🏵🏵🏵🏵🏵
ILHAM😪
🏵🏵🏵🏵🏵
3⃣
Bayan ta shirta ne takalli mahmud tace doctor akwai abinda kakeso ne? Yamata nuni da littafinshi ba musu tadauko ta mikamai da biro dan tasan magana yakesan yi hk ya ansa ya fara rubutu sannan ya miko mata
"Fatima yazanyi da rayuwata? Bana zaluntarki kuwa? Inaji ajikina kamar bana kyautawa"bayan tagama karantawa ta karaso kusa dashi ta zauna tare da rike hannunsa tace doctor plz kadaina irin wannan maganar kamanta so ne yasa na aureka?
Ya girgiza kai alamar bai mantaba tace toka gani plz doctor kadaina irin wannan zancen fatana kamin addu'a ya daga kai hawaye ne yazubo mai ta mike tace doctor mace kakesan zama?ina jarumtarka take? Asanina ban taba ganinka kana kuka ba amma yanxu abu kadan ne kesaka kuka? Nikuma kukan nan yafi komai bakantamin dan hakan na nunamin har cikin zuciyarka ka karaya tana gama fadar haka tadau ilham tai falo ta rungume ilham ta zube akasa tana kuka tace doctor plz be strong in kana hk ban san ni kuma yazanyi ba.....
Mahmud Saleh shine sunan mahaifin ilham sunan mahaifinshi Saleh wanda yake malami na almajirai dake makarfi a garin kaduna saleh nada mata 2 Ramatu wacce take uwar gida sai Hauwa dake amarya, saleh ya aure Ramatu tun saurayi da budurwa soyayya ta hadasu har sukai aure bayan aurensu da shekara 1 ta haifi danta akasamai Mahmud bayan haihuwar Ramatu mai unguwarsu yabashi auren yarsa Hauwa duk da bayaso bayadda zaiyi hk ya aure hauwa
Tunda Ramatu ta haifi mahmud Allah bai kara bata haihuwa ba sai dai hauwa data haifi hadiza daga baya ta kara haifar mace zulaiha
Sam hadiza batasan Ramla da mahmud dan tana bakin cikin ita batada namiji gashi malam saleh kullum suna tare da mahmud har ya isa zuwa makaranta yasashi a makarantar primary mahmud nada baiwa dan indai yakaranta abu sau daya to yazauna a kwakwalwarshi hakan yasa shugaban makarantarsu ke sanshi dakuma alfahari dashi malamaibma kiranshi genius suke
Bayan mahmud yagama primary makarantar ya shiga secondary lokacin ne hankali yazomai kuma yakara gane baiwar da Allah yamai mahmud bashida magana gashi hakan yasa duk wata bakar magana da hauwa zata fada baya kulata.
Lokacin daya gama secondary chairman din garin dakanshi yace yadau nauyin karatun mahmud dan duk garin bawanda yakaishi cin jarabawa dankuwa sai da akai bincike ko satar ansa yayi
Chairman yaneman mai Abu zaria wannan alamari yayiwa saleh dadi farinciki agunsa da Ramatu ba'a magana haka mahmud ya hada kayanshi yaje gidan chairman dan tare zasu tafi lokacin dayaje akace yajirashi a falo yana wanka yana zaune wata kyakyawar yarinya tashigo sanye da uniform din makaranta ta kalleshi tace ina wuni yace ina gajiya tace wakake jira? Yace anan gidan kike?tace ai ni nafara tambayarka😗 yai murmushi yace chairman nake nema tace to yace nibaki ban amsata ba tace eh sunana fatima yace nice name tai murmushi yace amma ba lokacin tashi bane ya akai kika dawo gida? Tace laa🙊 namanta kagan ni da shirme malamin mu nefa yabani ajiya books dinsa namanta dashi akaban pass inje indauko natsaya surutu yai murmushi yace aji nawa kike? Tace jss 2 yace hmm yanzu kuma me kikeyi dabaki je kin dauko ba tace ahh tare dadan dungure kanta kai nima sokuwa ce ko? Yace nibance ba tace hmm wayasan mekace aranka yace to yaushe zakije ki dauko books din ai da gudu tai ciki yasa dariya yace she is cute
Jiyai an bude kofa dasauri yadaga kai chairman ne ya fito rike da yarinyar dazu yace mahmud mutafi ko? Yace ina kwana yace lfy lau sannan yakalli yar tasa yace fatima ba gaisuwa?; tace mun gaisa dady yace wai haka tare da kallan mahmud yai murmushi yace mun gaisa tace Abba natafi yace to sai kin dawo ta kalli mahmud tace sai anjima yace to
By Ayusher Mohd📚
No comments:
Post a Comment