Friday, 19 May 2017

ZUCIYA.....kowa da irin tasa 28

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*Hi Fans please Vote me on Wattpad As_AyusherMohd*

{ *28*}

Nafi kwance a saman gado,  ba shakka taji zafin dukan da aka mata sosai,  ita kad'ai ce a d'akin tana kwance Ferry ta shigo,  kasancewar ba magana take mata ba yasa Nafi tace " Sannu da dawowa. "

  Kallan da Ferry ta mata yau ba kamar yanda ta saba mata ba,  wato kallan banzan data saba ba,  yau kallanta tai cikin mutunci,  Nafi tai murmushi sannan ta gyara kwanciyarta,  jitai Ferry tace " Nafisa ya akai kika kasa bada amsa d'azu? Baici ace duk dakikantarki kinkasa ba. "

  Nafi ta mike zaune sannan ta kalleta fuskarta cikin farin ciki,  tace " Bansan amsar na Ferry. "

  Ferry ta shiga cire kayanta tana  cewa " to in dai haka ne lalai zakici doka a gun malamai, ya kamata ki samu Jibiya ta koya miki tun kafin a gama raina ki. "

  Nafi ta jinjina kai cikin farinciki tace " Nagode Ferry. "

Ferry ta harareta tace " karkiyi tunanin sanki nake yanzu,  ni bana kawa da wacce bata kile ba,  bana kawa mara kwalliya,  ba kuma na kawa mara aji. "

  Nafi ta sauko daga sama tace " Ferry nikam kina burgeni wlh,  duk da ba kulani kike ba inasan tsarinki yana birgeni. "
  Ferry ta d'aura towel sannan tace " abinda yake b'atamin rai kenan da mata irin ku,  sam bakwa abin mace,  bakwa kwalliya,  yanzu kamar ke sam duk abinda mutum zai miki ban taba ji kin d'aga ma wani murya ba,  komai sai dai ki  bada hakuri,  ke ba dutse ba."
Taja tsaki ta zari kwandon wankanta tai waje.

   Nafi ta bita da kallo ba shakka abinda ta fad'a gaskiya ne,  to amma ya zatai?  Bayan haka halinta yake?

  A satin nan Nafi har sai da ta rame tsabar karatu kala biyu,  ga na lesson d'in da ake mata gana computer, a wannan zaman karatun da jibiya take koya mata anan ta fahimci Nafi batai wani karatu ba ganin duk yanda taso tai pronounce d'in kalmomi abun yake gagara,  sai dai hakan yasa ta kara tausayama Nafi sannan ta jajjirce wajen kara koya mata.

   Yanzu kam suna 'yar magana sama sama da Ferry.

  Sati d'aya ya cika,  malam ya kira Nafi gaban black board ya shiga zuba mata tambaya,  tambaya 5 ya mata da kyar Nafi ta amsa biyu,  wannan dalili yasa Malam ya yanke mata hakunci akan ta dawo gaba kusa da Ferry da zama sannan duk karshen week sati biyu zai dinga mata tambaya.

  Nafi kam duk ta rame saboda karatu,  sam bata samun damar tunanin gida ko wani abu,  sai dai ta rasa dalili duk sanda ta tashi daga bacci sai zuciyarta ta rage mata kwana d'aya akan kwanakin bikin Ashraf.



   *A KANO*

  An kai lefe sannan anata hidimomin biki, sai dai sam Ashraf abin nan baya gabansa,  tabbas yasan a ransa yanasan Aneesa sai dai bayajin wani farin ciki game da wannan auren.

  Ita kad'ai take kid'anta take rawarta,  duk dinkunansa sai Habib ta samu sukaje suka siyo,  sam Ashraf baya walwala bare farincikin wannan auran.

  Duk yanda Aneesa taso daurewa karta nunamai jin haushinta sai data kasa tamai magana,  sai dai duk sanda tamau magana kanta abin yake komawa, karshe tazo tana bada hakuri.

  Gida ya fara taruwa da mutane,  little kam sai rawar kai dinkuna tayi yakai kala 10 ta musu kuma anko da Nafi kala 5, murna kam ba'acewa komai agunsu Umma.


  Yau saura kwana biyu a fara hidimomin biki Mumy ta kira Ashraf zuwa falonta,  bayan ya zaunane Mumy ta kalleshi cikin kuluwa tare da tattara hankalinta kansa, ta fara magana cikin kulawa " Ashraf yau saura kwana biyu a d'aura maka aure da 'yar uwarka."

  Ashraf kansa na kasa sai dai baice komai ba,  tace " Muhammad! "
D'agowa yai cikin mamaki dan bai tab'aji ta fad'i wannan sunan ba d'an sunan baban mahaifinsa ne.

  Mumy ta kalleshi tace " kayi hakuri abinda na maka. "

  Kallan mamaki yake binta dashi, yace "name? "

Ta kalleshi idanunta a raunane tace " Ashraf na sani sarai abinda na maka shekarun baya masu yawa shine yasa ka zama haka,  sam bakasan 'yan uwanka,  kanka kawai ka sani,  ba ka tunanin maganar da zaka fad'a ko zai b'atama wani rai. "

  Ashraf dai kallanta kawai yakeyi,  Mumy tai ajiyar zuciya tace " bazaka tab'a fahimtar me yasani na auri kanin mahaifinka ba daga rasuwar Abbanka ba har sai lokacin da kasan komai na gidan nan da kuma abinda ke cikin zuciyar kowa na gidan nan. "

  Ashraf da mamaki yace " Mumy. "

Ta sakar masa murmushi tace " na sani nayi laifi a gareka,  na rashin sanar dakai komai danai har sai sanda aka haifi Little, sai dai inaso ka sani komai nai a rayuwa to tabbas d'an kai nayi shi,  ban tab'ayin wani abu dan in farantawa kaina rai ba,  a ko da yaushe kai nake fara sawa a gaba akan komai na rayuwata kafin inyi tunanin kaina. "

  Shiru tai sai dai ta kawar dakanta gefe kad'an alamar so take ta b'oye kwallar ta, Ashraf kam kalaman Mumy sun tab'ashi sai dai haryanzu gani yake koma meye dalili shi bai fahimci dalilin auranta da kanin Abbansa ba."

  Mumy ta d'anja hanci sannan tace " Mahaifinka na tsananin san kaninsa,  sannan babban burinsa bai wuce yaga ya had'a zuri'a dashi ba,  nasani da yana da rai sai yafi kowa farin cikin wannan abun duk da yasan shi kanin nasa ba sanshi yake ba. "

  Ashraf ya kalleta cikin mamaki yace " Mumy me kike nufi da basanshi yake ba? "

Mumy tai murmushi tace "la ba haka zan fad'a ba subutar harshe nai. "

  Ashraf yai shiru sai dai tabbas yasan da wani abu.

  Mumy tai saurin wayancewa da cewa " Ashraf kasan me ake nufi da aure ba sai na sanar dakai ba dan Allah ka rike matarka yanda ya dace,  Aneesa na sanka kowa ya sani. "

  Ashraf bai amsa hakan yasa Mumy tace " Ashraf maganar aiki. "

  Kallanta yai sannan ya daure yace " Mumy me yasa kike so im fara aiki a company d'in Abba? "

  Mumy tace " saboda hakkinka ne."

  Ashraf yai murmushi yace " idan na fara aiki a wani matsayi kawu zai zauna?  Sannan ni a wani matsayi employees na company d'in zasu d'auken?"

  Mumy da mamaki tace " Ashraf me kake nufi? "

  Yai murmushi sannan yace " zan fara aiki a company d'in Abba sai dai bawai a matsayina na magaji ba inasan ne in amshi hakkina da kokarina bawai dan ni d'an Abba bane. "

  Mumy ta jinjina kai tace " kana nufin zaka fara aiki a company d'in daga farko?  Tun daga kan interview?"

  Kai ya d'aga Mumy tai murmushi lalai ta yaba da tunanin d'an nata ta sani sarai dama yanada hangen nesa sai dai bata tab'a tunanin zaiyi tunani haka ba.

 

   ¤¤¤¤¤¤

  Nafi ce zaune tana shafa mai Ferry ta kalleta tace " Nafi yau tunda kika tashi naga kamar bakida lafiya. "

  Nafi ta kalli Ferry tace " Ferry dan Allah tambaya. "

Kai Ferry ta d'aga mata alamar eh tanaji.
"Yayanane zaiyi aure a satin nan,  na rasa meke damuna sam duk sanda na tuna sai inji raina yana b'aci. "

  Ferry ta kwashe da wani dariya tace " Innocent Feenah dama haka kike?  Oh a ido kamar.... " 

Nafi tace " ban gane ba,  wani abun ne? "

  Ferry ta fara tafi tace " Innocent girl,  yayan naki uwa d'aya kuke ko uba? "

  Nafi ta girgiza kai,  Ferry ta kara sa dariya sannan tace " gaskiya Feena kin tashi daga Innocent kin koma green snake. "

  Nafi ta mata kallan mamaki tace " ni na tambayeki abu ma baki amsa min ba kin bige da dariya. "

  Ferry tace " Good haka nakesanki in abu bai miki ba ki fito ki fad'i gaskiya,  sannan zancen yayanki ai ba komai bane sanshi kawai kike. "

  Da sauri Nafi ta mike ta zura hijab d'inta tai waje tana cewa " Ni?  Wacce ni?  Ni kaza?????



*THE INNOCENT TEAM*

1 comment: