Wednesday, 1 February 2017

JALALUDEEN 55

����������������
     �� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������




Na *AYUSHER MUHD*

ayushermohd.blogspot.com

  *This page is for you Ramalurv......*��������

   No. 5⃣5⃣

  _I am really sorry jiya da shekaranjiya kun jini shiru, wani uzuri ne ya hanani typing. ......luv u ol_

   Jalal ya kalli yarinyar ya mata wani murmushi yace " muje ko? Ta kalleshi sai dai idanunta nuna mata wani guy datakeso yake, hakan yasa ta d'aga kai da sauri tare da natsowa tana k'okarin kamamai hannu, Jalal yad'anyi baya tare da cewa "kiyi gaba ina binki."

   Tad'an tab'e baki kafin tai gaba, wani tafkeken falo ta bud'emai ya shiga da sunan falon baki sai dai duk dakiya irin ta Jalal sai da jikinsa ya amsa d'an kyan falon ya wuce inda mai karatu zaiyi tsamani, ta nuna mai kujera, Jalal ya zauna tare da karabin falon da kallo, sam ya shagala baiyi tsamani ba yaji mace ta zauna kusa dashi tare da sakalo hannunta, zabura yai ya mik'e cikin mamaki yace "me kike yi hakan?"
Ta tab'e fuska kamar zatai kuka, jitai ance tashi ki shiga ciki, atare suka kalli mai maganar, ta mik'e tana layi tai ciki shikuma Jalal ya sake kuramai ido.

  Har mutumin yazo ya zauna tare da kunna tv Jalal na tsaye sai da yace " zauna mana."
  Sannan Jalal ya farga tare da zama a kasa, yace "Ina wuni?"
   Mutumin bai amsa ba yabi Jalal da wani kalan wulakanci sannan yace "kaine kesan Huda?"
Jalal a ransa yace Huda sunanta?
  A fili ya d'ago ya kalleshi, zaiyi magana taji yace " Naji dad'i dana ganka haka, dama nafisan talaka wanda yake nema, yanda duk abinda na gindaya mai dole ne yabi, d'an haka ka sanar da iyayenka d'an nima na gaji da wannan iskancin nata da jamin magana datakeyi, a d'aura muku aure sai in turaku Australia kuje can kuzauna har karshen rayuwarku."

  Jalal ya d'ago ya kalleshi da tsananin mamakin kalaman fayake furtawa a matsayinsa na mahaifinta.

Daurewa yai tare da cewa " niba saurayinta bane sannan ni maganar danazo ma da ita......."
  Jiyai an katseshi da cewa " what? Kaikasan ko ni waye zaka rainamin hankali? Da kace gunta kazo yanzu kuma me? Ko dama ba da aure kake santa ba?"
  Ya mik'e yana kare ma Jalal kallo, Jalal ya dake tare da d'agowa ya kalleshi yace" akan maganar d'aya babbar 'yar taka nazo."
  Kallan mamaki yamai yace " Da alama bakasan ma mai kazo yi ba, bayan huda ragowar kannanta maza ne guda uku sai karama yanzu wacce ko shekara 4 bata kai ba." Cikin takaici ya fara kokarin juyawa.

   Jalal gani haka yasa yai saurin cewa " Ka manta Fatima ne? Ta garin birnin/gwari?"

  Da sauri ya juyo ya kalleshi idanunsa suka kad'a da sauri ya dawo kusa da Jalal ya d'agoshi tare da rik'emai kwalar riga cikin fad'a yace " Who are you? D'an jarida ne kai?"
  Har zuciya Jalal yaji tsoro sai dai da ya tuno Seemah sai ya dake yace " Ni ba d'an jarida bane, Sunana *JALAL* D'an gidan Amadu mai shago dake garin birnin/gwari."

  Sakeshi yai sannan yace " What?"
Jalal ya gyara tsayuwarsa, yace " 'yarka tananan lafiya agun mutumin da kuka ma sharri ya rik'eta, sai dai ko bata fad'a ba nasan itama tanasan ganin mahaifinta."

  Wata mahaukaciyar dariya Jalal yaji an fara mai kallan Abdul yai cikin tsoro, Ya dad'e yanayi kafin ya tsagaita yace " What?'ya ta?" HA HA HA HA
Ya cigaba " ko a da ba 'yata bace banga dalilin dazaisa yanzu ta zama 'yata ba."

   Jalal yai ajiyar zuciya tare da komawa ya zauna a kasa, yace " ka manta Fatima fa wacce kuka ketama......."
  Tsawa ya dakamai yace " na keta mata ko Isma'il ya keta mata?"
  Jalal ya d'ago cikin mamaki yace " me yasa kana babba kakesan take gaskiya? Me yasa bakajin kunyar karyata abinda kasan tabbas shine gaskiya?'
  Ya kalli Jalal yace "in ma turo ka akai ko d'an kanka kazo sai ka kama hanya ka fita, duk duniyar nan banga wanda zaizo ya wargazamin harkar siyasa ta dana shiryata da gumi na ba, dan rainin hankali sai da nakai wani matake sosai ina shirin kara hawa sama shine zakazomin da zancen banza d'an kasamin bak'in jini gun mutane? Da can bakuzo ba sai yanzu?"
  Ya nuna Jalal da yatsa yace " Wallahi kaji ma fad'ama ba 'yataba? Ba kuma matata ba ko mahaifiyata bata isa ta kawomin cikas a harkar siyasa taba in kyaleta bare kai da wata yarinya daban ma santa ba, in kud'i takeso kaje kace ta fad'i ko nawa ne, Ni Abdullahi nad'au alkawarin ba ta."

