*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
8⃣
Bakin wani katon gida Ashraf yace mai yai parking, daga bakin gate din mutane ne sosai a tsatsaye sannan wasu dauke da speaker da cameras hakan yasa Ashraf yasan 'yan jarida ne a gun, kallan Nafi yai wacce ke zaune yace " Nafisa kin gaji ko? "
Kallansa tai sannan ta girgiza kai alamar a'a, ya dan murmusa sannan yace " mun iso. "
Ta kalli waje ganin mutane yasa ta kalleshi, ya bud'e motar ya sauka sannan ya zaga ya bud'e mata, a hankali ta fito jikinta duk a sanyaye, ya kalli driver d'in yace " bari in kawo ma kudin ka. "
Ya amsa da to, juyawa yai ya fara tafiya, bai karasa gun mutanen ba kawun sa wato kanin babansa ya hangoshi cikin tsananin mamaki da farinciki ya taho da saurinsa, kusa da Ashraf ya tsaya yama kasa magana sai dariya kawai da yake ya kankame hannun Ashraf, mamakin da ya kamani banga Ashraf yana farinciki sosai ba sai dai yace " Kawu na tada muku hankali ko? "
Wanda ya kira da kawun ya gari fadada murmushinsa yace " Ashraf duk mun daga hankalinmu ganin jiya a rafin wudil muka wuni cur ana nemanka an rasaka tsoro yasa muka fara tunanin ko ka cika sai dai mahaifiyarka taki yarda sam tace lalai kana nan da rai. "
Yad'an yi murmushi kadan sannan yace " Bari na shiga ciki, sannan dan Allah aba mai mota kud'i."
Kai ya daga mai cikin farin ciki, Ashraf ya juya ya kalli Nafi dake tsaye yace " Mu shiga ko? "
Kallanta kawu yai saidai baice komai ba, Nafi kam a hankali ta karasa inda yake, nan suka fara tafiya, hannu kawai ya dagama 'yan jarida suka nufo inda yake, bai jirasu ba ya nufi gate, ya shige ciki.
Inalilahi abinda Nafi ta fada kenan a fili, wani tafkeken gida ta gani, ba wai haduwaa kad'ai ba gida ne kato flat flat dayawa, in ka gani zaka dauka ko gidan hayane na masu kud'i sai dai Ina gida ne na Marigayi Alhaji Saminu wato mahaifin Ashraf, ya gina wannan tafkeken gidan ne saboda yazauna shida d'an uwanshi sannan yayi flat dayawa ne saboda in 'ya'yansu sun taso kowa ya kama flat daya ya zauna da nasa iyalen.
Wannan kenan.
Ashraf har yad'anyi nisa ya juyo a bakin gate yaga Nafi a makalle tana ta fadin Inalilahi, a hankali ya tako yazo inda take, ya kalleta yaga ta runtse ido tsam, yace " Nafisa muje ko? "
Kallansa tai a tsorace tace " Muje ina? "
Ya nuna mata hanya yace " ciki mana. "
Yawu ta hadiya tace " Dan binni nan din inane? "
Ya dan canza fuska kadan yace " badai baki yadda dani ba? "
Kai ta girgiza da sauri alamar a'a, yace" good, to in har kin yadda dani muje ko? "
Duk da tsoro bai bar ranta ba sai dai bata daina binshi a baya ba, can wani flat sukaje, suna karya kwanar flat din sukaga wata yarinya wacce batafi sa'ar Nafi ba rike da faranti zata shiga ciki, Ashraf yace " Little! " yafad'a tare da daga mata hannu.
Cikin mamaki ta juyo, ganin Yayanta batasan sanda ta saki farantin ba wanda ke dauke da lemon kwalli akai ba, da gudu ta karaso gunsa ta rungumeshi, sai kuka.
Ya dagota kadan yace " Little kukan fa? "
Hawaye take tace " Yaya ina ka shiga? Hankalinmu ya tashi sosai. "
Kanta ya shafa sannan yace " to naji ya isa haka, ya dan juya ya kalli Nafi yace " Little zan shiga ciki so nake ki shiga da wannan tai wanka taci abinci ki bata kayankk tasa. "
Kallan Nafi tai sannan tace " waccece? "
Yace "Zan fada miki, Mumy fa? "
Tace " duk fa muna bangaren Umma muna zazzaune, mumy jiya cir ruwa kawai tasha. "
Ya dan juya kai, little tace " Yaya ya kamata kaje ka ganta kafin ka shiga ciki dan da alama nan kafara zuwa. "
Kai ya juya baice komai ba, Kallansa tai cikin rashin jin dadin yanda sam baya kula mahaifiyarsu sosai bayan kowa yasan yanda take tsananin sanshi, zatai magana kawai ta hango Aneesa ta taho da gudu, ganin tana kallan wani gun yasa Ashraf ya juya hakan yaba Nafi damar juyawa ta kalli gun itama.
