*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
*25*
Nafi wacce little ke janta akan su tafi b'angaren Mumy tana ganin Umma da Aslam sunyi b'angarensu a fusace yasa ta turje tare da kallan Little tace " Maryam wannan abun duk laifinane, kina ganin abun nan yana neman ya zama babba? Sannan ni kuma in gudu?"
Little ta tsaya itama tare da cewa " Laifinki? Ta ina ya zama laifinki?"
" laifinane mana tunda dai a hununa aka amshi kayan."
Haushi ya kama Little ta rasa Nafi wace irin yarinya ce, ta kalleta tare da dafata tace " Naji a kaddara laifinki ne mai zakiyi in kika koma?"
" Hakuri zan bada mana kina ganin su Umma sun tafi nasan kowa laifin yaya zai gani." Ta karasa maganar cikin rawar murya.
Little ta kalleta sai dai ta rasa me ma zata ce mata, gani tai Nafi ta fara tafiya nan ta bita tana mata magiya akan su tafi sai dai itakam gani take gwara taje kawai.
A falo kuwa Ashraf ne ya had'e rai kamar zai dake Aneesa ita kuma tana tsaye kyam kusa da kaya, ta kalleshi tace " Yaya nice fa?"
Ya buga mata wani kallo yace " kece wa? Ko dama a duniya akwai wanda ya isa inyayi ba daidai ba a kasa hukuntashi?"
Daga bayansa yaji ance kwarai kuwa, Asim ne yai maganar ya sani shiyasa kuma bai juya ba, Asim ya karaso rai b'ace sannan ya sa hannunsa ta bayan Ashraf iya karfinsa da niyar kai mai duka, Umma tai saurin rike hannun tare da balamai hararra.
Ashraf ya kalli Aneesa yace " idan kika bari na irga uku acikin raina wlh sai kinyi dana sanin wannan ranar."
Umma tai charaf tace " ai kuwa sai dai tayi dana sanin dan kaf duniya ba wanda ya isa ya sa 'yata ta kwashi kayan wannan yar kauyen."
Ashraf bai kalli Umma ba haka kuma bai bata amsa ba sai Aneesa da yake kallo yace " kin amince da abinda aka ce?"
Aneesa ta goge kwallarta tace " yaya me zakayi in na ki kwashewa? Badai cewa zakai ka fasa aurena akan wannan shirman ba?"
Ashraf ya saki wani mugun murmushi yace " me? Kina ganin bazan iya ba?"
Kallan mamaki sukamai su duka ukun, Aneesa wacce duk ta gama rikicewa tace " Ya Ashraf me kake fada haka?"
Ya kalleta yace " in kina tunanin bazan iya ba ki bar kayan nan har na karasa bakin kofa, ni kuma zan nuna miki magana d'aya nakeyi." Nan ya juya
Aneesa ko kara wata maganar batai ba ta shiga saurin kwashe kaya kamar zata kifa kansu, Ashraf kam ko a jikinsa ya wuce ta jikin Asim ba tare da ko kallan su yayi ba, bai kuma kara duba Aneesa ba dan yasan tabbas zata kwashe kayan nan.
Ana kai kofa, Nafi wacce ke tsaye jikinta sai rawa yake ta kalleshi a tsorace, bai kulata ba yai wucewarsa, Little ta dafa Nafi tace " Nafi jikinki rawa yake."
Juyowa Nafi tai cikin tsananin tsoro tace " Maryam wani irin mutum ne yayanki? Da gaske sai ya raba auren nan a dalilin da baikai ya kawo ba?"
Little tai shiru dan itama abin ya bata tsoro, Nafi ganin haka yasa ta girgiza kai tace " Maryam yayanki na bani tsoro dan ko Baffa banajin tsoronsa kamar yanda nake jin na yayanki."
Little ta dafata tace " yayana yaga rayuwa wanda itace ta maidashi haka, baya tausayin kowa ba kuma ya shakkar kowa, abu d'aya ya tsana kuka bayan wannan banaji akwai abinda ke tab'a mai rai."
Nafi tabi bayan inda Ashraf yabi da kallo, ace wacce zaka aura kuma kake so ita zaka dizga haka agaban iyayenta da yayanta? Kuma ya juya ya fita kamar ba abinda ya faru?
Little ce ta katseta da cewa "Nafi ina zuwa."ta juya da sauri.
A falo kam Aneesa tana ganin fitarsa bayan ta gama kwashe kayan ta tsugunna agun tare da fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi, Umma ta karaso kusa da ita jikinta itama a sanyaye ta jawota jikinta.
Kuka sosai Aneesa takeyi, Asim ya kalli Umma cikin takaici yace " Umma haka zamu zauna yaron nan yqna ci mana mutunci?"
Umma ta kalli Aneesa tace " da kinsani baki kwashe ba inga ta karyar iskanci."
Aneesa ta mike daga jikin Umma tace " Umma kamar bakisan Ashraf ba? Kin manta abinda ya faru shekarun baya da suka wuce? Kina sane da ciwon danai tayi a lokacin dayace bazai aureni ba, ya kuma daina kulani."
Umma tai shiru, Aneesa cikin kuka tace" alokacin bansan ciwon kaina sosai ba, kina tunanin inya fasa aurena yanzu zan iya rayuwa?"
Asim a kule yace " Dalla yima mutane shiru, sai ki kasa rayuwa dan an rabaki da Ashraf?"
Aneesa ta harareshi sannan ta mike cikin fushi tana kuka tace " kana tunanin in Ashraf bai aureni ba zai barka a matsayin da kake ne? "
Asim yai shiru, Umma tace " ya isa, taya za'ai ma muso auren ya rabu ba, kinsan dalili shima Asim d'in ya sani, mu tabbatar mun rufe maganar nan ma kafin Abbanku ya sani."
Nafi wacce ke tsaye duk taji me suke cewa tai shiru jikinta duk yai sanyi, ta fahimci wani abun amma bata gane wani abun ba.
Jin alamun zasu fito yasa tai saurin lab'ewa, Umma har tazo kofa ta juya tare da kallan Aneesa tace " karki kara yadda kuyi fada da Ashraf akan wannan kucakar yarinyar wacce riga ma bata fara zama mata ba bare...."
Ta juya, Nafi ta kalli rigar jikinta cikin ranta tace " bai fara zamamin ba?"
Ashraf kam yana shiga d'aki ya d'au littafin dake kunshe da wasiyar mahaifinsa ya bud'e wani shafi da mahaifin yace " Babban burina a rayuwa bai wuce na hada aure tsakanin d'ana da 'yar Kanina ba."
Sannan a kasa aka sa" Ashraf ka taimakeni ka cigaba da kula da zumuncin nan ko bayan raina."
Kai ya dafa, a cikin ransa yace " Abba meyasa kakesan wad'anda ba sanmu suke ba? Kasan yanda nakeji a raina in na tuna mahaifiyar Aneesa da tawa Mahaifiyar wai kishiyoyi ne?"
Ya kwantar da kansa a jikin gado, a da bai d'auki wasiyyar nan da wahala ba amma yanzu ya gane tafi komai wahala a rayuwar duniya.
☆☆☆☆☆☆☆
A can garin kachako kuwa D'an litti yana kwance a wani kango duk kayansa sun fara yagewa sai ga wani babban mutum yazo wucewa, ganin mutum kwance a kango cikin rana yasa ya karasa inda yake, hannu yasa ya tab'ashi yace " Bawan Allah me kake anan?"
D'an Litti ya mike zaune a zabure, yace " Wlh I am the one."
Kallansa mutumin yai sannan yai dariya yace " me kayi kuma?"
Ganin mutum yasa yasan ba mafarki yake ba, ya kalleshi baice komai ba, Mutumin yace " Sunana Malam Kabiru, ina zaune akarshen layin can, kai fa dan naga kamar ba daga nan kake ba."
Nan D'an litti ya kwashe komai ya fadamai, wani gurin yai dariya wani gun ya tausaya mai, nan yace yazo su tafi gidansa inya tara wani d'an kudin sai ya tafi kano ya nemi Ashraf d'in.
Sosai D'an litti yaji dadi ya kalleshi yace " Amma ta ina zan tara kud'in?"
Malam kabiru yai dariya yace " bakace kana tuka babur ba? Sai muje in baka babur d'in yarona wanda yai tafiya ci rani sai ka d'an tara."
Murna sosai d'an litti ya shiga yi cikin tsananin murna nan suka tashi suka tafi.....
☆☆☆☆☆
An anso d'inkunan Nafi sannan Littl da kanta ta zauna ta dinga mata bayani akan yanda zatai amfani da kayayyakin, sun dad'e sosai a daren ranar suna hira dan gobe akesa ran tafiyar ta, murna kuwa agunsu Aneesa da sukaji ba'a magana.
Sun nitsa cikin hira Nafi tace " Maryam in na tafi kuma shi kenan ko?"
Little ta kalleta cikin mamaki tace " shikenan me?"
A ranta tace " kafin in dawo Ya Ashraf yayi aure mana."
A fili kuwa sai tace " zamu dade wai bamu had'u ba."
Little tai dariya tare da gyara zama tace " Nafi inza'ai bikin yaya inzo ni da Ya Habib mu d'aukeki?"
Nafi ta kalleta cikin mamaki tace " a'a nida na tafi karatu? Sannan shima in yayan yaji ai kinsan fada zaiyi."
Little ta tab'e baki tace " shi da yaketa hidimar biki inama zai kula dake? Hmm ai ina cin burin bikin nan sosai wlh."
Nafi ta juya tare da gyara kwanciya tace" hmm."
Little kam ta zake sai zuba takeyi akan shirin biki, itakam Nafi a kwance kawai take sai eh kawai da take cewa dan itakam ta rasa me yasa batajin dadin hirar ta yanzu......
*THE INNOCENT TEAM*
No comments:
Post a Comment