  Jalal wani irin kallo yake binsa dashi na tsananin ban mamaki da kuma tsoron furucinsa, wani irin mutum ne wannan? Siyasa ce ta maidashi haka ko kud'i ne? Ko kuma dama can haka yake?"
  Kafin Jalal ya k'okarta yai magana haryakai bakin kofa, Securities ne suka shigo suka kalli Jalal sukace " fito ko mu fitar dakai."
Jalal ya kalli mutumin cikin takaici ya dake ya  matso kusa dashi kad'an yace " Wallahi kaji na rantse maka in dai ina raye sai ka tsuguna a gaban Seemah ka nemi yafiyarta da abinda kama mahaifiyarta, idan kafi karfi na ai bakafi karfin hukuma ba, Allah kuma na tare dani kajira ka gani."

Dariya Abdul yai tare da zaro 'yan bandir d'in dubu d'aya ya mik'amai yace " Daga kai har yarinyar har hukumar bakufi karfin wannan ba."

  Jalal cikin takaici yake kallansa ya kakaro murmushi yai sannan yace " in kafi karfin hukuma ai baka fi ta Allah ba."
Yana kainan yai waje.

  Ko securities d'in bai kula ba ya fita, kafa kawai yake sawa, yana tafe yana mamakin abinda idanunsa suka ganemai, kuma kunnensa suka jiyemai, a hankali wasu kwalla suka zubo mai, a fili yace " Seemah ya zamuyi?"


   Seemah kam tana zaune a kan gado rik'e da waya, tarasa abinda ke mata dad'i, d'azu Zaid yazo yace mata wai za'a sanya musu rana da Ammar, itakam ta rasa mema zatayi, motsin bud'e kofa ne yasa ta kalli kofar, Dad ne ya shigo tare da sallama, ta amsa tana neman kakaro murmushi,  ya karaso kusa da ita ya zauna tare da kamo hannunta yace " me kikeyi anan bayan kowa na falo?"
Tai kasa dakai batare da tace komai ba, yai murmushi yace " Kinji labari?"
  Da sauri ta d'ago ta kalleshi tace " name fa Dad?" A ranta kuwa addu'a take Allah yasa ba zancen Zaid yake nufi ba.
Dad ya sake murmushi tare da shafa mata kai yace " burina ya kusa cika Seemah, babban burina bai wuce inga kin auri d'aya daga cikin 'ya'yana ba, na sani kuma kowa ya sani Ammar ne yafi dacewa dake, shiyasa nakesan ki daure kicire san Jalal a ranki."

  Seemah jitai kafarta na rawa da sauri ta hawuda ita kan gado kar Dad ya gane, ta kakaro murmushin yake sannan tace " Dad nasani ya Ammar zai kula dani sosai. "

Dad yasa dariyar farin ciki yace " ko? Ashe kema kinsani, shiyasa muka yanke za'a samuku rana sai mukoma ki karasa karatunki sai ai auren."
Tai murmushi tare da cewa hakan yayi Dad, burina bai wuce inga nasanyaka farinciki ba."
Takarasa maganar cikin rawar murya.

Dad ya jawota jikinsa yana lalashi, yace "kicire komai a ranki ki koma yanda kike da nakuma gode sosai da amincewar da kikai."

  Ta d'ago tare da girgiza kai tace " nice da godiya Dad koda ace zan bauta maka har karshen rayuwata banaji zan biya kwatan abinda kamana nida mahaifiyata."

  Dad cikin wasa yace "oh ni Seemah yaushe zaki daina maimaita abin nan?"

Tai kasa da kai tana murmushi ya mike ya fita ta bi bayanshi da kallo tare da cewa "Deen yazanyi?"

   Jalal tsaye a kofar gidan Abba yanaso ya musu gaisuwa sai dai inaaa kunyar ma shiga yake in ya tuna abinda ya faru, gani yai an dalleshi da fitila, hannu yasa yad'an kare fuskarsa, a hankali mai fitilar yazo kusa dashi ya nuna shi da yatsa tare da kwashe wa da dariya yace " I am right kaine." Yafad'a tare da nuna kansa alamar naushi.
Jalal ya kalleshi sannan yai 'yar dariya yace" ashe baka manta ba."
Zaid yace " ya za'ai in manta bayan an nemi a gurd'eni?"
Jalal yace " Kayi hakuri time d'in....."
" baka hayyacinka ne saboda kishi ko?"Zaid ya karasa mai.
  Jalal yai murmushi baice komai ba, Zaid ya rik'e hannunsa yace " muje ciki kuyi sallama da Seemah an kusa sa mata rana."

  Bawai baiyi tsammanin ranar zatazo bane, bawai kuma tsoron hakan yake bane, bawai kuma baisan hakan a faru bane a'a shi aganinsa hakan ne daidai sai dai jin kalmar ya sa ya ja burki ya tsaya, gabansa ne yashiga fad'uwa, idanunsa suka canza kala, Jalal ya daure yace " dare yayi mubari sai gobe nazo."

  Zaid ya haska agoggon hannunsa yace "karfe 8 da rabi shine dare? Tab lalai inbaka gantaba yau banaji zaka kara samun wani lokacin."

  Jalal ya kalli Zaid sannan cikin sanyin murya yace " muje."

  Yana tafe yana " *_INALILAHI WA INA ILAHIHI RAJI'UN_*" har yai sa'a gaban nasa ya daina fad'uwar.

 



© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*

��‍♀

3 comments: