*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
6⃣
Gaba d'aya hankalinsa yakai kololuwar tashi muryar Ali yaji yana cewa " Kai yaro dakai muke magana, Kai zaka aureta amaimako na ko me? Yaran yanzu banda tsugudidi basuda aikin yi inbanda munafirci da shiga shara ba shanu dan ta taimakeka meye naka na shiga shirgin rayuwarta?"
Dan binni ya kalleshi cikin bacin rai yace " kai yanzu in 'yar ka ce zata auri sa'anka ko wanda yafika zakaji dadi?"
Ali ya kwashe da dariya yace " to menene? Baifi karin zumunci ba."
Dan binni zaiyi magana yaji an dafashi, juyawa yai dan ganin waye, ga mamakinsa dan litti ya gani a tsaye a bayanshi, ya kalli Dan litti cikin wani yanayi.
Dan litti yace " Abokina ka fita harkarnan tun kafin kuzo kuna arment."
Dan binni ya kalleshi yace " meye arment?"
D'an Litti ya wani sosa kai su kuma mutane suka kalleshi da sha'awa jin yana turanci.
D'an litti yace " baka gane ba? Kar kuzo kuna musu nake nufi."
Wani kululun takaici ne ya kamashi dama mutanen gun nan sun gama kona mai rai shikuma D'an litti zai so mai da wani sabon takaici wai arguments ne arment?
Kallanshi ya maida kan Liman wanda yake cewa " ni yanzu a wani matsayi nake? Datti yace " Aure za'a daura da Ali yanzun nan."
Ali ya gyara rigarsa, haushi ya kara turnuke dan binni yace " in kuma nace zan aureta fa?"
Gaba d'aya kowa juyawa yai ya kalleshi cikin tsananin mamaki, Datti yace " Kana nufin zaka aurenta?"
Gaban D'an Binni ya fad'i ya daure yace " Eh." Abinda kawaj zuciyarshi take rayamai Allah ya kawoshi garin nan ne dan ya taimake ta."
Matsowa D'an litti yai da kansa saitin kunnen D'an binni yace " I am Crazy? Kasan me kake kuwa?"
Dan binni ya juya ya kalli D'an litti sannan ya kalli Ali wanda yake hucci kamar zaki, shi a tunanin sa ai dan yace zai aureta baza'ace yanzu ba.
Sai dai abinda kunnensa ya jiyo masa ya tada masa hankali, jiyai Datti yace " to Liman yanzu sai a daura da wannan shikuma Ali sai ya amshi kudinsa yai gaba."
Kallan Datti yai cikin tsananin mamaki yace " nikam ka tabbatar kaine mahaifinta?"
Datti ya had'e rai yace " wani banza zance kake yi hakan? In ba 'yata bace 'yar kace?"
Dan binni ya dafa kai zaiyi magana yaji Ali yace " da alama bai shirya ba gwara a daura dani......"
Kallan da D'an binni yamai ne yasa yai shiru, yace " na dauka nace a daura dani?"
Datti yace " to banga alamar kanaso ba gashi mu kana bata mana lokaci."
D'an binni ya ciro d'ayan dubu ashirin d'in wanda ya d'auko domin ba Nafi inzai tafi ya mikama D'an litti yace " Sadaki ne mika musu."
D'an litti ya jinjina kai cikin mamaki yace " Lalai I am crazy." Yana kai nan ya karasa gun Liman yace " wai ga sadakin Wancan."
Liman ya kalleshi yace " to waye zai mai walliyanta? "
Datti ganin damin kudi yasa cikin saurin murya yace " Ladan kawai yamai ai musulmi dan uwan musulmi ne."
D'an binni ya bishi da kallan mamaki lalai mutanen nan basuda cikaken hankali kaf cikinsu ba wanda ya tambayi inda yake? Mugu ne shi? Haka kawai suke neman bashi 'ya ba wani bincike.
Jiyai Ladan yace " Ya sunan ka? "
" ASHRAF" Abinda ya fito daga bakinsa kenan, yana tsaye har aka gama d'aurin auren Nafisa da Ashraf akan sadaki dubu ashirin.
Nan su Ali da mukarabansa suka watse cikin tsananin takaici, Datti wanda ya cafki kudin sadaki ne ya matso kusa da Ashraf yace " Ashaf yanzu inane inda za'a kai ma Amaryarka?"
Kallan Datti yai cikin mugun takaici yace " Na dauka baka damu da inda za'a kai 'yarka ba tunda banga alamun kanaso ka sani ba."
Ya kafe Datti da ido yace " me Nafi take ma wanda kakeso tabar ma gidanka kota halin ka ka?"
Datti yad'an had'e rai yace " Kai Ashaf dan ka zama mijinta an fadama kanada damar fadamin magana san ranka?"
Ashraf ya kalli D'an litti yace " Please d'an jira ta fito mu tafi ka saukemu, dan banga alamar mashin ba ko zaka samomana d'aya saboda mu biyu ne?"
D'an litti yace " ba problem kaje ku shiryo I will came with one. "
Ashraf ya d'an yi murmushi kadan sannan ya kalli Datti yace " a sanar da ita ta shirya dan ni ba anan garin nake ba."
Datti yace " me?"
Ashraf ya juya kai bai kara magana ba, har Datti sai sake magana sai ya fasa ya shiga ciki.
Nafi kam ta kule a bayan gida banda kuka batada aiki shikenan Allah ne kadai yasan wace rayuwar zata fara daga yau, ina zata sa kanta?"
Jitai Hanne na kiranta, hakan yasa ta goge hawayen ta tafito, Hanne ta kalleta tace " kuka kike?"
Nafi tace " a'a."
