Friday, 26 May 2017

ZUCIYA.....kowa da irin tasa 33

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *HWA*
*na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*Wattpad As_AyusherMohd*

{ *33*}

   A can Little ta ganta falo zaune ta kifa kanta,  ajiyar zuciya Little tai tace " Feena meye hakan? Mun taho tare shine zaki taho nan ki barni. "

  Nafi ta d'ago ta kalleta sannan tace " Sry My Little wlh jinai kaina na d'an sarawa. "

  Cikin damuwa Little tace " ayya! Sannu,  ko zaki hakura da zuwa? "
  Kai Nafi ta girgiza tace " Muje nima ina san zuwa ai, kuma kan yama daina. "

  Nan suka mike Nafi ta kara gyara fuskarta sannan suka fito,  sunzo shiga mota shikuma ya fito daga b'angaren Mumy,  yana kallansu har suka shiga ya d'an yi wani smiling yace " lalai yara sun girma." abinda ya fada kawai kenan yai gaba.

  Su kuma suka shiga motar Little 'yar karama wanda Kawu ya sai mata wai murnar gama secondary.

¤¤¤¤¤¤¤

  Umma na zaune kusa da Asim acan kuryar d'aki, Asim ya nisa yace " Umma tanashan maganin nan kuwa?"

  Umma tai murmushi tace " Ai tunda muka bata magani tai b'arin nan na tsoratar da ita akan in har ta haihu yanzu da Ashraf to fa lalai wulakantata xaiyi dan kuwa maza basasan mace mai saurin haihuwa."

   Asim yace " to kidai tabbatar tanasha dan kuwa in har ta haihu da Ashraf to fa komai bazai yiwu ba,  bazata taba bamu hadin kai ba, sannan muma in muka halaka Ashraf bayan mun amshe company d'insa da sauran dukiyarsa in har abinda aka haifa ya girma ya gano nan ma kinga akwai matsala. "

  Umma ta jinjina kai tace "karka damu da wannan amma nikam har yanzu fa hankalina bai kwanta da wannan wasiyar da ya bata ba. "

  Asim ya kurawa kasa ido, sannan can yace " karya yakeyi ai ni da farko na yarda sai da naga wani murmushi da Kawu yai bayan ta kawomai haka kawai jikina yaban ba haka bane, sai daga baya nai tunani ta ina mutumin da zai mutu zai bar wasiyar kud'i kawai???? "

   Umma ta jinjina kai tace " nima yanda naga babanka nayi ne yasa nasan ba haka bane sannan nasan halin Yaya sarai bazai bada kudi kawai haka ba. "

  Nan suka cigaba da kule kulensu....Nikam nace Allah ya kyauta dama ita zuciya kowa da irin tasa.

  ¤¤¤¤¤¤¤¤

   Su Little kam an d'auko Amarya suka wuce inda za'ai event d'in,  suna tafe ana hira saboda duk kawayene,  Nafi ma yanzu bata kunyar shiga hira,  har suka isa.

   Guri yayi kyau bayan Amarya tazo ne aka fara gudanar da shagalin biki, Nafi tana zaune daga gefe ganin yanda 'yan mata keta rawa su Little ma an zake sosai,  Nafi dai tana gefe rike da wayar Little tana dadanawa,  tunanin kiran Ferry ne yazo mata,  nan ta mike ta d'an matsa kadan daga inda ake shagalin.

  Daga can ferry ta d'auka nan suka shiga hira,  tana nan a tsaye suna waya sai dai suk sanda ta kalli gun idanunsa na kanta,  hakan yasa ta fara tsarguwa,  daga gani shima gun bikin yazo yana zaune akan motarsa.

  Ganin kallan ya fara isarta yasa ta matsa daga gun,  bayan sun gama waya Nafi ta juya da shirin komawa.

   Ganin mutum tai kawai a bayanta tana juyawa suka hada ido,  Nafi ta zaro ido cikin mamaki tace " Malam lafiya? "

  Wani lalausan Murmushi ya sakar mata sannan yace " Aminci Allah su tabbata a gareki. "
  Ta kalleshi cikin mamaki sannan ta d'an motsa baki a hankali tace "tare da naka, amma..... "

" Shiiii dan Allah karki koreni kar kuma ki nuna bakya sona daga gani na yau d'aya."

  Nafi cikin mamaki ta kalleshi,  sai dai har kasan ranta yaso sata dariya yanda yai,  ya cigaba da cewa " Sunana Al-Amin masoyin wannan yarinyar. "

  Juyawa tai bayanta dan ganin wace yarinyar, ya sakar mata murmushi yace " ina kike dubawa bayan gatanan a tsaye. "

  Nafi ta harareshi yanzu kam ta gane da ita yake,  ya d'an rike kunnuwansa yace " Tuba nake ranki ya dade da alama na b'ata miki rai. "

  Nafi batasan sanda tai murmushi ba tace " ba wani b'ata rai sai dai kayi hakuri ni matar aurece. "

  Gani tai ya hau dariya, ya kalleta yace " matar aure?  Wow na gode da alama da wuri zamuyi aure in killeceki a d'aki."

  Nafi ta makamai harara,  da sauri ya kara rike kunne,  yace " Taya zakice min ke matar aurece? Ina mijin? "
Shiru Nafi tai a ranta ta ce " inafa yake?  Yana can gun matarsa. "

  Al-Amin yai murmushi yace " please ki amince dani,  zan kula dake yanda bakya tunani,  ni d'an Katsina ne, sannan kanwar maman yarinyar da ake aurenta ne. "

  Nafi ta kalleshi sannan tace " lalai yayi kyau."

  Hannunsa ya had'e guri d'aya yace " Dan Allah sunanki?????? "

  *FEENAH* abinda ta fada kenan,  yace "wow nice name, a ina kike? "

  Ta juya kai tace " zan koma ciki. "
Bata jira amsarsa ba ta fara tafiya,  Biyota ya fara yi sai data juyo tace " dan Allah Al-Amin ka kyaleni. "

  Kansa ya shafa yace " kai!!! Naji dadi dan sake ki kiran sunana."  ta kara harararsa sannan ta juya.

   Taji dad'i sosai dataga bai biyota ba,  haka kawai taji ta saki murmushi.

  Sai da aka gama,  wajen isha'i sannan suka fito zasu tafi,  suna fitowa ya taso ya karaso gunsu tare da musu sallama,  Little ta amsa tana mai kallan sani sai dai ta rasa a inane,  yace " Little manya,  can na ganki ai kinata rawa ana bikin Aminiya. "

    Little ta nunashi da yatsa tace " Ya Al-Amin."

  "Bingo!" ya fad'a yana murmushi,  itama murmushin tai tace " Ya Al-Amin ace kaine, nifa ince na rasaka sam ashe ka zama babba ko a hanya na ganka zanyi wahalar ganeka. "

  Ya harareta yace " Haba Little a gaban Swt Feenah kike fadar hakan? "

   Ta kalleshi sannan ta kalli Nafi data juya kanta,  tace " yaushe ka ganta?"

  Yace " gatannan sai wulakantani take ashe kawarki ce."

  Little ta kalli Naf tace " Feena d'an uwan namu kike wulakantawa? "

  Nafi ta kalli Little kamar zatai kuka,  yace " wlh ina zuwa na ajiye su Hajiya na dawo dan in kaita gida "

  Nafi ta harareshi tace "cewa nai zan bika? "
Ya kara had'e hannayensa yace " Little please."
  Little ta juya da sauri ta shige motarta taja tai gaba tana dariyar mugunta.

  Nafi ta saki baki tana kallan Little cikin mamaki,  Al-Amin ya kalleta yace " Cwt Feena da alama dai nid'in nan nine zan kaiki. "

  Ta juya kai cikin takaici tace " da wayace kazo nan ma. "
  Yace " Matata tana guri ba dole inzo ba?"

Nafi ta kalli agoggon hannunta karfe 8 ga gun duk ba mutane,  katseta yai da cewa. " Please Cwt Feenah ki taimaka,  ai indai gidansu Little ne na sani. "

  Nafi ba dan ranta yaso ba ta karasa gun motar ta shiga rai a b'ace,  tana shiga ya zuge glass tare da kunna mata AC,  itakam kanta ta maida gefe tana kallan waje.

   Sun fara tafiya shi kad'ai yake mata magana,  ganin batada niyyar kulashi yasa yai shiru.

   A daidai kofar gidan yai parking, a wannan lokacin kuma, Ashraf ya fito kenan zai fita,  kallan motar yai cikin mamaki,  har zai wuce sai yaga alamar mace ce a ciki,  badai Little bace? Abinda yazo mai kenan,  hakan yasa ya ja motar yai parking a gefe.

  Itakam Nafi tazo fita yasa lock cikin mamaki ta kalleshi ya kashe mata ido sannan yace " Cwt Feenah shikenan bako sallama?? "

  Nafi ta d'an turo baki tace" in na fita ai zan ma. "

  Kai ya girgiza alamar a'a sannan ya mika mata wayarsa yace "a'a na yafe numberki kawai nakeso. "

  Ta d'anyi murmushi tace " sry Al-Amin sai dai banida waya. "

  Kallan mamaki ya mata yace " mene? Shikenan wato dan bakyasan ki bani mumber ki shine zaki fad'i haka? "

  Kai ta girgiza alamar a'a tace "wlh ba haka bane,  banida itane. "

  Kallan mamaki ya mata, shikam Ashraf ya cika fam,  me Little take a cikin mota har yanzu? A zuciye ya fito yazo kofar da take shikuma daidai lokacin Al-Amin ya cire sim d'insa na Mtn ya bar glo ya mika mata wayar yace " ga tawa akwai sim a ciki ba wanda yasanni da sim d'in ni in na fita nasai wani..... "

Kallan mamaki takemai,  zatai magana sukaji an kwankwasa glass d'in motar,  inda take,  Al-Amin ya zuge cikin mamaki.

  Cikin tsananin mama ki Ashraf ke kallan Nafi,  ransa yakai kololuwa gun b'aci, itakam tunda ta ganshi gabanta ya shiga fad'uwa.

  Al-Amin ne ya katse mugun kallon da yake mata yace " Yaya Ina wuni? "

   Wani kallo ya bugamai batare da ya amsamai ba,  ya kalli Nafi cikin tsananin takaici yace " kin fito ko sai na karya ki? "

  Motar ta bud'e zata fita Al-Amin ya sake cewa " Cwt Feenah gashi. "

  Juyowa tai ta kalleshi haka kawai taji tanasan ansar wayar yanzu a gaban Ashraf,  hannu tasa ta amsa sannan tace " Nagode kawai tai waje. "

   Ta gabansa ta rab'a ta wuce haryanzu gabanta fad'uwa yake,  Ashraf ya bita rai a b'ace,  hannu yasa ya riko ta da karfi yace " abinda aka koya miki kenan a makarantar??? "

   Idanunta ne suka dan ciciko ta daure tace " me nayi yaya? "

  Yai wani murmushin takaici yace " me kikai?  Ke harkin kai ki zauna a motar namiji ku zuge glass? Ku kuma dade a ciki? "

  Nafi wacce hannunta ke mata rad'ad'in rikon da ya mata tace " kawoni yai daga gun biki."

  Xaiyi magana yaga hawaye sun zubo mata cikin rawar murya tace " Yaya hanuna. "

  Kallan hannunyai sai a lokacin ya kula da yadda ya matse mata hannu sosai ga agogo agun,  nan ya sake mata hannu,  agoggon kuwa har ya ji mata ciwo, mamakin kansa ya shiga yi.
  Ya juya da sauri ya shiga motarsa ba tare da ya kalli inda take ba, Nafi kam agoggon ta cire tabi ciwon da kallo lalai ta yarda Ashraf baya ko digon santa wasu zafafan hawayene suka zubo mata, ta juya a hankali tai ciki.

  Tana shiga ta cilar da wayar akan gado tana kallan Little tana mata dariya,  ta wuce toilet.

    A gaban madubi ta tsaya bayan tayi alwala ta kalli kanta a cikin ranta tace "dama kema kinyi laifi tun farko,  kinfi kowa sanin Ashraf yafi karfinki meya kaiki???? "

  Hawayenta ta share sannan ta fita  jiki a sanyaye.....

Bayan tayi sallah little ta dameta da zancen Al-Amin itakam shiru kawai tai, dama bata kunna wayar ba balle ma ya kirata.

   Ganin taki kulata yasa itama Little d'in tai shiru,  itakam Nafi kwanciya tai kamar mai bacci sai dai ranta fal yake da tunani kala kala.

    Shikam Ashraf yana shiga mota yai wani huccin takaici,  meye nashi na zakewa haka?  Wata zuciyar tace to yarinyace karama ko karatu bata gamaba ko kunya ace tana xama da saurayi a mota? Ai amanace ita agunsa shi ya d'aukota daga wani garin dolene ya kulada ita kafin mazan zamani su hure mata kunne.

  Ya d'an bigi sityari kadan yace " me yasa nai haka agaban wannan yaron?  Salan ya rainani? Ya kara jan tsakin takaici, haka ya gangara gun abokinsa nagun aiki dazai amshi takardu ransa duk a jagule.......

    Washe gari Nafi bayan ta tashi daga bacci ta fita zuwa kitchen nan suka gaisa cikin farinciki da kewar juna,  ta zake ta shiga tayasu aiyukan girki.

  Sun gama ta fito kenan sukai kicibis da Umma,  had'e rai Umma tai tace "ke wacece a kuma wani dalili kiika shigo mana kitchen? "
Nafi tad'an rusuna kad'an ta gaisheta sannan ta mike tsaye tace "Umma baki ganeni ba? "

  Umma ta kar had'e rai, Nafi tace " nice fa Nafi. "

  Umma ta kara kallanta ba shakka itace,  ta d'an harareta tace " uban me kike anan ba dama kina makaranta ba?? "

  Nafi tace " ai dama ana hutu nice dai kawai ban dawo ba. "

  Umma ta kara had'e rai tace " to yanzu gulma ce ta dawo dake ko me? "

  Nafi kam murmushi ta saki dan itakam bataji haushin kalaman Umma ba ta kalleta tace " Umma na shiga ciki. "

   Ran umma ya b'aci ganin yanda yanda yarinyar ma ba a kula ba,  gashi tasan yarinya da take 'yar riga yanzu ta girma? Gashi dai ba wanka tai ba amma gata tsaf,  ba kamar wannan kucakar tada ba.


