Sunday, 16 October 2016

ILJAM 8

🏵🏵🏵🏵🏵
            ILHAM😪
            🏵🏵🏵🏵🏵



8⃣
Haka umma tai ta masifa sai dai fatima ko ajikinta yazasuyi da ita? Ganin takicewa komai yasa umma da hadiza suka kara kufula hadiza ta matso tace amma bakida mutunci in mahaifiyarki ce zaki shareta fatima tace to mexance? Haushi yakama hadiza ta daga hannu zata mareta fatima ta rike hannun tace nizaki mara? Sannan tadan tureta kadan tsautsayi yasa ta fadi tadan bige ciki kan kace me tafara ihu tana rike ciki tsoro yakama fatima lokacin kuma mahmud yakaraso ganin wannan yanayi ga fatima a tsaye ko ta taimaka musu yasa yaji ba dadi dasauri ya dauketa suka koma mota yai asibitinsu da ita yana shiga ya cire coat dinshi yai labour room da ita batafi minti 30 ba ta haifi yarta mace mahmud yafito yana goge gumin dake fuskarsa



Nurses ne suka gyarata sannan suka turo gadonta sukai daki da ita umma takalluli mahmud tace sannu dan nan Ramatu datana duniya bansan wani irin farin ciki zatai ba yace umma kije gun hadiza tace to


Gida ya wuce yana shiga yaga fatima a falo tana waya dagaji da Mamanta take waya yaji tana cewa yanzu yaushe zaku koma lagos din? Baisan me akaceba yaji tace saura 1 month 😳? Dan Allah ku kara wata daya kafin ku tafi dan lokacin ne edd dina mahmud yakarasa ciki ganin yanda take murmushi yasan abin farin ciki aka fada mata daki ya wuce ya cire kaya ya shiga wanka yana fitowa yaganta a bakin kofar toilet tace sannu doctor ya jikin hadizan? Yace ta sauka tace Alhamdulila inanan ina tunani yace dakin damu ai ba a haka yakamata inganki ba tace mekake nufi? Yace yarinyarnan a gabanki ta fara nakuda amma ko kitaimaka musu tai shiru jikinta yafara rawa can tace doctor kaima kasan da dalili hk kawai bazanyi hk ba jawo hannunshi tai tazaunar dashi akan gado tafara shafa mai mai daga nan kuma ya huce..... nan ta sanar da shi mahaifinta zasu koma lagos yace meyasa? Tace nadaiji umma tace uban gidansa ne dake can yace ya koma dan ya dinga taimaka mai mahmud yace to Allah ya taimaka


Sai magrib  su umma suka dawo lokacin fatima tasa ansiyo mata kaji tayi farfesu ta dau kular tai cikin gida a falo taga Ashiru tace ina wuni ya mike da sauri yace fatima kawo in daukar miki tace me? Yace kular ta kalleshi kawai ta cigaba da tafiyarta ga mamakinta taji an riko mayafinta tana juyowa taji Ashiru yace ciki ne dake😠? Tace eh bacin ran nameye ran Ashiru yakara bacci yace amma fatima kinci amanata yai waje fuuu kallo tabishi dashi me wannan mutumin yake nufi? Ganin batada lokacin wannan shirman yasa tai cikin dakin azaune taga umma da zulaiha sai hadiza dake kwance ita da baby khalil na kusa da babyn yana mata wasa fatima ta karasa da sallama suka amsa amma kowa ya juya mata fuska tace sannu hadiza Allah yaraya mana hadiza tace Amin inma ba har zuciyarki kika fada ba tace hmmm


Sannan ta ajiye kular tace umma sannu naso binku asibiti sai dai ganin ba kowa a gidan yasa na hakura tace wannan kuma ke ya dama sai kije ki dauko mana katinki muje mu siyo kayan yara dan dama bamuyi siyaya ba fatima tace Ashirun bashida kudi ne? Hadiza tace kefa nakula yanzu bakida mutunci cemiki nai bashida kudi? Kawai dai shi kudinshi muna tarawa ne za'ayi abu dashi tace gaskiya ne ku tara naku ku karar dana wani umma tace nakula yau rashin mutunci kike ji tace bari inje in fadawa mahmud ke kika ture hadiza sai muga ko ba abinda zai ce ko kuma mu shiga mudauki abubuwa masu tsada mu siyar fatima tace hmm zulaiha muje ki anso ta juya ta fita ranta a bace



Anyi suna sai dai fatima bataji dadin sunan ba dan duk kawayen hadiza da zulaiha ne yan duniya sai yada mata magana suke dan dama tuni umma ta daina neman yan uwanta na makarfi ko zuwa sukai korarsu take tun bayan mutuwar mai unguwa mahaifinta, taro ya tashi yarinya taci sunan mahaifiyar Ashiru Amina sai suke cemata Meenal



Wata 2 da haihuwar hadiza itama fatima ta haifi yarta mace farin ciki agun mahmud da fatima ba'a cewa komai har fatima tafara tunanin mahmud yafita farin ciki shine ta tsokaneshi tace dama namiji nahaifa wanda zai gajeka ya xama likita yai murmushi yace ai wani sa'in mace tafi dadi ta gaji mutum bare irin aikina da muke neman mata masu ilimin sai dai karki sa rai in 'yata tace batasan tazama likita bamai takura mata sukai murmushi



Ana gobe suna fatima tai ta damun mahmud yafada mata sunan dayama yarinyar huduba dashi amma yaki fada hkn yasa tafara tunanin Ramatu yasa sunan mahaifiyarsa aikuwa ran suna ga mamakinta taji wai sunan yarinya Fatima dasauri tadaga waya ta kira mahmud tace doctor yace hmm kinji dadi ko? To nafiki jin dadi dan inaso inga nasawa 'yata sunanki tace nagode doctor nan tace sai mudinga cemata ilham gudun karkasa mu rasa wa kake kira inkace fatima nan yai murmushi sukai sallama



Suna kam ansha shi dan mahmud ya barar da kudi hk yan uwan mahaifinshi da mahaaifiyarshi sunzo daga makarfi sai dai fatima ce kawai ta karbesu su umma kam kamar su koresu suke ji




By Ayusher Mohd📚

No comments:

Post a Comment