Saturday, 15 April 2017

ZUCIYA......kowa da irin tasa. 2

ZUCIYA
kowa da irin tasa

   © NA AYUSHER MUHD

2⃣

   Kanta ta sake cusawa kan mutumin duk ta rikice, can ta tuna inda tasa kanta hakan yasa ta mike da sauri, jikinta na rawa, sai dai a wannan lokacin tsoronta yadan ragu ba kamar da ba.

  Hannu tasa ta zare takalmi mai saucikin dake kafarsa, sannan ta zare safar kafa ta gani kamar ta mutum sai kuma tausayin wanda ke kwance ya kamata, hannunsa ta kamo ta shiga kokarin jawoshi daga cikin ruwan, da kyar da nishi ta samu tadan jawoshi kadan, nan fa ta shiga kokarin murgunashi, nan ma da kyar da numfarfashi ta samu ta juyashi, tsugunawa tai a gabansa tana kallanshi.

    Tsoro ta fara ji kardai ya mutu? Nan tasa hannunta a sai tin hancinsa ta dan dade kadan jin baya numfashi yasa tsoro ya kara kamata, idanunta suka fara tara kwalla, hannunta tasa a saitin zuciyarsa, dariya ce ta bayanna a fuskarta a lokacin dataji bugun zuciyarsa.

Ta rufe fuskarta alamar kunya tace " Da ranta wallahi." Ta sake yin dariya tace " Wlh da ranta Allah da gaske."
  Ta sake dariya.

   Fuskarta ta zuro daf da tashi tana kallo, ba fari bane sannan kuma ba baki bane yanada kyau, hancinsa dogone, ta d'an yi murmushi sannan ta kalli kayansa tace " Kad'o ne wannan kam,  sannan da alama bama dan nan garin bane daga birni yake." Baki tad'an turo kadan ganin ita kadai take maganarta sannan ta shiga tunanin yanda zatai ta dawo da numfashinsa.

  Hannu tasa ta shiga danna mai kirji tana san ruwan daya shakka ya futo, sai dai ina,  ya shaka da yawa duk yanda ta zake tana dannawa ba alamar motsi a tattare dashi.

  Idanunta ne suka ciciko, ta kalleshi tace " Dan Birni ya zanyi?"

Ga ba kowa a gun, ta kafeshi da ido tana kallo jitake kamar tai ihu, tunawa tai sanda wasu fulanuwa suka ciro wani yaro daya fada ruwa kwanaki, tana kallo bayan sun danna mai kirji bai farfado ba sai wanda ya danna mai kirjin yasa bakinsa a nasa ya huramai iska alokacin mutane sukai ta ce masa dan iska, babar yaran tazo ta kwace danta itama tana masifa.

   A hankali ta matso itama da shirin kai bakinta, sai kuma ta tsaya ta kalleshi tace " Dan Birni ba iskanci zan maka ba kawai iska zan hurama, kaji? inka warke xan baka hakuri."

  Nan ta sa bakinta cikin nasa ta shiga huramai iska iyakar karfinta, sai datai tayi sannan can sai yadanyi tari sai ga ruwa dayawa ya zubo daga bakinsa, idanunsa ya bude a hankali ya kalleta, ta kifkiftamai ido tace " Hannu? Kin ganni?"

  Gani tai ya maida idanunsa ya rufe, sai dai yanzu numfashinsa na fita sai dai dad'an sauri yake fita, tai shiru tace " ya zanyi? Bacci yake? Ga dare nayi?"
  Jijigashi ta shiga yi tana cewa " Karkiyi bacci anan dan Allah kiyi hakuri ki tashi."

  Sam bataga alamar motsi a tattare dashi ba, ga gari ya fara rufewa, da sauri ta mike ta suri bokitin ruwanta ta nufi gida, tana shiga ta waiga taga bataga Baffa ba, ajiye ruwan tai ta karasa gun dabobbi ta dauko baro ta fito da sauri.

  Inda ta barshi anan yake babu alamun ya motsa, nan fa ta shiga kokarin d'orashi akan baron, sai dai ina.....sam ta kasa.
Duk wani karfi datake tunanin tanadashi ta sake akan mutumin sai dai daga ta dagoshi sai su fad'i tare, saboda rinjayarta dayake yi, duk su biyon sunyu butu butu dasu da jikakkiyar kasa, banda numfashin wahala ba abinda takeyi, ga duhu ya kawo kai, nan ta cigaba da gwadawa, dakyar da sid'in goshin wahala ta samu ta d'aurashi, tana daurashi hannunta ya kume ajikin baron.

  Kara tad'anyi saboda zafin dataji, sai dai tsoron rafin ta keyi dan duhu ya fara rufewa, da sauri ta shiga tura baron, sai dai dakyar shima take turawa kasancewar ba siminti bane ko kwalta a gun, iya wahala Nafi taji a wannan lokacin, har ta samu ta isa gida, tai sa'a baffa na kewaye (ban d'aki ) hakan yasa ta tura baron zuwa d'akinta tasani sarai mahaifinta ko wani ne zai mutu bazai taba yanda a kawoshi gidanshi ba koda kuwa dan uwansa ne bare wannan dabatasan inda ya fito  ba.

  Can gefen dakinta ta sa tabirmar datake kwanciya a kai ta shimfida zannuwa guda  uku sannan ta shiga  kokarin saukeshi, wannan karan batasha wahala sosai ba sai dai shi yadan kumu da bango garin saukeshi.

  Nan tasamai pillow ta kwantar dashi, itama nan ta zube ta kwanta dan tasha bakar wahala.

  Batai minti 3 a kwance ba taji muryar Baffa yana kwalla mata kira " Ke Nafi kina inane?"
  Dasauri ta mike ta kara jan labulen dakinta tai waje tace " ganinan Baffa."
  Yai tsaki yace " Bakida hankali ne zaki d'ebo ruwa baki zubama dabobin ba shinr zaki dangwarar anan? Ko ni kike jira in kai musu?"

  Kallan ruwan tai tadan yi kasa dakai tace " cikinane yadan murdamin kadan shiyasa......"
  "Ciki? Zancen banza kenan, dan cikinki ya murd'a sai ki barmin dabobi da kishi ruwa? Sannan ba madai kina nufin bokiti dayan nan kadai kika d'ebo ba ko?"

   Idanu tadan kifta na mara gaskiya, Datti ya shiga tafa hannu na mamaki yace " Lalai zance kwal ubanki kuwa a gidan nan, banza wacce mahaifiyarta ta gudu da kayan sata, sannan da auranta ta tafi yawan karuwanci."

  Idanun Nafi ne suka ciciko tai saurin yin kasa da idanunta a hankali tace " kayi hakuri Baffa wlh ba h......"

   "Billahilazi kika b'atamin rai goben nan sai in nemi wani can in aura miki, ni dama na gaji da ciyar dake abincin da bakisan darajarsa ba."
  Yanakainan yai waje a zuciye.
Tsugunnawa tai agun ta shiga wani irin kuka mai tsuma zuciya, tadade agun kafin taje ta maka alwalarta wacce batasan ko hakan akeyi ba, itadai kawai tasan ana wanke fuska, hannu da kafa, ta mike ta shigo daki tayi dunguren sallarta da batasan me ake cewa ba.

   Tana idarwa ta matso kusa da dan birni, kansa takai hannunta sai dai da sauri tadauke hannunta jin wani mugun zafi datai,  Mikewa tai da sauri tace " Hande inboni!! Karfa kad'on nan ya mutumin adaki in shiga uku?"
  Dasuri tai waje ta shiga lelekawa, abin haushi a can gefe suke wanda inzakaje rigar kusa dasu sai kayi tafiya mai dan yawa, gashi tana tsoron mahaifinta kar ya dawo yaga ba tannan.

   Komawa tai ciki, ta nufi d'akin baffa nan ta shiga duba gayayyakin magani ko zataga na zazzabi, tai sa'a kuwa ta samu nan ta sato rigarsa ta fito daga dakin, wuf ta shige d'akin ta.

    Tofa nan ake yinta gani take jikaken kayan dake jikinsa ne ya jawo mai zazzabin nan,  shiyasa ta dauko kayan baffa, to amma taya zata ciremai kayan dake jikinsa ta samai wannan?

  Tsayuwa tai akansa tai tsuru tsuru da ido tana tunani, maganin ta dauko ta jika a kofi sannan ta matso kusa dashi ta shiga bashi a hankali da cokali, wani yana shiga bakinsa wani kuma zubewa yake.

   Bayan ta gama ne ta kalleshi cikin kalaar tausayi tace ya zanyi dake?


No comments:

Post a Comment