JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
_'Yan Uwa rabin jiki godiya! Jinjina! Ga 'yan uwana._
_Na sadaukar da wannan shafin ne zuwa gareku My Sweet babbar Yaya Aunty Faty, Yaya Faen and my dearest kanwa Meema ('yar fara) love you sooo much_
No. 6⃣7⃣
Ammar ya koma falon inda Jalal yake, nan suka mik'e tare da yima su Dad sallama, Zaid ne ya shigo falon ko sallama baiyi ba ya kalli Jalal sannan ya kalli Ammar yace " shine zaku zame ku barni?"
Ammar ya kalleshi yace " Zaid mu zame kamar ya?"
Zaid ya burtso baki yace " ko ma miye I am in, dan kuwa dani za'ayi tafiyarnan."
Abbansa ya kalleshi yace " kai kuma me zakaje kayi? So kake kaje kawai ka hargitsa komai kome?"
Zaid ya shagwab'e fuska yace " ni wai meyasa akemin haka ne? Ni ba namiji bane? Koma menene nidai dani za'aje."
Jalal ya kalleshi yace " baka tsoro?"
Hararar Jalal yai yace " tsoro? Farauta zaku ko me? "
Junaid yai murmushin mugunta yace " Abba ina ganin ya kamata abar Zaid yaje, waya sani ko shima akwai tasa mahimmiyar gudun mawar dazai ba da?"
Abbansa yace " waye zai bada mahimmiyar gudub mawa? Wannan?"yafad'a yana nuna zaid da hannu.
Zaid cikin shagwab'a ya matsa gun Dad yace " Dad kaga Abba ko? San na kula bai yadda dani ba kallan soko kawai yake min."
Dad yace " to ya isa haka, yanzu dai kaje ka shirya kai ma ka je."
Zaid yace YES!!!!
Sun fito su uku, Seemah na tsaye a jikin kofar falo tana d'an lekowa kad'an,, ganin Ammar, Zaid da Jalal sun nufi mota a tare yasa tai saurin bud'e kofar ta fito, kallansu tai cikin mamaki.
Daurewa tai tace " Ya Ammar!"
Ammar ya juyo ya kalleta, murmushi ya mata sannan ya kallesu yace ina zuwa.
Zaid ya tab'e baki tare da girgiza kai yace " kuma wlh kar a shanyamu a tafi soy........"kallan Jalal dayai ne yasa ya kasa karasa abinda yake shirin fad'a.
Jalal dayakejin wani abu na kishi na tasomai ya daure tare da yin yake yace " karasa Zaid karka damu dani."
Yana fada ya kalli inda Seemah take, idanunta na kansa, ga Ammar na tafe kusa da ita, Jalal ya kurama Seemah ido, itama kallansa kawai takeyi har Ammar yazo kusa da ita bata kula ba.
Da mamaki Ammar ya kalli inda take kallo, ganin tana kallan Jalal yai shiru batare da ya katsesu ba, sai dai kasan zuciyarsa wani irin kuna ne ke ratsashi, haka zai zauna yana kallan Seemah daga gefe tana kaunar wani ba shi ba?
Jalal ne yai saurin dauke kansa daga kallan Seemah tare da saurin karasawa jikin mota ya bude ya shiga.
Seemah ta bishi da kallo harya shiga mota sannan ta juyo ta kalli Ammar da mamaki tace " yaya!"
Ammar ya kalleta sai dai duk yanda yakeso ya danne zuciyarsa karta gane ransa ya baci ya kasa.
Kallanta yai yace " naam"
Baki ta motsa dan ta fahimci ya dade agun, kasa tai da kanta da sauri tace " yaya I......."
Kai ya girgiza mata yace " Zamu wuce kar dare ya mana."
Ta kalleshi da mamaki tace " yaya wai da deen zaku tafi?"
Yamaimaita sunan Deen? Hmm haka ne da deen zamu tafi.
Ta kalleshi da mamaki yanda ya bata amsar, tace " yaya amma...."
Ammar ya kalleta tare da yi mata murmushi yace " karki damu Seemah kin manta kin bani izini?"
Ta d'an hade rai tace " amma ai bansan ba kai kadai bane."
Ammar yace " me? Bakyasan ki ganmu tare?"
Kai ta girgiza da sauri tace " a'a bafa haka nake nufi ba."
Yai sake yin murmushi yace " inje? Kar suyi ta jirana."
Ta daga kai tare da cewa " Amma me zakuje yi?"
Ammar yai shiru kawai yana kallanta.
Tai murmushi tare da cewa " shikenan Allah yakaiku lafiya."
Ya amsa da Ameen sannan ya juya.
Mota ya bud'e gaban mota gefen Jalal ya zaune.
Zaid ne a zaune ya hakimce.
Ammar a kalleshi yace " malam Zaid dan koma baya ko?"
Zaid ya kalleshi yace " kamar ya?"
Ammar ya furzar da wata iska yace " ahhh da ina tunanin baka number wata hadaddiyar yarinya dana gani amma da alama zan fasa."
Da sauri Zaid ya kalleshi yace " da gaske?"
Jalal ya guntse dariyarshi yace " gaskiya kam da alama zakai rashin yarinya.
Ai kan Jalal yagama magana Zaid ya haura baya da sauri.
Ammar yazauna tare da yin dariya Jalal ma dariya yasa basu san sanda suka tafa ba.
Sai da suka tafa kuma kowa ya kalli window irin waskewar nan.
Zaid ya matso da kansa yace " dariyar fa ta meye?"
Jalal ne ya tada mota yaja batare da ya bashi amsa ba.
Haka suka tafi Zaid na tasasu dariya har ya gaji yai shiru, motar tayi shiru kamar ba kowa, can cikin wata murya Jalal yace " nayi mamaki danaji zaka biyoni."
Ammar ya kalli window yace " sai ka daina mamakin tinda dai gamu a hanya."
Jalal ya jinjina kai baice komai ba.
Muryar Ammar yaji yace " Meyasa ka zama dan jarida?"
Jalal ya dan kalli Ammar kadan yace " Long wish dinane."
Ammar ya kalleshi ba tare da ya gamsu ba.
Jalal yai murmushi yace " why?bakai tunanin haka ba? Ko ka dauka saboda Seemah na zama?"
Ammar ya kalleshi da mamaki yace " me? Ba hakan bane?"
Jalal ya kalli Zaid dake bacci ta mirrow sannan yace " nidai nacema ba haka bane."
Ammar ya furzar da wata iska baice komai ba.
Shiru sukai har suka isa ba wanda ya sake magana.
Suna isa suka fito dukansu suka nufi lungun, Zaid kam ya kasa jurewa yace " wannan lungun fa...."
Ammar ne ya harareshi hakan yasa ya hadiya maganarsa.
Sai dai me? Suna isa suka tada sai watsi ake musu da kaya daga ciki ake cilo kaya zuwa waje, abubuwa sai farfashewa suke.
Idanun Jalal ne suka kada sukai jaaa, wani mugun bakin ciki ne da takaici suka ziyarceshi, a zuciye ya shiga cikin gidan daidai nan wanda ke watsi da kayan ya daga tabirma zai cillo.
Jalal ya kalleshi, bai taba ganin shiba, ga Zainab a tsugunne a kusa dashi tana kuka tana kuma bashi hakuri, Mutumin sai ihu yake yana cewa a kira mai Jalal.
A zuciye Jalal ya karasa ya rike tabirmar, mutumin ya kalleshi yace " kai kuma waye?"
Jalal ya dage ya wankamai mari tare da cewa " bakama san wanda kake nema ba?"wani irin ihu mutumin yai yace " ha ha ha! Yau ni aka mara? Ni Kumurci sarkin yaki, ba wanda ya isa yaja dani wanda kuwa yai gaggawar tabani to kuwa kabarinsa ne yake bukatar ziyararsa, ihuuuu sai ni Gatari bai sare namomin daji ihu ihuhu...."
Jalal ya kalli Zainab da ganinsa yasa ta mike da sauri tana hawayen tausayi, Jalal ya maida kansabkan mutumin yace " ba kumurci ba ko zaki ne kai baka isa kazo gidan iyayena ka dinga mana watsi da kaya ba."
Ya matso tare da nunashi da hannu yace " tun kafin in fasa ma baki ka koma ka sanarda wanda ya turo ka, in har yana san yamin wani abu to sai dai yazo da kansa bawai ya turo wasu tsolayen mutane kamar ka ba."
Yana kai nan ya fizgo hannunsa, yafara kokarin Jansa, Ammar ne ya matso ya kama dayan hannun nasa suka turashi waje suka rufe gidan.
Jalal ya kalli Ammar sukama juna murmushi, Zaid kam tafi ya fara yace " wow kaii Jalal ka burgeni dayawa."
Jalal ya girgiza kai sannan ya juya ya kalli Zainab, kusa dashi ta matso tace " yaya mai yasa ka fadi haka? In kuma ya turo wasu mutanen dayawa fa?"
Jalal ya kalleta duk ta canza ta rame, tausayinta ya kamashi, yace " ke kadai ce a gidan?"
Tace " nida kanwata ne to ta tafi islamiya ne."
Jalal yai ajiyar zuciya yace " shiga ciki zan gyara gun."
Kallansa tai tare da cewa " zan tayaka."
Jalal ya dago ya kalleta da sauri ta juya ta shiga ciki, da mamaki Zaid ya matso ya kalli Ammar yace " wacece?"
Ammar ya kalleshi yace " Zaid please keep quiet. "
©
*THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
Great
ReplyDelete