����������������
�� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 6⃣3⃣
Jalal kam da safe ya shirya ya fita, gidan Tv d'in *KARAMCI* ya nufa yana isa ya kira director Abbas, nan ya turo aka shiga dashi ciki, sai da aka gama yawo dashi ya gama kallan ko ina kafin ya karasa cikin office d'insa, yana shiga yaga mutane guda uku, nan ya mik'a musu hannu suka gaisa, bayan sun nutsune Director ya kalli Jalal sannan ya kallesu yace " Shine wanda nake baku labari, wanda da kyar ya amince da aiki damu."
Suka kalli Jalal sukai dariya d'aya daga cikinsu yace " lalai munsha labarinka tunda ya dawo daga Germany bashida hira sai ta ka."
Jalal ya d'an yi murmushi kad'an sannan yace " naga ko ina ba komai yayi sai dai na duba programs d'inku kamar akansu ne zamuyi gyara sannan bakwa zuwa neman rahotanni da kanku, in har munaso gidan Tv d'innan ya zama ba kamarshi to sai mun dinga yawon d'auko rahotannin dazai sa hankalin mutane ya raja'a a kanmu."
Director ya kwashe da dariya yace " hakane kam, ya kuka ga Journalists d'in namu?"
Nan suka shiga tafamai sukace lalai munyi dace.
Jalal ya juya kai shi mamaki yake gani yai abin baikai abin dariya ba ko tafamai ba amma ya kasa gane meyasa sukeyi.
Nan ya fara tambayarsa akan program d'in dayace yanaso yai, Abbas yai murmushi yace " Jalal anyi dace shi da jiya dana kirashi ma cewa yai ko yau ne ayi saboda dama zab'e ya kusa yanasan ya nunama talakawa yanda yake kaunarsu."
Jalal yai wani mugun murmushi yace " gaskiya ne yanzu ka d'an kirashi muje ko gobe yanada lokaci."
Ba musu Abbas ya kirashi, PA d'insa ne ya d'auka nan Abbas ya mai bayanin dalilin kiran, PA d'in yace "ok ba damuwa in ya fito daga meeting zan kiraka."
Bayan sunyi sallama ya kalli Jalal tare da fad'amai abinda ya faru, Jalal yace " ba wani abu nizan koma yanda kukai naji, sai dai ina so ka fad'amai shirin da zamuyi dashi LIVE zamuyi, munayin shirin alokacin kuma mutane suna kallo ba wai sai mun gama anyi editing ba ko wani abun."
Abbas ya jinjina kai yace " zam sanar mai."
Jalal ya musu sallama ya fita, gun Sagir ya wuce ya tattara takardun dayasa Sagir ya had'amai sannan yace " Sagir gida nake nema ina tunanin zan fara aiki anan gwara in nemi gida."
Sagir ya kalli Jalal yace " Karka damu zansa a dubama amma wani iri kake so?"
Jalal yai shiru can yace " gida dai dabazai wuce daidai karfina ba, kamar falo d'aya da d'akuna uku, saboda ina tunanin in nace zan dawo nan sai an tilastani d'auko Zainab."
Sagir ya girgiza kai yace " Yanzu Jalal matar taka ce sai ma an tilastaka zaka d'auko ta?"
Harararsa Jalal yai yace " mubar maganar nan kar raina ma ya b'aci."
Sagir ya girgiza kai yace lalai Jalal, wayarsa ya d'auko ya kira Abba, bayan sun gaisa ne Abba yace yanzu zamu taho inaji wajen magrib dai zamu iso, nan sukai sallama.
Su Seemah an dawo gidan Abba, kowa murna yakeyi,nan Dad ya sanar musu cewa ya shirya 'yar karamar walima gobe na taya Seemah murnar gama karatunta.
Dadaddare Abbas ya kira Jalal ya sanar dashi Abdul ya amince gobe da karfe 2 zai zo su gabatar da wannan shirin, Jalal ya saki wani murmushin farin ciki, Abba dake zaune yanacin abinci ya kalleshi yace " Jalal kai da waye naga kana farinciki haka?"
Jalal ya girgiza kai yace " ba komai, gobe in Allah yakaimu sai dai kai ka fara zuwa gidan su dad d'in ni sai zuwa la'asar zan karaso."
Abba ya jinjina kai yace " gwara hakan ma dama banasan muje tare insaka bada hakuri akan abinda bakama sani ba."
Jalal yai shiru baice komai ba, komawa yai kan kujerar da aka ware a d'akin hotel d'in dan masu aiki ya kunna laptop d'insa ya fito da takardunsa ya shiga dudubawa, har Abba yai bacci sai wajen karfe 1 sannan shima ya kwanta a kasan carpet d'in d'akin.
Jalal tun karfe bakwai da rabi ya fita sai dai ya samu wani driver da taxi ya sanar dashi karfe 1 yaxo ya d'auki Abba yakuma mai kwatancen inda za'akaishi, gidan Tvn Karamci ya wuce nan suka shiga shirye shiryen gun da zasuyi program d'in haka kuma tun jiya aka d'inga tallan shirin a gidan tv har yau da safe, komai ya shiryu yanda ya kamata.
Karfe 1 Abba ya fito duk da jikinsa a sanyaye yake sai dai inya tuno Zahida sai yaji bayajin shakkar ko ma menene.
Sukam gidan su Abba kowa yana cikin farin ciki, sani ne ba'ai ba amma Abba da Dad sun sa Mami da matar dad sun gama shirya komai na lefe yau ne kuma suke sa ran a nunama yaram tunda dai komai a gida ne, gida sai farin ciki akeyi, Abba ya karaso gidan ya tsaya a bakin kofa, mai gadi ya kalleshi yace " Malam gun wa kazo?"
Abba jiki a sanyaye yace " Isma'il nake nema."
Mai gadin yace " yana ciki zaka shiga ko a kirashi?"
Abba ya d'aga mai hannu yace " bakomai bari na shiga."
Nan Abba ya shiga harabar gidan ya tsaya yai shiru,; Ammar dake zaune a harabar gidan ne ya kalleshi da mamaki ya taso yazo kusa dashi, hannu ya mik'amai suka gaisa, Ammar yace " wa kake ne....."
Kamar Jalal dake d'auke a fuskar Abba ne yasa Ammar kasa karasawa, A ba yai d'an murmushin yak'e yace " Isma'il nanan kuwa bawan Allah?"
Ammar ya kara kallansa yace " yana ciki anma....."
Abba ya katseshi da cewa " Amadu sunana mahaifin Jalal."
Da sauri Ammar yai baya cikin mamaki yake kallansa, Abba yai murmushi yace " Ka ganeni kenan d'an saurayi, da gani kai sa'an Jalal ne nasan bazai wuce Ammar ba ko?"
Ammar ya kalleshi idanunsa sunyu jaa, Abba yai jinjina kai cikin kalar tausayi yace " ga kamanan ai nagani."
Ammar ya daure dakyar yace " muje yana ciki."
Abba ya gyad'a kai sannan yabi bayanshi.
Sun isa kofar falon, Ammar ya kwankwasa, Abba, kawu, Dad, da Habib suna zaune suna hirar yanda suke tunanin auren zai kasance, jin kwankwasa kofa yasa suka maida hankalinsu kan kofar.
A hankali Ammar ya murd'a kofar ya shigo, kallanshi sukai sai dai gani sukai shima yana kallan kofa, hakan yasa suka maida hankalinsu kan kofar d'an da alama wanine zai shigo.
Abba ne ya matso a hankali kansa a kasa, Dad ya kura masa ido, gani sukai Dad ya mik'e cikin b'acin rai ya nuna Abba yace " Amadu me kakeyi anan?"
Abba ya d'ago idanunsa da suka ciciko, Abban Zaid ma ya mik'e a zuciye yace " kai ko kunya bakaji ba ka zo gidan nan?"
Abba cikin wata murya yace " Ku bani izinin shigowa dan Allah."
Dad zaiyi magana kawu ya katseshi da cewa "ya isa haka, bakon mu ne bako kuwa ku menene ba'a wulakantashi."
Kawu ya kalli Abba yace shigo ko?
Jiki a sanyaye Abba ya shiga gwiwowinsa ya sa a kasa ya sadda kansa kasa, duk yanda yaso ya b'oye hawayensa sai da suka zubo ya share tare da d'agowa ya kalli Dad yace " Isma'il na fi kowa sanin yanda ka tsaneni haka kuma nafi kowa sanin dalilin tsanar dakamin, naci amanarka na kuma yaudareka, nasakaka a kuncin rayuwar da duk farin cikin da kake ciki bazai d'aikema wancan bakin cikin ba."
Ya goge hawayen dake zubo mai yacigaba " Na rok'eka ka yafemin ba wai dan ni ba sai d'an darajar ma'akinmu, Isma'il naga ishara kala kala akan cin amanar abotar danai, yarinyata tana kwance ko mek'ewa batayi haka magana tun tana karama take a kwance."
Ya kara goge hawayensa yacigaba " ga yaron da nakeso Jalal san da yakema Seemah ya wuce duk yanda kuke tunani saboda ita ya canza karatunsa sannan mun mai aure amma inaa babu alamar shakuwa ko wani abun tsakaninsu, wannan abun danai yasa d'ana haka cikin yanayin daban tab'a tunani ba sam yadaina farin ciki......."
Kuka ne yaci karfinsa, kowa yai shiru Ammar ya share kwallarsa, Dad kam kansa yai kasa dashi Abba ya d'ago cikin tsananin kalar tausayi yace " Isma'ila ka yafemin ni nasan abinda na gaji tun bayan faruwar abin nan muke cikin rashi mai karfi, Jalal shi yai wahalar karatunsa haka kuma ya taimakemu, sai yanzu da Allah yataimakeshi ya zama wani abun, ka yafemin ko d'ana zai fara aiki cikin sa'a sannan yarinyata ta samu lafiya."
Sunyi shiru kowa ya kasa magana sai dai tausayin Abba ya ratsa kowa, agoggo Abba ya kalla, ganin karfe 2 daidai yasa ya kalli Abban Zaid yace " D'an Allah a kunna tashar Karamci Jalal yace yanada sako mai amfani dazai isar, sannan Seemah ta taimaka itama ta kalla."
Kallan mamaki sukai mai, Habib ya mik'e da kanshi ya kunna sannan ya kalli Ammar yace " ka kira Seemah muga sakon."
Ammar ya juya ya fita.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
��♀
Barka da kokari, Allah taimaka....
ReplyDelete