JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ
NA
AYUSHER MUHD
No. 73
Sunyi nisa a hanya Zaid duk ya ishe Jalal da zancen Zahida, hakan yasa Jalal ya kwantar da kansa a jikin kujera tare da rufe ido kamar mai bacci, Ammar ma yasa earphone a kunnensa tare da maida hankalinsa kan titi, shikam Zaid sai zuba yakeyi, ganin shariyar tayi yawa yasa shima haushi ya isheshi yai shiru, sunyi nisa jin Zaid yayi shiru yasa Ammar ya lekashi ta glass din mota, ganin Zaid yayi bacci yasa ya zare earphone din tare da kallan Jalal kadan yace " Bacci?"
" Nope kawai idona na rufe."
Ammar yai ajiyar zuciya yace " Me ka tsara yanzu zakai?"
Jalal idanunsa a rufe yace " Ina tunanin neman aiki a kaduna ne so nake mu koma can gaba daya, banajin zaman Abujan nan yanzu."
Shiru Ammar yai hakan yasa Jalal ma yai shiru, sunyi shiru kawai Jalal jiyai Ammar yace " Saboda Seemah?"
Cikin mamaki Jalal ya bude ido ya kalli Ammar sai dai ya kasa magana, Ammar ya maida kansa titi tare dacewa " Hakane kenan?"
Jalal ya mike zaune ya kalli Ammar yace " Ammar."
Ammar ya dan kalleshi tare da yin murmushin karfin hali yace " Jalal menene matsayin Seemah a gunka?"
Jalal ya kalli Ammar cikin tsananin mamaki yace " Ammar meyasa kake wannan maganar?"
Ammar yace " Jalal tambaya kawai na maka amma in kana ganin bani amsar zatai wuya mubar maganar kawai."
Komawa Jalal yai ya kwanta tare da kallan window yace " Ammar karka manta ankusa aurenku da Seemah saboda haka karka fara sa wani abu a ranka."
Gefen titi Ammar ya koma da motar yai parking tare da tattara hankalinsa kan Jalal yace " Jalal bazaka gane me nakeji bane a wannan lokacin, kawai dai ina daurewa ne nai murmushi na kuma ci abinci amma kasan zuciya ta jinake kamar I am useless, na ka sa yima Seemah komai kai kuma ka sadaukar da komai naka akanta, bazaka fahimci me nakeji bane."
Jalal ya kalleshi cikin wani yanayi yace " Ammar kenan, haka kake tunani a ranka? Ni a zuciyata nine nake useless mahaifina shine dalilin lalatama mahaifinka rayuwa, sai dai duk da haka baiyi tunanin komai ba ya rike Seemah kamar 'yarsa, kana tunanin wannan dan abinda nai yakai kwatan abinda mahaifinka yai?"
Ammar ya juya kai yace " Jalal ka manta ne? Mahaifina fa kace bani ba, na sani Dad yayi komai domin Seemah amma ni fa?."
Ya juyo ya kalli Jalal idanunsa suka kada yace " Jalal what about me?"
Jalal yai wani murmushi yace " Ammar taya zaka fadi haka? Kaine kuwa ka mata komai kasan tun da muka hadu da Seemah zancenta daya Ya Ammar, na tabbata da tun farko tasan kai ba Yayanta na jini bane da ko kallona Seemah bazatai ba."
Ammar kallan Jalal yake kawai, Jalal ya dafashi yace " nayi tunani mai yawa bayan naji abinda ya faru tsakanin iyayenmu, zance daya ne ya tsayamin na kuma tabbatar dashi, Ammar shine mutum na farko a duniyarnan da nakeji zai iya rike Seemah fiya dani, zai kuma bata kulawar da ya kamata, zai kuma sa ta manta abinda ya faru da mahaifiyarta."
Ammar ya runtse ido tare da kallan window, a hankali yace " Jalal I I I......"
Sai kuma ya kasa karasawa, Jalal ya kalleshi da mamaki yace " Ammar na san ya kakeji aranka saboda abinda naji kenan a lokacin da naji abinda mahaifina yai, sai dai abu daya na sa a raina, zanyi kokarin ganin na rage gaba da tsanar dake tsakanin mahaifanmu, inaji kamar in nai hakan ne zaisa mahaifanmu su koma kamar da."
Ammar yamai murmushi tare da cewa " Jalal na gode sosai."
Jalal yamai murmushi yace " Ammar ba wanda Seemah ta dace dashi kamarka, zaka kula da ita sama dani na shaida hakan."
Murmushi sukama juna, Ammar ya tada motar tare da hawa kan titi yace " Jalal nagode sosai, sai dai Seemah fa? Inaji ajikina kamar...."
Jalal ya katseshi da cewa " Ammar trust in ur self, Seemah yarinyace bata gama sanin menene so ba sannam karka manta macece ita, nina fadama ka sa a ranka ko shekara bazaku rufa da aure ba zakaga Seemah ta manta dani."
Ammar yadan harareshi yace " ce maka akai inasan ta manta dakai?"
Jalal yai dariya yace " to me kakeso?"
" taya zata manta dakai bayan amintarmu nanan?"
Jalal ya sakeyin dariya kadan tare da nuna Ammar cikin zolaya yace " yanzu ka aminta da amintarmu kenan?"
Ammar yai murmushi tare da cewa " Jalal bansan meyasa ba abinda bazan iya fadama Junaid ko Habib ba inaji a jikina zan iya fadama, banaji zan iya boyema komai."
Jalal ya dan furzar da iska yace " nima haka Ammar jinake kamar munyi shekaru dayawa tare."
Dariya sukai nan suka shiga hirar rayuwa.
Sun isa Abuja Jalal yace " Ammar saukeni anan."
" ina zaka haka?"
Jalal yace " inasan ganin Sagir ne akan gidan danace ya samomin, yanzu banajin zan zauna anan."
Ammar ya mai wani kallo yace " Jalal please kazauna a inda ka samu aiki taya zakaki zama anan bayan ka riga kasamu aiki, kai zamanka kawai kenan kana so kacemin in mukai aure zumuncinmu ya tafi kenan?"
Jalal yace " Ahhh to bari inji me Abba zaice tukunna, amma yanzu saukeni tukun."
Nam Ammar yasamu guri yai parking Jalal ya fita tare da cewa " oh ni wannan Zaid din taya namiji zai zake yai ta bacci haka?"
Jiyai Zaid yace " Idona biyu nadai barku kuyi magana ne."
Da sauri Jalal ya kalli Ammar shima Ammar ya kalleshi, Jalal ya hadiye yawu yace Ammar sai munyi waya ko?"
Ammar ya daga mai kai, nan Jalal yai waje, Zaid ya kwashe da dariya yace " au wai kunya kukaji?"
Ammar ya tada mota ya wuce baice komai ba.
Sunkusa isa gida Jalal yakirashi, nan Ammar ya daga, Jalal yace " Ammar yanzu aka kirani daga police station sun iso dashi nan Abuja, amma kana ganin ya kamata Seemah taje?"
Ammar yace " mu bari tukunna ya nemeta da kanshi."
Jalal ya jinjina kai nam sukai sallama.
Suna isa gida Ammar ya shiga ciki da sauri, falo ya duba baiga Seemah ba Zahra ya gani ta fito daga daki yace " Zahra tana ina?"
Zahra tace " tana kitchen, abinci takema."
Wani sansanyar murmushi yai sannan ya wuce kitchen fin da sauri, tana tsaye tana gurza karas a greater, Ammar ya lalaba ta bayanta ya rufe mata fuska, murmushi tai tace " Ya Ammar ka iso?"
Saketa yai ya dawo ta gabanta yace " ohh na dauka bazaki ganeni ba."
Tai murmushi tace " Yaya na fadama taya za'ai in kasa gane ka?"
Turamai kujera tai tace zauna yaya ka gani.
Ammar ya kalleta yace " taya zanyi inzauna ke kuma kina aiki?"
Tace " me? Zaka tayani ne?"
Kai Ammar ya daga mata alamar eh, tai murmushi sannan ta dauko albasa da wuka da kwano ta mikamai tace " To gashi."
Hararar wasa ya mata yace " hmmm wato wayau ko? Kin dauka bansan albasa yaji gareta ba?"
Tadan hade rai kadan tace " shikenan tunda ba tayani zakai ba kawo na karasa kayana." Tafada tare da kokarin dauke kwanon.
Ansar kwannan yai a sauri yace " cewa nai bazan yi ba?"
Tai murmushi tare da ajiyemai, can ta daure tace " ina kuka je?"
Ya kalleta yace " mun danje birnin gwari ne."
Ta kalleshi kadan tace " da Deen?"
Kai ya daga mata tare da kura mata ido, murmushi tai tare da saurin wayancewa tace " ahh Yaya albasar dai ba yaji ko?"
Daurewa yai shima yace " akwai amma kadan."
Suka kalli juna sukai murmushi.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
��♀