*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*WELCOME BACK ZEE FRESH,* *WE REALLY MISS YOU*😍😘..
7⃣
Kallansa take cikin tsananin mamaki ya sake murmushi yace " Riga tafa? Ko kin barmin wannan d'in? "
Kasa tai da kanta sannan a hankali tace "na d'auka ka tafi ai. "
Datti yace " me kuke nufi kenan ka santa dama? Sani bana taimako ba? "
Ashraf yad'an yi murmushi dama so yake ya kular da Datti yace " sani kuwa tunda ji jiya a d'akin ta na kwana. "
Yai maganar yana kallan Nafi, gaba d'aya kowa ya kalleshi, Datti ya rike haba yace " Kwana? "
Ashraf yai wani murmushin rainin hankali sannan ya ya d'aga kai yace " Uhm hum"
Hannee da mamanta suka kalli Nafi cikin mamaki, Dan litti shima mamaki ne taf a ransa lalai wannan gayen ashe dan duniya ne?
Nafi ce tayi baya da sauri tai cikin gida, kallan kofar data shiga sukai suna tunanin me kuma zatai.
Nafi kam tana shiga da sauri tai d'aki tana tafe tana murmushi takasa gane dalilin murmushin nata, rigarsa data ninke d'azu ta dauka abin haushi ba tada turare hakan yasa ta fito, suna tsaye sai gata ta dawo.
Datti yai tsaye yace "Gungumar Munafuka ina kika je? "
Rigarsa ta mikamai fuskarta a sake tace " danaji bakai min magana ba sai na d'auka tafiyarka kayi. "
Ashraf ya amsa yace" ina kuwa zan tafi? Bayan nasan kina cikin wani hali? "
Salati Datti yasa yace " yau na shiga uku lalai yarinyarnan ke ba karamar 'yar iska bace, a haka kowa ya ganki sai ya d'auka ke ta Allah ce ba'asan tsantsar munafircin ki yafi na shaid'an ba, yanzu dan iskanci da so kikai ki auri Ali bayan kin gama lalata da wannan? "
Cikin mamakin kalamansa Nafi ta dago ta kalleshi, lalata? Me kenan?
Maman Hanne ma tace " Gaskiya Nafi kin ban mamaki ban taba tunanin zaki aikata haka ba. "
Itakam Hanne harara kawai take makama Nafi.
Ashraf ne ya kallesu yace " Gaskiya bakuda adalci, wato kai kana mahaifinta sanda nace ta taimakeni baka shi mata albarka ba ka yabe ta ba, sai yanzu dana fad'i na kwana a d'akin ta kaf cikinku ba wanda yai tunanin lalai kila ba abin banza akai ba. "
Ya d'an furzar da iska sannan ya matsa daga inda suke, ta baya ya zaga ya cire rigar jikin sa yasa tashi, tunda ya juyo ya fara tahowa kowa ya kuramai ido, lalai wannan gayen bana karya bane, tafiya yake cikin isa Nafi itama ba'a barta a baya ba gun kallansa, Hanne kam kishi duk ya isheta.
Ashraf har ya karaso basu daina kallanshi ba, D'an litti ya dafa yace " Babban gaye me kake tunani ne? "
D'an litti ya had'iyi miyau yace " Kai Ashraf gaskiya she is beautiful. "
Ashraf ya sakeshi tare da mikama Datti rigarsa yace" mu zamu wuce. "
Datti kam sam ya kasa magana, kallan Nafi yai yace " muje ko? "
Kallan mamaki tamai dan ita batasan shine mijin ba lokacin kanta ma kasa sai dai ta kasa mai musu nan ta kalli Datti tace "Baba mun wuce. "
"Ah to shikenan, sai munzo ganin gida, d'an litti ya kawo mu. "datti yai maganar yana kalle kalle.
Nafi tace to.
Maman Hanne ta mata sallama sai dai ganin yanda Hanne ta hade rai yasa Nafi ta juya ba tare da ta mata magana ba. "
Sunanan tsaye har suka hau mashin, nan suka nufi hanyar Gwaram inda zasu hau mota.
