Tuesday, 18 April 2017

ZUCIYA.......kowa da irin tasa 5

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

5⃣

   Sun fara tafiya akan Mashin Dan litti yace " Amma da alama kai ba dan garin nan bane ba ko?"

  Murmushi yai sannan yace " ni ba dan garin nan bane kuma yau nakesa ran barin nan."

   Dan litti yadan juyo sannan yace " When are u fom?"  Ya fada cikin irin isar nan wai shi a dole kwarare, Dariya Dan binni yasa hakan yasa Dan litti yace " U don't say English? "

   Dan binni kam dariya yake yi har ransa hakan yadan sa ran Dan litti ya soso, yace " Malam menene hakan ka sani a gaba sai dariya kake?"

   Dan binni ya daure yace " A wacce makaranta kau karatu ne haka?" Mazewa dan litti yai yace " Anan makarantar Gomnati ta Gwaram."
  Yadan kare hade rai yace " what matter?"

    Dan binni yace " lalai naga kanata kokari ne wajen yin turanci."

  Dan litti yai wani murmushin isa da takama yace " Kaf garin mu ni kadai ne nai karatu hakan yasa mahaifina ke ji dani kamar kwai sannan yan mata suke sona."

    Dan binni ya jinjina kai yace " hmmm gaskiya kam a garin Jahilai dama ai......"

  Dan litti yace " me kace?"

  Kai ya juya batareda yace komai ba.

    Inya tuna turancin Dan litti kawai sai ya saki murmushi lalai ana kwab'a a kasar nan.

    Tun yanajin dadin tafiya yana kalle kallen kauye har ya gaji kawai ya zauna yai dif.
    Yanaji Dan litti nata bashu labarin makaranta, shidai kam jinsa kawai yake fatansa Allah yasa suje su dawo kafin bakin alkalami ya bushe.

     Sunyi tafiya sosai kafin su isa Gwaram, nan Dan litti ya karasa bakin banki ya tsaya, ya kalli Dan binni yace " Gashi mun iso."

   Dan binni ya kalli bankin sannan ya kalli ATM din dake gun guda biyu ne a jere saidai mutanen dake tsaye a gun sunfi 20, wata iska ya furzar sannan yace "  Dan litti ba wani sai wannan?"

  Dan litti ya kalli mutanen gun yace " Kasan karshen wata yayi ko munje wani gun ma hakan ne gwara mu tsaya anan."

    Dan binni ya kalli mutanen gun sannan ya tuna Nafi wacce ake neman ruguza mata rayuwa, takawa yai yaje har ya tsaya a layi yaga abin kamar bazai yiwu ba, hakan yasa ya karasa ya fara neman alfarma, abinda tunda yake arayuwarsa bai tab'a yi ba kenan wai ace shi ne ya rusunar da kai yake neman alfarma gun wasu, ya taso rayuwarsa ba abinda ya rasa, haka ya daure yai ta neman alfarma har ya dawo na 8, suna nan tsaye har aka zi kansa, ya zaro wallet dinsa dake aljihun wandansa ya ciro ATM card dinsa ya sa.

   Dubu Ashirin ashirn sau biyu ya cira sannan ya ciri dubu goma ya kama hamsin kenan, ya musu godiya ya karasa gun Dan litti,  tafi Dan litti yamai yace " Gaskiya ka birgeni yanzu mu tafi?"

   Dan binni ya kalleshi yace " yunwa dai nake dan ji."

  Dan litti yace " Ga mai Yam  da Egg can muje sai ka siya."

  Murmushi yai sannan yace " Lalai Dan litti dan boko."
  Dan litti ya shafa keya yace "  Can we went?"

  Dan binni ya juya kai sannan suka karasa gun mai doya, kashi biyu yace asa musu wato shida Dan litti, har zasu juya sai ya koma yace a kara samai wani daban, haka kawai yaji zuciyarshi ta tuno mai da Nafi.

   Dan litti ya shiga godiya nan suka ci sukasha leman kwalba sannan suka mike suka juya.

              ************


     A can rigar Datti kuwa Nafi ce zaune a dakinta banda kuja ba abinda takeyi ga bakin cikin auren da za' a mata gana guduwar dan binni, mamaki ne ya kamata dataji mutane suna sallama, nan ta fito dan tasan su ba baki suke ba tunda Baffa baso yake ba, turus ta tsaya tana kallan kanwan mamanta, sai dai ta kasa farin cikin ganinta sam.

  Ganin haka yasa ta matso tare da rungume Nafi tace " Nafi shine kina ganina zaki shareni? Bayan har da kawarki Hanne nazo miki da ita? "

  Nafi ta maida hawayenta sannan tace " Aunty nayi mamakin ganinki ne."

  Tace" ai daga ke har Datti baku kyauta mana ba wau sai dazu aka turo mana almajiri wai yau ake auren ki? Haba Nafi ai ko Datti bai sanar damu ba ke kya fada mana ai."

  Nafi kam kasa magana tai dan batasan taka maimai mema zata ceba cewa zatai an bada ita biyan bashi ko me?

   Hanne ce ta matso kusa da ita tace " Nafi ya naga ba kowa a gidan? Kamar ba biki za'ai ba?"

   Nafi ta share hawayenta tace " eh kinsan Baffa bayasan mutanene shiyasa."

  Baki Hanne ta tab'e tace " amma dai duk da haka,  sannan ke ma kalleki kamar ba Amarya ba ko wanka ma da alama bakiyi ba."

Nafi tadan juya kanta gefe, Nan Maman Hanne tasa Hanne ta debo ruwa, da kanta ta tasata gaba sukaje ta wanketa fes, sannan suka fito, kayan Nafi ta kalla sam bana arziki bare aje ga sabo haushi da tausayi suka kamata ta kalli Hanne tace " Hanne da alama ke zaki taimaka ki ciro kayan jikinki ta saka inyaso ke sai kisa nata."

  Hanne ta kalli Nafi tace " Allah Nafi shi yasa kike ban haushi ke wai bazaki taba cewa asai miki kaya ba? Ko sanda innarku nanan itama banga ta wani damu da miki dinki ba, yanzu dan Allah meye amfanin hakan?"

  Nafi tai kasa dakai, Hanne taja wani dogon tsaki tace " sam ita wannan a kidahuman ma ita ta dabance, fa tsinanan kawaici da hakuri, wallahi babu inda zakiji ba'a cuce ki ba indai haka zaki cigaba."

  Maman ta tace " to ya isheni uwar 'yan masifa."

  Nan Hanne ta cire kayanta tana masifa.

  Nafi ta saka kayan sun amsheta kuwa nan Hanne ta shafa mata hoda tana shirin yi mata ja gira da kwalli Nafi tace " Bashi Hanne kema kinsan banasan kwalliya."

  Hanne ta mike cikin takaici tace " ni dai kam ban taba ganin mutum irin ki ba, gaskiya Nafi kina neman addu'a ni wallahi haushi wannan halayen naki suke bani."
Tana kainan tai hanyar waje, jitai Nafi tace " kiyi hakuri Hanne ba bata miki rai naso yi ba."

  Hanne ta kara had'e rai tace " kinganta ko Goggo? Yanzu me tayi na bada hakuri dan Allah?" Tai waje ba tareda ta jira amsa ba.

Maman Hanne ta kalli Nafi tace " Nafi kiyi hakuri kinsan kawartaki akwai masifa."

   Hanne ce ta shigo cikin mamaki tace "  Nafi naga sun fara taruwa inaji yanzu za'a daura, ni ko mijin ban gani ba."

  Gaban Nafi ne ya fadi tanasan yin kuka ba kuma taso su Hanne da mahaifiyarta susan halin da ake ciki, kasa kawai tai da kanta tana karanta Inalilahi a zuciyarta.

    Ango kam yasha babbar riga haka kuma ya taho da abokanansa dayawa dama yan uwa da makota, sannan sun taho da liman da maroka,  Datti ne yashigo gida fuskarsa a sake wasai ko a jikinsa, ya zura riga babba shima, yanajin Mahaifiyar Hanne na gaisheshi ya shareta yai waje.

  Ta birma manya aka shimfida musu sannan Ali ya taho da goro nan aka ajiye, Aka dan gagaisa sannan aka zauna.

  A ciki kuwa mahaifiyar Hanne ce ta kalli Nafi tace " Nafi amma an miki komai na kayan daki ko?"

  Nafi ta kalleta tare da kakaro murmushi kawai amma batace komai ba, hakan yasa itama tai shiru.

   An gama addu'oi nan aka ce ina Walliyin Alhaji Ali? Wani kanin mahifinsa yace " Ganinan."

Akace walliyin Nafi fa? Datti yace gani.
Kallan mamaki suka bishi dashi sukace " Dakanka malam Datti? Ai kyanta wani dan uwanka na kusa zaka wakilta."
  Datti ya hade rai yace " wannan damuwarku ce amma nine zan zama walliyi a auren 'yata ehe."

  Sunyi shiru, liman ya kalli Ali, kai Ali ya daga mai akan ba komai a kyaleshi, nan liman yace to shikenan yanzu zamu gabatar da.........

  Ji sukai ance " Ba abinda zaku gabatar domin kuwa ni na hana wannan auren."

  Gaba daya suka juyo suka kalli inda maganar ke fito wa, ga mamakinsu wani saurayi ne ya sauka daga kan mashin sannan ya fara takowa gunsu cikin isa da takama, basusan fuskarba sai dai Datti yasanshi dan kuwa bai manta shi ba.

  Dan binni ya karaso inda suke zaune ya gaida liman sannan ya kalli Ali wanda yasha manyan kaya, ba shakka ya girmi mahaifin Nafi lalai mutanen nan basuda imani.

Ali ya harareshi yace " Kai menene kakeyi haka? Ba ka gani aure ake shirin daurawa?"

  Dan binni yai murmushi yace " Aure?  Dama haka ake aure?"

  Ali da 'yan koronsa suka mike sukace " kai meye hakan? "
Dan binni yasa hannu a aljihu ya ciro dubu ashirin daya waresu tun a banku yace "  ungo! Ba bashi kake binsu ba har kake tunanin kwace mutum akan wata banza dubu ashirin dan tsabar rashin imani?"

  Ali ya kalli kudin sannan yace " ni na yafe Nafi nakeso a auren."

  Dan binni yace " Ai kuwa baka isa ba, yarinya ba sanka take ba kuma baka isa ka aureta ba, kai ko kunya ma bakaji ba kana yayan mahaifinta? Inbanda zuciyarka irin ta yarace ina kai ina neman wace batafi sa'an 'ya'yanka ba?"

     Datti dake zaune ya mike tsaye yace " Kai wai kai waye ne? Menene naka a ciki? "

  Dan binni ya kalli Datti cikin takaici yace " nine wanda 'yarka ta taimaka a lokacin da nake kan karagar mutuwa ta."

   Mamaki ya kama datti dama sauran 'yan gun, Datti yace " to naji, daga taimako sai akace ka isa da ita? Ka dubafa kaga yarinyar nan ta girma amma ba miji, in ka korar mata wannan d'in kai ne zaka aureta ko me?"

  Gaba daya kallo yakoma kan Dan binni suna jiran amsarsa.

   Gabansa ne ya fad'i baiyi tunanin abin zai juye haka ba, me kenan? Daga taimako?"


  Ali ya matso kusa dashi shima yace " eh muna jinka kai ne zaka aureta ko me?"

  Innalilahi wa ina ilaihi raji'un!!!!
Allahuma Ajirni fi Masibati wa aklifni kairan minha......
Addu'ar da Dan binni ya shiga yi kenan a ransa.





*THE INNOCENT TEAM*

No comments:

Post a Comment