Thursday, 16 February 2017

JALALUDEEN 65

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com

   No. 6⃣5⃣

  Abdul ya kara kallan mutanen a zuciye ya koma ciki, Jalal kam yana ma mutane sallama da kuma sai sun jisu a sabon shiri na gaba kawai yaji an shakumo mai riga, kallan Abdul yai cikin mamaki sam idanun Abdul ya rufe ya manta shiri akeyi kuma live, cikin masifa da bakin ciki yace " kai waye kai? Me na maka ko ince menene tsakanina dakai da zaka aikama ragowar 'yan jaridu dasuzo? Dama can ka shirya ci min mutunci ne bawai shirin mutunci kaso yi  ba ko?"

   Jalal ya kalleshi yace " Senate me kake yi haka bakaga shiri akeyi ba? Mutane fa suna kallanka."

  Cikin masifa yace " da a kalleni da kar a kalleni ai ka riga ka gama cimin mutunci ya fad'a tare da nunamai Jaridar da P.A d'insa ya kawo masa yanzu."

  Jalal ya kalli head line d'in inda ya bud'e " *SHIN DA GASKENE SENATE ABDULLAHI BASHI DA HANNU AKAN FYAD'EN DA AKAI?*

   Jalal yai murmushi tare da ba masu aikin umarnin su daina d'aukan rahotannin, bayan sun daina Jalal ya kalleshi ya sakar mai wani mugun murmushi yace " Bana tsoronka, ba kuma na tsoron abunda zakamin, ka manta kalamaina lokacin dana je gidanka?"

  Abdul ya kalleshi da mamaki "kai ne kaje gidana?"

  Jalal ya d'aga mai gira yace " Kayi tunani dakyau, sanda nazoma da zancan 'yarka wani cin mutunci kamin ko ince kama yarinyar da ba ruwanta?"

  Nan fa Abdul ya tuno jikinshi ne ya shiga rawa ya sake Jalal yana girgiza kai, kamar zararre.
  Jalal yad'an zumburo baki yace   " ayya I pity you,  gashi yanzu na kai kararka kuto kana zuwa gida zakaga sammaci."

   Kai Abdul ya cigaba da girgiza wa yace " karya kake d'an talakawa, ko Amadu bai isa yaja dani ba bare kai, inada arziki da karfin da ba wanda ya isa ya ja dani."

  Jalal ya jinjina kai tace " hmm gaskiya ne wannan ni kaina na shaida, sai dai wannan karan dukiyarka da matsayinka bazasuma amfani ba, d'an kuwa al'uma sunga halin da ake ciki kana tunanin wani zai taimaka maka bayan shima yana tsoron kar mutane su tsaneshi irinka?"

  Abdul cikin tsananin takaici ya d'aga hannu zai mari Jalal, hannu Jalal yasa ya rik'e hannunsa sannan yamai murmushin rainin hankali yace " wlh wlh kaci darajar jininka ne ke ya wo a jikin Seemah da wlh sai na maka abinda yafi wannan, sai naci ma zarafin da har karshen rayuwarka bazaka manta da abinda kama Fatima, Dad wato Malam Isma'il, Mahaifiyarsu Ammar da kuma Mahaifina Amadu ba da sai na sa ka fisu wulakanta a doron kasar nan."

   Abdul ya kalli idanun Jalal yanda sukai jaa, tsoron kalaman Jalal ne ya fara kamashi ya kalli Jalal a tsorace sannan ya fizge hannunsa, Jalal ya had'iye wani abu sannan yace " ka b'atama mutane dayawa rayuwarsu tayaya ma zakayi rayuwa cikin farin ciki? 'Yar ka da batama sanka ba baka tab'a tunanin nemanta ba saboda giyar mulki na d'ibanka."

  Harya bud'e baki zai sake magana sai kuma ya fasa ya juya ya fara tafiya,  har yad'anyi nisa ya tsaya tare da cewa " sai na ganka a kuto."
  Jalal ya wuce su Abbas da duk sukai tsuru tsuru suna kallansu cikin tsoro.

Jalal fita yai direct yahau sabuwar motar daya sa Sagir ya siyomai, kirar Mercedes benz fara tas, gidan su Abba ya wuce.

  Sukuwa a b'angarensu Abba jikin kowa yagama yin sanyi, Dad ya share hawayen daya rasa na dadi ne ko name, ya kalli Amadu yace " Amadu a wani dalilin zaka bar Jalal yai wannan abu mai hatsarin gaske? Me kakeyi da bazaka hanashi ba?"

  Amadu ya share kwallarsa yace " Isma'il wlh sam bansan me yaron nan yake shirya wa ba nidai kawai cemin yai ince a kunna tv a kuma kira Seemah."

