Wednesday, 26 April 2017

ZUCIYA......kowa da irin tasa 10

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*Kuyi hakuri jina shiru da kukai jiya, na shiga tarone wlh kuma dana dawo na gaji.....na gode kwarai da kulawarku da kuma san da kukema littafin nan*😍😍

     1⃣0⃣

  
     Little ce rike da hannunta kawai tana tafiya amma idanunta nakan Ashraf dake tafiya, Aneesa kam har wuya tazo ganin yanda Ashraf ya hauta da fada akan wata banza kucaka,  da saninta ta taho ta mangaje Nafi wanda har sai da ta kusa kai kasa,  Little ta kalleta tace "Haba Yaya Neesa? "

    Aneesa ta kalli Nafi tace "Sorry ban kula ba."tai gaba.

   Little ta kalli Nafi wanda ta kakaro murmushi tace "Maryam karki damu ai bata kula bane, kuma taban hakuri. "

   Little tai karamin hucci tace" Nafi kiyi hakuri. "

   D'aki suka shiga,  Nafi ta zauna a kasa, little na shirin mata magana wayarta tai kara, da sauri ta d'aga tace "Naam Yaya. "

   Daga can bangaren Ashraf yace " Little ki samarmata abinci dan banaji taci wani abinci. "

   To,  little ta fad'a tana kallan Nafi wacce itama hankalin ta ke kan Little tunda taji ance Yaya.

    Little ta kashe wayar sannan ta kalli Nafi tace "kinga Yaya ma ya kula bakici abinci ba."

   Nafi tad'anyi murmushi,  hakab yasa Little tai waje.

    Ashraf kam yana shiga bangarensa ya kwanta a kan kujera doguwa dake falo,  hannu yasa akan goshinsa,  meyasa duk sanda akace za'ai meeting indai har saboda shine sai an b'ata masa rai? Yai dan karamin tsaki zai juya yaji sallama,  muryar Mumy ce hakan yasa ya amsa sama sama.

   Mumy ta shigo ciki, shi kuma ya mike daga kwanciyar da yai ya sauka kasa,  mumy ta karaso ta zauna akan kujera, kansa na kasa bai ce komai ba.

   Kallansa tai cikin tsananin kulawa tace "Ashraf kayi hakuri. "
  Batare da ya d'ago ba yace " Ya wuce ai tunda dai ba wanda ya isa ya fitar da ita daga gidan. "

   Mumy ta jinjina kai sannan tace" Ashraf a gaskiya nima hukuncinka bai min ba,  bana ganin dan ta taimakeka ya kamata ka taho da ita,  sai dai in akwai wani dalili bayan wannan. "

   Bai kalleta ba haka kuma baice komai ba,  Mumy ta cigaba " ba komai nasan tausayinta ne yasa ka taho da ita insha Allah nikuma zan kula da ita. "

   Yanzu kam ya d'ago ya kalli Mumyn sai dai baice komai ba,  tai murmushi dan ta gane yaji dadin maganar ne tace "Ashraf zuwa nai muyi wata magana. "

   Inaji kawai yace.
Tace " Baka ganin lokaci yayi da zaka fara aiki a company d'in mahaifinka?? "

   Kallanta yai cikin mamaki yace " Ba Kawu da Asim suna kula da company d'in ba?  Meye kuma nawa na fara aiki acan?? "

  Mumy cikin damuwa tace " Ash raf mai yasa kake abu kamar bakasan komai ba? Companin nan na mahaifinka ne fa?  Kai kad'ai ne d'ansa sannan ya bar maka share d'in sa gaba d'aya kanada 50% na share d'in  company d'in kafi kowa,  akan me zakayi ta zama a gida bayan ka gama karatu? "

   Ashraf ya mike tsaye yace " Mumy banasan wannan maganar dan Allah. "

   Jikinta a sanyaye tace " Ashraf? "

  Ya d'an kalleta sai dai bai ce komai ba,  mikewa tai a hankali tai waje, yabi bayanta da kallo tare da dafa kansa,  meyasa kowa ba ya hango abinda shi yake hangowa?

    Idanu ya runtse yana tuno sanda akace fatiha an d'aura auren Nafi da Ashraf,  yai wani hucci sannan ya mike kawai ya zari makulli yai waje.

                    ************

     Sosai Nafi ta ci abinci,  ji take wani dad'i na ziyartarta,  tanaji tunda take bata tab'acin abinci mai dadi irin wannan ba,  tas ta cinye wanda little ta zubo mata,  ta kwankwad'i lemon kankana mai sanyi da ke cikin jug,  wata gyatsa tai sannan tasa dariya ita ka dai.

  Ita kad'aice a d'akin dan little ta fita,  tace " oh yau banyi gyatsar nono ko madara ba."

Ta sake yin dariya tace " Kai abincin nan yayi dad'i, wannan kuma ko menene?" ta fada tana d'aga ragowar juice d'in kankanar data sha,  tace " Tabdi lalai akwai abin dad'i a birni."

    Sai dataji abincin ya tsirga mata saboda cin datai dayawa,  tad'au tiren kamar yanda Little tace mata ta maida kitchen.

    Ta fito ta kalli gabas inda little ta mata kwatance, ta fara tafiya,  tafiya kawai take,  gani tai ta b'ata nan ta shiga waige waige,  jitai ance " Ke."
   Juyowa tai cikin mamaki, Ganin umma uwar Aneesa yasa tai saurin yin kasa dakanta,  Umma tace " Dan gidan ku uban me kike anan? "

   Nafi cikin tsoro ta fara magana  cikin in in na tace " Um kitchen nake nema. "

  Umma ta kalli kwanon sannan tad'an tabe baki tace " Kwarai dole ai,  a can kauye ba'a sami damar zakewa aci abinci ba shiyasa ake neman bud'e mana ciki? "

   Nafi wanda jikinta duk ya gama mutuwa ta kasa magana sai motsa baki kawai take.

   Umma ta kalleta kallan banza tace " wuce muje kitchen d'in. "

  Nafi ta kalleta da mamaki, Umma tace " To munafuka bakijini bane kike kif kif da ido? "

   Nafi tai saurin yin kasa dakai,  nan tai gaba Nafi ta bita.

    Sun isa katon kitchen d'in inda masu aiki keta hidima Umma ta tafa hannun ta hakan yasa duk suka taho,  Umma ta kallesu tace " Yauwa dama so nake in sanar daku kun samu kari. "

  Kallan juna sukai na mamaki, tasa hannu ta finciko Nafi tace " gatannan da safe zatazo ta tayaku aiki sannan da rana ma haka."

   Nafi ta kara kasa da kanta, Umma tace "na umarceku ku sata aiki sosai,  saboda ita ta fiku cin riba dan inda zata kwanta yafi naku haka abincinta da suturarta tafi taku. "

   Suka amsa da to,  ta kalli Nafi tace." Ke kuma dan gidanku kullum da sasaafe in ganki anan hakama da rana,  bazaki dinga cin abinci a banza ba. "

  Nafi ta d'aga kai,  Umma taja kunenta tace " kuma wlh inji maganarnan abakin wani ko da Little ce bare Ashraf Allah sai kin gane kuranki. "

  Tana kai nan tai gaba.

  Nafi tai shiru,  jitai ance ajiye kwanukan ki tafi gobe kya fara zuwa,  Nafi ta kalli mai maganar wata babba ce a kalla zatai sa'ar Innarta,  ta ajiye tiren sannan ta gaidasu tare da musu sallama.

                    **********

D'aki ta koma ta zauna a kasa tai shiru,  bacci ne yai gaba da ita.

   

    Ashraf kam bayan ya fito daga d'aki Aneesa yama waya yace ta fito ta rakashi an guwa.

   Jifatu ya wuce da ita,  tanata murna ganin yau gata ga masoyinta,  suna tafiya ne ta kalleshi tace " Yaya ya maganar sa ranar da akai ai tana nan ko? "

   Ya kalleta tare da murmushi yace " eh mana ko musa a kara matsowa da shi? "

  Idanu ta rufe tace " Kai yaya wata biyu ai kamar yau ne. "

Aneesa ta kalleshi cikin tsananin farinciki tace " Yaya wlh ni kad'ai nasan missing dinka danai jiya. "
 
Titi kawai ya kalla baice komai ba sai murmushi da yai.

  A bakin jifatu yai parking, nan ta fito shims ya fito suka shiga ciki,  bangaren kaya na atamfofi lace da mayafai sukai,  ce mata yai kawai ta zab'a,  hakan yasa tai tunanin nata ne,  sosai ta jidi kaya shima yana tayata,  suks wuce gun takalmi,  nan ne dai yace banda takalmi sai dai jaka,  saboda shikam yasan baisan size dinta ba.

  Itakam Aneesa sai farin ciki take har suka gama zaben suka fito,  sun shiga mota ta kalleshi cikin kauna tace " Yaya na gode sosai. "

   Ya kalleta cikin mamaki yace " name fa? "

  Tace "na kaya mana. "

   Murmushi yai yace "Aneesa ke kuma mai zakiyi da kaya?  Duk yawan kayanki? "

  Fuska ta had'e tace " na waye to? "

 

   Ya kalli titi yace " Nafeesa. "

  Gabanta ne ya fad'i cikin tsoro ta kalleshi sai dai gani tai shi ko a jikin sa,  ranta yai mugun b'aci........


   *THE INNOCENT TEAM*

1 comment: