Saturday, 4 February 2017

JALALUDEEN 57

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com

   No. 5⃣7⃣

    Jalal ya kalli  Ammar sannan ya juyo ya kalli Seemah jikinsa ya kara wani yin sanyi, murmushi yama Seemah sannan a hankali cikin wata murya yace " Nagode Meemah da duk abinda ya faru bai hanaki ganina ba, nagode sosai." Yana kai nan ya fara tafiya ya wuce Seemah, Ammar na tsaye ganin Jalal ya fara tafiya shima jikinsa yai sanyi,  har Jalal ya d'an wuceta kad'an Seemah tace "Deen?"
Tsayawa yai cak batare daya juyoba sai idanunsa da suka kara cicikowa, wato haka dama rabuwa take? Seemah ma bata juyaba tace " In ka tafi yanzu shikenan kuma ko?"
  Idanu Jalal ya runtse zuciyarshi ta shiga k'una, sai dai ya kasa amsa mata, kuma ya kasa wucewa, Seemah can ta kalli Ammar daya juya baya ta fara takawa ahankali har ta isa inda yake, sannan ta juyo ta kalli Jalal, daidainan shikuma yaji shirun yayi yawa ya juya d'an ya ma ta sallama, gani yai bai ganta ba nan ya shiga dubata, daga nesa ya hangota da Ammar, juyawa yai da sauri d'an zuciyarsa na wani irin zafi, a hankali ya d'inga takawa har ya fita.

  Seemah kam Ammar ta kalla tace " Yaya?"
Juyowa yai a hankali d'an baiyi zatan zai jita a kusa ba, ta kalleshi ta mai murmushi tace " Kayi hakuri na........"
  Girgiza mata kai yai yace " Kar kice komai, naji dad'i ma da kika fito daga d'aki, d'an nagaji da ganinki kullum a d'akin nan."

   Tai kasa dakai tana neman abin cewa can tace " yaya ni ban ma san......."
Hannu yasa akan leb'enta yace " karkice komai."
  Ta kalleshi kawai batace komai ba, a hankali tad'an juya baya ta zata yananan, gani tai ba kowa agun, ga mamakinta jitai Ammar yace " Ya tafi."
Da sauri ta kalleshi jikinta yai sanyi tace " nifa ba wanda nake nema."

  Yai murmushi yace " nasani, kin tambayeshi mahaifinki?"
  Idanunta ne suka ciciko ta d'ago ta kurama Ammar ido, yace " Seemah?"
  Share hawayen daya zubomata tayi tace " Banasan sanin ko waye shi."
Zaiyi magana sukaji ana tafi,juyawa sukai suka kalli Junaid.
  Ya karaso yana dariya yace " iyee? Abin ma ba kunya a kofar falon Abba? Da alama kun kosa a d'aura." Yai maganar cikin zolaya.
  Ammar ya kalleshi yace " Kai fa meza'ace?"
  Junaid yai dariya tareda karasowa yace "ne nai ni kuma?"
  Kallan Seemah yai yace " Kanwata kema bakya mamaki? Ace wai Junaid an had'ashi aure da Zahra amma ko meta baiyiba sai ma farin ciki dayake?"

   Seemah tai dariya tare da kallan Junaid tace "Gaskiya ne yaya nima ina wannan mamakin, itakanta Zahran da na d'auka kai takeso, amma da akace mata Ya Junaid za'a bata na d'auka zatai kuka sai naga kamas."
  Dariya sukai su dukansu, Junaid yace " Wato kukuma 'yan sa ido kenan ko?"
Seemah ta kalli Ammar tao murmushi, ido ya kura mata yana mata wani irin kallo, Junaid ya rik'e hab'a zaiyi magana yaji Ammar yace " Farin cikina bai wuce in ganki kina cikin farin ciki ba."
  D'agowa tai ta kalleshi, batare datace komai ba ganin yanda yake mata wani kallo yasa tai saurin d'auke idanta tare da kallan Junaid ta wayance da cewa " Ya Junaid ina Ya Zaid?"

   Hakan yasa Ammar ya d'auke idansa, tare da kallan Junaid,  tai sa'a yace " bazai wuce wajen gate ba."
Ta juya da sauri ba tare da tace komai ba, kallo kawai Amnar ya bita dashi.

  Jalal kam har yakai waje zuciyarsa ba dad'i, yana fita gate ya samu gefen gidan ya zauna, idanunsa ne suke gano mai Ammar da Seemah, da sauri yasa hannayinsa biyu yad'an bubuga fuskarsa yana cewa " Wake up Jalal me ke damunka? Kamanta alkawarinka? Katuna abinda mahaifinka yamata ta dalilin cetanka fa?."
  Wata nanauyiyar ajiyar zuciya yai tare da cewa " Gaskiya ne, nasani kuma Ammar ne yafi cancanta da ita."
  Ya dad'e a zaune kafin ya mik'e ya tafi, sam ya mantada cikinsa wanda tun d'azu yake kara, gidan Sagir ya wuce.

  Bayan sun gaisa Sagir ya kalleshi yace " Mutumin yaushe a gari haka?"
Yai murmushi baice mai komai ba, Sagir ya dafashi tare da cewa " duk ciwon soyayyar ne yasa ka rame haka?"
  Murmushi Jalal yai yace " Sagir sorry zan d'an takurama kad'an."
  Ya fahimci me yake nufi, ya d'an harareshi yace " Jalal me yasa kake min haka?"
  Hannu biyu Jalal ya had'a irin na ban hakurin nan suka shiga d'aki, gado Jalal ya fad'a Sagir ya matso kusa dashi yace "daga ina kake haka?"

Jalal yai shiru, hakan yasa Sagir yace " Jalal ba dai......"
Katseshi yai da cewa " yau fa aka d'auramin aure."
What? Me kake nufi?
Jalal ya juya baice komai ba.

   Sagir ya mik'e tare da sa hannunsa a kafad'ar Jalal irin na tausa ya fita.
  Jalal ya hard'e hannayensa tare da zarfafa cikin tunani, abinda mahaifin Seemah ya fad'a yafi komai tada mai hankali, dama akwai uban da bazai so ganin 'yarsa ba? Shi ya d'auka inyaji zancen hankalinsa ne zai tashi ya kuma nemi ganin 'yar tasa cikin gaggawa bayan laififukan daya tafka.
  Wata iska mai zafi ya furzar tunaninsa d'aya tayaya zai sa mutumin nan ya shiryu?
Sagir ne ya shigo, ya zauna kusa da Jalal yace " tunanin me kake?"
Jalal ya mike da sauri ya fuskanci Sagir yace " Sagir kasan Senate Abdullahi?"
Sagir ya kalleshi da mamaki yace " kai kuma ina kasanshi?"
Jalal yai shiru, Sagir yace " Amaryarsa kanwar Ummana ce."
  Jalal ya d'ago yace " What?"
Sagir yad'an tab'e baki yace " hmmm ni sam mutumin nan ba wani burgeni yake ba ita kanta Aunty tun bayan auransu da wata 2 ta fara kawo kara."
  Jalal yai tsaki yace " ai da alama, amma ita mai yakaita auransa? Ba'ai bincike bane?"

Kallan mamaki Sagir yama Jalal yace " lalai Jalal, mutum kamarsa wanda yakeda kud'i ga mulki shine kake tunanin za'ai wani bincike? Ita kanta Auntyn ai kud'in ne ya rufe mata ido."

   Jalal yai shiru, Sagir ya dafashi, yace " ka ga ka raba kanka da mutumin nan Jalal, a yanda Aunty take zancensa sam..."
Kai ya girgiza kawai, Jalal yai shiru ya shiga tunani, Tayaya zaiyi yasa mutum kamar Senate yaba 'yarsa hakuri kafin auranta?

  Dafashi Sagir yai, Jalal ya kalleshi zai yi magana cikinsa yai wani kara, murmushi Sagir yai yace " Bari in kawo ma abinci." Ya fita yana dariya.


  Jalal ya dad'e yana tunanin mafita kafin bacci ya d'aukeshi.
Washegari ya shirya ya koma Birnin/gwari.

 

  © *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*

��‍♀

1 comment: