🏵🏵🏵🏵🏵
ILHAM😪
🏵🏵🏵🏵🏵
"Dasunan Allah mai Rahama mai jin kai....Dafatan kowa yayi sallah lfy Allah ubangiji yamaimaita mana Ameen"
1⃣
Zaune take a kasa takurawa yarta yar wata 6 ido dake bacci yarinya kyakyawar gaske ta ce aranta ilham yazanyi? idanta ya ciko da kwalla, sannan tajuya takalli falonta kaya more rayuwa dai acikin falon ba'a magana sai dai babu abinda ke birgeta yanzu lafiyar mijinta ya fiye mata duk wadannan daga cikin daki taji kararrawar dasauri ta mike dan tasan mijintane ke magana takarasa dakin dasauri tana isa taje kusa dashi tace Doctor ya akai?
Yamata alama da hannu ta taimakamai zaiyi fitsari dasauri ta miki ta taimaka mai sannan tace sai me? Yamata alama da ruwa ta tsiyayomai a cup sannan tace kasha maganinka kawai sai ka kwanta gaba daya yamata alama da kai yana mata murmushi ta miko mai magani ya yasha tashafa fuskarshi tace yauwa Doctor na dama ku likitoci in baku sha magani ba waye zaisha ya riko hannunta tare da sumbata tadan sunkuyo tare da rungumeshi kwankwasa kofa taji anyi ta kalleshi tace doctor bari in duba ingani ya daga mata kai ta juya tana murmushi tai kofar falon tace waye taji ba'ai magana ba sai tai tunanin ko matar baban mahmud ce dasauri ta bude gudun laifi da mamaki taga Ashiru mijin hadiza kanwar mahmud ta uba tadaure tace mekazo yi? Yace fatima plz kitsaya muyi magana tace wai Ashiru meke damunka ne? Yace kezancewa meke damunki mezakiyi danamiji dayanzu ya nakasa? Tace Allah ne ya jarrabceshi kuma shi zai yaye mai yace fatima wlh ninasan yanda nake sanki mahmud baya miki wannan soyayyar
Cike da mamaki ta kalleshi tace Ashiru kanada hankali kuwa? Da aurena kazo kanamin wannan maganar? Yace nima ai da aurena kuma mijinki shiba kafa ba ba baki ba mezakiyi dashi? Ran Fatima ya baci tace nikuma ahaka nake sanshi ba yace ke dutse ce? Yaza'ayi kice ba kya sha'awa.....marin data tsinkamai ne yasashi rike kumatsunsa tace wlh kabala'in shiga hankalinka kuma wannan yazama rana takarshe dazaka kara zuwa kamin zance banza kuma karka kuskura kakara cin mutuncin mijina
Jitai ance awani mijin naki? Dasauri suka juya hadiza ce kanwar mahmud takaraso rike da hannun danta khalil dan shekara 4 tace Abban Khalil me kakeyi anan? Ya fara inda inda yace dama zuwa nai inji ya jikin mahmud tace saka nai? Ko cewa akai munada hadi dashi? Yace ba hk bane kema kinsan bai dameni ba kawai...jisukai fatima ta banko kofa da karfin tsiya hkn yasa suka tsorata khalil kuwa yasa kuka ran hadiza yabaci aikuwa tai gun mahaifiyarta tana munafikin kuka
Fatima kuwa tana shiga tadau ilham tai cikin daki da ita ta tadda mahmud a jingine yana hawayen bakin ciki dasauri takarasa tace menene doctor? Yasa hannu yagoge hawayen ya girgiza kai alamar bakomai ta sukunyo ta rungumeshi tana hawaye tace Allah yabaka lafiya doctor yadaga mata kai jitai ana kwankwasa kofa again aranta tace sai kuyi tayi jin yanda ake buga kofar yayi yawa yasa ta taho da niyar yimusu rashin mutunci sai dai tana bude kofar taga umma mahaifiyar hadiza kafin tai magana umma ta wanka mata mari sau 3 a jere tace wlh ba'a hallici dan dazai dakarmin 'ya ba fatima tace ni?😳 hadiza tace duka nawa kikamin dazu fatima tai kasa dakai tace yahkuri umma tace jeki daukon ATM dinki fatima tace umma kudin ciki duk kin karar..wani marin takara sauke mata tace kin wuce ko kuwa? Tai cikin gida abin tausayi tadauko tamika kata suka juya suna yar mita😏 a bakin kofa fatima tazube tana hawaye wannan wacce irin rayuwa ce? Ko mijin zata dauke su gudu da yarta? To tayyaya zata dauki namijin dabashida kafa baya magana jin kararrawar da ake dannawa tayi yawa yasa ta tashi dasauri tai gun mahmud😕
By Ayusher Mohd📚
No comments:
Post a Comment