Friday, 17 February 2017

JALALUDEEN 66

JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ


Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com

   No. 6⃣6⃣

 

    Ammar ya dawo da hankalinsa kan Jalal hannu ya mikamai suka gaisa, Ammar ya kalleshi yace " Jalal mutumin da kai magana dashi wannan mara mutuncin shine kakeso kacemana mahaifin Seemah ko me?"

  Jalal ya kalli Ammar yace " ni kaina dana fara ganinshi ban amince ma idanuna ba."

  Ammar yace " inaaa... da sake taya za'ayi Seemah wacce ba ruwanta me mutunci ace ta fito daga tsatson wannan mutumin? I just can't believe it."

  Jalal yad'an dafashi yace " Ammar kamar ka manta fyad'e yana mahaifiyarta? Duk mutumin da zai ma wacce saura kwana biyu ya aura fyad'e ai kasan sai a hankali sai dai koni banyi zatan rashin imani da mutuncin sa yakai haka ba."

   Ammar yai shiru, Jalal yai murmushi yacigaba da cewa " kamanta Allah ne ke fitar da rayyaye acikin mattace kuma mattace acikin rayayye? Please Ammar ka daure zuciyarka idan zuciyarka ta karaya tun yanzu ya kakeso Seemah tayi?"

  Ammar yad'an ture hannunsa daga kafad'ar sa ya kifta ido yace " waya fad'ama zuciyata takaraya? Sannan ce maka nai mun zama abokai da har zaka wani dafani?"
  Yanda yai maganar ne yasa Jalal yasa dariya yace " Ammar bansa kanada wannan cute site d'in ba, duk sanda muke had'uwa cikin d'aurewar fuska muke."
    Ammar ya d'an harareshi yace " yanzun ma acikin b'acin ran nake ai."

    Jalal ya kalleshi yace " tuba nake Ammar nasan akan me kake cikin b'acin rai sai dai nasani tuni Seemah ta cireni a ranta kaima kasani dazatamin magana fa sai data nemi izininka."

  Ammar yai shiru kawai yana kallan Jalal aransa yace Jalal kenan.
A fili ya wayancewa da cewa " kaje falo nasan Dad nasan ganinka."
  Jalal ya d'aga kai alamar to sannan ya kalli kofar d'akin da Seemah take ya wuce.

Ammar bayan yaga Jalal ya wucene shikuma ya wuce d'akin Seemah, knocking yai dama tana tsaye jikin kofar tanasan jin me suke cewa sai dai ta kasa jiyosu, bud'ewa tai Ammar ya shigo.
Kallanta yai ta kalleshi tanasan tambayarsa meya cema Jalal sai dai inaa bazata iya ba, ta daure tace  " Yaya amma ai ba mutumin nan bane mahaifina bako?"
Ammar ya kalleta kai ta girgiza tace " haba dai yaya it can't be,  mahaifi fa akace, da mahaifinane ina ganshi ai ina tunanin jikina zai bani munada alaka dashi amma ni farkon ganina da tsanarsa na wuce ta ya zakuzo kucemin mahaifinane?"

  Ammar yad'an harareta yace " na d'auka Seemah ta tace ba ruwanta koma waye mahaifinta itadai Dad ne nahaifinta."

    Da sauri tace " eh haka ne amma...amma...amma.."
Ammar yasa dariya yace " amma me? Yau kece kike in  ina?ko rasa abin cewa kikai?"

  Ta juya yai tare da rangwab'ar dakai, Ammar yai murmushi yace " karki damu kinji kinmanta nabarmiki Dad nina koma d'an gidan Abba?"

  Juyowa ai tana dariya tace " kai yaya."
Yace "ahhbhh aikina ya biya tunda kinyi dariya."
  Kallansa kawai tai batace komai ba, ya matso kusa da ita tare da turo fuskarshi kusa da ita yace " kallam fa?"

  Tasa hannu tad'an ture fuskarshi kad'an sannan tace " kai Yaya."
Tai maganar kamar zatai kuka, yai murmushi sannan ya fita, har yaje kusa da kofa ya tsaya, jitai yace " Jalal nagunsu Dad."
Da sauri tace cema akai inasan insan inda yake?"

Yanakai nan yai waje yana murmushi, Seemah kam yana fita ta furzar  da wata iska tace " Deen me kakeyi acan?"

   Jalal kam bayan ya shiga azazzaune ya taddasu suna maganar Abdul, Dad yace " nasan Abdul fa, bansan ya akai ya canza haka ba, duk ba bayaji amma iskancinsa baikai haryai fyad'e ko shan giya ba, nadaisan yana shan taba, ina mamakin yaushe ya koma haka."
  Abban Jalal yace " Abokan fa? D'an alokacin bazan manta ba shima kamar bayasan shawarar fyad'en da kuma kama Jalal kawai dai sun sugashi ne sannan yana kwad'ayin hakan dama a kasan ransa."

  Abban Zaid ya kalli Jalal yace " matsonan Jalal."
Nan Jalal yazauna kusa da Junaid tare da gaidasu, Dad yai ajiyar zuciya yace " Jalal kasan mutumin nan mai karfi ne tunda Senate ne da mutane ke sanshi meya kaika yimai haka? Sai ka sanar damu."

  Jalal zaiyi magana wayar Sagir ta buga Abban Zaid yace " d'aga mana."
Jalal ya d'aga tare da cewa " Sagir ya akai?"
  Sagir cikin tashin hankali yace " Jalal duk an tsayar da saida Jaridun nan sannan duk 'yan jaridan nan sun watse daga gidansa."

  Jalal yace " What?"
Sagir yai ajiyar zuciya yace " Jalal yazamuyi? Nasan yanzu kanka abin zai dawo."

  Jalal yad'an mike daga gunsu Abba zai d'an fita, Dad ne ya rikosa yace " yi wayar anan."
Kallansa Jalal yai sannan ya daure yace " Sagir karka damu ai dama nasan hakan zata faru, in ba'ai hakan ba kenan ba mutum bane mai matsayi."

  Sagir yace " to sai kazo."
Nan suka kashe wayar, Jalal ya kalli Dad yad'anyi murmushi yace " Dad is not a big deal."
  Junaid ha kalleshi yace   taya zakace haka bayan da alama Abdul is out to get you."

  Jalal ya kalli Abbansa sannan ya kalli Dad yace " Dad zan koma Birnin gwari yanzu nasan nan zai nufa dan cimin zarafi."

  Dad kallan Jalal kawai yake, Abban Zaid ne ya daure yace " Jalal ka cire hannunka daga abun mutumin nan, mu zamu karasa abinda ka fara."
  Jalal ya girgiza kai yace " me kenan akai Abba? Na fara abu sannan inbarku ku karasa? Idan Abun yazo da downfall d'ina sai in jawoku mu fad'i gaba d'aya kenan?"

  Ammar ne ya katseshi da cewa " Ni zan rakashi muje Birnin gwarin tare, Abba dukanki please karkusa hannu a wannan harkar."

  Jalal ya kalli Ammar yai murmushi, Ammar yai saurin juya kai tare da cewa " malam daina min murmushi bancema munzama abokai ba tukun."
Dariya dukansu sukasa a falon, Abban Jalal yace " nufinka kenan kunzama abokai, dama can abokan ne ku."
  Ammar yai saurin juyawa ya fita, Jalal yai kasa dakai yana murmushi, Junaid ya matso kusa dashi yace " Ammar tsoro yake karka tafi kai kad'ai wani abun ya sameka."
  Jalal ya jinjina kai yace " nagane nima, bayaso ya fad'i abinda ke ransa ne."

  Nan suka sakeyin murmushi.

Ammar d'akin Seemah ya koma, a bud'e kofar take, Seemah  tana zaune Zahra na tsaye tana 'yar mita yanzu shikenan baza ai partyn ba? Nafa fad'ama kawaye na, wai meke faruwa agidan ne?"

  Seemah ta girgiza mata kai tace " kedai fad'i gaskiya bawai partyn kikeso ba so kike kiga an kawo miki lefen ki."

Zahra ta turo baki tace " eh d'in nibama lefe ba na kosa ma ai auran."
  Seemah tace " dama ai na sani basai kin fad'a ba da alama kekam kin gaji da gida."
  Zahra ta murguda mata baki tace " kefa? Baki kosa a d'aura muku aure da Ya Ammar ba?"

  Seemah tai shiru zatai magana Ammar yai saurin katseta da shigowa yace " Ahh Zahra na kula kina neman takurama Seemah ta."

  Seemah ta kalleshi, Zahra tace " haka kace yaya? Shikenan nima zan rama ai." Tana fad'a tai waje.

  Ammar ya kalli Seemah yace " baki mamaki ba daga fitata harna dawo?"
Tai murmushi tace " nasani Yaya damuwa kai da halin da nake ciki."

  Yatsarsa ya nunata dashi yace "hmm wannan kanwartawa ta gama sanina."
  Ta juyar da kai tace " wa zai sanka bayan ni? Tare fa muka taso yaya?"

  Yai ajiyar zuciya yace " Haka ne kinci gari, amma naji dad'i naga kin ware."
  Tace " ba dole ba duk yanda kai kokari gurin sani dariya?"
  Ammar har kasan ransa yaji dad'in kalaman nan yace " ina neman izini."
Tace " name fa?"
  Yai shiru can yace " Zan d'anyi tafiya ne, amma yau zan dawo."

  Ta kalleshi tace " Yaya inzakai tafiya sai ka nemi izini ai kawai sanar dani zakai."
  Yace " haka ne amma ni nafisan in nemi izinin."

  Tai murmushi sannan tace " an baka Allah ya kiyaye hanya."
Yace Amin, sai naji kamar......."
Harararsa tai tace " zaka fara ko yaya?"

  Ammar yace " sorry na daina, sannan ya d'aga mata hannu yai waje."
Tabi bayansa da kalli tare da cewa " Deen ko ya tafi shima? Ahhh yazanyi?"

  Kai ta girgiza tace " me ya dameni ma da koma ina yake? Meye tsakanina dashi dazan damu?"


© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*

‍♀

1 comment:

  1. Its really enjoyable...
    Keep it up and rolling....
    Thanks....

    ReplyDelete