta d'ago ta kalli Mumy idanunta suka ciciko, Mumy tai murmushi tace " Karki damu kinji? Sannan karki kara cema Ashraf dan binni kidinga cemai Yaya kamar yanda kowa ke cemai. "
Ta d'aga kai, ba shakka yanda taga yanayin 'yan gidan lalai in tsautsayi ya sa akasan an d'aura musu aure da Ashraf to fa lalai tanaji ko Mumy bazata sakar mata fuska ba.
Nan Mumy ta mike tace " Little ba ta dawo ba? "
Nafi tace " eh. "
Mumy ta jinjina kai sannan tai waje.
Nafi tabi bayanta da kallo sannan tai murmushi.
Mumy na fitowa daidai nan Ashraf ya dawo daga masallaci yana shirin yima little magana, ganin Mumy ta fito yasa gabansa ya fad'i, yasan mumy da fasaha da iya bugar ciki da alama taje ta bigi cikin Nafi ta fada mata komai, Mumy na wucewa yai wuf ya shiga bangaren.
Nafi lokacin ta mike kenan zata shiga d'aki, jin sallamar Ashraf yasa ta tsaya cak ta kasa juyowa sai dai ta amsa, Ashraf ya shigo da hanzari yazo daf da ita yanda har numfashinsa take jiyowa hakan yasa gabanta ya shiga bugawa, juyowa tai cikin tsoro hakan yasa suka fuskanci juna daf da daf, gabanta ne ya cigaba da fad'uwa har tanaji kamar shima yanajin bugun da zuciyarta yake.
Shikam cikin rashin damuwa yace " Nafi me kika cema Mumy?"
Kasa magana tai sai bakinta dake motsi shi kadai, Ashraf cikin takaici yace " kin fada ko? "
Kai ta girgiza alamar a'a, yace " ke nake jira me kika ce mata? "
Gaba d'aya jitai ta kasa magana, da sauri ta murda kofar d'aki ta shige tabarshi a nan, tana shiga ta sulale ta zauna a kasa, ya za'ai ya matso mata haka daf yace wai tai magana?
Ashraf yabi dakin da kallo cikin takaici ya juya yai waje, yana zuwa kofa Aneesa na shigowa, tana ganinshi tai murmushi tace " Yaya sry ina gun Umma ne. "
Fuskar nan a had'e dama ransa ya gama b'aci yace "Ni har zaki rainawa hankali muna tafiya dake ki fita ki hau adaidaita? "
Kallansa tai cikin mamaki ta d'auka hakuri yazo bata, ta daure tace " Yahkuri Yaya dazun ne raina a b'ace yake. "
"Na gane" kawai yace ya wuceta yai gaba.
Kallansa tai cikin mamaki.
Ashraf yai waje a zuciye, d'akinsa ya wuce.
Itakam Nafi anan take a zaune har Little ta dawo wajen Isha'i, ta kalleta tace " Nafi me kike a nan? "
Nafi ta mike ba tare datace komai ba ta nufi ban d'aki, sai kuma ta dawo tace " Maryam taramin ruwa inyi alwala dan Allah. "
Little tai murmushi sannan ta ajiye takardun data amso ta tara mata.
Little ta kula da yanda Nafi take sallah tasan kuma da alama batamasan me ake cewa ba, sunci abinci wanda Little ta d'auko musu sannan suka zauna hira, Little tace Nafi ta bata labarin rayuwar kauye.
Nan Nafi ta fara bata labaruruka tace " ni ba shiga mutane nake ba amma fulanuwa masu tsayawa a rafi gunsu nake zama.
Little tayi dariya sosai in taji wani labarin cikin labarin ta bige cikinta akan sallah.
Nafi tace " Ni kawai yi nake yanda naga Innata tanayi. "
Little tace "Zan koya miki yanda akeyi. "
Nafi cikin farin ciki ta amsa da to.
Sun dade suna hira sosai kafin su kwanta.
***********
A bangaren Mumy kuwa ta sanar da mijinta abinda ya faru acan sannan ta karasa maganar da cewa " Alhaji kasan halin Ashraf tunda kaga ya d'auko yarinyar nan to tabbas tausayinta ne yamai yawa gashi ta taimakeshi. "
Kawu yai shiru can yace " shikenan Hajiya dama ni ban ce komai ba mamaki nake yanda akai Ashraf har ya shiga abinda ba nashi ba. "
Mumy ta ce" nima wannan abun ya ban mamaki sai dai inaji a jikina akwai dalilinsa nayin haka. "
Kawu yai murmushi yace " ai dama Ashraf baya laifi. "
Ta kalleshi kawai tai murmushi batace komai ba.
Ashraf kam ya kasa zama,yanzu in akaji ya auri wannan kucakar ai an gama zubar mai mutunci, hakan yasa ya kira wayar Mumy.
Da mamaki Mumy ta kalli mijinta sannan ta kalli wayar, cikin tsananin mamaki ta daga tace "Ashraf? "
Gyaran murya yai sannan yace " Mumy dazu me Nafi ta ce miki? "
Mumy da mamaki tace " me ya faru? "
Yace " ba komai, sai da safe. "
Da sauri ganin zai kashe wayar tace " Ashraf!"
Naam kawai yace.
Nan ta sanar dashi duk yanda sukai, ajiyar zuciya yai sannan yai saurin kashe wayar, mumy tabi wayar da kallo cikin mamaki da rashin fahimta sai dai hakan a tabbatar mata akwai wani abu.
Ashraf yabi wayar da kallo tare da furzar da wata iska yace " Da alama tanada wayau."
Murmushi yai sannan ya zauna a bakin gadonsa.
*THE INNOCENT TEAM*