*Anan ne zan dakatar da wannan littafin nawa mai taken Zuciya kowa da irin tasa,  ina fatan zaku jirani zuwa bayan sallah in Allah ya kaimu.*

  *Yanda zamu fara azumi lafiya Allah ubangiji yasa ku gama lafiya,  ya kuma bamu ikon yin ibada batare da gajiyawaba, ya karemu daga duk wani abu dazai d'aukemana hankali agun ibadaunmu,  ya yafemana kura kuranmu,  ya kuma sa mu gama da duniya lafiya.*

   Ameen suma Ameen.....

  *Nagode kwarai da irin san da kukema littafin nan,  banida abinda zancemuku face godiya,  Allah yabar zumunci, ya kara mana kaunar junan mu.*

    *Duk wani masoyin wannan Littafin ina mika sakon gaisuwata gare ta/shi, na gode kwarai da kauna.*

   *Sai Allah ya Kaimu Bayan Sallah in Muna da Rai da Kuma Lafiya.*

❤💛💛💙💜💜🖤💟💟

Wednesday, 24 May 2017

ZUCIYA....kowa da irin tasa 31

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*Wattpad As_AyusherMohd*

  *Gaisuwa gareku 'yan sauyi, 'yar gaya, sankach, nagudu, sharubutu, Aisha Idris, Sub, Zee Sa'id and many more, tunda yanzu kun daina neman Aisha sai Zuciya to ga sakon Zuciya nan tana muku fatan alkairi....lol*

{ *31*}

   Little jiki a sanyaye ta fito daga d'akin Mumy tai b'agarensu.

   A zaune taga Nafi kan sallaya, Little ta karasa gunta tare da sama a kusa da ita, Nafi ta kalleta sannan ta kakaro murmushi tace " Little nayi dana sanin zuwa bikin nan."

  Dafata Little tai tace " Laifinane dana d'aukoki duk da banga alamun kinasan zuwa ba."

  Kai Nafi ta girgiza alamar a'a kawai zatai magana taji kamar intai magana kuka ne zai kufce mata.
Little ta d'au waya ta kira Ashraf,  sai da ta kusa katsewa  sannan ya d'aga tace " Yaya."

  Daga can Ashraf dake zaune kusa da Habib yace " uhm ya akai? "

   Kasancewar a kusa suke yasa Nafi tana iya jiyo maganar Ashraf,  Little tace " dama fadama zanyi gobe Nafi zata koma inji Mumy."

   D'agowa Nafi tai ta kalli Little,  jitai Ashraf yace " to Allah ya kiyaye."

  Little taso ya hana Nafi tafiya jin ya fad'i haka yasa jikinta yai d'an sanyi tace " Yaya wa zai maidata?"

  A zuciye yace " da wani karambanin ne ma yasa ku d'auko yarinya tana makaranta? Sai kuje ku sami wanda ya saku ku tambayeshi."

  Little zatai magana taji ya katse, jiki a sanyaye ta kalli Nafi wacce ke wasa da hannunta a zahirin gaskiya kalaman Ashraf sun mata zafi sai dai tasan koma meye ai laifin ta ne.

Ta kalli Little tace taimakamin dan Allah in kwanta."

   Little ta kalli kafarta tace " Nafi ko muje Chemist? "

  Kai Nafi ta girgiza mata alamar a'a tace "bafa wani serious bane. " a zahiri kuwa tanajin zafin gun sai dai bataso a cire handkerchief d'in Ashraf daga kafarta.

  Little ta mike sannan ta shiga taimaka mata ta kwanta, idanu ta rufe kamar mai bacci, hakan yasa Little ta fito daga d'akin.

   Tana fita Nafi ta fara zubar da hawayen dake cinta, Ashraf ta tuno sanda ya d'auketa, idanu ta runtse kalaman Ferry ta tuna data cemata san Ashraf take, Nafi ta share hawayenta sannan a fili tace " Ina na isa? In kuwa har haka ne lalai ina cikin gararin rayuwa."

  Kalamansa na mota ta tuna dayace mata zai saketa in ta samu wanda takeso.

  Ta dad'e tana hawaye kafin bacci ya d'auketa.

  Washegari da sassafe kuwa Drivern Mumy ya mai da ta makaranta, ko Ashraf bata sa a idanta ba.

   Nafi ta dage sosai da ta koma makaranta, ba wai a kan karatu kad'ai ba sai dai kullum suna tare da Ferry tana kokarin canza halayenta.

   A wannan zuwa gidan datai lalai ta fahimci abu biyu, na farko Ashraf wasa kawai yake da ita da jawo mata tsana agun mutane bayan ba santa yake ba, na biyu kuwa lalai in har tanasan Ashraf ya fara santa sai ta zama mace daidai shi.

   A can kuwa an gama biki lafiya ankai Amarya d'akinta, sannan kowa ya watse.

   Anyi hutu amma Nafi ta kira Habib akan zata zauna a gidan Principal ya tambayar mata ita, saboda a lokacin hutun ta samu isashen lokaci na karatu, wannan jarabawar ita tazo ta karshe a aji batajin kuma za ta iya nunama Ashraf wannan dakikantar datai.

Habib ya tambaya, ba tare da wani dogon Nazari ba ta amince, bayan kowa ya tafi gida itama ta koma quaters.

  Little taji ba dadi sai dai bayan Nafi ta mata bayani ta waya yasa ta gamsu.
  Nafi ta dage sosai......

   Shekararta d'aya kenan a makaranta,  duk hutu ba ta wani zuwa gida, sai dai duk cikin hutu Little na zuwa ganinta da sakon Provision daga Mumy da kud'in kashewa.

   A iya wannan Shekara d'aya ba shakka Nafi ta canza sosai da sosai, ita da Ferry kam sun zama Aminai sosai, sai dai in a b'angaren karatu ne kuma da Jibiya sukeyi.

  Yanzu suna S1 Nafi ta canza sosai, bata tunani ko sha'awar zuwa gida duk da kuwa yanda zuciyarta take tsananin rashin Ashraf kamar ranta.

  Yanzu sun shiga Ss 2 a a wannan lokacin ne kuma Nafi ta shirya dan zuwa gida, Little tace "wannan karan kam gaskiya sai Nafi tazo gida, dan akwai bikin kawar Little ko ince Aminiyarta da za'ai.

  A wannan lokacin shekarun Nafi 18, duk da ba kiba gareta ba sai dai kirjinta ya cika da dukiyar fulani, Nafi ta goge sosai, kamar ba makarantar kwana take ba, komai nata tsaf dan in Little zata kawo mata kaya har da mayuka masu kyau take cewa ta had'o mata.

   Nafi tana tsaye kusa da Ferry ga Jibiya a gefensu, Nafi ta kalli Ferry tace " Na nawa kikai?"

  Ferry tai d'an tsaki tace " Ai   Yaya Yusuf ya rainan hankali wai ta 7 dan tsabar rashin mutunci."

  Nafi tasa dariya ita da Jibiya, Ferry ta had'e rai tace " kubarni da abinda ke damuna."

  Jibiya ta sake dariya tace " lalai zakisha Fada'a gun Abba dan ni na 2 nai."

  Idanu Ferry da Nafi suka zaro, Nafi ta kalleta sannan ta had'a hannayenta ta tafa mata tace " wow! Jibiya kina kasheni."

  Ferry ta harareta tace " Zama ta raya ki, ke Feena na nawa kika ci?"

  Nafi ta juya kai tace " Secret."

  Ferry tai dariya tace " badai irin na last term ba na 12 ba?"

  Nafi ta d'an rangwad'a kai cikin tsokana tace " na 8 nai."

  Ferry cikin d'aga murya tace " WHAT?"

  Nafi tai murmushi tare da ware takardar, murna suka shiga yi sosai, can Ferry tace " Kai naji dadi kin daina cin double number, amma da alama sai na dage kar next term ki dawo gabana."

  Suka sakeyin dariya.
Ferry ta kalleta tace " Feena zakizo d'in ko?"
  Nafi ta d'an juya ido tace " zanzo insha Allah amma banasan zuwa yayanki nanan."

  Ferry ta harareta tace " Gaskiya Feena bazan juri wulakantamin yaya da kike ba, tunda yazo visiting ya nuna yana sanki amma kike wani disgashi, in bakiyi wasa ba har gidanku zan kawoshi."

  Nafi ta zare ido tace " wa? Rufan asiri."

  Jibiya tace " kema kinsan bazata yarda wani saurayin ya bita gida ba saboda sanda takema yayan nan nata."

  Tsaki Ferry tai tace " wlh Feena in har kika bari ya gane kin mutu akansa haka lalai sunanki sorry."

  Nafi ta tsuke baki tace " Ke nima yanzu ba daina sanshi yaushe rabon ma da inganshi, kila ma ko a hanya naganshi bazan ganeshi ba."

   Ferry ta d'aka mata duka tace " ni zaki maida gara? Kullum fa sai kinyi labarin yayan nan naki."

  Nafi zatai magana ta hango kamar Little ta fito daga wata zukekiyar mota, tana sanye da sun glass tayi kyau sosai da sosai, Nafi tace " anzo d'aukana."

  Nan suka mik'e suka taimaka mata da kayanta, Ferry tundaga nesa tace " Kai Feena gaskiya Little tana kasheni da gayu, ki bari nika inje gida dattin makarantar nan ya fita daga jikina lalai zan tsorata maza."

  Nafi tace " Nima ki bari sai nazo gida kin ganni kiga yanda zan kasheki da nawa gayun."

  Dariya sukai harda tafawa.

  Sun karasa gun, Little ta karaso cikin murna, ta rungume Nafi.

  Sunsa kaya a motar sannan Nafi ta leka dan ganin wanda ya kawo Little.

    Habib ya sakar mata murmushi yace " Tantancewa akeyi ne?"

  Murmushi tamai itama tace " Ai ba sai na tantanceba dama can jikina yaban kai ka kawota."

  Nafi kenan ba shakka kim canza wato yanzu bakya kunyar maidamin kalamai na."

  Ta d'aga kanta batare da ta amsa mai ba, sannan sukai sallama dasu Ferry ta amshi number Ferry da jibiya tasa a wayar Little.

   Nan suka shiga mota, Habib jefi jefi yana kallanta ta glass d'in mota, ba shakka yarinyar nan ta girma, ganin haka yasa Nafi ta matsa daga setinshi ta koma ta can b'an garen.

  Little ce tace " Nafi yau ji kad'ai nasan farin cikin danakeyi, nayi missing d'inki sosai."

  Nafi tai murmushi sannan tace " nimafa kawai daurewa nakeyi jinake kamar na biyoki inkika zo ganina."

  Little ta harareta tace " ba wani nan kedai kawai kinzama 'yar college tafi gida dadi."

  Dariya suka d'anyi Nafi ta juya tan kallan window.

Little ta juyo ta kalleta tace " Nafi au Feena baki tambayi ina yaya ba, ko visiting nazo bakya tambayarsa."

  Habib ne yai katsal yace " ita meya dameta dashi bayan yayi aure yamanta da ita."

  Har cikin ranta Nafi taji haushin maganar Habib amma sai ta daure tace " Ya Habib kenan, dama can ba wani shiri muke dashi ba balle ya nemini."

  Little ta kalleta tace " Nafi yanzu kin daina shigar ma yaya ne?"

  Ta tab'e baki tace " ni a wa? Dama can bawai shigar mai nake ba kece baki fahimceni ba, ai Yaya Neesa itace zata shigar mai bawai ni ba."

  Habib ya saki dariya yace " Gaskiya ne Feena gwara ki fara bayyana musu komai."

  Nafi ta kwantar da kanta akan window tare da lumshe ido, tace " Little bacci."

  Little ta d'an had'e rai tace " shikenan nayi shiru."

  Habib ya kalli Little yace " Ai cewa tai bacci bawai kiyi shiru ba."
  "Hmm ai tun da dadewa na gane Nafi au Feena in batasan magana sai tace wai bacci."

  Habib ya juyo ya kalli Nafi sannan yace "yarinyar nan ta canza dayawa."

    kai little ta jinjina tace " ai naji dadin makarantar nan."

Haka sukai ta maganganunsu itakam tana kwance tana jinsu a cikin zuciyarta take magana " Yaya ba sai ka basar da ni ba, nafi kowa sanin rashin matsayi danake dashi agunka, kila ma inya ganni bazai ganeni ba, ba komai Allah ya kawomin wani mai sona nima inyi kokarin ganin na yakece wannan soyayyar da take one_side."

    Nace Uhmmmm zaki iya????.

   *THE INNOCENT TEAM*

ZUCIYA.....kowa da irin tasa 32

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

©
*na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*Wattpad As_AyusherMohd*

{ *32*}

    Sun isa gida Habib ya gangara yai parking,  sannan suka fito,  Nafi ta rataya jakar bayanta uta kuma Little ta ja wo trolly d'in ta.
  Habib ne ya matso kusa da ita yace " Gimbiya Feena kawo in tayaki mana. "

  Ta kalleshi sannan ta kalli kanta tace " da me fa? "
  Nuna mata jakar bayanta yai,  tai murmushi sannan tace " ni ai ba kaya na d'auka ba Little ce mai kaya, da alama baka kula ba. " tana fad'a tai gaba.

  Habib ya bita da kallo,  gaskiya yarinyar nan tayi, shi dama tun tana yar kauyenta burgeshi takeyi.

   Little ce ta karaso tace " yaya mun gode."
  Ya rufe ido tare da yin mika yace " Princess na gaji. "

  Ta kalleshi cikin kulawa sannan tace " yaya kaje b'angaren su Asim ka kwanta. "
Kai ya girgiza mata yace " a'a gida zan wuce,  ai tunda Ashraf yai aure na daina kwana a nan gidan. "

  Kanta ta sunkuyar kasa alamar rashin jin dad'i ya matso tare da sa yatsar sa ya d'ago kanta yace " sai munyi waya."

  Kai ta d'agamai,  ya mika mata key yace " Ungo kiba Ashraf zan d'auki motata nai gaba nima."

  Ta d'agamai kai,  tana kallo ya koma ya shiga motarsa yai gaba.

