����������������
�� *JÅĹÀĹÙĎĚĚÑ*��
����������������
Na *AYUSHER MUHD*
ayushermohd.blogspot.com
_Ina kara ba masoyan littafin nan hakuri na jina shiru da kukai kwana biyu, a min afuwa ina cikin taro ne.......Nagode kwarai da kulawarku da kuma kaunar da kukema littafin nan_
No. 5⃣9⃣
Abba ya kalleshi shi kanshi bai fahimci mai Jalal ke sakawa a ransa ba amma mamaki ne bayane a fuskarsa ganin Jalal na murmushi.
Daurewa yai yace " Jalal kazo ka fita gun abokanka anjima kad'an za'a kawo amarya."
Ya kalli Abba yace " yanzu Abba inza'a kawo Zainab gidan nan har sai na fita? A gidan nan take da fa, sannan ni gun wa zani kasan ba abokai garan ba."
Abba yace " Al'ada ce hakan yaza'ayi akawo Amarya kuma Ango na cikin gidan? Ai sai daga baya zakuzo siyan baki da abokanka."
"Siyan baki? Bakin wa kuma zan siya?" Yai maganar cikin mamaki.
Abba yai murmushi yace " Jalal ya akai bakasan komai na aure ba? Ai in aka kawota sai kunzo kun ba kawayenta kud'i sannan su tafi."
" Ah wannan ba siyan baki bane, neman kud'i dai kawai."
Abba yace " Haka dai akeyi d'an haka kazo ka fita sannan ga wannan." Ya mik'a mai bakar leda an d'an nad'eta, Jalal ya amsa yana kallan Abba.
Abba ya cigaba " 'Yan uwanka ne suka tara maka, sai ka ciri wani abun kaba 'yan siyan baki sannan a ciki ka siyo kaza da madara ko yogurt ko lemo, na fad'ama su Kafilu suzo su rakako anjima."
Jalal ya irga kud'i dubu 20 ne cif, ya kalli Abba yace " Yanzu Abba meyasa akasa su tara kud'i haka?"
Abba ya sake Murmushi yace " ba wanda ya sasu, dama haka akeyi, had'awa akeyi kowa ya kawo nawa yai niyyar bayarwa."
Jalal yai shiru yana kallan kud'in, Abba ya juya tare da cewa, kai wanka kasa sabon kayanka kazo ka fita.
Jalal yace to, sannan yace " Amma Abba baka tambayeni......."
Abba ya juyo ya kalleshi yace " nasani Jalal, amma daga baya mayi maganar."
Yana fad'a yai waje.
Kallo yabishi dashi sannan ya zauna a bakin gado, shifa sam baiyadda wai shine akama wani aure ba, shi da yad'auka in mutum aka mai aure wani farin ciki ne ke mamayeshi, to shi ya yake jinsa ba wani farin ciki? Sai ma wani bakim ciki na mahaifin Seemah dake nukurkusar sa? Ga zafin rabuwa da abinda zuciya da gangar jiki ke bege."
Ya zaiyi?
Haka dai ya mik'e yai wanka ya zura shaddarsa sabowa da Umma ta d'inkamai ya fita, cikin gida ya kara shiga ya musu godiya sannan ya fita.
Waya ya d'auko ya kira Sagir, shikam Sagir haushin Jalal duk ya isheshi, da kyar ya d'aga wayar, Jalal yace " Sagir d'an Allah tambaya, a tsakanin Lawyer da d'an Jarida wanne yafi d'aukan lokaci wajen gama karatunshi?"
Haushi ya kara kama Sagir yace " Au bama zancen aikinka ka k'ira kamin ba?"
Jalal ya saki Murmushi yace " Sagir d'an Allah kabani amsa."
Sagir baice komai ba ya katse layin.
Jalal ya girgiza kai fuskarsa d'auke da murmushi, jiyai am dafashi ta baya, ya juya Kafilu(d'an gidan goggo) ne da abokansa, Jalal ya kara sakin fuska yace " Kafilu?"
Kafilu yasa hannu a hab'a dayake shi mutum ne mai barkwanci, yace " Haba tun dana karyo kan lungun nan nake ganin haske d'an nima hasken na d'inga bi, abin mamaki hasken ya d'ireni anan."
Jalal ya kalleshi yace " Au nine nake haskem kenan?"
Dariya Kafilu yasa yace "Sosai ma, abinka da sabun shiga, saurayi zaiyi sabon aure."
Ya fad'a yana kallan abokansa, Dariya dukansu suka kwashe mai dashi, har Jalal d'in.
Ya cigaba " ni gashi ina shirin kara ta uku amma kai sai yanzu zakai d'aya gaskiya dai anji kunya."
Kallan mamaki Jalal yamai yace " Kafilu? Ka rufa mana asiri ina zaka kai mata uku?"
Dariya suka sakeyi Kafilu yace " ah to kaidai ba d'an boko ba sai kayi ta zama ni ai sai na ciki hud'un nan rass."
Jalal ya girgiza kai yace " Lalai abin naka babba ne, kaje kana kwance a kwarama ruwan zafi."
Suka kara sa dariya, Kafilu yace " tab, ai sai dai suyi ta fad'a akaina ni kuma inzauna akan kujera ind'inga kad'a kafa."
Jalal ya kalleshi cikin mamaki yace " Allah ya shirya, wato kai fad'an ma dad'i yake maka."
"Sosai ma."
Sun dad'e suna hira suka d'anje yawo.
