Saturday, 25 February 2017

JALALUDEEN 71

JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ

Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com

   No.7⃣1⃣

   Abdul jin loudspeaker yai ana kiran sunansa, jikinsa ne ya shiga rawa ya matso kusa da Jalal tare da shakemai wuya da  karfinsa, Jalal ya fara kakari, ko meya tuna kuma sai yai saurin sakinsa yana yin baya baya yana cewa " nafi karfin wannan, nine Senate Abdul wanda mutane ke so."

  Jalal yarasa dalili kawai ganin yanda yake rawa da jikinsa yasa tausayinshi ya fara ziyartar zuciyarsa, kallansa yai idanunsa sun ciciko da kwalla matsowa yai kusa dashi ya rike hannunsa yace " wacce irin rayuwa kai? Bayan rashin adalcin dakama Fatima baka jin tausayinta da dana sanin abinda ka aikata a kasan zuciyarka?"

  Hawaye suka zubo ma Abdul ya kalli Jalal yace " Fatima ta rasu dolene ni danake darai inyi rayuwar danakeso."
  Jalal cikin wata sanyin murya ta ban tausayi yace " zaka iya rantsuwa tun bayan abinda yafaru baka taba dana sani ba? Sannan baka taba tunanin 'yar ka ba?"

   Bakin Abdul ya fara rawa, kai ya shiga girgizawa hawaye na zubomai, Jalal ya kara matsowa kusa dashi yace " Zaka iya rantsuwa?"

  Abdul ya dago jajjayen idanunsa yace " in ma nayi dana sanin ko tunaninsu menene amfaninsu yanzu? Fatima ta rasu ba tare da na nemi yafiyarta ba, sannan yarinyar data haifa ban taba ganinta ba bare inma san sunanta kana tunanin akwai amfanin da tunanin zaimin ko dana sanin?"

  Jalal yai ajiyar zuciya yace " You are not a cruel person, da ace kai mugune da randa nazo gidanka dazancen nan bazaka barni na fita ba sannan da bazaka ce sarki ya kamani ba sawa zakai a kasheni ba tare da kowa ya sani ba, sai dai na kasa gane kai wani irin mutum ne da kake kokarin canza abinda ke zuciyarka."

  Abdul ya kalli Jalal tare da share hawayensa yace   " da farko I am not greedy but zama da abokai da cusa min ra'ayuyuka da kuma matsayi na power danake samu ba, hmmm bansan sanda nima na riked'e gaba daya na zama haka ba, bana tausayin kowa burina daya ne insamu abinda  nakeso......"

  Kasa karasa maganar yai, jiki a sanyaye ya dago tare da yima Jalal murmushi yace " hmm inaji Allah ne ke nemana da rahama shiyasa ya baka damar tsayar dani daga cigaba da abubuwan danakeyi."

  Hanyar kofa ya nufa, da sauri Jalal ya riko hannunsa yace " 'Yar ka fa?"

  Abdul ya runtse ido yace " a'a karka sanarda ita komai, in har bata gan ni cikin mutuncina ba bazan bari ta ganni cikin wannan yanayin ba."
Yana kainan ya bude kofar 'yan sanda suka matso tare da samai ankwai.

  Shiru Jalal yai zuciyarshi kuma ta shiga radad'i abinda yake fata ne ya tabbata but meyasa yakejin shi haka?.

   Ammar ne suka dawo shida likita, suna shiga dakin Zaid ya kirashi a waya, yace na siyo kayayyakin kana ina? Ammar ya fadamai number dakin nan Zaid ya taho, likita bayan ya duba Zahida yace bari yasa a kawo mata magunguna, yana fita Zaid ya shigo, Umma ta kallesu tace " ban gane ku bafa?"
Ammar yai kasa dakai tare da gaisheta yace " Ammar ne dan gidan Malam Isma'il."

  Cikin tsananin mamaki Umma ta kalleshi tace " Ammar?"
  Zaid ya matso tare da cewa ni kuma Zaid, ta kalli Zaid da mamaki tace " tare kuke?"

  Ammar ya daga kai, Zaid ne ya karasa kusa da Zahida dake jingine da gado, fuskarta ya tsaya kallo, inya kalli nan sai ya juya kansa ta daya barin, Zahi ta gaji da wannan abin nasa ta kalleshi tace " malam lafiya?"
  Zaid yace " wow! Ahh dan sake fada kinji?"
Zahi tace " me zan sake?"

Zaid ya rike kirjinsa bangaren zuciyarsa yace   " Ammar wannan muryar tamin dayawa."

  Kai Ammar ya girgiza ya kalli umma yace " karki damu Umma haka yake."
  Umma tai murmushi tace  " da alama yanada san wasa."

  Zaid ya dago cikin shagwaba ya kalli Zahida yace   " Yanzu bazaki sake fada ba."
Zahi ta makamai harara  tare da cizan leb'enta tace " Naki d'in, kuma ka matsamin daga sai tin fuska."

  Zaid ya sa dariya tare da toshe baki yace " in naki fa? Me zakiyi?"

Ya fada tare dasa hannu a haba, Zahi ta juya kanta gefe tace  " Umma kice ya matsa min."
Tai maganar kamar zatai kuka, Ammar ya kalli Zaid yace " Zaid ka matsa mata mana tace bataso."

  Zaid ya kalli Ammar yace " meya dameka? Hira muje tsakanin masoya ko patient. ...ahhh dama karatun likita na karanta."

Zahi tai wani irin dariya ta kularwa tace " masoya? Ha ha lalai mutumin nan da alama kai player ne, harda wani dama karatun likita ka karanta? Ahhh Allah yasa duk da akwance nake inajin labarai, dan yayata tana karantamin har littafin hausa, nasani sarai in naga mutun na neman yaudara."

Ta hade rai tare da juya kai.

  Zaid ya matso kusa da Umma yace " Umma kun tabbatar yarinyar nan mara lafiya ce da gaske? Bakinta abude fa yake?"

  Umma tai murmushi tace " to ko zata mik'e ta rakaka unguwa?"
Da sauri Zaid yace " Eh Umma in....."
Kafa Ammar yasa ya takamai kafa da karfi Zaid yai kara tare da cewa " me kuma nai?

  Ammar yace " bata fa tafiya akwance take tun tana karama, Zaid meke damunka ne?"

  Jikin Zaid ne yai sanyi ya kalli Zahi sannan ya kalli Umma yace   " Bansani ba Umma nadaiji jiya ana cewa ta fara magana nadauka matsalar ta magana ce kawai. "
Umma tai murmushi tace " ba komai zuwanku ma ya isheni farinciki tun balle ganin Ammar danai wanda ban taba zata ba."

  Ta fada tare da kallan Ammar.


...©
   *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*

‍♀

2 comments: