🏵🏵🏵🏵🏵
ILHAM😪
🏵🏵🏵🏵🏵
Na Ayusher Mohd✍🏼
6⃣
Rashin haihuwar fatima yadameta duk gwajin da akai ance lafiyarta kalau ga kuma wani habaici dayan gida suka tsiri yi mata tana mamaki wannan alamari ita da gidan mijinta amma azo ana ci mata mutunci bayan ita bata taba gorantawa hadiza ba sanda akai auren hadiza mijinta ashiru ya ziga hadiza ta dinga kuka wai ita tafisan zama agidan tana tsoro tana marainiya mara uba tayi nesa da mahaifiyarta to dama ba hk sukabar mahmud ba fatima tayi tunanin zai hana amma ga mamakinta yace tazaune gida da mutane ai yafi dadi kuma Ashiru yadinga taimakamai gun kula da asibitinshi sai dai azahiri ashiruya ziga hadiza ne dan yadinga ganin fatima.
Wannan abun yabakanta mata rai yama za'ayi mahmud yamata haka? Datamai magana sai yace tayi hakuri shine ita bata musu gorin zama a gidan ba sai sune zasu mata gori?
Yau weekend kamar yanda fatima da mahmud suka saba suna dadewa suna bacci sai dai cikin baccinsu suka dingajin guda sai yi akeyi haushi yakama fatima tafito azuciye ta zira hijjab tai cikin gida hadiza tagani da zulaiha sunata guda gakuma hauwa da khalil tare da mahaifinsa azaune fatima cikin bacin rai takarasa tace haba umma yaza'ayi kina kallo sudinga yimana guda kamar gidan biki? Hadiza tayo kanta kewai meyasa bakida mutuncine in mahaifiyar mahmud ce zaki fadamata hk? Fatima tace in itace ai nasan kafin ta karasa hadiza tace oho dai koma meye muna cikin farin cikine kuma dole mu nunama makiya
Fatima tace abin farin ciki? Zulaiha tace hadiza ciki ne da ita dajin haka sai da gaban fatima ya fadi amma da yake tanada dauriya tace hb kai amma naji dadi Allah yaraba lafiya hadiza tace to amma dai yakamata yaya yasake aure dan zama da juya bashida amfani wannan kalma taba fatima haushi hakama ashiru azuciye yace hadiza meye hakan? Umma tace barta ai gaskiya tafada ashiru yai waje a zuciye dan bakin cikinshi yaji anayiwa fatima haka mahmud kam ganin fatima bata dawo ba yasa ya fito dan ya duba
Sunajin motsinshi umma ta wayance fatima kinga jiya dana fita naga wasu mayafai masu masifar kyau shiyasa na daukar miki ta mika mata mayafi fatima ta tsaya tana kallanta tace umma meye kuma hakan? Mahmud ya karaso tare da rike hannun fatima yace haba fatima ba asan adinga maida hannun kyauta baya jin muryar mahmud yasa ta juyo sannan takalli umma tai murmushi sai yanzu ta fahimceta wato sunji mahmud zasu raina mata hankali ta ansa tare da sakala hannunta jikin mahmud tace nima gani nai anbani nikadai umma batasaiwa su hadiza ba ☹ yai murmushi sannan yace kyallesu ita ai umman tasan zaifi miki kyau shiyasa umma tace ah to wake ta wadannan yaran? Hadiza da zulaiha sukai shiru fatima takalli umma sannann ta maida kallanta gun mahmud tace doctor khalil fa yakusa yai kani ko kanwa? Cike da murna mahmud yamusu Allah yasanya alkairi sukai part dinsu
Suna shiga fatima tace doctor nikam ina tsoro? Yace name? Tace kar inje nice bana....dasauri yarufe mata baki sannan ya rungumeta yace fatima inaji ajikina rabon mu yakusa zuwa dan hk mu roki Allah amma kidaina fadar haka kara kankameshi tai tana hawaye.
Hadiza kuwa suna shiga daki taja tsaki sannan tace umma yama za'ayi ki bada mayafina tace dallacan daya gane ya koremu fa wake ta wanu banzan mayafi kina ganin nikaina in na fita bina ake da kallo dan ansan nafito daga gidan manya muje muyiwa kanmu saki na dafe? Wayasan yaran nan gaba mezai zama? Gwara mu kwashi rabonmu in bai haihu ba mu kwashe dukiyar suka tafa nace Allah yashirya ni Aysha
By Ayusher Mohd📚
No comments:
Post a Comment