Sunday, 26 February 2017

JALALUDEEN 72


JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ

Na AYUSHER MUHD

ayushermohd.blogspot.com

   No.72

     Seemah na xaune a daki tana cin Abinci Dad ya shigo, kallansa tai cikin sakin fuska tace " Dad shigo mana."
Dad ya karaso tare da zama kusa da ita ya anshi cokalin da take cin abincin ya deba tare da kaiwa kusa da bakinta yace  Ahh....
Murmushi tai sannan ta bude bakin ya zuba mata, tanaci tana murmushi, Dad ya kalleta cikin tsananin kulawa yace " babban farinciki na bai wuce inganki kina cikin farin ciki ba."
  Murmushi Seemah tai tace   " Dad daga yanzu ko banasan dariya inna ganka zan dinga washe baki."
  Dariya yasa mata yace " ni bance kuma a dingamin haka ba."
  Kallansa tai cikin kulawa tace " Dad su ya Ammar fa? Sam na kasa samunshi a waya."
  Dad yai shiru batare daya bata amsa ba cikin wata murya yace " Seemah?"
Kallansa tai cikin mamaki da tattara nutsuwarta saboda yanda ya kirata.
  Dad ya kalleta cikin kulawa yace  " Seemah bakyajin ba dadi ko bacin rai? "
Cikin mamaki ta kalleshi tace " saboda me kenan Dad?"

  Yai murmushin karfin hali yace " Seemah nasani sarai Jalal kike so amma na hadaki aure da Ammar bakyajin haushin hakan a kasan ranki?"

  Iska tadan furzar sannan ta rangwabar da kanta ta kalli Dad tace " Dad a kaf duniyan nan bani da kamarka, ko dan garuwa wanda bashida kwabo ka ce in aura to tabbas shi din nan zan aura babu musu balle tambayar dalili bare Ya Ammar?."
Tai ajiyar zuciya sannan tai murmushi tace " Dad bazan boyema komai ba saboda a haka muka taso banaiya boye ma komai da gaske inasan Deen sai dai duk sanda nake masa bazan iya ture Ya Ammar in zabeshi ba koda kuwa bansan abinda ya faru da ba, balle kuma yanzu na sani."

  Hannun Dad ta kama tace " karka damu Dad bazan bari hallacin daka mana nida mahaifiyata ba ya kare akan san zuciya ta ba."
  Dad idanunsa suka dan ciciko, yace " Seemah na sani naso kaina dayawa dana hada auranki da Ammar, sai dai babban burina daya ne a duniyan nan, bai wuce inga zuri'ar Fatima da tawa sunyi aure sun hayayyafa ba."

  Seemah tai murmushi tace " Karka damu Dad insha Allah wannan burin naka zan cikama shi, tunda na taso agunka ni nake neman abu agurinka baka taba neman wani abu aguna ba sai wannan, ka sha wahala sosai akanmu nida Mahaifiyata insha Allahu wannan burinaka nizan cikama shi."

  Tai magana tana kokarin boye hawayenta, Dad cikin tsananin sanda yake mata yace " Seemah inhar auren Ammar bazai......"

  Da sauri tasa hannu ta rufemai baki, tace " karka karasa Dad kafi kowa sanin yanda Ya Ammar ke sona, tun ina karama har kawo yanzu, hawaye wannan bayaso yaga nayi, nima kasan yanda na damu dashi, insha Allah zanyi kokarin juya soyayyar danake masa ta 'yan uwantaka ta koma ta......."
Kasa tai dakai bata karasa ba, Dad ya kalleta shima baice komai ba tunani yakeyi, anya ya kyauta ma Seemah kuwa? Jalal ma a yanda ya gani yana tsananin santa.

  Katse mai tunani tai da cewa " karka damu Dad zanyi kokarin ganin na cire san Deen a raina sannan na maka alkawari zan kula da Ya Ammar sosai, inaji a jikina wannan shine abinda zanyi wanda zaisa dukda mahaifiyata batada rai zatai alfahari dani."

  Idanunsa ne yaji suna neman zubar ruwa da sauri ya mike yai waje, binsa tai da kallo tare da yin murmushi hawaye suka fara zubo mata, tafara cewa " Is Okay Seemah, cool down."

    Jalal kwance akan gago yayi shiru tare da kankame memory din daya cire na cikin camera din daya daukesu shida Abdul, nurse ne ya shigo ya kara dubashi tare da bashi magunguna, Jalal ya sha tare da mikewa ya zauna yace " wayata please. "

  Nan nurse din ya mikamai, Jalal ya amsa tare da kiran Zaid, dan yasan wayar Ammar a kashe take.
Ringing uku Zaid ya daga yace " Jalal ya akai? Ina cikin shaukin kauna zaka kirani?"

  Jalal ya girgiza kai yace " Zaid matarka zatai fama, ni ba Ammar please. "
Zaid yasa dariya tare da cewa " ai matar tawa kanwarka ce kaga sai kushirya yin faman dakyai."
Jalal yace " me kake nufi?"
Dariya Zaid yai tare da mikama Ammar wayar, Ammar dake tuki suna hanyar dawowa ya amsa tare da cewa " Jalal ya? Allah dai yasa ba wata matsalar bace?"
Jalal yace " Ba wata matsalar Senate din sun wuce dashi police station sai dai....."sai kuma yai shiru.

Ammar cikin damuwa yace " menene? "
Jalal yace " tunani nakeyi anya ya kamata mu bada evidence din nan? Naga kamar zuciyarshi ta karaya  shi yasa nake tunani."

  Ammar yai shiru nadan sakwanni sannan yace " Haka ne mu barshi kawai kodan Seemah ma ina tsoron kar tagani dan ko bata fadaba nasan abin zai zamar mata gyambo a zuciyarta."

  Jalal ya jinjina kai yace " kuna ina yanzu?"
Ammar yace " muna hanya munkusa shigowa birnin gwarin ma, Jalal yace " nagode Ammar sosai...."
Ammar ya katseshi " Zaka fara ko?"
Jalal yai murmushi yace " Sorry amma me dazu Zaid yake nufi?"

Ammar ya girgiza kai yace " kasanshi ai, daga gani Zahida wai ita yakeso kuma yanzu."

  Jalal yai dan dariya kaan yace " kaii Zaid sai a slow...."

   Nan sukai sallama suka kashe.
Jalal na zama wani bafade yazo yace " mai martaba na nemanka."
Jalal ya mike suka fita tare, zaune yake a kasa, mai martaba yace " ya jikin naka?
Jalal yace  " da sauki."
Sarki yace " ya ya ina abinda aka dauka nima na gani?"

Jalal yai shiru, Sarki yace " ya akai kuma?"

Jalal ya kalleshi yace " matsala aka samu ai, ashe bamu kunna recording ba a lokacin."

"OHHHH abin dai baiyi dadi ba amma ba komai naji ance ya aminta da lefin yimata fyaden a station din 'yan sandan."

Jalal ya kalli shi jiki a sanyaye, yace " mun gode sosai da taimakon da ka mana, zan wuce nima yanxu 'yan uwana suna hanya."
Sarki ya jinjina kai tare da cewa " Kuma Abujan zakuyi?naji shima can za'a wuce dashi "

Jalal yace " eh."
Nan yamai Sallama zai mike Sarki yace " Jalal?"
Juyowa Jalal yai ya kalleshi, Sarki yai murmushi yace " ka birgeni sosai, I wish ina da yarinya da na hadaka da ita, sai dai inaso kaje ka duba ko wani gun aiki ne indai har ya maka kanaso to ka sanar dani ni kuma zan nemar maka aiki a ko inane a doron kasar nan."

Jalal yai murmushi yace " na gode."
Nan yamai sallama ya fita, Sarki yai murmushi cikin gaskiya Jalal ya kwantamai a ransa.

  Jalal gidansu ya koma ya dan shishigar da kaya, yana gamawa su Ammar na isowa nan suka shiga mota suka kama hanyar Abuja.



© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*

‍♀

1 comment: