🏵🏵🏵🏵🏵
ILHAM😪
🏵🏵🏵🏵🏵
Na Ayusher Mohd✍🏼
4⃣
Haka mahmud yatafi makarantar Abu cike da farin ciki gashi course din dayakeso yasamu wato Medicine mahmud yafara karatu a sa'a bayan wata 1 yake zuwa ganin gida
Yauma kamar yadda yasaba yazo hutu makarfi, yazo wucewa ta gidan chairman yaga yarinyar nan tadawo daga makarantar islamiya sanye da uniform brown da dogon hijab duk da bamai san magana bane ganin bataganshi ba yasa yace kee parrot ta fara waige kozataga parrot din yace ke dake nake tace nice partot😳?yace eh mana yau yan maganar basa nan takaraso kusa dashi tace laa ashe kaine kasan da bangane ba yace hmm lalai tace amma ni mutum ce mai ya hadani da aku? Yace inye lalai nayarda kan nan yana jaa tace hmm daga ina kake naganka da jaka? yace daga makaranta nake tace wacce? Yace zariya tace uhm wai a garin nan kake naga bana ganinka yace to da cemiki akai sai kinga kowa a garin ko garin karami ne?
Tace hm amma ai natambayi Abba yacemin gidan malam saleh ne gidanku kuma rannan naje akace bakanan mahmud yasa dariya yace nikikaje nema? Tace uhm rannan zaiyi magana wata mata ta fito daga gani mai aikinsu ce ta fito nemanta dasauri tace natafi kar aga na dade ta juya tai gun matar ya juya yana murmushi tun sanda yafara ganinta yake yawan tunaninta yarinyar tana burgeshi
Bayan ya karasa gida yataradda abin bakin ciki mahaifiyarshi yagani tana kuka akofar dakinta yakarasa gunta yace umma meya faru bai rufe baki ba yaji an jikesu da ruwa cike da mamaki ya mike? Yace lafiya? Meye hakan? Hauwa ta cigaba da bala'i ni wato anhana 'yayana cigaba da karatu ke sarauniya danki na makaranta amma ko kunya bakiji ba zakicewa saleh wai yama su hadiza fada akan zancen da suke😠ke zaki aurar mun dasu in basuyi zance ba shi kuma harzaizo ya rufemin 'ya'ya da fada to wlh kunyi kadan dukanku mahmud da ranshi yagama bacci yace amma ai kome tayi hakkin tane tunda 'yayan mijinta ne dasauri Ramatu tajashi sukai daki ta rufo kafar haka hauwa tai ta masifa
Mahmud kam bayasan zaman gidan hakan yasa washegari yakoma dama sunkusa fara jarabawa yafito babanshi yacemai chairman na nemanshi hakan yasa ya wuce gidan a tsakar gida yaga fatima zaune a kujerun rubar da aka ajiye a gun rike da waya a hannunta karasawa yai dauke da murmushi a fuskarsa harya karasa batasan ya iso ba ya leka wayar yaga game take yace parrot nan kika gudu da sauri ta mike tace laaa yaushe kazo?; yace yanzu tace yaya mahmud makaranta zaka koma nakara ganinka da jaka? Yace ya akai kikasan sunana? Tace dadyna na tambaya yace hmm
Haka shakuwa mai karfi ta shiga tsakanin mahmud da fatima dan duk sanda yadawo hutu sai sun hadu harya fahimci santa yakeyi har mahaifansu sun sani
Alhamdulila karatun mahmud yazo karshe kuma tunda yashiga first class yake fita dashi lokacin daya zana jarabawar karshenshi fatima tagama secondary ta zama yan mata lokacin kuma mahaifinta bayakan kujerar chairman yabar siyasa sai dai yakoma kasuwanci kuma Allah ya budamai sosai
Yau ake ceremony na gama makarantar su mahmud a makaranta fatima da dadynta sun taho saleh ma yadauko Ramatu a yar karamar motarsu civic sunzo zariya cikin tsautsayi wata mita tashigo basu sani ba tai gaba dasu agun kafin akarasa asibiti Allah yadauki ransu wannan rana maimakon ranar farin ciki takoma ranar bakin ciki kuka kam yashashi haka yazama marayan sai dai cikin ikon Allah jarabawar su tana fitowa yasamu aiki a asibitin cikin garin kaduna
By Ayusher Mohd📚
By Ayusher Mohd📚
No comments:
Post a Comment