Sunday, 16 April 2017

ZUCIYA.......kowa da irin tasa 3

ZUCIYA
       ĸowa da ιrιn тaѕa

© na Ayυѕнer Mυнd
    ayushermohd.blogspot.com

3⃣

Duk ta rud'e ta zauna kusa dashi tare da daura hannunta akan goshinsa, tsoro da fargaba ne suka cika mata zuciya jin yanda jikinshi yai zafi dauuu.
   Yawo ta had'iya sannan tace " bazamuyi ta zama a haka ba d'an birni kiyi hakuri bazan kalleki ba, zan cire miki riga idanuna a rufe, kinji?"

   Tana fadar haka ta ajiye rigar Baffa a kusa da ita ta matso kusa tare da rufe ido, irin rigarnan mai dogon hannu da kwala ce, sai botir dake jikin rigar daga sama har kasa, nan ta shiga b'allewa idanunta na rufe tana yi tana magana, "yanzu kaga bana kallanka, sannan namaki laifi guda biyu, na farko nasa bakina a naki sannan yanzu ina cire miki rifa, sai dai inaso karki manta wallahi ba asan raina duk nai hakan ba, banaso ne ki mutu kinji?"

   Tana kainan ta shiga kokarin zare rigar, jin ta kasa zarewa yasa ta manta ta bud'e idanunta kallansa ta shiga yi, sam ta manta, yauce rana ta farko data tab'a kallan jikin namiji dan kaninta tun daya tasa mahaifiyarsu ta raba musu d'aki, ita ba gurin wasan shad'i ake barinta taje ba, nan ne dai tasan maza basa sa riga sai wando, to ita inama take zuwa banda ta mika nono da madara cikin gari inda mahaifinta yake saidawa, dan rashin yadda irin na datti bai yadda ace wani yasai da mai abu sai dai shi dakanshi, nan shago ya bud'e yake saida madara da nonon shanu.

   Ganin yanda gabanta ke fad'uwa yasa tai saurin rufe idanunta sai dai wannan karan ta guntse bakinta gum, haka tasamai riga sannan ta fito waje da sauri.

   Sam bata kula da Baffa dake zaune akan tabirma ba, ta tsaya a waje tare da rik'e inda zuciyarta take, a tsaye take kamar gunki, jitai ance " Wato Nafi kin fara zarewa ko?"

  Dasauri ta kalli inda maganar ta fito, Baffa ta gani a zaune, hannunta ta zare cikin tsoro ta kalleshi tsoru tsuru tace " Baffa.."
" Inajiyoki daga d'aki kina magana ke kadai wato zama ke kadai a gida yasa kin fara zarewa ko? "

  Tai kasa dakai cikin tsoro batace komai ba, baffa yai tsaki sannan ya juya kansa yace " damomin fura insha dare nayi."

   Cikin rawar murya tace " to Baffa yauma bazamuci abinci ba......"
Katseta yai cikin masifa yace " Inkin gaji dashan fura da nono kiyi zuciya kiyi aure, nifa banga dalilin dazaisa yarinya kin kai aure incigaba da ciyar dake ba, sannan haka kawai inada shanaye dayawa bazanje insai abinci ba ah to."

   Nafi bata amsa ba ta juya dan shiga d'akin dasuke ajiye fura, nan ta debo, ta d'ebo nono a kwarya ta zauna ta dama, itakam yanzu warin nono ma yafara damunta, tunda uwarta tabar kasar nan kullum abincin da suke ci kenan, sam Baffa ya rufe ido ita kuma tasan inya fita shago yana siyan shinkafa yaci amma ita kullum abinda takesha kenan.

  Tana gamawa ta zubomai a langa ta rufe ta daura ludayi ta kawomai, sannan ta dauki nata tai d'aki, kallan mutumin dake kwance tai, tace " Nasan kaima yunwa kake ji ko?"
  Matsawa tai ta kara tab'a goshinsa, da zafi har yanzu, nan ta matsa kusa dashi ta dan dagoshi kadan tasa kafarta ta tareshi, ta dinga deban furar data dama tana bashi a hankali da cokali, wani yasha wani ya zube, ganin yadan sha dayawa yasa ta mik'e jiki a sanyaye ta zare zanen data shimfida na saman ta goge mai jikinsa sannan ta dauke numfashinta itama tasha, dan sam batasan sha.


   Waje ta fito da kwaryar sannan ta koma ciki tare da tura kofarta ta rufe, kusa da mara lafiyar ta koma ta zauna, ta hard'e cinyoyinta kallansa kawai takeyi, sai dai tunaninta nakan mahaifiyarta, a haka har bacci yai awun gaba da ita.

    Wajen gabanin asuba ya bud'e idanunsa a hankali, yarinya ya gani kwance kusa dashi ta dan dukunkune jiki tana baccinta, kallanta yai sannan ya shiga kallan dakin, mamaki yashiga yi a ina yake hakan? Yadauka ya mutu shikam, Nan ya shiga juye juye, tare da kallan d'akin dakyau "wannan kuma inane hakan?"
  Gashidai kamar d'aki sai dai gaba daya baisan dame akai rufin dakin ba, sannan ba komai a dakin banda ta birmar dayake kai sai gefe kuma bakko da 'yan samiru, kokarin mik'ewa ya fara sai kuma yaga kamar yarinyar tana neman tashi, dasauri ya maida idanunsa ya rufe.

  Nafi ta mik'e zaune tare da sa hannu akan goshinsa,  murmushi ne ya bayyana a fuskarta jin zazzabin yaragu sosai,  ta kalleshi fuskarta dauke da murmushi tace " Zazzabin ya ragu aradu, dan binni ya kamata ka farfado ko na samu in baka hakurin abinda nai maka."
Tai kasa dakai tana murmushi tace " kaga sanda na sa bakina a naka a bakin ruwa wannan taimakon ka nai. "

   Shikam dake kwance jiyai kamar yasa ihu, bakinki?  Yamaimaita a ransa,  wayyo ni.
Tacigaba " sanda kuma na cire maka kaya har tsautsayi yasa na kalleka wannan shine zan baka hakuri, bansan me yasa na kafeka da ido ba.

  " wayyo na shiga uku,  kallon jikina?  Ciremin kaya?  Inalilahi,  hannu wa na fada haka?  Ba dai har wando tacire............?

   Jiyai ya kasa tunanin komai saboda tsoron abinda yake tunani.
  Nafi ta mike jin mostin baffa tasan yanzu zaice ta tashi tayi tatsar madara,  ta mike hartaje kusa da kofa ta juyo tace " kema kina shan madara? "
  Sai ta juya tana murmushi.

  Tana fita ya mike zaune da sauri ya duba wandansa,  ajiyar zuciya yai a sanda yaga wandansa nannan ya koma ya kwanta yana hakki kamar wanda yai gudu ba shakka ya tsorata kwarai,  tunani ya shiga yi ya zaiyi yai alwala yai sallah? 

   Muryar namiji ne ya katseshi yaji yana cewa " ke nafi? Ke Nafi. "

   Saurin amsawa tai daga garke tace "Baffa ganinan. "
  Ya kalli inda take yace " Dan gidan ku jiya bance ki karo wa dabobbi ruwa ba?? "

  Ta dan matso inda yake jiki a sanyaye tace " Baffa naga jiyan dare yayi nasan kuma bazakaso inje rafi dadaddare ba. "

  " to yar gidan manyan mutane, kin rika sosai wato ina miki magana shine bakiji kunyar maidamin ba ko??"
   Duk maganar da sukeyi da yarensu sukeyi hakan yasa baisan me suke cewa ba amma tabbas ya fahimci abu daya masifa akema yarinyar,  har kasan ransa yaji tausayinta masifa da sanyin safiyar nan?

   Nafi tai kasa dakai cikin hausarsa mara fita  yace " Kin wuce ko kuwa? "

   Nan ta shigo ta dau kallabinta tai waje,  yana kallan yanda take share kwalla dazata fita.

   Bokiti ta dauka cikin tsoro t nufi rafi,  tayi sa'a gari ya fara haske,  nan ta shiga debo ruwa sai datai sawu hud'u ta debo na karshen ne taje shiga gida taga maza carko carko a kofar gidan rike da sanda sunata masifa,  cikin mamaki ta kallesu sai dai ganin yanda ransu yake a b'ace yasa ta shige gidan sukuku....

   Tana juye ruwan ta shige daki dan da alama wad'annnan mutanen ba alheri ne ya kawo su ba,  zama tai a kusa dashi tace " kasan me?"

  "Bansan me wasu maza sukazo yi ba amma da alama masifa sukazo yi, hmmm basusan halin Baffa bane. "
  Tad'an tab'e baki tace " ni kaina tsoronsa nake gani nake kamar ba shi ya haifen ba,  mahaifiyata ma saboda masifarshi tsoronshi take,  hmmm bansan ko su basa tsoron Baffan ba. "

    Dariya yake a cikin ransa lalai wannan akwai surutu.

   Jitai an fasa abu yasa ta mik'e da sauri tai waje,  yabi bayanta dakallo tareda yin dariya lalai wannan yarinyar ga hausartata mai abin dariya.

   Tana fita taga mutanen nan ne suka  fasa musu randa,  ga mamakinta Baffa na zaune a gefe yana kallansu, wani daga cikinsu yace " wallahi kaji na fad'ama Datti ka bani kud'ina tun kafin rai ya b'aci. "

    Baffa ya juya kai yana murmushi yace " Nina rantar muku kud'i? "

  Mutumin yace " bakai bane amma ai matarka ce tace injika. "
  Yasa dariya yace " Matata?  Wa kenan? "

Haushi ya kara kamasu,  Nafi dake tsaye jikin kofa ta matso  kadan,  ai kuwa Mutumin na ganinta ya matso tare da rike hannunta yace " Uwar wannan yarinyar."

  Baffa yai dariya yace "Ali kasan Allah ficikata bazatai ciwo ba dan ba ninace ka bata uban kudi ba,  banda sacemin saniya datai har kake tunanin zan kara kashe mata wani kud? "

   Wanda ya kira da Ali shine ya matso a shekaru ya girmi baffa sai dai bai tsufa ba,  yace " Datti wlh in har ka cigaba da batan rai to kuwa zan dauki wannan 'yar taka amaimakon kud'ina ne.?

   Baffa ya bugamai wani kallo, Nafi wanda tsananin tsoro ya kamata ta kalli Baffa hawaye suka fara zubo mata.

  Baffa ya juyar da kai.
Ali yace " Aradun Allah ko ka biyani kud'ina ko kuma a yau d'innan insa a auramin 'yarka sai ka zab'a.
 

   Dan binni dake tsaye yana jinsu ya mike cikin tsananin mamaki kasancewar da hausa suke maganar yasa ya fahimta,  ya kula su masu masifar kamar hausawa ne, meke faruwa?
Muryar Nafi ce ta katseshi tana kuka tana cewa  " Baffa dan Allah ka taimakeni kaji? "

   Baffa ya kallesu kallan wulakanci yace " kuna tunanin saboda 'yata sai in sadaukar da dukiyata? "
Ya sa dariya yace " Dama na gaji da ita, in kanaso yanzu ma sai in aurama ita menene a ciki? "

    Ba Nafi ba ba kuma Dan binni ba hatta 'yan ansan bashi sai da tsananin mamaki ya kamasu,  Nafi ta kalli Mahaifinta cikin tsananin mamaki sam tama kasa magana banda rawa da jikinta ya shigayi.

  Baffa yai tsaki yace " Zancen banza kenan. "

  Ali ya kalli mutanen gun yace " kowa yaji abinda Datti yace ko?  "
Duk suka amsa da eh, Ali yace dan haka anjima da azahar zamu dawo a bakin nan za'a daura aure lalai zanga karyar iskaninka Datti. "

  Suna kainan suka saki Nafi suka juya.

    Nafi kam haf yanzu jikinta rawa yake,  baffa ya kalleta yace " ke menene damuwarki?  Ali fa nada kudi da dabobbi sannan matansa uku sai 'ya'ya guda sha shida kinga gwara ki aureshi can ki xauna cikin mutane ko kyafiyin hankali. "

    Yana kainan ya juya yai waje.

Dan binni yai tsuru yana kallan ikon Allah wace irin zuciya ce da wannan mutumin?  Bakomai a ransa sai dukiyarsa?


  

No comments:

Post a Comment