*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
4⃣
D'akinta ta shiga tana tafe tana layi, shikam yana jin motsinta yai saurin kwanciya dan ya tabbata bazataso wani yaji wannan mumunan abun ba, Nafi na shiga ta karasa kusa dashi ta zauna hawaye ne kawai ke malala a idanunta, can tasa hannu ta goge sannan ta kalleshi cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa tace "Dan binni yazanyi da ke? Gashi baki farfad'o ba bare ki bar wannan gidan mai cike da abin takaici dasan zuciya. "
Zuciyarshi ce ta karye da mamakin tana cikin wannan halin amma tausayinsa take? Wannan wace irin yarinya ce wacce zuciyarta take da tsananin kyau?
Nafi ta kara sa hannunta ta goge hawayenta sannan ta cigaba " Dan Binni ina cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa, Mahaifina baisan komai ba sai dukiyarsa baya ganin mutunci ko darajar kowa banda ta dukiyarsa, mahaifiyata kuma san kanta ya mata yawa haka na taso a cikin irin iyayen nan, ba wanda ya damu da halin da nake ciki ko wanda zan shiga, a dazu nafijin haushin Baffa akan kin biyan bashin dayai sannan bai damu da in auri sa'ansa ba wanda a cikin 'ya'yansa akwai wad'anda suka girmeni ba. "
Tai ajiyar zuciya sannan ta cigaba " yanzu kuwa nafijin haushin Inna ta, tafi kowa sannin halin Baffa amma duk da haka taje ta ranci kud'i da sunansa, ni kuma da ko naira biyar bangani ba bashi na neman............ "
Kuka ne yaci karfinta ta kasa karasawa, mikewa tai tsaye tace "bari in samoma madara kasha nasan yunwa kake ji."
Tana fita ya bud'e idanunsa ga mamakinsa jiyai gaba daya jikinsa yayi wani mugun sanyi, meyasa mutane basuda imani?
Yanzu me wannan yarinyar tayi da hakan ke faruwa da ita?
Shiru yai yana tunanin meya kamata yai dan cetan rayuwarta? Bata dade ba ta shigo dauke da kwarya karami da chokali, nan ta dagoshi kadan ta shiga bashi, mamaki tayi dan kuwa yau madarar bata zubewa sai dai batai tunanin komai ba.
Shikam sha kawai yake gardin madarar ce kesashi sha sai dai rashin sigari yasa madarar batamai armashi sosai ba.
Ganin yadansha dayawa yasa ta gyaramai kwanciya sannan ta mike tai waje.
A can bangaren Datti kuwa yatafi rigar Mahaifinsa nan ya shiga suka gaisa da iyayensa da 'yan uwansa ya kuma sanar dasu auren Nafi wanda za'a daura anjima, tsananin mamaki ne ya kama Iyayensa da yayensa, mahaifinsa wanda ya tsufa sosai ya kalleshi yace " yanzu Datti za'ai auren Nahi shine sai ranar auren zaka sanar damu? "
Datti cikin halin ko in kula yace " to Kawo menene aciki nima sai yau naji zancen auren. "
Gaba daya suka kalleshi cikin tsananin mamakin kalamansa, Aji mahaifiyarsa tace " Datti me kake san kace? "
Ya kalleta yace " Aji to menene ban fada ba? Nima aradun Allah sai dazu nan na sani."
Tsannnanin akaici ne ya kama Aji ta mike cikin zafi tai gaba hartaje wajen dakinta ta dawo ta kallesu tace " in har na isa da ku babu wanda zaije daurin auren Nahi ta gurin datti sannan ba wanda zai aika mata ko da kwayar samira ce, na sani ba laihinta bane sai dai Datti ya ja mata komai. "
Tana kai nan tai gaba a fusace Tanaji Datti nacewa " Karki damu Aji nima ba kai mata samirun zan ba mijinta inya damu ya sai mata. "
Yayansa Sambo yace " Datti me kake san fad'a? Bazaka mata kayan daki ba ko me?"
Datti ya mike yace " nifa nazo sanar daku ne bawai cewa nai kuzo ba, yar nan tawace ra'ayinane in mata kayan daki ko inki. "
Kallan mamaki suka bishi dashi inda sabo sun saba da halin Datti sai dai mamaki suke tunda yanzu abun ya shafi zancen 'yarsa.
***********
Sukam su Ali da ragowar abokansa murna suka shiga tayashi akan yasamu abu a bagas, lalai sun yadda Datti baya cikin hayyacinsa, waye zai saida 'yarsa saboda dubu ashirin?
Sukam sunje sun sanar da liman nan suka shiga shirye shiryen, Ali yasa aka share mata daki daya acikin gidansa, matansa kansu basuyi kishi ba jin yarinya ce suna ganin baifisu kara samun mai musu girki ba.