  Nafi kam tana shiga d'akinsu tai wani ajiyar zuciya tace " Kai nayi Missing d'akin nan. "

  Kaya ta shiga cirewa ta d'aura karamin towel sannan ta fara ninke kayan makaranta.
Little ce ta shigo,  ta kalleta cikin shagwab'a tace " kina gani Feena har Ya Habib ya tafi? "

   Nafi ta karasa ninkewa sannan tasa agun kayan datti ta kalleta tace " Little wani irin so kikema Ya Habib? "

  Little tace " so mai yawa wanda yanzu ya zama jinin jikina."

  Nafi ta tab'e karamin bakinta tace " Shifa? "
Little ta fad'a kan gado,  ta d'an mirgina tace " Shifa haryanzu a kanwa ya d'auken."

   Nafi ta girgiza kai a ranta tace " Little nima matsalar dake damuna kenan,  gwara kema banaji kinajin rad'ad'in da nakeji in na tuna Ashraf fa mijina ne  sai dai yamin nisa. "

  Toilet kawai ta shige batare databa Little amsa ba tai wanka.
Ta dad'e tana gurza jikinta a cewarta dattin makaranta ya fita.

  Sannan ta fito,  bataga Little a d'akin ba hakan yasa ta zauna a gaban madubi ta fara goge fuskarta da cleanser.

   Hoda kawai tasa batai wani kwalliya ba, sai dai tayi kyau sosai,  ta mike kenan sai ga Little ta shigo ta tiren Abinci,  Nafi ta kalleta tace " Little ina kayana? "

  Little ta bud'e mata inda ta jera mata nata kayan,  Nafi tai murmushi ta sani sarai daba dan Little ba lalai da zaman gidan nan ya gagareta,  nan ta zab'o wata atamfa riga da siket, mamaki tayi dataga tana sa kayan da kyar,  Little tai dariya tace " ai dole kigafa dad'ewar da kikai bakizo ba,  ga yanzu kin kara girma bawai kiba ba ina nufin kin girma ta sama da kasa. "

  Nafi ta harareta tace " lokacin girman ne yazo,  da alama Little sai kin ban aran kayanki inyaso sai mukai a bud'amin nawa anjima. "

  Little tace " ki d'auka mana,  sannan kinsan fa yau da yamma zamu kamun Yusra sai ki gwada kayan ko da yake cewa nai a kiki daidai ni kawai dai karya kai nawa fad'i ne saboda nad'an fiki kiba. "

  Nafi ta saka wata doguwar rigar material sannan ta zauna suka zuba abinci suka faraci.

  Nafi ta kalleta tace " Little ya gunsu Amarya?"

  Little ta tab'e baki tace " hmm ke dai bari Nafi bayan kin tafi biki an gamashi lafiya sai dai a ranar da aka kaita sukai fad'a kaca kaca. "

  Cikin mamaki Nafi tace " fad'a kuma? "

  Little taja wani tsaki tace " Ita wai a dole a daren takesan ya bata wasiyyar mahaifinsa shikuma yace ba wanda ya isa ya sashi ya bada abinda baiyi niyya ba. "

  Nafi ta tab'e baki tace " ya suka kare to? "
"Hmm kedai bari Dady ne yaje da kansa ya sasanta yace Yaya yai hakuri gobe ya bata tunda dai hakkinta ne,  ita kuma karta kuskura ta sake tambayarsa. "

  Nafi ta d'an juya kai tace " Na d'auka tanasan shi dayawa, meye nata na damuwa da abinda baiyi niyyar bata ba?  Indai har tana gudun b'acin ransa? "

   Little tace " Zigata akai ya Asim da Umma."
Nafi ta d'anyi karamin tsaki tace " san da takemai baiyi nisa dayawa ba kenan indai har za'a zigata akan dukiyarsa."

  Little tai ajiyan zuciya,  Nafi tace " yanzu fa?  An bata ai nasan hankali ya kwanta. "

  Little tace "Hmm Yaya wai cewa yai wasiyyar dama mahaifinsa ne yace aba matar sa ta farko million d'aya ko ince wai ya ajiye kud'in a banki, to Yaya yabata kud'in sai dai Umma tace itakam gaskiya bata yarda wai kud'i kawai akace ba."

  Nafi ta had'e rai tace " shi kuma yayan me yace? "
"Uhm bai kulasu ba kinsan shi ai. "
Nafi ta kara tab'e baki tace " Allah ya sauwake. "

  Little ta amsa da Amin sannan ta d'aura da cewa " kigama muje ki gaida Mumy sannan kije kiga b'angaren Amarya. "

  "wa? Bada ni ba, inje in musu me? " sukasa dariya a tare.

¤¤¤¤¤¤¤¤

   A b'anagren Ashraf kuwa ya nemi aiki yanda kowa yake nema ya kuma samu ba babban aiki bane sai dai yanajin dad'in yanda yake fahimtar matsalolin ma'aikatansa tundaga kasa,  yana kuma fahimtar abinda ya cancanta da zai musu bayan ya amshi company d'in.
Sai dai su Asim da Kawu kam shar take a gunsu, Asim kam gani yake kamar saboda Aneesa ne ya hakura da mukaminsa,  sai dai shi kawu haryanzu yana tunanin da wani abu a kasa.

     Kamar kullum yau ma ya dawo gida daga gun aiki,  yana zuwa daidai saitin kofa yaji maganar mutane da karfe,  da alama ma musu sukeyi,  kai ya dafe cikin tsananin takaici sannan ya kwankwasa tare da murd'a kofar.
 
  Aneesa ce zaune cikin kawayenta su uku, sallama yai sannan suka kalli inda yake, Aneesa cikin kissa ta taso da sauri tazo ba kunyar mutane a falon ta rungumeshi tare da manna mai kiss a kunci,  Ashraf ya d'an zareta kad'an sannan yace " Bari in shiga ciki.."
  Hannunta ta sakala cikin nasa sannan suka fara tafiya,  shidai takaici ma hanashi magana yai.

  Yana shiga d'akinsa ya kwace hannunsa sannan ya kalli d'akin yanda ya tafi ya barshi haka dai ya dawo ya sameshi, ya kalleta cikin takaici yace " Anie mekenan?  Ba nace ki gyaramin d'aki na ba? "

   Ta shagwab'e tare da kwantowa jikinsa tace " kana fita su Laila suka zo ni ko tunawa ma banyi ba. "

  Ya kalleta cikin takaici yace "yau kwanan d'akin nan uku kenan a haka kullum da abinda kike cewa,  wasa wasa ma falo da mai aiki bata zuwa ta gyara haka nan zaki barshi da sunan kinada abinyi ko? "

   Aneesa ta kara shagwab'ewa tace " Hubby kayi hakuri zan gyara. "

  Wani mugun kallo ya mata yace " banaso fitarmin daga d'aki. "

  Zatai magana ya nuna mata kofa da yatsarsa sannan ya had'e rai sosai,  jiki a sanyaye ta fito,  sai dai dankar kawayenta su gane ta saki fuska.
Shikam tana fita ya sawa kofar makuli tare dajan wani tsaki yabi d'akin da kallo,  ko sanda yana shi kad'ai baya barin d'akinsa haka amma yanzu ji d'akisa?

Gadon ya gyrara sannan yai wanka ya kwanta a kai,  bai dade ba bacci ya d'aukeshi.
  Bacci yai sosai harya makara sallar la'asar sai karfe 5 ya tashi,  da saurinsa yai alwala ya fito masallaci.

  Sukam su Nafi ganin anyi sallar la'asar suka shiga yib kwalliya dan tafiya gidan biki,  saboda kawar Little ce sosai,  sunaso suje da wuri dan a gamama Amarya kwalliya su tafi da ita gun biki.

   Anko suka saka,  light purple d'in wani yadi ne,  shiba lace bane sannan ba material bane,  riga sukai da siket sannan sai head shima kalar kayan, sunyi kyau sosai da sosai, balle abin kan nasu Little ce ta d'aurama Nafi sannan ta d'aurana kanta,  Nafi tace " amma ankon yayi kyau. "

  Little tai murmushi tace " kawayenta ne kawai zasu sa wannan ragowar atamfa ce. "
Nafi ta jinjina kai sannan tace " Farin mayafi zamusa? "

  Little ta girgiza kai tace " a haka zamu. "

  Nafi ta kalli kanta sannan ta kalli Little tace " taya zamu fita a haka? "
Little tace " haka ake yi ai in ma mun d'au mayafin sai dai mu rike a hannu. "

  Nafi ta jin jina kai sannan ta zaro wani mayafinta karami golden color tace "ni dai da wannan zani. "

  Little tace " to. "
Sun fito abin sha'awa dan hatta takalminsu iri d'aya ne,  sai dai ba kyan kwalliya ba duk wanda ya kalli Nafi sai ta birgeshi,  kamar yanda nace Nafi ba fara bace can sai dai tana da kyau gashi batada jiki.

  Sun fito suka wuce gun Mumy dan amsar kud'in liki inji Little.

   A lokacin shi kuma Ashraf bayan ya idar da sallah yaga kiran Mumy hakan yasa ya karasa gunta,  yana zaune a kasa ta kawomai tiren abinci ya bud'e cikin mamaki ganin ba anan yake cin abinci ba.

  Ganin d'an wake yasa ya gane dalilin kiran,  zubawa yai yafara ci kenan,  Little tai sallama,  amsawa yai saidai bai d'ago ba,  lokacin Mumy ta tashi  daga falon,  wata sallama ya sakeji bayan ta little sai dai wannan muryar cikin sanyi take.

   Ya amsa sai dai yanasan juyawa kasancewar hali irin nasa yasa ya d'auke kai sai dai bai cigaba da cin abincin ba.

  Little ta karaso cikin murna tace " Yaya kaine anan? "

  Nafi ta kalleshi ta baya gabanta yai wani fad'uwa yaushe rabon data ganshi,  Ashraf ya kalli Little yace " ke wato kin girma ko? Sam bakya ma zuwa ganina sai dai inmun had'u a wani gun. "

  Ta rike hab'a tace ina na isa yaya?  Kana gani Yaya Neesa sam batasan muje mata wai muna takura muku nikuwa ina zaka ganni? "

  Baiyi magana ba, tace"Mumy fa? "
Ya ce tana ciki,  da sauri Little tai ciki.

  Nafi ta karaso jiki a sanyaye ta tsuguna daga ta bayansa tace " Yaya ina wuni? "

  Juyowa yai dan ganin mai magana,  kallan mamaki yake mata lalai yasan fuskarnan sai dai wacce ya sani inaa....  She can't be.
   Nafi ta mike ganin yaki amsawa sai wani kallo da yake mata,  tai hanyar waje,  dasauri yace  " Ke! "
  Ta tsaya sai dai bata juya ba, ya mike tsaye sannan yace " ke! "

  Nafi dai tana tsaye bata juyo ba,  a hankali ya tako zuwa inda take cikin fad'a yace " ba dake nake ba? "

Nafi ta juyo fuska  a had'e duk da tana shakkarsa amma ta daure tace " ganinai ba sunana kenan ba."

  "mene? "
Nafi tad'an burtso baki,  kallan mamaki ya mata yace " Ba Nafisa bace? "
Ta kara had'e rai ta kalleshi tace " au kama mantani? Ka d'aukoni daga garin mu amma kama manta da sunana? "

  Ta juya cikin takaici zata wuce,  da karfi ya fizgo hannunta ya jawota, kallan tsoro tamai,  tace " Yaya mai kake yi? "

  Kallanta ya karayi yace lalai itace ya fad'a a ransa,  a fili yace " ancemin kun kusa hutu ashe har kunyi. "
  Ta d'ago ta kalleshi sai dai batai magana ba,  yace " wato yanzu makaranta ta maidake mara kunya ko? "

  Tace " menai kuma? "yanda tai maganar yasa yace "Lalai yarinyar nan. "

  Kokarin kwace jikinta tai tace " ni ba yarinya bace. "
  Ya saketa tare da cewa " ke ya hanaki dawowa har kusan 2yrs. "

  Ta juya kanta gefe tace " nemana akeyi?"

  Ya koma ya zauna yace " ina zaku haka? "

  Biki zamuje.
Ya fara cin abincinsa, ya juyo da niyyar magana yaga batannan.

  Mama  ne ya kamashi yace " lalai yarinyar nan,  yaushe ta girma haka? Gaba d'aya tama canza kamar ba Nafin riga ba."

  Itakam tana fita tai d'akinsu,  a falo ta zauna ta matse hannayenta,  jikinta sai rawa yakeyi,  meyasa suka had'u?


*THE INNOCENT TEAM*

ZUCIYA....kowa da irin tasa 31

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*Wattpad As_AyusherMohd*

  *Gaisuwa gareku 'yan sauyi, 'yar gaya, sankach, nagudu, sharubutu, Aisha Idris, Sub, Zee Sa'id and many more, tunda yanzu kun daina neman Aisha sai Zuciya to ga sakon Zuciya nan tana muku fatan alkairi....lol*

{ *31*}

   Little jiki a sanyaye ta fito daga d'akin Mumy tai b'agarensu.

   A zaune taga Nafi kan sallaya, Little ta karasa gunta tare da sama a kusa da ita, Nafi ta kalleta sannan ta kakaro murmushi tace " Little nayi dana sanin zuwa bikin nan."

  Dafata Little tai tace " Laifinane dana d'aukoki duk da banga alamun kinasan zuwa ba."

  Kai Nafi ta girgiza alamar a'a kawai zatai magana taji kamar intai magana kuka ne zai kufce mata.
Little ta d'au waya ta kira Ashraf,  sai da ta kusa katsewa  sannan ya d'aga tace " Yaya."

  Daga can Ashraf dake zaune kusa da Habib yace " uhm ya akai? "

   Kasancewar a kusa suke yasa Nafi tana iya jiyo maganar Ashraf,  Little tace " dama fadama zanyi gobe Nafi zata koma inji Mumy."

   D'agowa Nafi tai ta kalli Little,  jitai Ashraf yace " to Allah ya kiyaye."

  Little taso ya hana Nafi tafiya jin ya fad'i haka yasa jikinta yai d'an sanyi tace " Yaya wa zai maidata?"

  A zuciye yace " da wani karambanin ne ma yasa ku d'auko yarinya tana makaranta? Sai kuje ku sami wanda ya saku ku tambayeshi."