Seemah kam duk motsin datai sai ta tuna, Shikenan Jalal ya zama ba nata ba, yana can yau za'a kaimai matarsa, wani sabon kishi da takaici ne ke nukurkusarta, kwankwasa kofar dataji ne yasa ta mik'e tare da bud'e kofar, Ammar ne ya kalleta fuskarsa d'auke da murmushi ya bud'e mata hannayensa yace " Suprise! !!! "
Ta kalleshi tare da matsamai, Ammar ya shiga yana cewa " Kodai in koma? Kamar wannan kanwar batai farin cikin ganina ba."
Seemah ta shiga ciki batare data amsa ba, a kan kujera ya zauna tare da nuna mata kusa dashi, ta karaso ta zauna, ya kalleta ya d'an langwab'ar dakai yace " ko in tafi?"
Kai ta girgiza mai, alamar a'a yace " in bakyasan na tafi to lalai ki saki fuskarki."
Ya fad'a tareda had'e fuska, Seemah ta kalleshi cikin shagwab'a tace " Fuskata fa a sake take."
Ya juyo yai murmushi sannan ya mik'e ya dawo gabanta ya tsugunna, ta kalleshi tare da yin murmushi ganin yanda yake kallanta, tace " Yaya kallan fa?"
Ya kara kafeta da ido yana mata wani kallo yace " Seemah bansan ganinki cikin damuwa kema kinsan haka."
Ta d'auke idanunta da sauri tare da juyar dakau tace " Yaya?"
Ya mik'e tare da juyawa ya fara tafiya, jikin gado yaje ya tsaya, ba tare da ya juyo ba yace " na sani Seemah, soyayyar da kikemin ta 'yan uwantaka ce bawai ta saurayi da budurwa ba, a da na d'auka nima wannan soyayyar nake miki, amma bayan sanin ba jinin mu d'aya ba na gane cewa soyayyar danake miki kala biyu ce."
Ya juyo ya kalleta idanunsa sunyi jaa, yace " in har bazaki iya aurena ba wani abu, ni zan iya hakura koda kuwa sanki zai kasheni zan jure, abinda bazan iya jurewa ba shine inganki cikin bakin ciki."
Seemah hawaye suka gangaro mata, ta kalleshi cikin tausayi, sai dai ta kasa magana juyawa yai yafara takawa, da niyyar barin d'akin, mik'ewa Seemah tai da sauri ta zo ta rungumeshi ta baya (abinka da rainon da ba na kasar nan ba, bare sun taso tare basu d'auki hakan komai ba.)
Cak Ammar ya tsaya, tare da had'iyar wani abu, idanunsa na neman kawo ruwa, Seemah cikin kuka tace " Ba haka bane Yaya, ba haka bane."
Hannunta ya zare tare da juyowa saitinta, hannu yasa ya share mata ta tsugunna a kasanshi tasa kuka tace " Yaya ya ya zanyi? Ni kaina haushin kaina nakeji, banasan abinda nakeyi, tayama za'ayi zuciyata ta kasa tsanar wanda mahaifinsa shine sanadiyyar wulakantar mahaifiyata, kila ma shine sanadin rasa rayuwarta?"
Ta kalli Ammar idanunta na zubar da kwalla abin tausayi tace " Yaya inaji bana cikin hankali na, a da nad'auka ko ganinsa bazan nemi sakeyi ba, amma da kaina na fita gunsa, kuma na kasa ko tambayarsa bare inyi masa masifa, yaya anya mahaifiyata zata yafemin?"
Ammar ya share kwallarsa shima, ya tsugunna kusa da ita tare da rike hannayenta, ta cigaba da kuka sannan tace " Yaya ka taimakeni kasa na manta da Deen d'an Allah, in daina mafarkinsa da tunaninsa, banasan na........"
Hannu yasa ya rufe mata baki, ta kalleshi hawaye na cigaba da zubowa, har kan hannunsa, baice mata komai ba, sun dad'e a haka, Kafin a hankali Ammar ya zare hannunsa daga kan bakinta ya kalleta yace " Ya isa kukan haka, banasan ki zubarda hawaye koda kuwa akainane bama akan wani ba, hakan nasa zuciyata shiga wani hali."
Kallansa tai ta kasa magana, yace " bari naje masallaci."
Ta d'aga kai a hankali, ya mik'e ya fita, ta bishi da kallo, jikinta ya kara sanyi, taya zata ki jinin Dad, a yanda takejinta koda Dad wani can talakan gaske ya d'auko yace Seemah wannam nakeso ki aura, bataji zata bijire masa bare Ya Ammar? Mutumin datasan bazai tab'a barinta ta wulakanta ba bare yasata kuka, jinin Dad, sannan a 'ya'yan Dad d'in ma wanda tafi shakuwa dashi tafi kuma sansa? To amma meyasa take neman b'ata masa rai saboda Deen? Meyasa?
Wani sabon kuka ne ya kara zuwa mata........
An kai Amarya, mutane sun cika a gidan Jalal su kafilu a gaba suka sashi aka siyo kaza da lemon kwalli da hollandiya mai sanyi, Kafilu sai tsokanarsa yakeyi, sunje shiga gida Kafilu ya kalleshi yace " Jalal sai naga kamar farincikinka baikai zuciya ba."
Kallansa Jalal yai baice komai ba, Kafilu yai dariya yace " ko duk ka kosa ne kayi......."
Harara Jalal ya dokamai yace " kai wannan ya dama mai iyalai."
Kafilu ya kalleshi yace " Kai!!!!! Ai abin ne....."
Jalal ya kara makamai wata hararar yace " bamasan jin sirrinka uban 'yan surutu, Allah ya shiryeka."
Nima nace Ameen, d'an kuwa fad'ar sirrin aure babbar illa ce......Allah yasa mu kiyaye Ameen.
© *THE SEEMAH'S LOVE TEAM*
⛹��♀
Fair...
ReplyDeleteSo interested
ReplyDelete