Tuesday, 9 May 2017

Zuciya.... Kowa da irin tasa 20

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*_Hakika bani da bakin da zan muku godiya, nagode kwarai da so da kaunar da kuka nunamin, ina kara godiya ga masu min ta'aziya ta waya, ta text,  da ta chat nagode kwarai Allah ubangiji ya barmu tare......_*

   2⃣0⃣

      Shiru Ashraf yai  a mota bayan sun fito daga Asibiti, tunani yake mai zurfi ina zai sa Nafi a makaranta?  A kalaa dai shekarunsu d'aya da Little banbancinsu dai Little nada d'an jiki sai dai Nafi siririyace sosai sai tsayi,  ko alphabet bata iya ba.

   Ya d'an juya kai,  ina zai sata? Yarinyar nan dai bamai ansarta ko Js1 ne to a hakan ma Js1 ya mata kankanta saboda ita ba yarinya bace,  yai d'an karamin tsaki lalai Malam dama wahala ya d'auramai.

  Sam baiji sanda Driver yake ta cemai Oga ina zamu?
  Can bayan ya gama tunani ya kalli Adamu yace "Adamu me muke jira kuma? "

  Adamu ya dan saki fuska yace " tun d'azu nake tambayar inda zamu banji kace komai ba. "
Tsaki ya kara ja sannan yace "Mu tafi gida,  tunani ne suka min yawa. "

   A gida kam kan kace me kowa yasan abinda Ashraf yama Aneesa akan wasiyyar da za'a bata, duk ta yad'ashi tana fadama mutane tana kukan sakalci,  anyi carko carko a waje kowa nata fada'an albarkacin bakinsa, sai dai kaf Ashraf suke bama laifi gani suke ai ta cancanci abata ta gani,  dan ankusa d'aura musu aure.

   Mumy kam tana d'aki abin duniya ya dameta itakam ba abinda ta tsana irin taji ance Ashraf yayi abu.

    Tun da suka shigo Ashraf ya fuskanci da matsala sai dai har sukai parking ya fito bai nuna komai ba,  ba kuma yasan ya san meke faruwa,  direct hanyar banharensa ya nufa, suna daga tsaye ko kallan inda suke baiyi ba, Ga Aneesa da su Umma suma daga d'an gefe.

  Asim ne cikin kuluwa yace " Ashraf bakaga dan kai muke tsaye ba? "

  Kallansu yai ya saki wani mugun smiling na rainin hankali yace " Da alama tsayuwar domin ni tana muku dadi ne. "
Ya ci gaba da tafiyarsa,  a xabure Asim da kannansa suka matso inda Ashraf yake,  Asim ya tafi a zuciye zai shake Ashraf,  saura kiris ya karaso Ashraf yace " D'an daba muka samu a gidan?  Ka tabbatar kasan me kake shirin yi kafin a samu matsala. "

  Jin haka yasa kannensa sukai saurin tare Asim d'in shikam sai hucci yake,  ya nuna Ashraf yace " Dan kut........ Kai har ka isa kasa kanwata kuka?"

  Kallan inda su Umma suke yai sai a lokacin ma ya kula da su,  cikin zuciyarshi kwarai takaici ya lulube shi sai dai murmushi ya sake saki yace " Kanwarka?  Sai kai azama ka bata hakuri sannan kai gaggawar yi mata kashedi akan zubar da hawaye akan wani bare. "

  Ran Asim ne ya kara dugunzuma,  yanzu kam har kannansa abin ya kular dasu,  Aneesa ta matso, Ashraf ya d'an buga mata wani kallo sannan ya kalli Asim fuskarsa a sake sosai kamar ba'amai komai ba yace " Ya?  Gatannan sai ka tambayeta me baren nan ya mata. "

  Asim ya kalli Ashraf cikin masifa yace " kai dan rashin mutunci baza ka bata wasiyyar mahaifinka ba?  Ko dan tsabar mugunta rikewa zakai?  Oh andaiji jiki uba ya mutu ya bar wasiyya amma d'a ya kasa......"

   Kasa karasawa yai saboda ganin Ashraf yana murmushi harr hakoransa suka fito, cikin tsananin takaici ya kalli Ashraf yace " kut!  Dariya ma na baka? "

   Ashraf ya juya kai tare da shafar kasan kansa da hannun da baya mai ciwo yace " Uba?  Sai kuma ka manta wannan Uban nawa ne ko?  Sannan banaji a wasiyyarsa yace inba matar da ban aura ba ko? "

  Aneesa ta matso kusa dashi tace " Yaya?"

  Matsawa yai daga kusa da ita baice musu komai ba ya juya ya fara tafiya,  sai dai abin mamaki kasa cemai komai sukai sai Aneesa data bishi da sauri,  tana kiranshi.

  Ko Kallanta baiyi ba,  ransu Umma ya sake b'aci,  yana shiga falonsa ta bishi itama tace "Hubby? "

  Matsowa ya farayi inda take harta isa jikin bango yasa hannunsa ya matseta har sai datai dan kara,  sannan yace " wlh ki shiga hankalinki, inkikai wasa Wlh kinji na rantse duk sanda nake miki sai in ajiye maganar auranki,  kinfi kowa sannin ni Ashraf nafi karfin mace ta wulakantani ko ta juyani. " saketa yai sannan yai d'akinsa.

  Da kallo ta bishi dashi, wani mugun tsoro ne ya shigeta,A tsorace tai waje.

    Ashraf kam yana shiga d'aki ya durkushe agun,  kafad'arsa har kasan hannunsa banda azabar zafi ba abinda yake ji,  d'ayan hannun yasa da niyyar sa magani,  sai dai ina jin gun yai ya kara kumbura,  ya tuna abinda likita yace mai.

"Ashraf a ina ka bugu haka? "
Da mamaki yace" ni ban bugu ba kawai da daddare ciwo ya tashi min."

   Likitan yai shiru can yace " A 'yan kwanakin nan baka bugu ba? "

  Ashraf ya kalleshi yace " na dai d'an sanu karamin accident to daga nan ina d'anjin gun ba dadi to amma bawai ciwi ya kemin ba. "

   Likitan yai d'an ajiyar zuciya yace " Ashraf ya akai haka?  Me yasa bakazo checkup ba bayan abin? "

   Ganin bashida niyyar magana yasa ya mik'e ya bashi magunguna,  sannan yace " a sa  tsuma a ruwan zafi a dinga matsewa ana gasa ma gun,  sai a shafa wannan. "

   Asharf ya amsa,  yacigaba "wannan kuma na had'iya ne. "

   Nan ya bashi kud'inshi Ashraf ya mike,  har ya fara tafiya likitan yace " Ashraf ka tabbatar an gasa ma sannan karkai amfani da jikinka sosai. "

Nan yai gaba, ta ina zai iya gasa gun da kansa? Gashi sunyi fada da waccan yarinyar,  shikuma kaf mazan gidan bayaji akwai wanda zai iya kira.

   Wayarsa ya d'aga ya dannan number Little yana fatan Allah yasa ta dawo.
Daga can b'angaren Little wacce ke kwance batajin dadi ta daga,  bayan tagaisheshi bai amsa ba kawai yace "little kizo yanzu. "

  Abinda ya fada kenan ya kashe,  little wacce da alama ciwon mara take ganin yanda take a durkushe sai dai ita batasan meke damunta ba,  ta kalli Nafi wacce ke xaune kusa da ita duk ta rikice kamar ita take ciwo.

   Tace "Nafi dan Allah jeki yayane ke kirana nikuma kinga cikina murd'amin yake. "

Nafi ta kalleta daa idanunta da sukai raurau tace " taya zan tafi in barki? "

   Little tace " naji muryar yayan ma kamar......"

   Ai Nafi da sauri ta mike batama jira karashen zancen ba tai waje da sauri, ganin saurin bai mata ba ga ba mutane agun yasa tadan sa gudu,  tabbas ciwonsa ne ya motsa abinda kawai tasa a ranta kenan.

   Sam bata kula da Asim ba wanda ke kokarin shawo kwana ita kuma zata mike,  dayake gudu takeyi iya karfinta kuwa ta bangaje shi,  Asim ya juyo cikin tsananin mamaki ganin wani kwararen ne?

  Nafi kam jikinta ya fara tsuma ta kalleshi a tsorace tace " Yahkuri yaya dan Allah. "

Asim ya d'ago da niyyar masifa,  sai dai me?  Can ya ganta ta mai nisa sai sauri take, ta sani bazai kyaleta ba sai dai yanzu abu d'aya ne a gabanta ba kuma taji akwai abinda zai tsayar da ita.

    Tana murd'a kofar tajishi a bud'e nan ta shiga ta fara sallama,  jin shiru cikin tsoro kawai ta dannu ciki,  baya falo hakan yasa ta wuce d'akin shi.

   A zaune yake a kasa ya kifa kansa akan gado, ba riga a jikinsa sai dogon wando hakan yasa Nafi ta juya baya da sauri,  a hankali tace "Yaya ga...... "

  Yanda yakeji yasa bai bari ta karasa ba ya katseta "Little yi sauri ki d'au roba a toilet ki taro ruwan zafi ki sa tsuma a ciki kizo ki dinga matsewa kina gasamin gun nan. "

   Nafi ta juyo a hankali tana san cemai ba little bace tace " Ya.... "

"Little wuce mana"

Jiki a sanyaye Nafi ta wuce toilet yanzu ta iya kunna famfo ta kuma san inda ruwan sanyi dana zafi yake,  nan ta tara a roba ta saka towel karami dake rataye a ban d'akin ta fito,  ganin yanda ya kifa kansa ko d'agowa baiyi ba yasa tasan yanajin zafin gurin,  kallan gun tai taga ya kara tashi ba kamar da safe ba,  idanunta ne suka fara cicikowa,  ta karasa a hankali tai kneel down ta bayansa ta fara matsewa tana gasa mai gun,  dun sanda tasa sai taga ya d'an motsa kad'an.
 
  Kamar a jikinta takejin ciwo nan,  intaga ya motsa sai ta runtse ido.

  Asim kam wanda ransa yakai kololuwar tashi ya tsaya ya d'auka yanzu zata dawo yaci mutuncinta, jin shiru yasa yabi bayanta a kufule.

   Bud'e kofar yai a zuciye yai ciki,  me zai gani????? Me kuma idanunsa suke gane mai??????? 
Tofah!  Babbar magana........

   ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤

A b'angaren su Datti kam haka sukai ta yawo suna neman taimako,  kayan da maman hanne tazo dasu suma sai siyarwa tai.

  Da kyar suka hada kudin mota suka koma Gwaram.....

  ¤¤¤¤¤¤¤

  Shikam d'an litti ya musu bayani har ya gaji amma ina... Sunce dole sai ya fada musu wanda ya sani yazo yayi bailing shi.

  D'an litti yace " ku nemo min Ashraf. "

Officer yace " Ashraf wa?  A ina yake?  Meye number wayarsa? "

To fa!  Da masifa D'an litti yace  " nidai ba na fada muku ba?  Sunanshi Ashraf a kuma kano yake. "

  Officer yace " me kake nufi to?  So kake mu shiga kano mu fara neman masu suna Ashraf ko me? "

   D'an litti takaici ya kamashi ya zauna a cell d'in kamar yasa ihu,  gashi sunce inya sake musu turancin nan nasa sai sun fasamai kai........

*THE INNOCENT TEAM**ZUCIYA*

*THE INNOCENT TEAM*

No comments:

Post a Comment