**************
Nafi ta gama aikin gida tsaf ta gyara dabobbi, shikam zaune yake yana addu'a fatansa d'ayane Allah ya bashi ikon taimakon wannan baiwar Allah, kamar yanda ta taimakeshi, yanaji a kasan ransa kamar Allah ya kawoshi garin nan ne dan ya ceci wannan baiwar Allah.
Tunani guda d'aya ne ya tsayamai dole ne shi ha dauki nauyin biyan wannan bashin kila itace mafita.
Mikewa yai ya fito daga dakin, ba kowa a wajen hakan yasa ya fita daga gidan.
Toh fah!!!! Ganinsa yai a tsurar daji baya ganin komai sai daji mamaki ne ya kamashi, yanzu ace mutum ne yake rayuwa anan? Sai kace mara gaskiya?
Jiyai ance kai waye nan? Da fillo akai maganar, Juyawa yai dan jin yasan kamar mai muryar nan.
Ya kalleshi tare da da dan yin kasa dakai sannan ya mikamai hannu alamar gaisuwa, Datti ya bugamai harara sannan yace " me kake anan? "
Yaa fada tare da kallan kayan jikinsa kamar yasan kayan nan, shikam dan binni ya daure ya sauke hannunsa sannan yace " Dan Allah cikin gari nake tambaya.
Jin yamai hausa yasa Datti yace " Ka mike nan hanyar inkai tafiya mai tsaye zakaga gari. "
Bai jira komai ba yace " Na gode yai gaba. "
Datti ya bishi da kallo kamar kayansa, sai dai ta ina kayansa zaije gun wannann kad'on?
Yayi tafiya mai nisa dan har ya gaji sannan yaga gari, a ransa yace nan ne garin?
Kauye ne sai dai yanada girma sosai ga mutane sunata hada hadarsu, wajen wani mai tabir din rake ya tsaya ya mikamai hannu suka gaisa sannan yace " Dan Allah akwai ATM anan kusa? "
Kallan mamaki mai raken ya masa yace " A me? "
Yadan dafa kansa sannan yace " Banki fa? "
Me raki ya kalleshi sosai kana ganinshi duk da rigar dake jikinsa zaka gane ba daga nan yake ba, ya girgiza mai kai alamar bai sani ba sannan yace " amma kaje can gurin masu mashina akwai Dan liti wanda yai karatun boko sai ka tambaye shi. "
Yamai godiya sannan ya karasa gun masu mashina, sallama ya musu sannan ya tambayesu waye D'an liti, wanda ke zaune ya sha riga da wando ya wani tsuke shi a dole dan boko ya kalleshi yace " Yes ganinan. "
Kallansa yai ya wani daura kafa d'aya kan d'aya akan mashin, dariya tadan so kamashi ya daure yace " Dan Allah tambaya nake san ma. "
Dan litti ya dan wani rangwad'a kai sannan yace " what is your ansa? . " wai so yake yace "what is your question?" lol
Dariya ce ta kama Dan binni yai kasa da kansa tareda murmusawa jiyai abokansa sunce " Kai Dan litti ka kure gayu fa. "
Dan litti ya wani sosa keya irin jin dadin nan, Dan binni ya dago sannan yace " So nake in tambayeka ko akwai ATM anan kusa."
Fuska dan litti ya canza yadan gyara zama sannan yace " AT me? "
Dan binni yai murmushi yace " ka gane mana inda ake cirar kudi ba tare da anshiga banki ba. "
Tafi Dan litti yai yace " Ohhhhhh ATN? Ha ha ha kai ne bakamin bayani ba, akwai amma gaskiya sai dai muje can gwaram. "
Dan binni yace " inane kenan? "
Dan litti yai murmushi yace " local gommant d'in mu."
Kai ya jinjina alamar gamsuwa sannan yace " Zai kai minti nawa kan mu isa? "
" A kalla minti 40 inaji. "
Shiru Dan binni yai sannan yace " Muje to Allah yasa mu dawo kan azahar. "
Dan litti yace " Maganar kudina fa?"
" in mun dawo mayi maganar ai tare zamu mu dawo tare. "
Dan litti ya kwama glass dinsa sannan yace " Hau muje. "
Dan binni ya hau yana tunanin yanda zaiyi tafiyar kusan hour daya da rabi akan mashin shida rabonsa da mashin har ya manta inbadai race suke da 'yan uwansa ba shima race d'in sun dade basuyi ba kasancewar canjin yanayi da suke fuskanta a tsakaninsu.
************
Nafi zuciya d'aya tana gama aiki ta shigo gun D'an binni sai dai me? Ba shi ba alamarsa, tsoro da fargaba ne suka kamata nan ta fito ta shiga nemansa sai dai samm babu shi, idanunta ne suka ciciko da kwalla tace " Wato ya warke shine ko sallama baxai min bako? Me yasa mutane suke min haka? Kowa baya sona? Kowa bai damuwa da halin da nake ciki ko wanda zan shiga? Wato shi kuma wannan zuciyarsa mara rama alkairi ce ko????????
*THE INNOCENT TEAM*
No comments:
Post a Comment