Hanne tai tsaki tace " wato memakon kiyi kuka a gabanmu mu samu damar lallashinki ki gwammace kinyi kuka ke kadai kin share hawayenki? Nafi nikam ina tsananin mamakin halayenki."
Tai gaba, Nafi ta bi ta a baya, har sunyi hanyar dakinta ta kalli igiya inda ta shanya kayan D'an binni ka ra sawa tai ta zare rigar ta rike a hannunta.
D'aki ta shiga ga mamakinta Datti ta gani zaune akan tabirma wanda rabon da ko dakinta ya leka yaga a wani hali take ciki ita kanta ta manta.
Shiga tai kanta a kasa, ta gaidashi sannan ta zauna kusa da Maman Hanne.
Datti ya kallesu yace " To aure dai an daura sai dai an samu canji daga Ali zuwa wani Ashaf."
Cikin tsananin mamaki Nafi ta d'ago ta kalli Baffa tace " Ashaf?"
Datti ya jinjina kai yace " Kwarai nikaina nafisanshi akan Ali da alama yana da arziki sannan kuma shi saurayi ne."
Maman Hanne ta kalleshi tace " nifa sam ban fahimci me ake nufi ba, banga ne daga Ali ba an koma Ashaf? Meye ma wani Ashaf? Ni bantaba jin sunan ba."
Datti ya buga mata wani kallo yace " meye naki a ciki? ' yata ce ba 'yar uban kowa ba sannan in baki tabajin suna Ashaf ba yau ai kinji."
Ya mike rai a bace sannan yace " ke kuma ki shirya yanzun nan dan yace ba agarin nan yake ba zaku wuce yanzu."
Kallan mamaki kawai take ma babanta ta sani shi dabobinshi su kadai ne abinda ke gabansa kuma suka dameshi sai dai bata taba tunanin zai ma 'yarsa ta cikinsa haka ba, sai kace wata kaza?
Ganin kallan datake mai yasa yace " in tunanin sadakinki kikeyi kima manta dan nima na dauki rabona na satar da uwarki tamin, yana kainan yai waje.
Nafi kam kuka ma kasa zuwa mata yai jitai idanunta sun kafe kaf, sai dai rigar dake hannunta kawai ta shiga ninkewa jitake zuciyarya kamar zata tsage, Maman Hanne ta kalleta tace " Nafi ki taimaka ki fadamin abinda ke faruwa dan Allah."
Nafi ta kalleta tace " Auntu ko na fada miki menene amfani? Tunda aikin gama ya riga ya gama? "
Hanne ta mike cikin takaici tai waje.
Nafi kam a zaune kawai take tana jiyo muryar Datti yana cewa suyi sauri.
Ashraf kam yana tsaye a waje tunani sun taru sun mai yawa, ina zai sa kansa? Mai zai cewa masoyiyarsa kuma 'yar uwarsa wacce saura wata biyu a daura musu aure? Yasan ta sarai yanda take tsananin so da kishinsa lalai zata iya yin komai inhar taji abinda ya faru, kansa ya dafa wanda yakeji yana sara mai.
Karar mashin ne yasa ya kalli hanya, Su D'an litti ya hango nan suka karaso D'an litti ya kalleshi yace " yama kace name d'inka?"
"ASHRAF. "
D'an litti yai murmushi yace " Gaskiya an cucen da aka samin D'an litti sunan ka yafimin dadi."
Ashraf yai musrmushi sannan yace " D'an litti kenan."
Datti ne ya fito ya tsaya kusa da Ashraf yace " Ashaf gatannan amma ya za'ayi in anaso aje gunta ina zance? "
Ashraf ya kalleshi sannan yace " Kano anan garin nake, sannan ai kasan sunana."yai maganar cikin bacin rai.
D'an litti ya tafa mai yace " Haba? Living Kano? I also came to kano."
Ashraf ya furzar da iskar takaici yace " nikam D'an litti kadingamin hausa banasan turancin nan."
Dariya Datti yai yace " gaskiya kam, yanzu kenan in wasu zasuje sai D'an litti ka rakasu ko?"
D'an litti yai murmushi tare da sosa keya.
Nafice ta fito sanye da lulub'i Hanne da mamanta na gefenta, Hanne ce ta kalli mazan gun su uku, tace waye mijin a ciki? Ta fada tana fatan Allah yasa ba wannan bane dan ya birgeta Allah yasa D'an litti ne."
Gani tai D'an litti ya nuna wanda yai masifar burgeta da yatsa, dukda rigar kauye ce a jikinsa kana ganinshi kasan daban yake, tadan yi yake tace " to a rike mana 'yar uwarmu dakyau, amma bamu zamu kaita ba?"
. Datti yace " bakiji me nace ba aciki ko kuma wani sabon kinibibi ne hakan? Ai nace su biyu zasu tafi ko?"
Mamaki ne ya kama maman Hanne tace " su biyu? Dama abinda kake nufi kenan? Taya zamu bari 'yar mu ta tafi daga ita sai shi? "
Datti yace " karki damu D'an litti yasan gidan."
Tai shiru, Nafi kam hawaye ne ya fara zubo mata itakam tana ganin rayuwa? Wasa wasa kaza ma ta fita matsayi itakam.
Jitai ance " Ina rigata? Ko kin barmin wannan?"
D'agowa tai cikin tsananin mamaki, idanunsu ne suka hadu........gabanta ne ya shiga fad'uwa sai dai ta kasa dauke ido daga kansa, ya sakar mata wani sansanyan murmushi........
*THE INNOCENT TEAM*
Wow! This novel is really enjoyable. More grease to your elbow sister. But you need to be a little faster coz the novel is too slow
ReplyDeleteEnter your comment...
ReplyDeletereally love this story.
pls continue old woman.
frm this 6 i didnt cee any other post again pls sis do post on time. thank u
may d lord increase u in knowledge