Sunday, 16 October 2016

ILHAM 10

🏵🏵🏵🏵🏵
            ILHAM😪
         🏵🏵🏵🏵🏵




Na Ayusher Mohd✍🏼


1⃣0⃣
Sanda fatima ta usa asibiti tagama firgita tana zuwa tai emergency tai musu bayani sukace ita ake jira tai signing a shiga dashi operation ai tanajin hk tafara baya baya sai da wata nurse ta rike ta ta mika mata takardar hannunta na rawa hk tai signing taso ganin mahmud amma hk kawai taji tana tsoron ganinshi sun dade a emergency kafin taga an turo gadonshi da gudu ta karasa daidai lokacin su umma suka karaso itada Ashiru da hadiza

Ganin fatima a wannan yanayin yasa tasan da matsala da gudu fatima tabisu dakin da sukai dashi tana zuwa likitan yace ke kadai kikazo tace eh ni matarshi ce ka fadamin keya sameshi? Ashiru ne ya shigo yace doctor ya akai? Doctor din yace biyoni office


Fatima kam kuka take sosai duk abin umma da hadiza sai da suka tausayawa mahmud ba ayi minti 20 ashiru ya dawo jiki asanyaye idanshi yayi jaa dana sani duk ya isheshi umma tace me sukace? Ashiru ya nisa sannan yace kafafuwanshi sun halaka dan shikanshi zaiji kamar ba'a jikinsa suke ba sannan magana baxai iyataba fatima tace wani irin zancene wannan? Ashiru yace fatima ki nutsu plz dasauri takoma kusa da mahmud tafara wani irin kuka hadiza tazo ta rungumeta tana bata hakuri ita kanta ilham dake baya sai kuka takeyi umma tasa hannu ta amsheta sai dai taji jikinta zafi hkn yasq suka tafi gun nurse
Yan uwan mahmud sunzo dubashi hk ba na fatima

Sabi'u driver yayi kuka yace sai dana rubuta nabashi fa nasanar dashi karya hau motar cike da mamaki fatima ta kalli Ashiru tasan tabbas batada hujjar zargi dan agabanta yabada takardar sai dai bata yarda mahmud yaga ance karya hau motar ba dan tasan ba dalilin dazaisa ya hau motar dabatada lfy

Sai da mahmud ya kwanta ciwo ne sannan yasan halin da fatima ke ciki a gidan dan yanzu a gaban idansa ake mata rashin mutunci gashi rashin mutincin da sukema yan uwanshi yasa sun rage zuwa kuma ashiru ko kunya yafadamai san fatima yake sai dai fatima batasan yasani ba.



Wannan shine abinda ya faru a baya.....yanzu sai mu cigaba😉

Asitin mahmud daxa'a bude sai dakatarwa akai Ashiru ke kula da karamin dama can

Fatima kamar yadda tasaba ta shirya mijinta da yarta zama tai tana karanta mai wani litafin taki "Kudin Tsatsuba" sai murmushi yakeyi  yasa hannu ya mata alama ta matso ta karaso kusa dashi ta kwanta tsakaninsu yanzu ba wani abu dan yanzu shi bazai iya wani abuba....


Kwankwasa kofa taji ta mike tare da cewa inaji an kawon kayan miyar bari inje inyi lunch ya daga mata kai tadau ilham suka fita ganitai gidan ba kowa mamaki ya kamata ina sukaje? Ta tabe baki ta ajiye ilham a kasa tana wasanta itakuma ta fara girki jitai an sakalo hannu ta baya an rungumeta cikin tsoro ta fara kokarin kwacewa sai dai an matseta sosai tace meye hakan? Wani salon hauka ne kuma wannan? Kansa yasa a bayanta ya saki wani nannauyan ajiyar zuciya a zuciye tadau wukar dake hannunta tace wlh ko ka matsa ko na caka ma dajin haka ya saketa ta juyo ta daga hannu zata mareshi ya rike hannun yace karki karamin hk fatima ke ai ba dutse bace kina bukatar namiji nasani basai kin fada ba tai wani murmushin mugunta tace lalai nayarda kanada matsala a kanka ya matso sosai kusa da ita hkn yasa tafara jaa da baya hartaje bango ta tsaya ganin ya daga hannu ta dauka marinta zai yi ta runtse ido da karfi



Salati sukaji anayi a bayansu cikin salon yaudara fatima kawai taji ashiru ya sauke hannun afuskarta ta bude ido tare da rike kuncin tace ni ka mara? Yace an mareki kuma Wlh tau takasance rana ta karshe dazaki nemi shigamin daki hadiza ta karaso tace daki? Yace ina bacci kawai nadanji motsi nadauka kece ganinai anzo kusa dani nikuma ina tunanin kece yasa na jawota nace kin dawo? Jin shiru yasa na farka nace ta fitarmin a daki gashi ba komai a jikina sai gajeran wando shina nasa riga nafito in mata magana