********
Sunyi tafiya sosai kafin su isa, nan D'an litti yakaisu inda zasu shiga mota, wata karamar golf suka samu D'an litti jiyai Ashraf yace " Shata muke so. "
Dasauri ya jawo rigarsa yace " Ashraf kasan me kake fad'a kuwa? Inkace shata yana nufin fa ku biyu za'a kai har kano kaga kuwa zaka biya money panty. "
Ashraf yai d'an murmushi yace " meye kuma panty? "
D'an litti yace " Kudi dayawa nake nufi. "
Kafadarsa Ashraf ya dafa yace " Plenty ake nufi. "
Yana kainan ya wuce gun driver yace " Muje ko? "
Nafi ce ta kalleshi sanda taga ya bud'e mata bayan mota ta shiga, ya dawo inda yabar D'an litti a tsaye kamar gunki ya ciro dubu uku ya bashi yace " Nagode sosai d'an litti Allah ya karama ilimi. "
Kallan kudin yai yace " Ashraf ina zan kai kudin nan? "
Murmushi yamai sannan ya mikamai wata dubu d'ayan yace " ka ba abokinka. "
Ya juya ya nufi motar, tsayawa yai yana tunanin ko dai yabada number wayarsa in case ko iyayenta zasuzo Kano? Kai ya girgiza alamar a'a lalai dole ne ya koya musu sanin darajar yarinyar nan, dan ya kula zaman dasuke tare da ita ne yasa ba wanda yake ganin darajarta da mutuncinta.
Shima bayan motar ya shiga, Nafi kam tana zaune duk jikinta a sanyaye, bata taba shiga mota ba sai yau, sai dai taitajin labarin agun Hanne yau gataa ciki, Driver ya tada mota.
D'an litti ne ya matso da sauri ya turo kansa ta window yace " Nagodee Ashraf sannan yanzu na rike plenty ko? "
Ashraf ya mai murmushi yace " kana burgeni ta yanda kake kokarin yin turancin nan, Allah ya hada fuskokinmu da alkairi. "
Murmushi sukama juna D'an litti ya dagamai hannu yace "Sai munxo gidan ka. "
Kai ya daga nan mota ta ja suka fara tafiya..........
Sun danyi nisa a hanya kad'an Ashraf ya kalli Nafi sannan yai gyaran murya, d'agowa tai ta kalleshi da idanunta, Yad'an mata murmushi sannan yace " Nafisa? "
Gabanta ne ya fad'i jin ankirata da cikaken sunnanta, sai dai bata amsa ba sai dai hankalinta data tattara zuwa kansa.
Ashraf ya cigaba " ki nutsu zamuyi magana mai mahimmanci ne. "
Ta d'aga kai alamar tanaji.
Ashraf yadanyi ajiyar zuciya sannan yace " Nafisa bazan miki alkawarin so ba, ba kuma zan miki alkawarin kulawa ba sai dai zan miki alkawarin ni Ashraf bazan taba bari ki wulakanta ba. "
Kanta na kasa sai dai gaba daya gabanta har yanzu bai daina bugawa ba, ya cigaba " Na aureki ne domin ceton rayuwarki daga gun mutanen nan da babu imani a zuciyarsu, sai dai inaso ki kama bakinki kamar yanda nima zan kama. "
Dagowa tai cikin mamaki ta kalleshi yace " kada ki kuskura ki fadama kowa na aureki, wannan sirri ne a tsakaninmu ni dake, karki fadama kowa wannan shine abinda zai kareki."
Idanunta ne suka fara cicikowa nan ta shiga kokarin maidasu, kai ta daga mai alamar ta fahimta, Ashraf ya cigaba " Nafisa zan ajiyeki a gidanmu har Allah ya kawo miki wanda kike so shima yake sanki, in kun aminta da juna sai in sauwake miki ki aureshi......... "
Kallan datamai ne yasa yai shiru shima, me kenan? Abinda zuciyarta ke raya mata kenan? Wani irin aurene a ranar aurenta ake mata zancen saki????
Ashraf yadan juya kai sannan yace " Bazaki fahimci me nake nufi ba yanzu amma na sani nan gaba zaki gane, a inda zamuje zakiga zuciyoyin mutane iri iri sai dai inaso ki daure ki zauna da kowa a yanda yake. "
Nafi wanda hawaye yake yawo a fuskarta tai saurin jan mayafi ta tarufe fuskarta, kallanta yai sai dai ya za'ayi? Dole ne ya fadamata gaskiya.......
Nafi tai shiru sai dai tunanin dake zuciyarta yawa garesu sai dai tasan abu d'aya dama, tabbas Dan binni ba santa yake ba taimakon ta kawai yai kamar yanda ta taimakeshi, tana ta tunani har bacci yai awun gaba da ita.
Ashraf kam yayi shiru yana tunani, tabbas motarsa lafiya kalau ya ajiye ta, to amma mezai sa lokaci daya burkin motar yakiyi? Girgiza kai yai da sauri yace " zato zunubi, ikon Allah ne. "
*THE INNOCENT TEAM*
No comments:
Post a Comment