  Little zatai magana taji ya katse, jiki a sanyaye ta kalli Nafi wacce ke wasa da hannunta a zahirin gaskiya kalaman Ashraf sun mata zafi sai dai tasan koma meye ai laifin ta ne.

Ta kalli Little tace taimakamin dan Allah in kwanta."

   Little ta kalli kafarta tace " Nafi ko muje Chemist? "

  Kai Nafi ta girgiza mata alamar a'a tace "bafa wani serious bane. " a zahiri kuwa tanajin zafin gun sai dai bataso a cire handkerchief d'in Ashraf daga kafarta.

  Little ta mike sannan ta shiga taimaka mata ta kwanta, idanu ta rufe kamar mai bacci, hakan yasa Little ta fito daga d'akin.

   Tana fita Nafi ta fara zubar da hawayen dake cinta, Ashraf ta tuno sanda ya d'auketa, idanu ta runtse kalaman Ferry ta tuna data cemata san Ashraf take, Nafi ta share hawayenta sannan a fili tace " Ina na isa? In kuwa har haka ne lalai ina cikin gararin rayuwa."

  Kalamansa na mota ta tuna dayace mata zai saketa in ta samu wanda takeso.

  Ta dad'e tana hawaye kafin bacci ya d'auketa.

  Washegari da sassafe kuwa Drivern Mumy ya mai da ta makaranta, ko Ashraf bata sa a idanta ba.

   Nafi ta dage sosai da ta koma makaranta, ba wai a kan karatu kad'ai ba sai dai kullum suna tare da Ferry tana kokarin canza halayenta.

   A wannan zuwa gidan datai lalai ta fahimci abu biyu, na farko Ashraf wasa kawai yake da ita da jawo mata tsana agun mutane bayan ba santa yake ba, na biyu kuwa lalai in har tanasan Ashraf ya fara santa sai ta zama mace daidai shi.

   A can kuwa an gama biki lafiya ankai Amarya d'akinta, sannan kowa ya watse.

   Anyi hutu amma Nafi ta kira Habib akan zata zauna a gidan Principal ya tambayar mata ita, saboda a lokacin hutun ta samu isashen lokaci na karatu, wannan jarabawar ita tazo ta karshe a aji batajin kuma za ta iya nunama Ashraf wannan dakikantar datai.

Habib ya tambaya, ba tare da wani dogon Nazari ba ta amince, bayan kowa ya tafi gida itama ta koma quaters.

  Little taji ba dadi sai dai bayan Nafi ta mata bayani ta waya yasa ta gamsu.
  Nafi ta dage sosai......

   Shekararta d'aya kenan a makaranta,  duk hutu ba ta wani zuwa gida, sai dai duk cikin hutu Little na zuwa ganinta da sakon Provision daga Mumy da kud'in kashewa.

   A iya wannan Shekara d'aya ba shakka Nafi ta canza sosai da sosai, ita da Ferry kam sun zama Aminai sosai, sai dai in a b'angaren karatu ne kuma da Jibiya sukeyi.

  Yanzu suna S1 Nafi ta canza sosai, bata tunani ko sha'awar zuwa gida duk da kuwa yanda zuciyarta take tsananin rashin Ashraf kamar ranta.

  Yanzu sun shiga Ss 2 a a wannan lokacin ne kuma Nafi ta shirya dan zuwa gida, Little tace "wannan karan kam gaskiya sai Nafi tazo gida, dan akwai bikin kawar Little ko ince Aminiyarta da za'ai.

  A wannan lokacin shekarun Nafi 18, duk da ba kiba gareta ba sai dai kirjinta ya cika da dukiyar fulani, Nafi ta goge sosai, kamar ba makarantar kwana take ba, komai nata tsaf dan in Little zata kawo mata kaya har da mayuka masu kyau take cewa ta had'o mata.

   Nafi tana tsaye kusa da Ferry ga Jibiya a gefensu, Nafi ta kalli Ferry tace " Na nawa kikai?"

  Ferry tai d'an tsaki tace " Ai   Yaya Yusuf ya rainan hankali wai ta 7 dan tsabar rashin mutunci."

  Nafi tasa dariya ita da Jibiya, Ferry ta had'e rai tace " kubarni da abinda ke damuna."

  Jibiya ta sake dariya tace " lalai zakisha Fada'a gun Abba dan ni na 2 nai."

  Idanu Ferry da Nafi suka zaro, Nafi ta kalleta sannan ta had'a hannayenta ta tafa mata tace " wow! Jibiya kina kasheni."

  Ferry ta harareta tace " Zama ta raya ki, ke Feena na nawa kika ci?"

  Nafi ta juya kai tace " Secret."

  Ferry tai dariya tace " badai irin na last term ba na 12 ba?"

  Nafi ta d'an rangwad'a kai cikin tsokana tace " na 8 nai."

  Ferry cikin d'aga murya tace " WHAT?"

  Nafi tai murmushi tare da ware takardar, murna suka shiga yi sosai, can Ferry tace " Kai naji dadi kin daina cin double number, amma da alama sai na dage kar next term ki dawo gabana."

  Suka sakeyin dariya.
Ferry ta kalleta tace " Feena zakizo d'in ko?"
  Nafi ta d'an juya ido tace " zanzo insha Allah amma banasan zuwa yayanki nanan."

  Ferry ta harareta tace " Gaskiya Feena bazan juri wulakantamin yaya da kike ba, tunda yazo visiting ya nuna yana sanki amma kike wani disgashi, in bakiyi wasa ba har gidanku zan kawoshi."

  Nafi ta zare ido tace " wa? Rufan asiri."

  Jibiya tace " kema kinsan bazata yarda wani saurayin ya bita gida ba saboda sanda takema yayan nan nata."

  Tsaki Ferry tai tace " wlh Feena in har kika bari ya gane kin mutu akansa haka lalai sunanki sorry."

  Nafi ta tsuke baki tace " Ke nima yanzu ba daina sanshi yaushe rabon ma da inganshi, kila ma ko a hanya naganshi bazan ganeshi ba."

   Ferry ta d'aka mata duka tace " ni zaki maida gara? Kullum fa sai kinyi labarin yayan nan naki."

  Nafi zatai magana ta hango kamar Little ta fito daga wata zukekiyar mota, tana sanye da sun glass tayi kyau sosai da sosai, Nafi tace " anzo d'aukana."

  Nan suka mik'e suka taimaka mata da kayanta, Ferry tundaga nesa tace " Kai Feena gaskiya Little tana kasheni da gayu, ki bari nika inje gida dattin makarantar nan ya fita daga jikina lalai zan tsorata maza."

  Nafi tace " Nima ki bari sai nazo gida kin ganni kiga yanda zan kasheki da nawa gayun."

  Dariya sukai harda tafawa.

  Sun karasa gun, Little ta karaso cikin murna, ta rungume Nafi.

  Sunsa kaya a motar sannan Nafi ta leka dan ganin wanda ya kawo Little.

    Habib ya sakar mata murmushi yace " Tantancewa akeyi ne?"

  Murmushi tamai itama tace " Ai ba sai na tantanceba dama can jikina yaban kai ka kawota."

  Nafi kenan ba shakka kim canza wato yanzu bakya kunyar maidamin kalamai na."

  Ta d'aga kanta batare da ta amsa mai ba, sannan sukai sallama dasu Ferry ta amshi number Ferry da jibiya tasa a wayar Little.

   Nan suka shiga mota, Habib jefi jefi yana kallanta ta glass d'in mota, ba shakka yarinyar nan ta girma, ganin haka yasa Nafi ta matsa daga setinshi ta koma ta can b'an garen.

  Little ce tace " Nafi yau ji kad'ai nasan farin cikin danakeyi, nayi missing d'inki sosai."

  Nafi tai murmushi sannan tace " nimafa kawai daurewa nakeyi jinake kamar na biyoki inkika zo ganina."

  Little ta harareta tace " ba wani nan kedai kawai kinzama 'yar college tafi gida dadi."

  Dariya suka d'anyi Nafi ta juya tan kallan window.

Little ta juyo ta kalleta tace " Nafi au Feena baki tambayi ina yaya ba, ko visiting nazo bakya tambayarsa."

  Habib ne yai katsal yace " ita meya dameta dashi bayan yayi aure yamanta da ita."

  Har cikin ranta Nafi taji haushin maganar Habib amma sai ta daure tace " Ya Habib kenan, dama can ba wani shiri muke dashi ba balle ya nemini."

  Little ta kalleta tace " Nafi yanzu kin daina shigar ma yaya ne?"

  Ta tab'e baki tace " ni a wa? Dama can bawai shigar mai nake ba kece baki fahimceni ba, ai Yaya Neesa itace zata shigar mai bawai ni ba."

  Habib ya saki dariya yace " Gaskiya ne Feena gwara ki fara bayyana musu komai."

  Nafi ta kwantar da kanta akan window tare da lumshe ido, tace " Little bacci."

  Little ta d'an had'e rai tace " shikenan nayi shiru."

  Habib ya kalli Little yace " Ai cewa tai bacci bawai kiyi shiru ba."
  "Hmm ai tun da dadewa na gane Nafi au Feena in batasan magana sai tace wai bacci."

  Habib ya juyo ya kalli Nafi sannan yace "yarinyar nan ta canza dayawa."

    kai little ta jinjina tace " ai naji dadin makarantar nan."

Haka sukai ta maganganunsu itakam tana kwance tana jinsu a cikin zuciyarta take magana " Yaya ba sai ka basar da ni ba, nafi kowa sanin rashin matsayi danake dashi agunka, kila ma inya ganni bazai ganeni ba, ba komai Allah ya kawomin wani mai sona nima inyi kokarin ganin na yakece wannan soyayyar da take one_side."

    Nace Uhmmmm zaki iya????.

   *THE INNOCENT TEAM*

Sunday, 21 May 2017

ZUCIYA.... Kowa da irin tasa 30

ZUCIYA
       ĸowa da ιrιn тaѕa

© na Ayυѕнer Mυнd
    ayushermohd.blogspot.com

Wattpad As_AyusherMohd

Gaisuwa gareku Aminan Arziki Mom Hamra,  Mom Farhan,  Agra,  Mom Farouk and Fresh LUSM

{ *30*}

   Gaba d'aya Nafi ta kasa d'auke ido daga kanshi,  har ya gama d'ebo ruwa ya wanke mata duk da rad'ad'in da takeji sai leb'e kawai da take ciza, sannan ya kalli inda ta yanke,  sosai gun ya shiga ciki da alama karfe ne ko kwalba ya mata wannan aikin,  hannu yasa a aljihunsa ya ciro handkerchief sannan ya d'aure mata gun dashi.

  Mik'ewa yai tsaye sannan ya kalleta yace " zaki iya tashi? "

  Kai ta d'aga mai idanunta subyi tsuru tsuru,  ta d'aga zata mike taji wani zugi a kafarta wanda sai da tayi 'yar kara saboda azaba,  baya tai kamar zata koma kan kujera da sauri yasa hannu ya taro ta,  idanunsu ne suka had'u da juna,  Ashraf ya kalleta sannan yace " bakya gani ne? "

  Kallansa tai batare da ta amsa ba,  ya girgiza kai sannan yace " taya zaki bari har kiji irin wannan ciwon? "

  Kasa tai da idanunta,  saukar da ita yai ta koma ta zauna kan kujerar da ta mike.
  Harararta yai yace " yanzu ya kike so muyi? "
  Tai kasa da kai sannan tace " kaje kai ai jeranka ake ni zan karaso da kaina."

Ta d'auka bazai tafi ba ganin ba yanda za'ai ta iya tafiya,  amma ga mamakin ta gani tai yayi gaba,  kallansa tai idanunta suka ciciko,  ta sukunyar da kanta cikin rashin jin dadi.

  Batai auni ba taji kawai an sungumeta, a tsorace ta bud'e idanunta cikin rud'ewa tace " Yaya saukeni dan Allah. "
Ya murtuke fuska yace " kina tunanin bazan iya ba? "

  Kai ta girgiza alamar a'a, sannan tace " tsoro nake kar wani ya ganmu a haka."

  Wani murmushin rainin hankali ya mata yace " ke dai kina tsoro kar Aneesa ta miki duka."

  Nafi tai kasa dakai sannan tace " Allah dagaske nake ka ajiyeni please."

  Bai kulata ba ya cigaba da tafiya,  sun kusa isa filin gun sai ga Little da Habib sun taho ta gun suna Neman Ashraf.

   Daga d'an nesa kad'an Little taga alamun kamar sune hakan yasa ta karaso gun da sauri.

  Kallan mamaki ta musu,  Habib ne ya karaso gun shima cikin mamaki yace " Ashraf meye hakan? "

  Batare da ya kalleshi ba yace " name fa? "

  Habib ya kalli Nafi wacce tai tsuru tsuru da ita yace " event d'in auranka fa akeyi? "

  Yace " ehen sai me?  Abun haramun nai ko me? "

  Habib ya kara kallansu, sai dai amsar Ashraf yasa ma ya kasa magana,  Little ta daure tace" yaya yanzu in mutane suka ganku a haka me kake tunani? "

  Zaiyi magana kenan sukaji ana zabga salati daga bayansu.

  Ashraf ya kallesu Umma ce da 'yan uwanta ga Aneesa a tsaye cikin tsananin mamaki.

  Ashraf wuce su Little yai ba tare da damuwa ba ya gifta su Umma sannan ya ajiye ta a kan kujera daga baya,  sannan ya kalli Umma yace" Umma me kuke anan?? "

   "Kan jakar uba,  abinda za ka tambayemu kenan? "
Ashraf ya kalli Aneesa wacce ta fara hawayen bakin ciki sannan yace" naga kamar abun yara ne ban d'auka manya ma zasu zo ba. "

   A zuciye Umma ta matso tace " me kake aikatawa anan kai da waccan munafukar yarinyar a ranar shagalin bikinka? "

  Ya kalli Nafi cikin salon rainin hankali yace " wacce?  Waccan yarinyar? "

  Umma ta kumbura kam,  yai murmushi sannan yace" karamin accident ne ya sameta shine na taimaka mata."

  Umma ta kalli Nafi cikin kuluwa sannan ta kalli Ashraf tace " accident? Shi accident d'in bai tashi ba sai a ranar bikinka?  Ko dai tsabar kinibibi da muafurci ne hakan? "
  Ashraf bai tanka ba ya kalli Aneesa  da take kuka,  matsowa yai kad'an sannan yace " muje ko mutane na jira. "

  Hawayenta ta share sannan cikin b'acin rai tace " Duk wayar danake ma baka d'auka ba dan kana tare da waccan ne ko me? "
  Kallanta yai cikin rashin kulawa yace " zakije ko kuwa in tafi?  Dan naga kamar lokaci na kawai ake b'atawa anan."

Wata 'yar uwar Umma ta kalli Nafi wacce tai kasa da kanta hawaye kawai takeyi,  tace " waccan munafukar ai d'azu muna jere itace ta shiga d'akinsa ba kunya ta dade aciki kafin ta fito,  kun tabbatar ba wani abu na masha'a tsakaninsu? "

   Umma ta kalli Ashraf sai dai gani tai kamar ma baisan me suke cewa ba waya kawai yake danna wa,  zatai magana taga kamar tafiya ma zaiyi.

  Da sauri Habib ya rike hannunsa yace " Ashraf ka jiraya mana. "

  Hannunsa ya fizge sannan yace " zamanta nake?  Ita har takai in mata magana taki tahowa? "

  Aneesa ta matso inda yake jiki a sanyaye tace " Yaya amma.... "

  Cikin fada yace " amma me?  Ba ki yadda dani ba ko me? "

  Kai ta girgiza sannan tace " ba haka nake nufi ba. "

  Ya kalli su Umma sannan yace " to me kike nufi?"

Tace " ba komai kawai dai dama. "

  Tsaki yai sannan yace " inzaki wuce muje to,  in kuma bazaki ba ni inada gun zuwa. "

  Nan ya fara tafiya,  Umma ta maka mata harara alamar kar taje, da sauri Aneesa ta d'auke idanta akan Umma tabi bayan Ashraf da sauri.

  Ran Umma ya b'aci sosai lalai ta kosa Aneesa ta auri yarannan insun samu kan dukiyarsa su salwantar dashi dan kuwa bazata iya jurar bakin cikin yaron nan ba.

  Kan Nafi suka dawo a zuciye,  gashi Habib ya tafi,  duk yanda Little ke ba umma hakuri amma inaa idanta ya rufe duka ta shiga yima Nafi ba ji ba gani, itakam Nafi hawaye kawai takeyi.

Gaba d'ayawannan ranar mutane dayawa da bakin ciki suka taso daga gun nan.

  Su Nafi suna sauka a mota, Little ta sakala hannunta ta kafa'adarta suka nufi ciki,sai dai me?

  Suna shiga sukaga cincirindon mutane a tsakiyar farfajiya banda masifa ba abinda akeyi,  Little ta kalli Nafi tace"ko me aka sake yi oho. "

  Ji sukai da karfi wata tace " dan kut...... Uban yarinyar ai karyata zakuyi ba barinta zakuyi ba. "

  Nafi kam ta rasa me yasa takejin gabanta na fad'uwa haka,   jisukai ance " wai yarinyar ma daga ina take?  Akan ke zaku yadda ta zauna a nan gidan? "
Little ce ta kalli Nafi yanzu kam sun gane inda maganar a dosa,  Little ta kalleta tace " mu wuce ciki. "

  Suna shiga ciki Little ta ajiye Nafi sannan ta fito tai gun Mumy.

  A zaune taga Mumy tayi tagumi ga 'yan uwanta suma sunata magana, Little ta karasa ta zauna kusa da ita tace "Mumy wlh ciwo taji a dalilin neman yaya,  ganin bazata iya takawa ba yasa ya d'auketa. "

  Mumy tai ajiyar zuciya tace" Little ki fadama Nafi gobe ta shirya da safe a maidata makaranta saboda tsoron abinda mutane zasu mata dan nasan 'yan uwan maman Aneesa sarai bazasu tab'a barin maganar nan ba. "

  Little tai shiru jikinta yai sanyi sosai,  sai dai tana ganin hakan ne yafi sauki.



¤¤¤¤¤¤¤¤

  A kachako kuwa d'an litti ya zake sosai yana aikin kasuwancin sa na babur, yana kuma jin dadin yanda uban gidan sa yake sanshi,  fatanshi d'aya yai sauri ya kammala kud'insa ya taho kano neman Ashaf........


*THE INNOCENT TEAM*

Friday, 19 May 2017

ZUCIYA.....kowa da irin tasa 28

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*Hi Fans please Vote me on Wattpad As_AyusherMohd*

{ *28*}

Nafi kwance a saman gado,  ba shakka taji zafin dukan da aka mata sosai,  ita kad'ai ce a d'akin tana kwance Ferry ta shigo,  kasancewar ba magana take mata ba yasa Nafi tace " Sannu da dawowa. "

  Kallan da Ferry ta mata yau ba kamar yanda ta saba mata ba,  wato kallan banzan data saba ba,  yau kallanta tai cikin mutunci,  Nafi tai murmushi sannan ta gyara kwanciyarta,  jitai Ferry tace " Nafisa ya akai kika kasa bada amsa d'azu? Baici ace duk dakikantarki kinkasa ba. "

  Nafi ta mike zaune sannan ta kalleta fuskarta cikin farin ciki,  tace " Bansan amsar na Ferry. "

  Ferry ta shiga cire kayanta tana  cewa " to in dai haka ne lalai zakici doka a gun malamai, ya kamata ki samu Jibiya ta koya miki tun kafin a gama raina ki. "

  Nafi ta jinjina kai cikin farinciki tace " Nagode Ferry. "

Ferry ta harareta tace " karkiyi tunanin sanki nake yanzu,  ni bana kawa da wacce bata kile ba,  bana kawa mara kwalliya,  ba kuma na kawa mara aji. "

  Nafi ta sauko daga sama tace " Ferry nikam kina burgeni wlh,  duk da ba kulani kike ba inasan tsarinki yana birgeni. "
  Ferry ta d'aura towel sannan tace " abinda yake b'atamin rai kenan da mata irin ku,  sam bakwa abin mace,  bakwa kwalliya,  yanzu kamar ke sam duk abinda mutum zai miki ban taba ji kin d'aga ma wani murya ba,  komai sai dai ki  bada hakuri,  ke ba dutse ba."
Taja tsaki ta zari kwandon wankanta tai waje.

   Nafi ta bita da kallo ba shakka abinda ta fad'a gaskiya ne,  to amma ya zatai?  Bayan haka halinta yake?

  A satin nan Nafi har sai da ta rame tsabar karatu kala biyu,  ga na lesson d'in da ake mata gana computer, a wannan zaman karatun da jibiya take koya mata anan ta fahimci Nafi batai wani karatu ba ganin duk yanda taso tai pronounce d'in kalmomi abun yake gagara,  sai dai hakan yasa ta kara tausayama Nafi sannan ta jajjirce wajen kara koya mata.

   Yanzu kam suna 'yar magana sama sama da Ferry.

  Sati d'aya ya cika,  malam ya kira Nafi gaban black board ya shiga zuba mata tambaya,  tambaya 5 ya mata da kyar Nafi ta amsa biyu,  wannan dalili yasa Malam ya yanke mata hakunci akan ta dawo gaba kusa da Ferry da zama sannan duk karshen week sati biyu zai dinga mata tambaya.

  Nafi kam duk ta rame saboda karatu,  sam bata samun damar tunanin gida ko wani abu,  sai dai ta rasa dalili duk sanda ta tashi daga bacci sai zuciyarta ta rage mata kwana d'aya akan kwanakin bikin Ashraf.



   *A KANO*

  An kai lefe sannan anata hidimomin biki, sai dai sam Ashraf abin nan baya gabansa,  tabbas yasan a ransa yanasan Aneesa sai dai bayajin wani farin ciki game da wannan auren.

  Ita kad'ai take kid'anta take rawarta,  duk dinkunansa sai Habib ta samu sukaje suka siyo,  sam Ashraf baya walwala bare farincikin wannan auran.

  Duk yanda Aneesa taso daurewa karta nunamai jin haushinta sai data kasa tamai magana,  sai dai duk sanda tamau magana kanta abin yake komawa, karshe tazo tana bada hakuri.

  Gida ya fara taruwa da mutane,  little kam sai rawar kai dinkuna tayi yakai kala 10 ta musu kuma anko da Nafi kala 5, murna kam ba'acewa komai agunsu Umma.


  Yau saura kwana biyu a fara hidimomin biki Mumy ta kira Ashraf zuwa falonta,  bayan ya zaunane Mumy ta kalleshi cikin kuluwa tare da tattara hankalinta kansa, ta fara magana cikin kulawa " Ashraf yau saura kwana biyu a d'aura maka aure da 'yar uwarka."

  Ashraf kansa na kasa sai dai baice komai ba,  tace " Muhammad! "
D'agowa yai cikin mamaki dan bai tab'aji ta fad'i wannan sunan ba d'an sunan baban mahaifinsa ne.

  Mumy ta kalleshi tace " kayi hakuri abinda na maka. "

  Kallan mamaki yake binta dashi, yace "name? "

Ta kalleshi idanunta a raunane tace " Ashraf na sani sarai abinda na maka shekarun baya masu yawa shine yasa ka zama haka,  sam bakasan 'yan uwanka,  kanka kawai ka sani,  ba ka tunanin maganar da zaka fad'a ko zai b'atama wani rai. "

  Ashraf dai kallanta kawai yakeyi,  Mumy tai ajiyar zuciya tace " bazaka tab'a fahimtar me yasani na auri kanin mahaifinka ba daga rasuwar Abbanka ba har sai lokacin da kasan komai na gidan nan da kuma abinda ke cikin zuciyar kowa na gidan nan. "

  Ashraf da mamaki yace " Mumy. "

Ta sakar masa murmushi tace " na sani nayi laifi a gareka,  na rashin sanar dakai komai danai har sai sanda aka haifi Little, sai dai inaso ka sani komai nai a rayuwa to tabbas d'an kai nayi shi,  ban tab'ayin wani abu dan in farantawa kaina rai ba,  a ko da yaushe kai nake fara sawa a gaba akan komai na rayuwata kafin inyi tunanin kaina. "

  Shiru tai sai dai ta kawar dakanta gefe kad'an alamar so take ta b'oye kwallar ta, Ashraf kam kalaman Mumy sun tab'ashi sai dai haryanzu gani yake koma meye dalili shi bai fahimci dalilin auranta da kanin Abbansa ba."

  Mumy ta d'anja hanci sannan tace " Mahaifinka na tsananin san kaninsa,  sannan babban burinsa bai wuce yaga ya had'a zuri'a dashi ba,  nasani da yana da rai sai yafi kowa farin cikin wannan abun duk da yasan shi kanin nasa ba sanshi yake ba. "

  Ashraf ya kalleta cikin mamaki yace " Mumy me kike nufi da basanshi yake ba? "

Mumy tai murmushi tace "la ba haka zan fad'a ba subutar harshe nai. "

  Ashraf yai shiru sai dai tabbas yasan da wani abu.

  Mumy tai saurin wayancewa da cewa " Ashraf kasan me ake nufi da aure ba sai na sanar dakai ba dan Allah ka rike matarka yanda ya dace,  Aneesa na sanka kowa ya sani. "

  Ashraf bai amsa hakan yasa Mumy tace " Ashraf maganar aiki. "

  Kallanta yai sannan ya daure yace " Mumy me yasa kike so im fara aiki a company d'in Abba? "

  Mumy tace " saboda hakkinka ne."

  Ashraf yai murmushi yace " idan na fara aiki a wani matsayi kawu zai zauna?  Sannan ni a wani matsayi employees na company d'in zasu d'auken?"

  Mumy da mamaki tace " Ashraf me kake nufi? "

  Yai murmushi sannan yace " zan fara aiki a company d'in Abba sai dai bawai a matsayina na magaji ba inasan ne in amshi hakkina da kokarina bawai dan ni d'an Abba bane. "

  Mumy ta jinjina kai tace " kana nufin zaka fara aiki a company d'in daga farko?  Tun daga kan interview?"

  Kai ya d'aga Mumy tai murmushi lalai ta yaba da tunanin d'an nata ta sani sarai dama yanada hangen nesa sai dai bata tab'a tunanin zaiyi tunani haka ba.

 

   ¤¤¤¤¤¤

  Nafi ce zaune tana shafa mai Ferry ta kalleta tace " Nafi yau tunda kika tashi naga kamar bakida lafiya. "

  Nafi ta kalli Ferry tace " Ferry dan Allah tambaya. "

Kai Ferry ta d'aga mata alamar eh tanaji.
"Yayanane zaiyi aure a satin nan,  na rasa meke damuna sam duk sanda na tuna sai inji raina yana b'aci. "

  Ferry ta kwashe da wani dariya tace " Innocent Feenah dama haka kike?  Oh a ido kamar.... " 

Nafi tace " ban gane ba,  wani abun ne? "

  Ferry ta fara tafi tace " Innocent girl,  yayan naki uwa d'aya kuke ko uba? "

  Nafi ta girgiza kai,  Ferry ta kara sa dariya sannan tace " gaskiya Feena kin tashi daga Innocent kin koma green snake. "

  Nafi ta mata kallan mamaki tace " ni na tambayeki abu ma baki amsa min ba kin bige da dariya. "

  Ferry tace " Good haka nakesanki in abu bai miki ba ki fito ki fad'i gaskiya,  sannan zancen yayanki ai ba komai bane sanshi kawai kike. "

  Da sauri Nafi ta mike ta zura hijab d'inta tai waje tana cewa " Ni?  Wacce ni?  Ni kaza?????



*THE INNOCENT TEAM*

Wednesday, 17 May 2017

ZUCIYA....kowa da irin tasa 23

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*Fatie Shafi'u ina tayaki murnar kammala Jarabawarki. May Almighty Allah help and protect u.... ILYSM*

    Washe gari da safe Habib yaje makarantar mahaifinsa yama Nafi takardun karya na primary da kuma Js 1 and 2, sai dai takardun sun nuna sam batada kokari.

   Nan ya taho da shi gidansu Ashraf.

   Yau gidan an tashi kowa zuciyarsa ba dadi musamman ma Umma da Aneesa, Little kam ta fita makaranta.

Itakam Nafi tana kitchen ta zake sai aikin girki take,  sunayi suna 'yar hirarsu da Goggo.
  Suna gamawa ta fito duk jikinta ya d'an baci Amra ce ta karaso gunta da gudu tace " Wai kizo inji yaya. "

  Nafi ta kalleta cikin zak'uwa tace " Ya Ashraf?  " kai Amra ta d'aga mata ai kam Nafi da sauri ta nufi b'angarensa tana tafe tana gogee fuskarta da hannu,  tun jiya takesan ganinshi sai dai ba yanda zatai.

   Fuskarta a sake ta kwankwasa kofar, ta saba in yana ciki sai dai yace ta shigo in dai har ba makulli yasa ba,  sai dai yau gani tai anzo an bud'e da fara'arta ta kalli mai bud'ewa tace " Yaya ina kwa...... "kalamanta ne suka tsaya ganin Habib a tsaye yana mata murmushi.

  Jin ta tsaya da magana yad'an kanne ido cikin salonsa yace " Haba Nafi ba ni kika so gani bane? "

  Da sauri ta girgiza kai alamar a'a sannan ta d'ora da cewa " ba haka bane Ya Habib. "

  Habib ya d'an matso kad'an hakan yasa ta d'an kara matsawa,  kara matsowa yai itama ta kara matsawa,  sam bata kula tazo karshe ba tayi baya zata matsa kawai taji zata fad'i,  da sauri yasa hannu a kugunta ya tarota.

   Nafi kam har ta runtse idanta kam,  jin an riketa yasa ta bud'e ido a hankali,  Habib ya sakar mata wani lalausan murmushi,  sannan ya matso da fuskarsa yace " Me yasa kika tsaya da maganar ki to? "

  Yawu ta had'iya da karfi sannan ta d'an motsa baki tace " Ya Habib d'an sakeni. "

  Jin ta waske bata bashi amsa ba yasa ya d'agota tare da sake cewa " Shikenan na hakura da gaisu.... "
Bata jira ya karasa ba tace ina kwana? "

  Dariya ya d'anyi sannan yace " Nafi kina burgeni na rasa me yasa. "

  Kasa tai da kai dan itakam tasan wasa ne ace tana burge wani.

  Ashraf dake zaune a kujera duk yana kallan me sukeyi kasancewar kofar a bud'e Habib ya bata yaja wani karamin tsaki tare da girgiza kai yace " in kun gama sai ku shigo,  dan ni inada abinyi. "

  Nafi ta kalli inda Ashraf yake haka kawai taji gabanta ya fad'i tare da tsananin takaicin ganin ta dayai.

Habib ya matso da niyyar rike mata hannu da sauri ta b'oye hannun a baya kallanta yai fuska a sake sannan ya d'anyi gaba yace " Ki shigo. "

  Da sauri ta shige jikinta duk yai sanyi.

  Ashraf na zaune yana kallo ta karasa tare da zama a kasa,  Habib ya kalleta yace " zauna a kan kujera mana? "

  Ashraf ya bugamai wani mugun kallo yace " Mu sa'aninta ne? Kai meyasa kake kokarin zubar mana da mutunci agurin yara kanana? "

  Nafi wacce ko alamar tashi dama batai ba ta d'ago ta kalleshi sai dai zuciyarta ta d'anji ba dadi.

  Ashraf ya d'auke idansa,  Habib ma kasa magana yai,  Shiru ne ya d'an biyo baya kafin Ashraf yace " Nafisa! "

  Gaba d'aya tun daga kan yatsar kafarta har zuwa kanta sai dataji wani abu ya wuce mata, d'agowa tai a hankali ta kalleshi.

Ashraf kam ko a jikinsa yace " yau zuwa gobe zakuje da Little da kuma mumy xakuje siyayyar kayan makarantarki. "

  Kallonsa tai cikin mamaki batasan sanda tace " naam? "

Ya had'e fuska sosai yace " bakiji me nace ba? "

  Tace " Naji kace makaranta. "

Yace " eh,  in kun gama siyayya da komai zuwa jibi zaki wuce makarantar kwana dake kazaure. "

  Nafi kam idanunta ne suka ciciko,  wani irin farin ciki ne wanda ita kanta batasan irinshi ba yake ratsata,  Ashraf yace " meye hakan? "

  Hawayenta ta goge wanda suka zubo,  ta girgiza kai tace ba komai.

Habib cikin damuwa yace " Bakyaso ne? "

Kai ta girgiza da sauri tace "a'a ba haka bane. "

  Ashraf ya d'an kuraa mata ido kamar yanasan gano wani abun,  idanunta tai saurin yin kasa dasu tace a hankali tace " Yaya babana fa?"
  Jiyai ransa ya b'aci ya ce " Bansan inda yake ba,  kuma bana fata insani, sannan in har da haka kike tunanin yin karatun to gwarama karkije,  dan ni na tsani mutum mai raunanniyar zuciya. " ya mike yai ciki.

  Kallo ta bishi dashi zuciyarta tana dana sanin tambayar datai,  sai dai duk yanda taso da daurewa ai dole ne tai rashin mahaifinta.
A ranta ta maimaita Raunanniyar Zuciya? Me kenan?

Kamar Habib yasan meke ranta yace " karki damu da fadan Ashraf dan shi yawancin maganarsa haka take. "

  Nafi tabi d'akinsa da kallo tanasan ta bashi hakuri ta kuma tambayeshi ciwon sa,  daurewa tai ta kalli Habib tace " Ya Habib meye raunanniyar zuciya? Ma dai san me zuciya take nufi"

  Dariya yai yace " rauni fa? "
Tace " na sani. "

Ya sake dariya yace " to sai ki had'asu guri d'aya ki gani. "

Tace " Rauni Zuciya? "
  Wannan karan dariya sosai Habib yai yace " lalai Nafi inkinje makaranta cikin mutane a hankali zaki fahimta. "

  Tace to,  sannan ta sake kallan d'akin Ashraf sai dai ba yanda zatai, mikewa tai zata fita,  Habib yace " aiki kikai ne?  Naga kayanyi sun b'aci kamar daga kitchen kika fito. "

  A'a kawai tace tai saurin fita.

Tana gaba kad'an sai ga Aneesa wacce tasha kwalliya tana tafe kamar sarauniya.
Idanunsu ne suka had'u,  gaban Nafi ne ya fad'i bawai dan tsoro ba a'a sai dan ganin kyan datai,  a cikin zuciyarta tace " Dole Ya Ashraf yasoki. "

   Tun datazo gidan bata taba ganin Aneesa ta d'au kwalliya irin haka ba,  ba namiji ba ko mace ce ta wuce dole ne ta kalleta dan tayi kyau sosai,  Aneesa wacce takura ma Nafi ido cikin tsananin takaici ta karaso.

  Kwalliya tai dan taje su shirya da Ashraf amma me take gani haka?
A zuciye ta karaso tare da kallan Nafi cikin tsananin takaici tace me kike anan? "

  Nafi ta kalleta sai dai ta kasa cewa komai,  Aneesa ta sake kuluwa tace " ke dan gidan ku ba magana nake miki ba? "

  Nafi ta daure kawai jitai ta sami kanta da cewa" Ya Habib ne ya kirani. "

  Aneesa wacce bata gamsu da zancen ba tace " Nafi karkiga jiya nazo da niyyar dukanki ki d'auka wai ko kishi nake dake ko wani abun. "

  Ta d'anyi dariyar kissa tace " Tausayi kike bani,  kinfi kowa sanin ni dake ba d'aya bane sannan ke da kanki zaki iya warewa kisan wa ya dace da Ashraf ko ince wa Ashraf yake so,  dan haka ina baki shawara in ma da wani shirme ko yarinta akanki gwara tun wuri ki cireta dan kinsan wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa, ke ko masu aikin gidan nan sun fiki daraja. "

Ta bangaje ta tai gaba,  jitai ranta yayi sanyi ta tuno maganar Umma datace " ki nuna mata ita ba komai bace ta hakan ne inma da wani munafircin a ranta zai sa ta shiga hankalinta."juyowa tai ta kalli Nafi tana nan a inda ta barta, ta sake dariya sannan tai gaba.

  Nafi kam sai juya kalamun take a ranta,  tafi kowa sanin Ashraf yafi karfinta,  ta kuma sani ko kata sun kare ba abinda zaiyi da ita sai dai meyasa takejin zuciyarta ba dadi? Wata zuciyar tace kema Nafi kina ganin mai mace kamar Aneesa me zaiyi dake? Jiki duk a rame?  Gaki yar kauye wacce ake neman biyan bashi da ita? "


   Da kyar ta karasa d'aki tai wanka sannan tasa abinci a gaba, da kyar takeci ta rasa me yasa batajin dadin abincin sam.

    Aneesa kam tana shiga taga Habib zaune a kan dinning yana cin abinci,  tai murmushi tace " Yaushe a gari d'an uwan Ango? "

  Habib ya kalleta yace " Amarya irin wannan kwalliyar kamar yauce ranar? Ko dai anzo seducing d'in d'an uwa nane? "

  Aneesa ta d'anyi dariya har hakoranta suka fito ta d'an karkace kadan tace " me?  Kana tsoro ne?  Ko kuwa kishi kake ba kada me ma?"

  Habib ya rike haba yace " tab lalai d'an uwana yana cikin tashin hankali gwara muyi sauri mu kawoki kafin ki burkice mana d'an uwa."

  Aneesa ta d'an fara tafiya cikin salo tare da cewa " ah to wayace kukai bikin da nisa?"

  Habib ya bita da kallo yana murmushi.

  D'akin Ashraf ta murd'a,  kai tsaye ta shiga, Ashraf wanda ke kokarin shiga wanka ya kalli kofar kansa tsaye ya d'auka ko Habib ne, ganin Aneesa yasa ya had'e fuska tamau,  ta sakar nai wani murmushi tace " Sorry Hubby ashe wanka zakai. "

  Ya kalleta yace " Aneesa bakisan ya ake sallama ba ko kwankwasa kofa ba? "

  Ta shagwab'e tare da shiga ta zauna a bakin gado tace " nida d'akin mijina? "

  Ya girgiza kai cikin takaici yai hanyar toilet sannan ya tsaya ya kalleta tare da cewa " nine mijin kuma banaji na bada sadaki bare a shafa fatiha,  dan haka ki kiyaye shigomin d'aki kai tsaye." yana kainan ya shige toilet.

  Aneesa ta turo baki cikin jin haushi sai dai ta kasa cewa komai sannan tana kunyar fita kar Habib ya mata dariya......





  *THE INNOCENT TEAM*

ZUCIYA.....kowa da irin tasa 24

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*Hajja ce! I Sincerely Dedicate This Page to You... ILYSM😍*

*24*

    Tana nan a zaune jugum har ya fito daga wanka,  daga bakin kofa ya kalleta fuskar nan a had'e tam yace" me kikeyi har yanzu? "

  Mikewa tai ta d'anyi rau da ido tace " Haba Hubby na taya na ciwo kwalliya dan in birgeka zaka dinga wulakantani haka? Tunda kaga nazo ai kasan hakuri nazo in baka. "

   Ashraf ya wani saki murmushin rainin hankali sannan ya mata wani kallo wanda ita da akawa ita kadai tasan me yake nufi yace " Ko? "

  Tace " bangane ba? "

Ya d'an juya kai gefe yace " ke kina tunanin har kinkai matsayin da zaki tozartani a gaban mutane sannan ki biyo ta baya kice zaki ban hakuri? "

  Aneesa ta d'an canza fuska kad'an tace " Amma Yaya kasan dai ko waye dole yaji haushi,  ko bakasan na dinga kishin ka? "

  Kallanta yai sannan yad'an girgiza kai na takaici hanyar waje ya nuna mata da yatsarsa yace " yi nan. "

  Ta kare lagub'e fuska,  yace " kinfi karfi? "

  Juyawa tai a hankali tai waje tana fita yasama kofar makuli,  tare da jan tsaki.

  Nan ya shafa maganinsa sannan ya shiga kokawar sa kaya,  bayan yasa ma kwanciyarsa yai a kan gado.

    Itakam Aneesa tana fita Habib ya kalleta tare da guntse dariyar datake kokarin tahomai yace " Badai fada kukai ba? "

   Ta kalli Habib kamar zatai kuka sai kuma ta daure tace " a'a kaya zai sa. "

  Habib ya jinjina kai, zama tai a kan kujera shikuma ta mike yai waje, Aneesa ta dade a zaune tun tana irgaminti har ta dawo hour, ganin hour din Ashraf biyu a ciki gashi har bacci yana neman d'aukan ta yasa ta mike kamar ta kurma ihu.

  Abin haushi taje tana kwankwasa kofar Ashraf sai ga Habib ya shigo,  yana ganinta baisan sanda dariya ta zo mai ba.

Aneesa takalleshi cikin kuluwa tace " Abokin Ango meye hakan? "

  Habib ya had'e hannayensa biyu alamar ban hakuri yace " Tuba nake Amarya amma naga kamar fada kukai da Angon."

Aneesa wani takaici ya kara kamata ta kalli kofar Ashraf sannan ta kalli Habib dake juya kai yana d'an dariya haushi yakamata kawai ta tsugunna a gun tasa kukan shagwab'a.

  Kuka take sosai Habib ganin haka ya kara komawa waje.

Ashraf kam wanda kukan duk ya dameshi ya mike jiki a sanyaye ya bud'e kofar,  Aneesa tana jin ya bud'e ta kara sautin kuka.

   Ashraf ya tako a hankali,  ya tsugunna shima tare da sa hannu akan kafad'arta, kamar jira take dama ya tab'a ta kawai ta kankameshi tana kuka,  Ashraf ya shiga kokarin zare jikinsa amma ta kankameshi tamau sai kuka take.

   Ganin bata da niyyar sakinshi yasa ya mike da karfi,  Aneesa ta d'ago fuskarta wacce duk ta b'aci kaca kaca sakamakon kwalliyar datasha,  Ashraf ya dafata yace " Anie na fada miki ba sau d'aya ba kidaina kankameni haka."

  Ta turo baki tace " kai fa mijinane. "

  Ashraf yace " banzama ba tukunna,  sai an d'aura mana tukunna,  sau nawa ina sanar dake hakan? "

  Aneesa ta kara share hawaye tace " Yaya naji to zan daina amma d'an Allah kadaina wahalar da zuciyata. "

  Mikewa yai batare da ya amsa ba ya bud'e kofar d'akinsa yace " zo ki wanke fuskarki. "

  Ta turo baki tace " bakasan kwalliyar? "

  Kai ya girgiza alamar a'a yace " ki shiga kya gani "

  Ta mike zuciya ba dadi tai toilet.
  Tana shiga taga fuskarta a madubi kamar dodo,  da sauri ta matso liquid soap ta shiga wanke wa tana yi tanajin haushin ganinta a haka da Ashraf yai.

      ¤¤¤¤¤¤

  Da yamma bayan little ta dawo Mumy ta sasu a mota suka fita shopping, sunyi siyayyar kayan abincinta sannan aka sai uniforms,  da house wear sannan suka wuce gun mai d'inki,  nan suka bashi sannan suka amshi ragowar sababbin d'inkunenta, wannan kuma akan gobe za'a mata tunda uniform ne bawai style za ai ba.

   Nafi kam kana kallanta zakasan tana cikin farin ciki dan little ma sai tsokanarta takeyi.

  Sun gama komai kafin su nufi hanyar gida,  Little ta kalli Nafi tace " Nafi kinsan Ice cream?"

   Kallan mumy tai wacce tai kamar batajinsu sannan ta kalli Little ta girgiza mata kai alamar a'a.

  Little ta zunguro kusa da Mumy tace " mumy asai mana Ice cream. "

  Murmushi Mumy tai tace " to. "

Nan suka karkata suka gangara 212, Little ta kama hannun Nafi suka shiga ciki, Nafi kam sai sadda kai kasa take,  dama Mumy bata bisu ba tana zaune cikin mota sai dai tabi Nafi da kallo wacce ta ke kula da nutsuwarta tunda suka fito.
Tana jinta sanda suna siyayya tana tab'a Little akan wai duk kayan na makaranta ne?  Ai sunyi yawa ina zata kaisu? Tanaji sai dai Little tai dariya tace "ke dai me ya dameki? "

  Mumy ta saki fuska tabi bayansu da kallo.

  Sukam suna shiga Little ta shiga zab'an abubuwan da zasu siya da yake duk sunayen da turanci take fada yasa Nafi kawai ta zura mata ido tanaji inama itama tasan ke ake cewa?
Sunyi siyayya sosai kafin su fito,  Nafi ta kalli Little tace " ku kam wani irin kud'i gareku?  Na ga sam bakwajin wahalar kashesu. "

  Little ta d'an harareta tace " Ke dai in an miki abu kawai kiyi godiya ki daina cewa ya miki yawa. "

  Nafi bata amsa ba sai dai ta bita da kallo,  nan suka koma mota.

   Mumy ta ja mota suka tafi,  sun isa gida mumy tai parking zasu fito Nafi tace " Mumy angode Allah ubangiji ya kara bud'i."
  Murmushi Mumy tai sannan ta amsa da Amin.

  Zasu fita sai ga Habib da sauri ya karaso,  shiya rike musu kofar motar,  Little kam wani shaukin farin ciki ne ya ziyarci zuciyarta tace " Ya Habib? "

  Yakwantar da kansa a jikin kofar kad'an yace " My Little Princess i really miss u"

   Little wacce zuciyarta ta kara yin haske ta juya fuska cikin shagwab'a tace " bayan yaya ya daina damuwa dani? "

  Habib ya kalli Nafi ba tare daya ba Little amsa ba yace " Nafisa ba magana? "

   Ina wuni ta fad'a cikin sanyin muryarta,  Ya amsa tare da kallan cikin motar yace " Mumy sannu. "

Mumy ta fito tare da cilamai makulli tace " akwai kaya a boot ka tayasu kwasa zuwa b'angarensu. "

  Ya chafe tare da yi mata salute yace " yes maa. "

  Mumy tai gaba,  Little ya kalla yace " Little Princess ba a huce bane? "

   Tace " Yaya Allah kuwa..... "

  Ya katseta tare da had'e hannayensa biyu alamar ban hakuri,  hakan yasa ta kasa karasawa,  itakam Nafi dama tad'an matsa nesa da su kad'an,  jitai Habib yace " To gimbiya sai ki matso mu kwashi kayanki ko? "

  Da mamaki ta juyo tace " Ba dai  nice Gimbiyar ba ko? "

  Habib yai dariya yace " me?  Bakyasan sunan? "

Zatai magana Little tace " Ni Princess ita Gimbiya?  Ya Habib to meye marabarsu? "

  Ya saki dariya yace " Princess ba dai tana kishi ba? "

  Da sauri tace " ni dai bance ba. "

  Nafi itakam ta karaso ta d'au ledoji manya manya ta nufi hanyar ciki,  Habib da sauri ya sha gabanta yace " ta ina mace yarinya kamarki zata iya d'aukan kayan nan? "

  Nafi ta kalleshi tace " zan iya,  kai dai kaba Maryam hakuri. "

   Ya kalli Little sannan ya juyo da niyyar yima Nafi magana sai dai can ya ganta tayi gaba,  ya saki murmushi tare da shafar keyarsa sannan ya koma gun Little.

  A falo Nafi ta tadda Aneesa da kawarta a zaune suna hira,  Nafi ta tsugunna ta gaidasu sannan ta nufi hanyar d'akinsu,  Aneesa ganin manyan ledoji yasa tace " ke zo nan."

  Nafi ta juyo ta kalleta sai dai bata karasa ba,  Aneesa tace " ke munafuka ba dake nake ba? "

  Nafi ta ajiye kayan a bakin kofa ta nufi gunta,  cikin masifa Aneesa tace " da ke da kayan nakesan ganinki. "

Nafi ta koma ta d'auko kayan ta karasa gunta, gyara zamanta tai sannan ta fizgi Ledar da karfinta ta shiga bincikewa,  Nafi kam yau ta kulu,  har ranta sai dataji haushin wannan abun,  tana kallon Aneesa ta juye ledar ma gaba d'aya akan carpet dai dai nan Little ta shigo falon,  mamaki ne ya kamata tace "me kenan? "

  Habib ya karaso shima ya kalli wannam cin mutuncin,  ga Nafi a gefe ta tsugunna,  Aneesa ta bugama Little harara idanta ya rufe ko Habib bata gani ba tace " Little wa aka saima kayan nan? "

  Little ta kalleta rai b'ace tace " Ya Neesa me ya dameki da wanda aka saiwa? "

   Aneesa ranta ya b'aci ga kawarta a zaune a kusa da ita,  tace " mene?"

  Little a zuciye ta karaso tace " Ya Neesa wai meke damunki ne? Taya zakiga kayan mutane kawai ki zubar a kasa? "

  Kawar Aneesa ta kalli Little tace " lalai Little yaushe kika zama mara kunya haka?  Aneesa ba yayarki bace?  Sannan yanzu da kika ganni anan tsara shirye shiryen da za'ai da bikinta da yayanki mukeyi ai ko bata zama matarsa ba ai yayarki ce bare an kusa. "

  Little ta kalleta a kule sai dai ta kasa magana ta kalli Nafi cikin takaici ta wani takure kanta a kasa zatai magana kawai sukaji ance "Tsugunna ki kwashe kayan da kika zubar. "

  Gaban Aneesa ne ya fad'i ta juyo a tsorace,  ba ita ba Little da Nafi ma kofa suka kalla haka ma kawar.

  Ashraf ne a tsaya kana ganinsa kasan ba wasa a fuskarsa,  Little ta kalli Habib wanda ke tsaye daga kofa,  a ranta tace " yaushe ya kira shi? "

  Aneesa ta kalleshi tace " Yaya.... "

  Wani kallo ya mata wanda yasa ta had'iye maganar ta cikin tsawa wacce ta razana kowa dake falon yace " Kowa ya fita."

  Nafi kam jikinta rawa ya kauri dashi,  bata tabajin yayi tsawa haka ba,  Little ta kamata sukai waje a sukwane itama kawar Aneesa da sauri tai waje ta nufi d'akin Umman Aneesa.

  Ya rage daga Aneesa sai Ashraf a d'akin,  ya kara kallanta yace " ba dake nake ba? "

  Idanunta na kansa kallan mamakin dizgata dayai take,  ta daure tace " Yaya ni zaka wulakanta akan Nafi? "

Shi baimasan a hannun Nafi aka anshi kayanba,  shidai Habib yace yazo akwai matsala a b'angaren su Little, da ya iso shine yake cemai Mumy ta siyo kaya Aneesa ta zubar.

   Ashraf ya kara kallanta,  idanunta suka ciciko tace " Yaya kana san ka nunamin ka fifita Nafi akaina kenan ko me? "

  Ashraf ya kalleta cikin tsananin takaici zaiyi magana kawai sai ga Asim da Umma sun shigo cikin masifa........



*THE INNOCENT TEAM*

ZUCIYA.... kowa da irin tasa 25

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
   

*25*

    Nafi wacce little ke janta akan su tafi b'angaren Mumy tana ganin Umma da Aslam sunyi b'angarensu a fusace yasa ta turje tare da kallan Little tace " Maryam wannan abun duk laifinane, kina ganin abun nan yana neman ya zama babba? Sannan ni kuma in gudu?"

   Little ta tsaya itama tare da cewa " Laifinki? Ta ina ya zama laifinki?"
" laifinane mana tunda dai a hununa aka amshi kayan."
Haushi ya kama Little ta rasa Nafi wace irin yarinya ce, ta kalleta tare da dafata tace " Naji a kaddara laifinki ne mai zakiyi in kika koma?"

  " Hakuri zan bada mana kina ganin su Umma sun tafi nasan kowa laifin yaya zai gani." Ta karasa maganar cikin rawar murya.

  Little ta kalleta sai dai ta rasa me ma zata ce mata, gani tai Nafi ta fara tafiya nan ta bita tana mata magiya akan su tafi sai dai itakam gani take gwara taje kawai.

  A falo kuwa Ashraf ne ya had'e rai kamar zai dake Aneesa ita kuma tana tsaye kyam kusa da kaya, ta kalleshi tace " Yaya nice fa?"
Ya buga mata wani kallo yace " kece wa? Ko dama a duniya akwai wanda ya isa inyayi ba daidai ba a kasa hukuntashi?"

  Daga bayansa yaji ance kwarai kuwa, Asim ne yai maganar ya sani shiyasa kuma bai juya ba, Asim ya karaso rai b'ace sannan ya sa hannunsa ta bayan Ashraf iya karfinsa da niyar kai mai duka, Umma tai saurin rike hannun tare da balamai hararra.

   Ashraf ya kalli Aneesa yace " idan kika bari na irga uku acikin raina wlh sai kinyi dana sanin wannan ranar."

  Umma tai charaf tace " ai kuwa sai dai tayi dana sanin dan kaf duniya ba wanda ya isa ya sa 'yata ta kwashi kayan wannan yar kauyen."

Ashraf bai kalli Umma ba haka kuma bai bata amsa ba sai Aneesa da yake kallo yace " kin amince da abinda aka ce?"

  Aneesa ta goge kwallarta tace " yaya me zakayi in na ki kwashewa? Badai cewa zakai ka fasa aurena akan wannan shirman ba?"

  Ashraf ya saki wani mugun murmushi yace " me? Kina ganin bazan iya ba?"

  Kallan mamaki sukamai su duka ukun, Aneesa wacce duk ta gama rikicewa tace " Ya Ashraf me kake fada haka?"

  Ya kalleta yace " in kina tunanin bazan iya ba ki bar kayan nan har na karasa bakin kofa, ni kuma zan nuna miki magana d'aya nakeyi." Nan ya juya

  Aneesa ko kara wata maganar batai ba ta shiga saurin kwashe kaya kamar zata kifa kansu, Ashraf kam ko a jikinsa ya wuce ta jikin Asim ba tare da ko kallan su yayi ba, bai kuma kara duba Aneesa ba dan yasan tabbas zata kwashe kayan nan.

   Ana kai kofa, Nafi wacce ke tsaye jikinta sai rawa yake ta kalleshi a tsorace, bai kulata ba yai wucewarsa, Little ta dafa Nafi tace " Nafi jikinki rawa yake."

  Juyowa Nafi tai cikin tsananin tsoro tace " Maryam wani irin mutum ne yayanki? Da gaske sai ya raba auren nan a dalilin da baikai ya kawo ba?"

  Little tai shiru dan itama abin ya bata tsoro, Nafi ganin haka yasa ta girgiza kai tace " Maryam yayanki na bani tsoro dan ko Baffa banajin tsoronsa kamar yanda nake jin na yayanki."

Little ta dafata tace " yayana yaga rayuwa wanda itace ta maidashi haka, baya tausayin kowa ba kuma ya shakkar kowa, abu d'aya ya tsana kuka bayan wannan banaji akwai abinda ke tab'a mai rai."

  Nafi tabi bayan inda Ashraf yabi da kallo, ace wacce zaka aura kuma kake so ita zaka dizga haka agaban iyayenta da yayanta? Kuma ya juya ya fita kamar ba abinda ya faru?

   Little ce ta katseta da cewa "Nafi ina zuwa."ta juya da sauri.

   A falo kam Aneesa tana ganin fitarsa bayan ta gama kwashe kayan ta tsugunna agun tare da fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi, Umma ta karaso kusa da ita jikinta itama a sanyaye ta jawota jikinta.

  Kuka sosai Aneesa takeyi, Asim ya kalli Umma cikin takaici yace " Umma haka zamu zauna yaron nan yqna ci mana mutunci?"

  Umma ta kalli Aneesa tace " da kinsani baki kwashe ba inga ta karyar iskanci."

Aneesa ta mike daga jikin Umma tace " Umma kamar bakisan Ashraf ba? Kin manta abinda ya faru shekarun baya da suka wuce? Kina sane da ciwon danai tayi a lokacin dayace bazai aureni ba, ya kuma daina kulani."

  Umma tai shiru, Aneesa cikin kuka tace" alokacin bansan ciwon kaina sosai ba, kina tunanin inya fasa aurena yanzu zan iya rayuwa?"

  Asim a kule yace " Dalla yima mutane shiru, sai ki kasa rayuwa dan an rabaki da Ashraf?"

  Aneesa ta harareshi sannan ta mike cikin fushi tana kuka tace " kana tunanin in Ashraf bai aureni ba zai barka a matsayin da kake ne? "

  Asim yai shiru, Umma tace " ya isa, taya za'ai ma muso auren ya rabu ba, kinsan dalili shima Asim d'in ya sani, mu tabbatar mun rufe maganar nan ma kafin Abbanku ya sani."

  Nafi wacce ke tsaye duk taji me suke cewa tai shiru jikinta duk yai sanyi, ta fahimci wani abun amma bata gane wani abun ba.

  Jin alamun zasu fito yasa tai saurin lab'ewa, Umma har tazo kofa ta juya tare da kallan Aneesa tace " karki kara yadda kuyi fada da Ashraf akan wannan kucakar yarinyar wacce riga ma bata fara zama mata ba bare...."

  Ta juya, Nafi ta kalli rigar jikinta cikin ranta tace " bai fara zamamin ba?"

   Ashraf kam yana shiga d'aki ya d'au littafin dake kunshe da wasiyar mahaifinsa ya bud'e wani shafi da mahaifin yace " Babban burina a rayuwa bai wuce na hada aure tsakanin d'ana da 'yar Kanina ba."

  Sannan a kasa aka sa" Ashraf ka taimakeni ka cigaba da kula da zumuncin nan ko bayan raina."

  Kai ya dafa, a cikin ransa yace " Abba meyasa kakesan wad'anda ba sanmu suke ba? Kasan yanda nakeji a raina in na tuna mahaifiyar Aneesa da tawa Mahaifiyar wai kishiyoyi ne?"

  Ya kwantar da kansa a jikin gado, a da bai d'auki wasiyyar nan da wahala ba amma yanzu ya gane tafi komai wahala a rayuwar duniya.




  ☆☆☆☆☆☆☆

   A can garin kachako kuwa D'an litti yana kwance a wani kango duk kayansa sun fara yagewa sai ga wani babban mutum yazo wucewa, ganin mutum kwance a kango cikin rana yasa ya karasa inda yake, hannu yasa ya tab'ashi yace " Bawan Allah me kake anan?"
D'an Litti ya mike zaune a zabure, yace " Wlh I am the one."

  Kallansa mutumin yai sannan yai dariya yace " me kayi kuma?"
Ganin mutum yasa yasan ba mafarki yake ba, ya kalleshi baice komai ba, Mutumin yace " Sunana Malam Kabiru, ina zaune akarshen layin can, kai fa dan naga kamar ba daga nan kake ba."

  Nan D'an litti ya kwashe komai ya fadamai, wani gurin yai dariya wani gun ya tausaya mai, nan yace yazo su tafi gidansa inya tara wani d'an kudin sai ya tafi kano ya nemi Ashraf d'in.

  Sosai D'an litti yaji dadi ya kalleshi yace " Amma ta ina zan tara kud'in?"

  Malam kabiru yai dariya yace " bakace kana tuka babur ba? Sai muje in baka babur d'in yarona wanda yai tafiya ci rani sai ka d'an tara."

  Murna sosai d'an litti ya shiga yi cikin tsananin murna nan suka tashi suka tafi.....

  ☆☆☆☆☆

  An anso d'inkunan Nafi sannan Littl da kanta ta zauna ta dinga mata bayani akan yanda zatai amfani da kayayyakin, sun dad'e sosai a daren ranar suna hira dan gobe akesa ran tafiyar ta, murna kuwa agunsu Aneesa da sukaji ba'a magana.

  Sun nitsa cikin hira Nafi tace " Maryam in na tafi kuma shi kenan ko?"

  Little ta kalleta cikin mamaki tace " shikenan me?"
  A ranta tace " kafin in dawo Ya Ashraf yayi aure mana."

  A fili kuwa sai tace " zamu dade wai bamu had'u ba."

  Little tai dariya tare da gyara zama tace " Nafi inza'ai bikin yaya inzo ni da Ya Habib mu d'aukeki?"

  Nafi ta kalleta cikin mamaki tace " a'a nida na tafi karatu? Sannan shima in yayan yaji ai kinsan fada zaiyi."

  Little ta tab'e baki tace " shi da yaketa hidimar biki inama zai kula dake? Hmm ai ina cin burin bikin nan sosai wlh."

  Nafi ta juya tare da gyara kwanciya tace" hmm."

  Little kam ta zake sai zuba takeyi akan shirin biki, itakam Nafi a kwance kawai take sai eh kawai da take cewa dan itakam ta rasa me yasa batajin dadin hirar ta yanzu......




*THE INNOCENT TEAM*

ZUCIYA....kowa da irin tasa 27

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*Gaisuwa da jinjinar ban girma gareku masoyan arziki, soyayyarku daban take 'yan group d'ina na The Queen Bee da Ayusher Fan Club..... ILYSM💋*

{ *27*}

  Sun fara daga kan farkon karatu wato English Alphabet,Nafi ta zake sosai wajen ganin ta koyi abinda ake koya mata,  sai karfe 5 sannan wannan matar ta mike akan sai gobe a daidai wannan lokacin zasu sake haduwa.

  A galabaice ta dawo hostel yunwa duk ta isheta,  ba kowa a d'akin hakan yasa taji dadi, cornflakes ta had'a ta zauna tasha, jin cikinta ya d'auka yasa ta fito tai alwala tai sallar la'asar.

  Tana zaune a kan sallaya tana kara tisa karatunta a ranta sai gashi 'yan d'akin sun dawo.

  Nan suka mata wani kallo Ferry tace " ke kina nan wato mu muna can an samu wankin toilet ko? "

  Nafi ta kalleta tace " wlh bam sani ba. "

Wacce ta dafata d'azu yanzun ma ita tace " haba Ferry taya za'ayi yarinya tazo yau d'in nan amma kice tai aiki? "

  Ferryn ta kalleta cikin kuluwa tace " Ke Jibiya banasan salon iskanci, meye naki a ciki?  Ko dake nake magana? "

  Wacce aka kira da Jibiya itama cikin fad'a tace " badani kike ba amma hakki nane in fada miki gaskiya sannan ko yanzu kika kara abinda bai dace ba dole ne in fada miki gaskiya koda kuwa zakiji haushina."
Ta ja tsaki a karshen maganarta sannan tai waje a zuciye,  Ferry ta bita da harara tace " Yarinyar nan ta gama rainani wlh. "

  Itakam Nafi tana zaune duk jikinta yai sanyi,ba abinda ta tsana irin taga anyi fad'a a kanta.

  Mik'ewa tai ta kalli Ferry tace " D'an Allah kiyi hakuri." sannan tai waje inda taga waccan ta fita.

Ga mamakinta a zaune taganta cikin mutane suna ta hira da dariya.

  Nafi ta karasa inda take tare da musu sallama,  Jibiya ta d'ago ta kalleta sannan tace " new comer  ya akai? "

  Nafi ta d'an motsa baki alamar tana san magana,  ganin haka yasa ta mike taso kusa da ita,  Nafi ta kalleta tace " Banji dadi ba daga zuwana kuna fada akaina,  d'an Allah kiyi hakuri. "

  Jibiya tasa dariya sannan ta kama hannun Nafi suka zauna tace " Karki damu da wannan,  Ferry yayatace, ubanmu d'aya,  indai fad'a ne irin wannan mun saba. "

  Nafi ta kalleta cikin mamaki tace " Ayya bansani ba. "

  Hannu ta mika mata alamar suyi musabaha tare da cewa " Sunana Aisha Isma'il. "

  Nafi tai murmushi sannan ta mika mata hannu itama tace " Sunana Nafisa Abubakar. "

   Murmushi sukama juna,  Jibiya ta kalleta tace " a kano kike? "
Nafi ta d'aga kai alamar eh,  fara'arta ce ta kara bayyana tace nima haka. "

  Nafi tai murmushi, jibiya tace " Karki damu da Farida ko ince Ferry kamar yanda ake cemata, a ido ne take haka amma a zuciyarta sam mace ce mai saukin kai. "

  Nafi kam murmushi kawai tai,  suna nan a zaune Jibiya na janta da hira sama sama har magrib tayi.
Nam suka mike sukai alwala suka nufi massallaci.

   Washegari bayan sun shirya da safe suka fito aji dukansu 'yan d'akin,  Nafi an shiga cikin Uniform ba laifi tayi kyau dagwas da ita.
Sunshiga aji malamin Math ne ya fara shigowa,  itakam Nafi kawai iya kacinta kallon duk malamin daya shigo dan ko kad'an bata fahimtar kalma d'aya da take fahimta ba.

  Sai dai ta kalli Malami ta kuma kalli alo, haka malamai sukai ta fita wasu na shiga har aka tashi,  itadai tasan kawai dumama benci kawai takeyi.

   ¤¤¤¤¤¤¤¤

  Wani mugun kallo Ashraf ya ma wata kawar Aneesa da sauri ta kalli Aneesa a tsorace, Aneesa ta kalleshi tace "  Hubby me kake nufi?  Events d'in ne bakaso kome?"

  Ashraf ya kalleta yace " Anie kanki d'aya kuwa? Biki kwaya d'aya shine kike neman yin event kusan guda 10? Sannan kina san ni in hallarci guda 8? Akan me? "
  Aneesa ta kalleshi tace " bangane akan me ba?"
  Ya dan rufe ido kad'an sannan yace " tambayar ki ai nake akan me zanje? "

  Kawar Aneesa ta daure tace " Ashraf amma..... "kallan daya mata yasa tajs bakinta tai dif, Aneesa ta mike rai b'ace tace " Yaya meyasa kake min haka?"

  Murmushi ya sakar mata sannan yace " me kuma nai yanzun? "

  Aneesa ta kafeshi da ido ranta duk ya gama b'aci ta daure tace " Ka tab'a ganin mijin daya ce ma matar da zai aura akan me zaije gun bikinsu? "

  Ashraf ya d'an daga kafad'a tare da d'aukan wayarsa ya fara dannawa sannan can yace " kowa da irin zuciyarsa,  sannan dama namiji aka sani dayin kyale kyalen biki ko mace? "

  Aneesa idanunta ns kansa ranta yakau kololuwa gun tashi,  ta bud'e baki zatai magana tags ya d'au waya ya kira wata number sanan taga yaa mike yai cikin d'aki.

  Idanu ta bishi da shi sannan tai waje fuuu,  kawarta ta mike ta biyo bayanta.

  D'akin Umma ta shiga da gudu ba ko sallama,  Umma na zaune tanacin abinci,  Aneesa ta fad'o kanta sannan ta saki kuka.

  Nan Umma duk ta rud'e ta shiga tambayarta abinda ke faruwa,  kawarta ce ta sanar ma Umma komai,  ran Umma ya b'aci sosaii ta kalli Aneesa rai a b'ace tace " Akan haka ne kike kuka?  Ai nasha fad'a miki ki cire san Ashraf aranki kiso kud'insa kawai ba wai shi ba amma nsga alama sam kin kasa fahimtata. "

  Aneesa cikin kuka tace " Umma ya zanyi?  Nafa fad'ama friends d'ina zancen events d'innnan. "

  Umma ya shafa kanta tare da kama hannunta sukai d'aki.

A bakin gado suka zauna,  Umma ta kalleta tace" ki rage events d'in daga goma zuwa bakwai,  a wannan lokacin kibar Ashraf ya sami duk abinda yakeso,  karki kuskura ki b'ata masa rai har zuwa lokacin da zai aureki ki amshi wasiyyar mahaifinsa. "

   Aneesa ta kalli Umma sai dai batace komai ba,  Umma ta cigaba "a sanda kika samu kansa kikasan ya gama mutuwa akanki lokacin ne zamu samu ya barma yayanki company d'insa."

  Aneesa da mamaki tace "Umma taya zanso mijina yabarma Yayana Company d'in mahaifinsa? "

  Umma tai wani tsaki na kulawar tace " Aneesa ke yarinyace bazaki tab'a fahimta ba,  alokacin da Ashraf ya amshi aikinsa,  dukiya da aiki suka fara mai yawa kina tunanin zai samu lokacin ki? "

  Aneesa ta girgiza kai,  Umma ta dafata tace " Aneesa kiyi tunani dakyau a haka ma mutumin da ba aiki yake ba baya ganin wani darajarki bare kunyi aure?  Yana ganin shi ke da iko dake? "

  Aneesa tai shiru sai dai Umma ta tabbatar kalamanta sun ratsa Aneesa sosai......

   Nan ta mike ta barta a d'akin,  shiru Aneesa tai tana tunani kalakala da wulakancin da Ashraf ke mata duk suna dawowa cikin zuciyarta, kwanciya tai akan gadon zuciyarta na mata sake sake kala kala......

¤¤¤¤¤¤

  Yau satin Nafi d'aya a makaranta,  har a wannan lokacin itadai bata fahimtar me ake a aji,  sai dai tana kokari sosai a gun karatun da ake koya mata.

  Yau aka kawo musu wani sabon malami na Computer bayan yayi introducing d'in kansa ne ya fara tashin mutane one by one dan tabbatar da abinda suka sani a gun waccan malamin nasu.

  "Ke tashi." abinda Nafi taji malamin ya fad'a kenan idanunsa ns kanta, a tsorace Nafi ta kalleshi sai da ya kara ce mata ta tashi kafin ta mike jikinta duk ya fara rawa,  Malamin ya kalleta yace "List 3 input of computer."

  Nafi ta zare ido cikin tsoro,  'yan aji kam gani sukau ba wanda ya samu saukin tambaya irin tata.

  Nafi tai shiru sai wasa da hannunta data shiga yi, zufa sai keto mata take a cikin jikinta.

  Ran malamin yakai kololuwa gun tashi gani yake kamar yamata tambayar yara taya za'ai wannan tambayar ta gagari 'yar Js 3?

  Ranshi ya b'aci yace " get out. " ya fad'a tare da nuna mata hanyar waje.

  Batasan me yace ba sai dai ganin ya nuna da hannu yasa ta had'a hannayenta biyu tashiga bashi hakuri.

Dariya 'yan aji suka saka mata,  ran Malam ya kara b'aci ganin taki fita, a zuciye ya d'au bulsla ya fara zuba mata,  Nafi kam ta daku sannan yace " ya bata nan da sati d'aya zai kirata a gaban class ya mata tambayoyi,  inta kuskura ta kasa to wlh ba shakka sai tayi dana sani mai tsanani."

Nafi kam zama kawai tai tana hawaye.......

Ni kaina ganin halin da Nafi take ciki sai dayasa hannuna ya fara rawa wanda na kasa cigaba da rubutun nan......


*LYSM MY FANS*😍😍😍😍

*THE INNOCENT TEAM*