🏵🏵🏵🏵🏵
ILHAM😪
🏵🏵🏵🏵🏵
By Ayusher Mohd✍🏼
1⃣1⃣
Cikin mota ta shiga sannan ta sauko ilhamm ta rike jitai har tashar an iso ana nemanta hkn yasa tai kasa da kanta ga Cikinta dake ciwo kamar me? Sai dataga sun tafi sannan ta dago motar lagos ta cika hkn yasa driver shigowa ya ja motar fatima tai ajiyar zuciya sai dai ana fara tafiya cikinta kamar an zigashi ya shiga murdawa ba sassauci haryakai ta dukursa a kasa wacce kezaune kusa da ita tace lfy? Fatima ta kasa magana matar da karfi ta fadawa driver yace yanzu yaza'ayi? Wani a motar yace akaita asibiti? nan wani yace akwai asibiti anan kusa sukace ya musu kwatance jin ana kwatancen asibitin yasa fatima tafara tsoro dan tanaji kamar asibitin mahmud nada ake kwatantawa sai dai lokacin tagama fita hayyacinta batasan komai ba suna isa asibitin akai ciki da ita yanzu har amai takeyi nurses din suka kira wani doctor yai emergency da ita sannan suka kira Ashiru sukace matar oga ba lafiya gata a asibiti cikin kidima yace ganinan a fara dubata sukace to
Sannan wata nurse ta anshi ilham da jakar fatima ta musu bayani asibitin ma na mijintane sannan suka wuce suka tafi
Likitoci uku ne akan fatima ga nurses sai dai inaa abin yaci tura ashiru ya shigo a birkice daidai lokacin da fatima ta daina numfashin da gudu yazo yaga wani doctor na danna mata kirji doctor ya dago yana girgiza kai ai ashiru naganin haka yakarasa da gudu ya shiga jijigata amma ina kuka wiwi yakeyi.
Duk asibitin yayi tsit sai can ilham tasa kuka hkn ne ya dawo dasu daga tunanin rashin fatima sannan wata nurse ta daurw tace akira gida asanar ko? Ashiru ya dau waya dakyar yakira waya
Su umma sunji mutuwar mahmud kam jiyai kamar shima ya mutu ga bakin cikin bai isa ya mike ba wannan rana ta kasance ranar bakin ciki ga mahmud da Ashiru dakuma yan uwanta.
Mahaifiyar fatima taso daukan ilham sai dai umma harda hawaye wai abarta anan ko mahaifinta zaidinga ganinta yaji dadi dawannan shawara suka amince sai dai bayan 40 suka sai da gidan suka koma wani gidan da ba wanda ya sani acewar umma ta gaji daganin yan uwan mahmud da fatima na zuwa itakuma hadiza da Ashiru so suke subar gidan yanda inya bude asibintin mahmud kowa zai dauka nashine agidan da suka siya sunsa an gina musu daki daya da toilet a can cikin gidan sun katange nan sukasa mahmud suka daukarmai mai anki namiji na kula dashi duk takardun filayensa sun siyar bakincikinsu daya wai duk yanda sukaso suga kudin mahmud ya faskara ance musu mahmud yace dole ilham ce kawai zata iya ansar kudi wannan abu ya kona musu rai ga kuma asibitin ya hada da banki dolene duk wata kudin da mahmud ya cike sai ya shiga account din mahmud wannan abu ya bata musu rai shiyasa suka saida shagon fatima kudin hadiza ta bude wani boutique a unguwar da suka koma.
Lokacin kuma labarin rayuwar ilham ya fara😪
Bayan shekara 8
Ilham ce zaune a bayan gidansu inda tasaba zama sai hucci takeyi muryar meenal ce ta daki kunnanta ke ilham mumy tace in bakizo ba wlh sai ranki ya baci ta mike ko kallan meenal batai ba tai cikin gida tana isa taga hadiza rike da bulala hadiza tace dan iskanci ina tambayarki abu dazu shine kika shareni? Tace ni banina dau miki dari biyar ba mari taji an saukar mata ta juyo ta kalli hadiza sannan tai kasa dakai tace yau zanga inda taurin kan nan naki ya tsaya nanta shiga zane ilham sai dai ilham taki bata hakuri ran hadiza ya bacci kwarai yarinya sai dan banzan taurin kai tuntana karama indai tace xatai abu ko batai niyar yin abuba duk abinda xakamata tofa baxatai ba meenal dake tsaye tana murmushin mugunta ganin yanda jikin ilham yafara fashewa da gudu khalil yakaraso ya rike hannun hadiza yace mumy meye hakan? Tace khalil barni da yarinyarnan yace meta miki hb mumy yaza'ayi ki kama jikin 'yarki kidinga jibga tace wacce......saurin hadiye maganarta tai tunawa datai ashefa umma da ashiru sun gargadeta karta kuskura tace ba 'yarta bace dasauri ta wayance tace ko 'yatace intai sata dole in hukuntata yace sata kuma? Tace dari 5 dina tadauka yace indai wannan ne nizaki daka dan nina dauka dazu nazo ansar kudi zan sai littafi naga kina toilet nadauka na fita hadiza ranta ya baci tai faki fuu itakuma ilham ta mike da gudu ta koma gun xamanta khalil yazo yace ilham kiyi hakuri laifinane? Tasa kuka tace yaya anya kuwa mumy ce ta haifeni? Yace hb ilham wace irin tambaya ce wannan?
By Ayusher Mohd📚.
No comments:
Post a Comment