Fatima kam dariya yama bata tace lalai yanzu sharrin daga gun mata yakoma gun maza? Ankan ta rufe baki ta farajin duka hadixa ta ajiye meenal ta shiga dukan fatima kamar zata kasheta dakyar ashiru ya janyeta


Umma takaraso rai a bace tace wato mijinki ya nakasa shine dan zalama kike neman mijin wani? Lalai fatima na yarda ke tantiriyace wuce muje taja hannun fatima dakarfi tai gun mahmud da ita suna isa ta fara zayyanewa mahmud abinda yafaru shidai sai kada kai yakeyi alamar ba hk bane yana nuna musu su bashi littafinshi yai rubutu amma ba wanda ya kula da hkn sai fatima


Sai da suka gama fadan sannan umma tace ki dau kayanki kibar gidan nan dan bazamu iya zama dake ba kina neman mijin hadiza



Fatima kam akwai taurin kai dan duk abin nan ko kuka batai ba tace umma nida gidan mijina zakice inta....marin da aka saukar mata ne yasa ta dago ta kalli umma idanta yai jaa umma tacigaba nabaki yau zuwa gobe ki tattara ki tafi kibar kuma ilham anan suka juya suka fita




Suna fita ta bisu suka ce lfy? Tace 'yata zan dauko dake falo ta wucesu tana zuwa ta tadda khalil na Mata wasa ta dauketa azuciya takoma ciki hadiza tace kai wannan fatima shakiyiyace ji idanta ko hawaye umma tace kinsan taurin kanta ai




Tana shiga ta tadda mahmud na kuka sosai ta karasa ta rungumeshi sai a lokacin hawaye yafara zubo mata ta dago a zuciye tace doctor zan dau mataki a daren nan ya dago alamar bai ganeba tace yau da daddare zamubar gidan da ilham zantafi lagos a daren nan inaje zan sa dady yataho dakanshi ko ya daukeka ku taho tare ko yasa su umma subar gidan ya daga kai alamar yayi ta kara rungumeshi


Mahmud ya mata alama data duba safe dinsa ta duba taga takardu dayawa ta kwaso tazo kusa dashi ya cire guda daya sannan yasa a maida sauran sannan ya mika mata takardar takarba ta duba takardar asibitin shine tace meza'ayi? Ta mika mai littafin rubutunshi yasa ki kira lawyer na ki bashi tace to yace sannan kice mai karya bawa ilham takardar asibitin ko kuma kudaden dana bar mata harsai takai 20yrs ko tazo kafin nan karya bata kifadamai date din da aka haifeta tace to doctor daga hk bata kara cewa komai ba sai dai ya kula tanadan rike ciki tun dazu ya mata alama da hannnu menene? Tace bakomai ciki nane kedan ciwo ya tambayeta kuma ahk zatai tafiya tace ba wani abu ai ba serious bane.




Tun magrib tadau karamar jaka tasa karanta kala 2 dana ilham sannan tadau kudi a safe dinsu ta hada komai takarasa gun mahmud ta rungumeshi tsam tace doctor sai jibi kenan? Dan nasan gobe in Abba yazo bazaku zo goben ba yadaga mata kai yana murmushi jiyake kamar bazai sake ganinta ba ganin sallamar nadaukan lokaci yasa ta mike ya riko hannunta sun dan jima a hk sannan ta zare tace bari in fita dan nasan da magrib suna daki ya daga kaii tadau ilham tasa a baya ta fita cikin sanda tana murda kofa khalil na. Fitowa daga kitchen hannunshi rike da biscuit yace Aunty fita zakiyi? Ta daga kaii tare dayin waje da sauri ta fita taga mai gadi batace mai komaii ba tai waje



Khalil na shiga yacewa  hadiza umma yanzu Aunty tafita da jaka ina zata? Dasauri hadiza ta fito tai gun umma tafada mata umma tace dama ai hk mukeso ko? Hadiza tace wayasan meta shirya yi a wajen harda ilham fa ta fita umma tace hk ne sa Ashiru ya nemota nan suka fadama Ashiru dake asibiti azauce yai waje ya shiga nemanta layi layi


Gudu fatima take duk yanda cikinta ke ciwo batabar gudu ba fatanta taga mota tahau sai dai duk wacce tazo wucewa da mutane hakan yasa ta kira lawyer ta fada mai inda take ya karaso dasauri sannan tamai bayanin sakon mahmud tace kuma yakaita tasha dan ta kula tafara ganin mutane na nemanta



Ba musu ya kaita airport sannan yace karki damu duk yanda sukaso suci kudin sabon asibitin mahmud bazasu iyaba dan nina bashi shawara ya hada asibitin da banki yanda duk kudin da aka samu dolene su shiga banki tace mungode yace amma kamar baki da lfy? Tace ba komai sannan tasauka tai tasha





By Ayusher Mohd📚

No comments:

Post a Comment