Sunday, 16 October 2016

ILHAM 5

🏵🏵🏵🏵🏵
            ILHAM😪
           🏵🏵🏵🏵🏵




Na Ayusher Mohd✍🏼

5⃣

Sanda akai rabon gado gidan saleh yakasance na mahmud sai dai hauwa ta fito da wani salo agaban mutane tai ta kuka wai yama za'ayi tabar gidan bayan ga danta aciki? In ta tafi wazai dinga kula dashi wannan dalilin yasa mutane sukai ta jinjinawa kokarinta mahmud ma yace ba matsala, haka mahaifinta ma ya aminta da zabinta sai dai yace mata inhar mahmud yai aure tofa dole ta dawo gida da wannan shawara hauwa tacigaba da zama a gidan



Lokacin da mahmud yasamu aiki da taimakon mahaifin fatima zo kaga murna agun hauwa mutane kam suna yaba mata sai dai acikin zuciyarta bakin ciki ne fall gashi mahmud dole zai bar gidan yakoma kaduna wannan dalili yasa tai gun malami akan arufe bakin mahmud yakasa cewa badasu zai koma kaduna ba.


Lokacin da mahmud yafara aiki jeka ka dawo yakeyi haryai wata 6 ganin anasamun alheri sosai yasa yakama gida dan yanaso ya auri fatima sukoma can da zama, gidan falo daya ne sai dakuna guda 3 ko wannne da toilet dinsa bai fadawa kowa ya kama gida ba sai fatima itakam murna agunta kamar me ba dadewa akasanya rana tunda yan uwan mahaifinshi sunanan wata 2 akasa lokacin ne kuma ya sanar da hauwa tsarin dayai zai barsu anan acikin gidanshi su cigaba da zama shikuma zai koma cikin garin kaduna ran hauwa yabaci dan gaskiya bazata yarda yabarta anan ba hakan na nufin bazatasan meyake samu ba ita kuma tafisan komai ai da ita sai dai alokacin tacemai ba komai dan tagane aikin malamin nan bai ci ba



Bayan auren mahmud da fatima suka koma kaduna lokacin kuma abubuwan alheri sukai ta faruwa mahmud tsantsan gwazanshi yasa wani babban likita dake da asibiti private yanemi yadinga zuwa suna aiki tare lokacin dayake free sannan fatima mahaifinta yabata jari tafara business wannan yasa kudi yafara shigo kusu sosai har fatima taba mahmud shawarar yasai fili


Hauwa kam sai shiga malamai take akan ajuyo da hankalin mahmud yaji dole sai ya zauna dasu harta samu nasara wata rana mahmud yana tashi daga bacci yaji duk duniya babu wani buri dayake dashi daya wuce yazauna dasu hauwa hakan yasa yafadawa fatima itakam bataso ba tace doctor duk abinda kake fadamin suna maka yau da kanka kakeso kuzauna tare? Yace fatima wannan ai duk ya wuce nidai ki amincemin itakam batasan hakan sai dai bayadda zatai tunda abinda mijinta yakeso ne tace shikenan doctor amma yazamu zauna ku 6 a wannan gidan?yace karki damu kafin muyi gidan kanmu ne sai su hadiza da zulaiha su zauna a daki daya ummansu ma haka muma daki daya tace hmm shikenan ga mamakinta alokacin yashirya wai makarfi zaije



Ai sanda yasanar da hauwa wannan shawara farin ciki ya cikata tace to tunda kaga hakan ne yadace sai muje din dama mai unguwa yace inkoma gida yace a'a zan mai magana tace to su hadiza murna kamar me dama suma so suke su koma kaduna a fasa dasu dan yanzu mahmud yasai mota honda


Wannan shine mafarin dawowarsu hadiza gidan basu nuna komai ba dan fatima ma najin dadin zama dasu sau tari hadiza na taimaka mata ta hanyar kasuwanci dama aikin gida sun dauke mata


Shekarar auren Mahmud 5 kenan sai dai haryau Allah bai basu haihuwa ba sai dai yanzun arzikin mahmud ya bunkasa dan yanzu har asibintin kanshi ne dashi kuma sun hada gwiwa da fatima suka bude shago suka zuba kaya Alhamdulila kudi kam Allah yabasu sai dai yanzu su hadiza ta aure wani abokin mahmud ashiru da suke aiki guri daya sai dai ashiru nurse ne ba likita bane sanda yaga hadiza yazo lokacin yazo tarun bude asibitin mahmud ne



Hadiza ce tace tana sanshi danshikam ganin matar mahmud yasa yaji duk duniya ba wacce yakeso irinta auren ma ya amincene ko zai dinga ganinta yanzu hadiza danta daya khalil dan Shekara 3

Rayuwar gidan tafarawa fatima zafi dan in mahmud bayannan hadiza da hauwa basa raga mata haka zasuzo suce sai ta basu kudi intaki suce zasu dau kayanta su siyar gashi kallan da Ashiru yake mata ya fara isarta wannan dalilin yasa bata shiga part dinsu sosai a part dinta take girki da mahmud yatambayeta tace kawai sunga yafi saukine ganin har part dinta suke biyota yasa ta fara zama a shagonta gun kanin mamanta dake rike da shagon.




By Ayusher Mohd📚

No comments:

Post a Comment