🏵🏵🏵🏵🏵
ILHAM😪
🏵🏵🏵🏵🏵
Na Ayusher Mohd✍🏼
7⃣
yanzu cikin hadiza yakai wata 3 sai wani salo datake tsira agidan komai tace bataso bata tashi yin salon sai fatima nanan, yau fatima tare suka fita da mahmud yakaita shopping tunda suka fita takejin ba dadi jikinta kwanakin nan haka takeji bayan sun sauka daga mota mahmud ya anshi ledojin yace fatima naga tunda muka fita kamar bakyajin dadi muje ciki in dubaki tai murmushi tare da ansar leda daya tace ba waninan ni lafiyata kalau dama so nake ka daukan min ledojin kaga sai in rike daya karkace nayi sankai yace hmm fatima nasanki fa mudai je indubaki dan na kula sam bakyasan kiganni cikin damuwa shiyasa duk sanda kike ciwo sai dai inya cikine kike nunawa to nima yanzu nagane dan hk daga yanzu nizan dinga kula dake tace da aiki zakaji ko da kula dani doctor? Zaiyi magana sai ga zulaiha tashigo tace yaya ina wuni yace ina kika je? Tace Bashir ne yasaukeni munje gaida iyayensa ne yace auho ai gwara dai ayi auren nan kar lokaci ya kure ta karasa tace Aunty fati ina wuni? Fatima ta amsa ba yabo ba falasa zulaiha tasa hannu ta karbi ledojin tace yaya bari inshiga dasu yace to fatima ta kaudakai aranta tana mamakin kinibibin mutanen nan
Suna shiga gida sukaga umma da hadiza zaune a dan tsakar gidansu sunashan farfesun kayan ciki umma tana ganinsu ta mike lale maraba da dan albarka yace umma ya gida? Tace lafiya lau zo ka zauna a zuboma farfesu yace to tare da kallen fatima umma tace fatima taho mana sai kace wata bakuwa kefa dama bakida saurin sabo fatima ta kalleta sannan tai wani murmushi😏 tace banajin ci ne umma dakafin kifada ma xan zauna inci hadiza tace yaya yau tunda natashi naji farfesu nakesan ci kasan yanayin yace hmm balaifi sannan yace muje ciki tare da kallan fatima haushi yakama umma ta riko hannun fati tare da cewa nikam mahmud banajin dadi muna tare amma baxamu dinga komai tareba? Fatima ta raba girki yanzu kuma batacin abincinmu kaima ta hanaka? Yace ah hb umma ba hk bane fatima dake tsaye jiri kawai ke dibanta ta zare hannunta daga gun umma batare datayi maganaba tafara tafiya tana tangadi mahmud yatsaya basu hkri yaji fatima ta zube a kasa dasauri yakarasa yana jijigata duk ya rude lokacin kuma ashiru yashigo ganin fatima shima ya karasa gun dasauri yana jijigata ga mamakin mahmud yaga ashiru kwalla ta zubomai amma tunda bashida lokacin tambayarshi kawai yasuri fatima sai part dinsu su umma kuwa dan munafirci harda hawaye yana isa ya shiga dubata sai dai tsananin mamakin abinda yake gani yasa shi yin shiru dasauri yadaga wayarsa yaduba kwanan wata yakamata fatima tai aladarta kwana 14 da suka wuce amma gudin kar zumudi yasa ya yanke hukunci yasa yadan sa hannunsa ya danna kasan cikinta ahankali tace doctor zafi yace fatima zaki iya zuwa toilet? Tace sai dai ka rikeni amma mexanyi acan yace mudai je haka sukaje yamiko mata roba tai fitsari batai musu batai dan so take kawai takoma ta kwanta yana kwantar da ita yace fatima bari inje asibiti indawo tace da yamman nan?yace asibitin mu zani kinga ai kusa yake tunda bayan layi ne yanzu zandawo tace to sannan ya fita
Su umma ya gani a bakin kofarsu dukansu har khalil a ashiru wai so suke suji ya jikin fatima yace dasauki magani zan samo mata sukace to sannan umma tace zulaiha jeki zauna agunta ko zata nemi wani abun yace yauwa umma nagode sannan yai waje
Direct yai asibiti yashiga yin gwaji lalai abinda yake zargine fatima cikine da ita wani mugun farin ciki ne ya rufeshi haka ya fito duk wanda yagani a asibitin sai ya bashi kudi daya iso gida kuwa yai sa'a bakowa direct part dinsu yai yana isa yaga fatima ita kadai dan dama karyar umma ne ba wata zulaiha data shiga shikam yama manta fatima kawai yaje ya daga sama yana juyata tace doctor lafiya? Yace kaaii wannan matar tawa sai ahankali tayi batan wata amma bata sani ba? Tace batan wata? Yace ba tsakiyar wata kike period ba tace eh amma ninaga baizo ba kasan wani sa'in yana juyawa ya sauketa tare a dungure mata kai yace oh ace mutum yanada juna 2 amma bai sani ba? Tace me😳 ? Yace yes tare da manna mata kiss yace munkusa yin baby fatima Allah ya anshi addu'ar mu ai tashi tai ta daka tsalle dasauri ya rungumeta yace fatima rufamin asiri tai murmushi ya rike hannunta tare da zaunar da ita yasa hannunshi a kan cikinta yace fatima bansan wani irin farin ciki nake ciki ba tace doctor inrokeka wani abu? Yace menene? Tace plz karka fadawa kowa xancen cikin nan yace ban ganeba? Tace kawai so nake abun yazama suprise kasan yafi dadi ya lakuci kumatunta yace wato daban sani ba nima suprise din za'amin? Tace ina na isa inyiwa doctor suprise yace shikenan amma adinga kulamin da baby ko insa zulaiha tadinga yin aikin part din mu? Tace a'a karka damu zan iya yace toh fatima na😘
Babu wanda yasan fatima nada ciki dan tarage shiga gunsu sai dai su in suna nemann kudi dan ba kunya suke cewa tabasu katinta bayan mahmud duk sati yake ajiye musu kudi shiyasa itama tai dabara ta bude sabon account sai take raba kudin 2
Cikin hadiza yana wata 9 ita kuma fatima wata 7 lokacin ne umma tafara zargin akwai wani abu ganin yanda fatima kullum cikin dogowar riga da hijab gashi bata fita waje kuma duk sanda suka shiga gidan tana zaune wannan yasa yau umma tashirya sai taga fatima
Fatima yau da ciwon baya ta tashi jin kwankwasa kofa yasa ta zira hijab ta bude tana budewa kawai taji anja hijab dinta cike da mamaki ta dago umma ce da hadiza suka yaye mata hijab tace umma sannu da zuwa ai umma tashiga salati lalai fatima ciki ne dake shine dan baki daukeni abakin komai ba kikaki fadamin ko? Wannan yarinya anyi mara mutunci nan suka cigaba da tijara fatima kam ko ajikinta dan bazata taba manta sanda tajisu suna cewa basaxu bari fatima tasamu ciki ba bare ma mahmud yasamu magaji
By Ayusher Mohd📚
No comments:
Post a Comment