Da gudu ta taho sai data kusa zuwa inda suke sai kuma ta tsaya daga nesa ta kafe Ashraf da ido idanunta na zubar da hawaye, Nafi ta bi Ashraf da kallo, yanda taga yana kallan ta yasa tasan akwai wani abun tsakaninsu.
A hankali Ashraf ya fara takawa zuwa inda take tana tsaye tana mai wani kallo mai tattare da ma'a noni sanda hawaye nabin kuncinta.
Nafi tai tsaye jiki a sanyaye tana kallansu, sai da Ashraf yazo kusa da ita kawai ta gifta ta gefensa tasa gudu, ta kusa da Nafi ta wuce, ta nufi inda little ta nufa d'azu.
Turus yai agun, jikinsa duk yai sanyi, little ta kama hannun Nafi tace " wuce mu tafi xasu fara abin nasu. "
Sun je zasu shiga sai ga mutane kowa ya taho harda Mumy da Umma sun taho gun Ashraf, sudai suka karasa ciki.
Kallan fallon Nafi tai, aranta tace " lalai rayuwa tana wani gun. "
Sunje shiga d'aki Nafi ta kalli Little jin sheshekar kuka, Little tai murmushi tace" Neesan yaya kenan yau sai yayi lalashi mai karfi kafin abarmu musamu bacci. "
Nafi ta kalli kofar d'akin jikinta ya kara sanyi, Little tace" karki damu inda sabo sun saba, ita shagwab'a shikuma saurin b'ata mata rai shiyasa wannan kukan harya fara daina damuna. "
Nafi ta jinjina kai sannan tace " Amma kuna kama da ita. "
Little tai murmushi tare da tura kofar d'akin tace " Yaya tace ta gurin uba, shi kuma ya Ashraf yaya nane na gun uwa. "
Kallan mamaki Nafi ta mata tace " Ban gane ba. "
Dariya Little tai tace"Maman Mu ce ta auri baban Ya Neesah bayan Baban Ashraf wato yayan babanmu ya rasu. "
Nafi ta zaro ido cikin mamaki zatai magana sai idanunta yakai kan tangamemen d'akin, kallo tabi d'akin dashi cikin tsananin mamaki lalai dukiya tana wani gun, yanzu nan d'akine? Jitai Little tace " Yes. "
Nafi ta hadiye wani yawu cikin mamaki, take kallan d'akin.
Ashraf kam yana tsaye gurin 'yan uwansa manyan 'ya'ya maza na kanin babansa da kuma kannensa, yake kawai yakeyi dan shikansa yasan ba kowa bane yake farin cikin dawowarsa sannan shi ya kosa subarshi yaje ya lallab'a Neesarsa.
Mumy ta kalleshi tace " Ashraf kai wanka sai kazo kaci abinci ko??"
Ta sani sarai bazai amsa mata ba sai dai tasan zaiyi abinda tace, kallan yayen sa yai yace " Zan shiga ciki."
Yana kai nan ya wuce, nan suka juya, dadi da farin ciki ya kama Mumy da sauri ta nufi hanyar kitchen dan shiryamai abinci, duk wannan kin kulatan da Ashraf yake sam bata ganin laifinsa tasan dole ya ji haushi daga mutuwar mahaifinsa ba dadewa ta sake aure kuma gidan datake da anan take sannan ta auri kanin mahaifinsa.
Ashraf har ya nufi bangarensu ya zagaye ya koma bangaren su Aneesa.
Nafi dake zaune akan gado sai dan tsalle take kadan taji ana kwankwasa kofa sannan taji muryar Ashraf ya na cewa "Neesah?? "
Nafi tadaina wasa da gadon, tai shiru tana jin Ashraf, ya dan dade yana knocking kafin yace " shikenan Neesa na dauka kece ta farko da zaki fara farincikin ganina shine zaki shige d'aki kina jina ina magana? Shikenan na tafi. "
Nafi tanaji daga ciki cikin wata murya mai salo da jan hankali tace " Amma yaya kasan halin dakasani kuwa? Jiya ko bacci kasa yi nai ina tsoron kar in fara ace min ga gawarka can. ......."
Kasa karasawa tai, Ashraf ya murmusa yace " Neesah ki bud'e inganki please...."
Nafi ta sauka daga kan gadon ta zauna a kasa, murmushi ta kakaro da kyar tace " dama ai baice yana sona ba, kuma ya sanar dani hakan, shikenan."
Tanajin motsin bude kofar.
Ashraf na shiga ya karasa inda take akan gado, tana ganinsa tasa pillow ta rufe fuskarta, Ashraf ya matso sosai saitin kanta ya kwantar da kansa yace " Ko kallo na bazakiyi ba? Na d'auka yau in kika fara kallona sai na kwace kaina? "
Ta dago a hankali ta dan harareshi sannan ta dau pillow din ta makamai ta kara makamai, ta daga zata sake na uku yai saurin rikewa, yace " ya isa to dear ai kin huce ko? "
Ya fada yana mata wani kallo.......
*THE INNOCENT TEAM*
No comments:
Post a Comment