   Abban Zaid ya kalli Amadu yace " Abdul bazai bar jalal haka ba, amma dama Abdul shine yama Fatima fyad'e?"

  Nan Amadu ya warware musu komai na abinda ya faru.

  Sunyi shiru kowa na tunanin mafita, samari 'yan gari kuwa sun fito da sanduna suna zanga zanga a kofar gidan Abdul akan dolene ayi bincike dan suma basu yarda ba.


   Jalal kam bayan ya isa gidan yai parking motarsa ya fito, a harabar gidan yaga Zahra da Zaid a tsaye, jiyai Zahra tana cewa " Yaya Zaid kazo ka duba Seemah inajinfa ba lafiya take ba wani abu takeyi kamar ba'a hayacinta take ba."

  JALAL ya matso da sauri yace " ina Seeman?"
Zahra ta kalleshi da mamaki, Zaid yace " Jalal zo muje."
Nan sukai d'akin da Seemah ta rufe kanta a ciki,  Ammar suka gani a tsaye a kofar yana kwankwasawa tare da kiran sunanta.
Jalal yasha jinin jikinsa, tsayawa yai cak batare da ya karasa ba.
  Ammar ya kara buga kofar yace  " Seemah meyasa kike min haka? So kike kiga hankalina yayi matukar b'aci ko kuwa?"

  A hankali Seemah ta mik'e tazo ta bud'e mai kofa tana bud'ewa ta fad'a jikinsa ta rungumeshi tana wani irin kuka, Ammar ma kwalla ce ta taro mai a ido, yace " Seemah menene? Mahaifin naki ne bakyaso ko kuma nakiso akacimai mutunci ba?"

  Kai ta girgiza tace" ni ba mahaifina bane, Dad ne kawai mahaifina, sai dai Ya Ammar nasan mutumin nan, na tab'a ganinshi a hotel d'in daka zauna, yaya bashida mutunci na tsorata da gani mutum irin haka. "
  
  Jalal ya share hawayen daya zubo mai sannan ya kakaro murmushi tare da juyawa zai fita, Seemah zata sake magana kawai ta hango kamar Jalal,  da sauri ta saki Ammar sannan cikin kakusar murya tace " *DEEN WAIT*

Tsayawa Jalal yai cak ba tare daya juyo ba, Seemah ta kalli Ammar tace " Yaya in mai magana?"

  Gaban Jalal ne ya fad'i jin kalaman Seemah, amai magana? Au in zata mai magana sai ta nemi izini? Idanunsa ya runste.

  Ammar ya d'agama Seemah kai sannan ya juya ya bar falon, ba shakka yaji dad'in yanda Seemah tabashi matsayi.

   Zaid ma ya juya yai waje, Jalal baisan Seemah ta karaso ba jin kanshin turarenta yasa ya fahimta, a hankali ya bud'e idanunsa ya zubasu akanta.

  Seemah ta kuramai ido gyambon data d'auka ya warke ne ya motsa, hawaye ne ya zubo mata, shima hawayen ne ya zubo, bakinta ya fara rawa ta kasa mai magana.

  Jalal ya goge hawayensa sannan ya kalleta da murmushi a fuskarsa yace " how have you been?"

  Kallansa kawai take ta kasa magana, Jalal ya d'aga kai ya d'an ja hanci yace " I see, ya za'ai ma in tambayeki haka bayan nagani you are fine."
  Ya had'iye wani abu yace " kinga abinda akai?"

  Kai ta d'aga mai tana hawaye, Jalal ya share nashi hawayen tareda cewa   " meyasa ruwan nan yaki daina zubowa daga idona, inaji wani abu ya fad'amin ne."

   Kallan tausayi tamai tace " Deen me ya kaika shiga harkar mutumin can? Kasanshi kuwa? Kasan wani irin mutum ne?"

  Jalal ya kalleta ya d'anyi dariya tare da cewa " Koma wani irin mutum ne ai baifi karfin Allah ba, sannan ni ba tsoronshi nake ba kin manta nine?"

  Tasa hannu ta dakeshi da karfi a kirji tace " Deen meyasa kake abu domin ni? Meyasa bazaka manta dani ba? Why? Why are you making me miserable. "
  Ta sa wani irin kuja tare da tsugunawa akasa.
  Jalal ya kalleta zaiyi magana Ammar ya karaso gun ya d'agata sannan ya kalli Jalal, Seemah ta kara sa kuka tace " Ya Ammar?"

  Ammar ya mata alama datai shiru yace " wuce d'aki." Ya fad'a tare da goge hawayensa.
  Seemah ta juya tai d'aki tana tafe tana waiwayen Jalal.




© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*

��‍♀

1 comment: