Thursday, 2 February 2017

JALALUDEEN 56

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com

   No. 5⃣6⃣

 

   Jikin Jalal yai sanyi haka suka shiga gidan, Zaid yace " ka ga ka nausheni ashe kaima gaba kai za'a nausa?"
Jalal yai murmushi yace " hakane dama, to amma karfa mu shiga cikin gidan ka d'inga cewa na nausheka."
Dariya Zaid yai yai alamar zip a bakinsa, Jalal yai murmushi, sun shiga falon mami, mata me 'yan uwa a zaune, nan Jalal ya tsugunna kansa a kasa ya gaishesu, suka amsa suna kallansa, ya musu ya hakuri, Zaid ne ya kalli mami yace " mami kin ganeshi? Jalal d'in........"
  Kafarsa Jalal ya mintsina da karfi, Zaid yai 'yar kara tare da kallan Jalal, da sauri ya mik'e yace " Sai da safenku."
Ya fad'a yana kallan Zaid, muryar mami suka ji tace " Ka kaishi ya gaida su Abbanka."
  Jalal ya kalleta jiki a sanyaye, da alama ta ganeshi tunda sun had'u a asibiti, Zaid ya kalli Jalal yace muje ko?
  Nan suka wuce falon Abba, a hanya Jalal ya kalli Zaid yace " d'azu mai kake san fad'a?"
"AUUUU wannan? Hmm dama cewa zanyi Jalal d'in Seemah in na fad'a za'afi ganewa."
  Jalal ya kalleshi cike da mamaki yace " mene? Jalal d'in Seemah?"
Dagewa yai ya takamai kafarsa da karfi Zaid sai da yai 'yar kara yace " Wai ni menai?"
  Girgiza kai Jalal yai yace " lalai Zaid mema kai kake tambaya? Da alama........."
  Ammar ne ya karaso gun yana cewa " Zaid meye hakan?"
   Ya fad'a yana kallan wanda ke tsaye, kalan kallo suka shiga yi, Jalal ya daure tare da mik'a mai hannu, Ammar ya mik'amai shima suka gaisa.
  Jalal ya kalli Zaid sannan ya kalli Ammar yace " Gaisuwa nazo."
  Gyad'a kai yai alamar gamsuwa sannan ya nuna mai kofar falon yace " muje?"
  Nan suka shiga su uku tare da sallama, Abba, Dad, da kawu suna zaune a falo ga Junaid a kasa da alama nasiha ko fad'a ake mai, jin sallama yasa suka amsa, Junaid ya kalli Kawu yace " Zan rik'eta amana insha Allah."
  Yana kainan ya maida kallansa kansu Ammar, Zaid ne ya fara shigowa, sai Ammar sai Jalal a baya, dukansu suka canza fuska shikam Junaid kallan Jalal yai nan suka karasa suka zauna a kasa.
   A hankali Jalal ya gaidasu, suka amsa kamar basa so, ya musu ya hukuri, nan ma suka amsa kamar d'azu, sunyi shiru a falon kafin Junaid yace " daga ina?"
  Jalal ya kalleshi suna kamada ya Habib hakan yasa ya gane shine d'ayan yayan Seema, mik'ewa yai a hankali ya dawo sautinsu Dad a hankali yakai gwiwowinsa kasa, kallan mamaki suka mai, idanun Jalal suka cicoko ya d'ago a hankali ya kalli Dad yace " Nasani banida bakin magana, bankuma san da wacce kalma zan fara ba, da ace abin bai faru bane shine zan sami karfin gwiwar yin magana." Yai ajiyar zuciya sannan ya cigaba" na sani dani da mahaifina bamu da bakin da zamu nemi yafiya daga gareku, sai dai.......sai dai....."
  Hawaye ne yafara zubomai hakan yasa ya kasa karasa maganar, kansa ya durkusar a kasa yana hawaye sosai, dukansu tausayinsa ya kamasu, Junaid ma ya gano shine Jalal d'in, Dad yanasan Jalal tunsanda aka haifeshi, ganinsa cikin wannan yanayi yasa shikansa yaji idanunsa sun ciciko.
   Ammar mik'ewa yai yaje kusa da Jalal a hankali yace " Tashi mu tafi."
  Jalal ya runtse ido, ba tare da ya motsa ba, Ammar ya kalleshi cikin tausayawa, Zaid ne ya mik'e shima ya kalli Jalal yace " Katashi ka tafi Jalal."
  Nan ma bai motsa ba, Zaid ya kalli su Dad cikin b'acin rai d'an shi baisan meya faru ba, yace " Abba shiya muku laifi? Me yai? Meyai muku da zai tsugunna yana neman yafiya amma dukanku ku shareshi? Bayan yarinyar dayakeso take sanshi kun......"
  Da karfi kuma cikin tsawa Jalal yace *ZAID* kowa sai da ya kalli Jalal, Zaid a zuciye yai waje, a zahiri shikam ya kasa gane menene dalilin dazai sa a hana yarinya yaron da takeso.

  Jalal yai ajiyar zuciya tare da kara share hawayensa ya kakaro murmushin da kana gani kasan na bakin ciki ne ya kalli Dad yace "Dad an d'auramin aure."
  Kallan sa sukai su dukansu, ya sake murmushi sannan ya kalli Ammar yace " Ammar ina tayaka farinciki, naji an kusa sa rana."
   Ya sake wanni murmushin tare da goge kwalla ya maida kallansa kansu dad yace " Dad Allah yasanya alkairi, naji dad'i."
   Hawaye suka kara zubomai, yace " Bakomai in har zuciyarka bazata iya yafemin ba, na sani wannan wani gyambo ne da ke zuciyarka, tunda Amininka ne ya cuce ka."
  Yai murmushi har hakoransa suka fito, ya share hawayensa sannan yace " Amma nikam a kasan zuciyata nayi tunanin wani abu guda d'aya, naji dad'i daya kasance kaine ka raini Seemah har kawo wannan lokacin, da Allah ne kad'ai yasan wace rayuwa zatayi a gidan wannan mutumin da zuciyarsa ba imani."

   Ya share kwalla sannan yace " in na duba abin ta fuskar daya kamata sai inga Allah ne ya taimaki Seemah......."

  Dukansu tausayin Jalal ya ratsasu sosai, dan Dad sai daya kauda kai ya share kwalla a fakaice, Junaid ma idanunsa sun ciciko, Ammar kam shima hawayen yakeyi, a hankali Abba yace " Kasan mahaifinta ne?"
  Jalal ya kalli Abba yana hawaye yace " nasanshi, sai dai ba amfani a sanin nashi."
  Dad ya mik'e yazo kusa da Jalal yace " Me kake nufi?"
Jalal yai murmushin takaici yace " Dad karka damu, bazan iya fad'a muku ko waye a wannan lokacin ba, sai dai nama Ammar alkawari, kafin a d'aura masa aure da Seemah sai mutumin nan yazo da kansa yaba Seemah hakuri koda kuwa hakan shine zai zamo abu na karshe dazanyi a rayuwa ta."

   Dad ya kalleshi cikin tsananin tausayawa, Ammar ya share kwalla ya kalli Jalal yace " kar ka kuskura kayi abinda zai jama matsala a rayuwa da sunan alkawari."
  Jalal yai murmushi, ya mik'e yazo kusa da Ammar ya dafashi, baice komai ba yai hanyar kofa.

  Zaid kam yana fita gun Seemah yaje, tana zaune da waya tana rubuta sunan Jalal sai ta goge, ta sake ta kuma sake gogewa, tafi hour 1 tana abu d'aya, Zaid ya shigo ya kalleta yace " Seemah albishir?"
Kallansa tai batace komai ba, yace " Jalal yazo yana gunsu Dad gwiwowinsa a kasa."

  A zabure ta mik'e ta zauna tare da cewa " Deen?"
Deen?
   Deen d'i.....?
  Zaid ya d'aga mata kai, fita tai da sauri d'an ko mayafi ta manta bata d'auka ba, sai datakai kusa da falon ta tuna ashe fa sun rabu, hartayi alamar juyawa taji motsin bud'e kofar falon, tsayawa tai cak ta baya gabanta na dukan uku_uku, Jalal shima yana fitowa daga d'an nesa kad'an ya kalleta, gabansa ne ya fad'i a hankali Seemah ta juyo, cikin tsoron wanda zata gani, Jalal ma idanunsa na kanta.

  Tana juyowa suka kafe juna da ido, dukansu idanunsu ya ciciko da kwalla, Seemah jitake kamar taje ta rungumeshi, a hankali Jalal ya fara takowa, suna kallan juna, har yazo kusa da ita kad'an, ya fara kokarin maida kwallarsa tare da kakaro murmushi ya rasa me zaice mata, itakam kallansa kawai take.
  Can ya dake yace " Long time?"
  Ta kalleshi tare da share kwalla tace " ka rame"
   Yai murmushi yace " kema."
  Ta d'an d'auke idanunta, a hankali yace " bantab'a tunani zan ganki ba."
  Ta d'ago ta kalleshi tace " nima bansan ya akai nazo nan ba."
  Murmushi mai cike da tausayin juna sukama kansu, ya kalleta yace " an kusa ko?"
  Kai ta d'aga mai, yace " Congrats. "
  Itama tace " anyi ko?"
  Shima kai ya d'aga mata, ta share kwalla tace " I see."
   Shiru sukai suna kallan juna can Jalal yace " bakya cin abinci ko?"
    Ta kalleshi batace komai ba, yace " do you not resent me?"
   D'agowa tai ta kalleshi, ya jinjina kai yace " dole ne ko?"
  Kallansa kawai take batace komai ba, yace " bazan nemi yafiyarki yanzu ba, sai na cika alkawarin dana d'auka."
  Ta bud'e baki zatai magana, taga Ammar ya fito daga falo, cak ya tsaya daga nesa kawai yana kallansu, itama kallanshi takeyi, hakan yasa Jalal ya juya...........




Ruguntsemi sai ran sallah�� Ruguntsemi sai mata�� ranar bikinmu akwai shagali Ruguntseminmu da nairori���� oh ni Ayush ina ganin haka kawai na tuno wakar daa.......

  

  © *THE MEEMAH'S LOVE TEAM*

��‍♀

1 comment: