Wednesday, 8 February 2017

JALALUDEEN 60

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com

   _I Sincerely dedicated this page for you *ASY KHALEEL*._��

   No. 7⃣0⃣

   Sun shiga cikin d'akin, nan Kafilu ya samu abinda yake so wato hira, shikam Jalal ko kallan Zainab dake  lullub'e cikin mayafi baiyi ba, Sai can d'aya daga cikin abokin Kafilun ya tab'ashi yace " ya kamata mu yafi fa."
Nan suka ba kawayen Amarya dubu biyar kud'in siyan baki sannan akai addu'a suka fita.
  Toh fa!!!! D'aki ya rage daga Zainab sai Jalal, zaman dukum sukai wato zaman kurma har na wajen minti talatin, kafin can Jalal ganin zamanshi anan bashi da amfani ya mik'e ya kalleta, yace " Zainab?"
"Naam"ta fad'a cikin sanyin murya.

  Yace " bud'e fuskarki mana muyi magana."
A hankali ta zare mayafin idanunta a kasa, tasha kwalliya d'an kuwa tayi kyau, sai dai wanda akai dominsa baimasan tayi ba, kallanta yai yace " ungo wannan." Ya fad'a tare da mika mata leda, hannu tasa ta karb'a tana kallansa.

  Yace " Abincine ki samu kici, inadai kinyi Sallah?"
  A hankali ta furta " eh, amma kai yaya kaci abincin ne?"

  Ya d'an juya kai yace " ni na koshi, kedai kici abinci sannan ki shiga d'aki ki kwanta d'an nasan kingaji."

   D'agowa tai ta kalleshi, duk da dai itama tasan ba santa yake ba amma bata tab'a tunanin abinda zai ce mata kenan ba.
Kai kawai ta d'aga, yai cikin d'akinn, dama d'aki d'aya ne da toilet a cikin d'akin sai falo, toilet d'in ya shiga yai alwala yai sallah a d'akin.

  Itakam dakyar ta iya cin cinya guda d'aya sai yoghurt d'in data d'an kurb'a tai shiru tana tunanin wannan abu, kawayenta jiya sun bata labarin yanda maza ke kula da mace ranar da aka kaita, yau gashi ita taga wani abu.

   Jalal bayan yayi addu'oinsa ne ya fito falon tare da kallanta yace " kinci abincin?" Ta d'aga kai, yace " Good, kishiga ki kwanta."
  Ta kalleshi tare da mik'ewa tai d'aki, har takai bakin kofa tad'an juyo, ganinshi tai ya kwanta akan doguwar kujera, tace " yaya kaifa?"
Ya kalleta kad'an tare da cewa ni inanan.

  Kallan mamaki tamai sannan tace " yaya."

Jalal ya had'e rai yace " to so kike inshiga mu kwanta tare?"
  Shiru tai tana kallansa, yace " ki wuce kije ki kwanta karki damu dani."

    Shiga tai cikin d'akin ta zauna a bakin gado tai shiru, ta rasa ma me zatai, shikam Jalal waya ya d'auko yai tai binciken abinda yasa gaba wato sanin harkar karatun law dana mass com.
  Yana cikin binciken ne yaga wata kungiya masu bada scholarship na PTDF sun bud'e a fara siyan form.
  Nan fa ya sai katin yana fatan Allah yakaimu gobe ya tafi cafe yaje ya cike.



  Haka rayuwa ta cigaba, 'yan taron biki sun watse, sai dai tsakanin Jalal da Zainab, intai abinci ta bashi ya ci sai kuma gaisuwa, kamar yanda ta saba kullum tana cikin gida kamar da, wannan ne ya rage mata kewa da kuma sanya abin aranta.

  

  Hmm rana bata karya, yau tun safe ake ta shirye_shirye a gidan Abba kowa ya shiga hidima, kowa murna yake yi banda Seemah wacce kwai yake take yima kowa, tana tsaye a kitchen d'an Mami tasata kullum ta d'inga shiga kitchen tana ganin yanda Zahra da mai aikinsu ke girki, yau dai ita kad'ai ce a kitchen d'in tana dafama Dad indomie babban burinta Dad yaci abincin ta,  Ta dage tana ta aiki sai kace mai dafa sakwara duk ta b'ata kitchen d'in, ji tai an rufe mata ido ta baya, tai murmurishi tace " Ya Ammar ka tashi?"
 
  Sakinta yai tare da juyowa saitinta yace " Seemah ya akainkiga ganeni?"
  Ta d'an harareshi kad'an tace " lalai ma Yaya, tambayar dazakamin kenen? Inada hanyoyin sanin kaine dayawa."

  Ya kalleta cikin jin d'adin kalamanta, ta kalleshi tare da cemai "yaya yau Dad nakema girki."

  Ammar ya hau saman kanta daga gefe ya zauna tare da cewa " lalai duk wannan d'in na dad ne kenan? Bama a tuno da ni?"
Ya d'an matso ta da fuskarta kusa dashi yace " ur husband to be."
  Kasa tai dakai da sauri sannan ta d'ago ta d'an kankance ido tace " oh ni yaya yaushe ka zama haka wai?"
  Murmushi yai sannan ya nunata da hannu yace " yazanyi tunda kanwata ta maida ni haka?"

  Ta d'an juya kai tace " gobe dai zan tafi ai."
Yad'an bata rai yace "gaskiya ji nake kamar zan biki,  bansan ya zanyu ba inkika tafi MEEMAH."

  Da sauri ta d'ago ta kalleshi gabanta ya fad'i, idanunta yaga sun ciciko, cikin tsoro yace " SEEMAH? Menene?"

  Ta share hawayenta tare  da saurin maida kanta kan girkinta tace " please yaya karka kara cemin Meemah."

  Ammar da mamaki yace " meyasa? Naga kinasan sunan?"
Ta kara goge kwallar vata amsa ba kawai ta cigaba da yanka albasa, aranta tace" sunan da Deen ke kirana dashi ne, na rabu dashi ina fatan zuciyata ta manta dashi sai dai banasan wannan sunan ya fito daga bakin kowa sai shi, tunda mun rabu dashi wannan sunan inasan ya zama tarihin daya rage tsakaninmu."

  Ammar kallanta kawai yakeyi, har ta gama nan ya tayata gyara kitchen d'in.

  A ranar da yamma aka sanya ma Ammar da Sewmah sannan Junaid da Zainab ranar aurensu nan da shekara 2 daidainan Seemah ta gama karatunta a hankali ta dawo sun karasa shiri, itama Zahra ta gama nata.

  Washegari Seemah da Dad da matarsa suka calla England.

  Jalal kam yayi sa'a ya samu wannan scholarship d'in murna kamar yai me, nan ya fad'ama Abba shima ya tayashi murna duk dadai a kasan ransa yasan manufar Jalal, nan fa yafara shirin tafiya dan kasar Germany ya cike karatun d'an Jarida, d'an yaga a can shekara 2 ne an gama.

  Yagama komai shima sannan ya calla kasar Germany d'an yin nasa karatun.



© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*

⛹��‍♀

4 comments:

  1. Enter your comment...SLM, I always enjoying ds noble, we ere expecting next page

    ReplyDelete
  2. Taking shape but relationship between author and fan and timely postings are both erratic gaskiya, Sau dai hakuri tunda ya zama dole don ga alamu shawarin ma ba a karba balle a sa ran gyara da alkintawa.... Allah taimaka n tnx.

    ReplyDelete
    Replies
    1. Ba haka bane, na aminta da shawarar sai dai ina tunanin amfani da ita next in zanyi wani littafin, because yanzu time ya kuremin d'an littafin yayi nisan da bazan iya yin hakan ba.
      Tnx alot.

      Delete
  3. Toh Hajiya, Allah ya taimaka kuma ya kaimu next one din daga farkonsa har karshe da rai da Lafiya da kuma Zaman Lafiya kuma Allah yasa yayi dadi Kamar wannan ko ma fiye....Amin ya Allah.

    ReplyDelete