����������������
�� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
No. 6⃣2⃣
Yana gama waya da Zaid ya kira Abbansa, bayan sun gaisa ne yace " Abba kun isa lafiya?"
Abba ya kalli Zahida dake kwance, yace " gamunan tun azahar muka iso, gaskiya asibitin nada kyau ga kulawa."
Jalal yai murmushi yace " Mai suka ce gama da ciwon ta?"
Abba yai shiru can yace " Sunce ba wani abu bane serious kawai dai tun tana karama ya dace mukaita asibiti sai dai barin kashinta da mukai har yai kwari haka shine zai sa a sha wahala kafin ta mik'e."
Jalal ya jinjina kai sannan yace " Dad ya dawo yau."
Gaban Abba ne ya fad'i yai shiru baice komai ba, Jalal ya cigaba " Bai tsaya taron kammala karatu Seemah ba naga yataho." yai ajiyar zuciya sannan yace " tunda ka duba komai na asibitin sannan Umma nacan ka dawo muje ka roki gafarar Dad hakan zaisa Allah ya dubi zuciyarmu ya ba Zaheeda lafiya."
Abba ya runtse ido sannan yace " gaskiya ne Jalal na auna naga gudin nan danakeyi ya isa haka, abinda yafi dacewa dani shine in nemi gafarar Isma'il ita kad'ai ce zatasa hankalina ya kwanta."
Jalal ya d'an murmusa kad'an yace " yaushe zaka taho nan d'in?"
Abba yace " gobe ma, mai zan jira?"
Jalal ya jinjina kai yace " inkazo gobe sai muje jibi."
" Allah yakaimu, amma ka kira Zainab?"
Jalal yad'an tsuke fuska kad'an yace " Zan kirata."
Abba yace " Jalal ba dan ni ba saboda darajar aure agun ma'aiki zaka duba, nasani sarai Zainab bata gabanka ba kuma santa kake ba, sai dai kada ka manta d'aura muku aure akai, hakkinta dake kanka yazama dole ka saukesu in dai kana neman rahamar Allah. "
Jalal yai shiru, can yace " Zan kirata Abba."
Nan sukai sallama.
A bakin gado ya zauna ya kurama sunan ta ido dake kan wayarsa, Zainab yasa ya dade yana kallan sunan kafin ya daure ya kira.
Zainab kam ita kad'ai aka bari a gidan hakan yasa ta d'auko kanwarta, suna zaune suna 'yar hira sama sama ita wani sa'in mantawa ma take tanada wani aure, ganin kiran Jalal yasa taji gabanta ya fad'i rabonta dashi har ta manta, mik'ewa tai ta shiga d'aki da sauri, ta zauna a bakin gado sannan ta d'aga wayar.
A hankali tai sallama, Jalal ya amsa tare da cewa ya gidan? Tace lafiya kalau, shiru sukai dan basusan me zasu cema juna ba, can Zainab ta daure tace " Umma tace yau zaka dawo kasar nan ko?"
Jalal yace "nama dawo ina Abuja ne."
Zuciyarta taji ba dad'i amma ta daure tace " Yaushe zaka dawo nan kenan?"
" Ina da aiyukan yi anan zan d'au lokaci kafin in dawo."
Ta jinjina kai a ranta tace " Lokaci? Shekara 2 tayi kad'an kenan?"
Jalal ya katseta da cewa "ba abinda kike bukata ko?"
A zuciyarta tace " me nake bukata kuwa banda inganka?"
Amma a fili tace " babu."
Yace " okay" batai auni ba taji ya katse wayar, tabi wayar da kallo idannunta suka ciciko da kwalla ya zatayi?
Jalal kam agoggon hannunsa ya kalla wanda yakai aka canza mai glass d'in kullum yanzu shi ne a hannunsa ko da wasa bazakaga yasa wani agoggonba bayan shi, murmushi yai yace " Yau nasan kina cikin farin ciki mai yawa."
Kan kujera ya zauna ya d'auko laptop d'insa ya bud'e yafara aikinsa.
Jalal kenan in ka ganshi yanzu bazaka ce shi bane da, kwarewa da kwazo sun canzashi, kaifin tunaninsa ya karo sosai fiye dana da, tunda yabar kasar nan ya fara karatu ya samu wani company na gidan radio yana musu aiki, in zasu dauko rahoto ko wani bincike dashi ake zuwa, hakan yasa ya samu experience dayawa akan harkar karatunsa, haka kuma kud'in da suke biyanshi mai d'an kauri ne, ga kud'in da aka basu na scholarship.
Sunso rikeshi acan amma inaaa ai ko da wasa bai tab'a sawa a ransa zai iya zama a wata kasar ba.
Seemah kam sun gama taro an d'au hotuna kala kala, sun koma gida abin haushi wai Dad har ya tafi Nigeria shida matarsa, haka suka baje a falo akai ta hira, Seemah kam ganin hirar taki karewa yasa ta sulale ta gudu d'akinta, tana shiga tana kokarin Zama a bakin gado tace an murd'a kofar, ta kalli kofar da sauri, Ammar ne ya shigo da sallama ta kalleshi tad'an had'a rai kad'an tace " Yaya baka kwankwasa bafa?"
Ya had'a hannunsa biyu yace " au amin afuwa." Ya fad'a tare da komawa ya rufe sannan yai knocking, tad'anyi dariya sannan tace shigo, nan ya shigo yana cewa " yanzu dai banyi laifi ba ko?"
Ta d'aga kai tare da zama, ya matso ya zauna kusa da ita sannan yace " ya kamata ki kwanta da wuri d'an nasan kin gaji gashi gobe zamu tafi."
Ta kalleshi sannan tace " Yaya?"
Yace " Ummm"
Ta girgiza kai tace " Shikenan ma."
Yad'an d'aure fuska yace " So kike muyi fad'a?"
Ta girgiza kai tare da cewa " ba fa wani abu important bane."
Ya harareta tare da kafeta da ido, tai kasa dakai tana wasa da 'yan yatsun hannunta tace " Yaya dama so nake ka tambayar min Dad a wani gari mahaifiyata take sunan kawai nake san ji."
Ya kalleta cikin tausayawa yace " Karki damu insha Allah kafin aurenmu zan kaiki har garin."
Kai ta girgiza mai tace " basan zuwa nakeyi ba nima kawai sunan nake san ji."
Ya kalleta kawai baice komai ba, cam ya wayence yace "Saura wata d'aya bikin mu ba wani abu da kikeso ko kike tunanin yi?"
Kallansa kawai tai sannan ta girgiza kai, alamar a'a, jikinsa yai sanyi amma ya daure ya shiga bata labari har sai da ta saki ranta, sun dad'e suna hira kafin Ammar yai shiru, kallansa tai tace " Yaya lafiya?"
Ya mik' e jiki a sanyaye ya tsugunna a gaban Seemah tare da rik'o hannayenta, a hankali ta d'ago ta kalleshi ta kasa furta komai, Ammar idanunsa na kanta, ganin bazata iya jure kallan dayake mata ba yasa tai saurin yin kasa da idanta, Ammar cikin wata irin murya mai ban tausayi taji yace " Seemah wani abu na damuna."
D'ago wa tai ta kalleshi idannunta sukayi raurau tace " Name fa?"
Ya kalleta a hankali yace " Tunda aka fara zancen auren mu ba wanda naji ya tambayeki ko kin amince da hakan, na sani sarai haryanzu son da kike ma Jalal bai bar zuciyarki ba haka kuma bana kaunar wani abu dazai sa in zama nine sillar tauye miki rayuwar farin cikin ki, Seemah ina tsoro......."
Hannu tasa ta rufe mai baki hawaye suka zubo mata a hankali ta shiga girgiza mai kai, tace " Ya Ammar na san sarai meke ranka haka kuma nice na zab'a ma kaina auranka bawai d'an ance ba, a'a sai dan nima na amince, kasani sarai bazan iya auran Deen ba bayan abinda ke tsakanin iyayenmu bazan tab'a bin san zuciyata ba akan farin cikin ka dana Dad, nasani kuma ko ince jikina ya bani da ace mahaifiyata nada rai itama wannan zab'in zata min."
Ta share hawayenta sannan ta zare hannunta daga bakin Ammar tad'an yi murmushi tace " Karka damu Yaya nasani a hankali zuciyata zata manta da Deen sannan ka manta shima yayi aure? Maybe ma ya manta dani."
Ammar ya goge kwallar data zubo mai yace " Seemah?"
Mik'ewa tai da sauri tad'an juyamai baya tace "Yaya nafi kowa sanin babban farin cikinka a duniya bai wuce ka ganni ina cikin farin ciki ba na sani sarai da hakan sai dai nima bazan iya jurar ganinka cikin bakin ciki ba."
Ammar ya matso kusa da ita baice komai ba sai dai kalamanta sun mai dad'i sosai, juyowa tai ta kalleshi sannan tamai murmushi.
Kasa magana yai hakan yasa ta rangwab'ar dakai tace " Yaya baza'a barni in kwanta da wuri ba?"
Da sauri yai hanyar waje yana cewa " Inafa zanso hakan."
Ta kalleshi har ya fita, yana fita ta sulale ta tsugunna a katsa tare da rufe fuskarta da hannu biyu, hawaye ne suka gangaro mata ta d'aga hannu sannan tace a fili " Allah na rok'eka ka yayemin san Deen daga Zuciyata kakuma taimaken soyayyar danake ma Ammar ta 'yan uwanta ka ta juye ta koma soyayyar aure."
Nan ta shafa sannan ta zauna a gun.......
Washe gari da safe suka hau jirgi suka baro kasar England....
Nima nace Allah ya tsare...
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
��♀
tnx a lot... we appreciate
ReplyDeleteplz posting yazama sau daya a rana neh??
ReplyDeleteShe said due to her other commitments and tight schedules she couldn't continue with daily postings... So far so good, ai an zo gangara... Allah kara basira dai kuma ya amfanar damu darussan ciki....
ReplyDelete