*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*Where are u my Cwt Nafeesa? Ur page is here!!! Hope banyi late ba? Happie Birthday dear wish u long life and prosperity.....*
1⃣8⃣
Duk yanda Nafi taso ta kwantar da hankalinta ta kasa, ganin azahar tayi tai sallah dan yanzu ba laifi Little ta koya mata duk da suratul Iklas kawai ta iya ko hijab d'in datai sallah bata cire ba tai waje da sauri, knocking tai ganin ba'a bud'e ba yasa tasa makuli ta bud'e.
Ko kofar bata rufe ba ta shiga da sauri tana fatan Allah yasa ba wani abun bane ya sami Ashraf.
D'akinsa ta nufa kofar nanan a bud'e kai tsaye tai nufin shiga sai dai me? Aneesa ta gani zaune kusa da Ashraf ta rike plate a hannunta ta d'ebi Faten dankali tana kokarin kai bakinsa, da sauri ta matsa daga kofar ta tsaya a jikin bango, hannu.
Ashraf yasa da niyar amsar cokalin ta noke kafad'a tace " ni zan baka Hubby. "
Kallan mamaki ya mata, ta kashe mai ido cikin salo tace " daga yau na daina cema Yaya tunda bikinmu ya matso, Hubbyna zan dinga kiranka. "
Ashraf baice komai ba sai kula da hijab dayai a bakin kofa, Nafi wacce ke lab'e tad'an leko kad'an jin abinda Aneesa ta fad'a.
Idanunsu ne suka had'u juyawa tai da gudu tai waje, baice komai ba haka kuma bai mike ba sai murmushi dayai.
Aneesa ta d'auka cemai Hubby datai shiyasa yai murmushi, ta kalleshi cikin kauna tace "ahhh! "
Amsar cokalin yai, ta turo baku cikin shagwab'a tace "Hubby ya maganar sakon Abbanka? Sai yaushe za'a bani. "
Kallan mamaki ya mata yace "me? "
Ta d'an mai hararrar wasa tace " haba Hubby na kagu inga menene. "
Fuska Ashraf ya canza, cikin takaici ya kalleta yace " Get out."
Mikewa tai cikin mamaki tace "me kuma nai? "
Yace "what? Me kikai? Ina kwance ba lafiya amma ki rasa me zaki ce sai zancen wani abu? Fita nace. "
Idanu ta fara canzawa zatai alamun kuka, yace "wlh Anisa kika min kuka anan sai kinyi bala'in dana sani. "
Ta kalleshi cikin tsoro tace "Tayaya zaka iya abu kai kad'ai bayan kafad'ar ka a kumbure take? "
Ya juya kai yace "da sanda kika gani a mace kika ganni? Fita nace ko? "
Aneesa ta mike ta fita cikin takaici.
Tsaki yai sannan ya tuno sanda Nafi take hawaye sanda taganshi haka da sanda takesamai magani, tsaki yaja kawai.
Nafi kam tana fita d'aki ta koma ta rasa me yasa takejin zafin Ashraf, Hubby? A fili tace ko meye hakan oho....
Harta zauna ta mike tai kitchen.
_A Mota_
Tunda suka isa birnin kudu aka tsaya aka ajiye mutane sannan aka d'ebi wasu, kowa ya kalli D'an litti wanda ke sanye da wuka a katara sai ya matsa, sai kuma yasha jinin jikinsa, duk mutane sunyi tsit a mota duk tunaninsu d'aya wancan me zaiyi da wuka? "
Haka dai akai ta tafiyar kurma shikam yana nan kwame da glass d'iinsa baicewa komai, haushinshi ma su Datti da suka isheshi da zancen wai gaskiya sun gaji har yanzu ba'a iso ba? Wani gida ne kano haka?
Sun isa kachako anan kwandasta ya kalli kowa yace "a kawo kud'in mota."
D'an litti yace "nawa ne? "
"dari 700."
A zabure Datti yace "me? Dari 700?hauka kuke? Kunsan ma miye d'ari bakwai? "
Wani ne wanda ke gaban d'an Litti ya d'an mike yace "To wlh anmin sata. "
Gangarawa mai mota yai, parking yai sannan akace kowa ya fito, wanda akama sata yace wlh an d'auken kudina a dunkule.
D'an litti yaja tsaki yace "kudai kawai baku ajiye kudi ba yanda ya kamata zakuzo kuce am d'auke muku. "
Nan aka fara hayaniya kwandasta da kansa yake tambayan kowa ko ya d'auka har akazo kan d'an litti yace "Kai Tsakanin ka da Allah kaika d'auka? "
"I am the one. "abinda d'an litti ya fad'a kenan cikin gadara da takaici, shi harga Allah ya dauka i am the one yana nufin ba i am not ne.
Nan aka shiga zaginsa wasu na cewa dama su basu yadda dashi ba, hannu yasa ganin ana mai hayaniya da jiyar fito musu da aljihun sa akan su tabbatar ba komai a ciki, da sauri Driver ya rike hannun sa ta baya, yace " me kake shirin d'aukowa? "
Mamaki ya kama d'an litti zai magana sai ga 'yan sanda, nan suka fad'a musu, su kansu suna kallan yanda d'an litti yasa wuka zargab'ebiya a gefen riga suka tabbatar da lalai da alamar tambaya.
Cafkeshi sukai sukace sai sun kaishi office an charge shi, Datti a zabure yace "Aradun Allah baku isa ba rakamu gurin 'yata fa zai. "
Kallansa sukai sukace "sai dai ku koma in ya dawo ya rakaku amma wannan dole me ya bimu."
Dan litti sai kokawa yake akan a kyaleshi amma ina...ankwa aka garkama mai akai gaba dashi sai ihu yake yana cewa Wallahi Allah bani bane, Allah I am the one. "
Su Datti kam abin duniya ya damesu, maman Hanne tace "Yaya aikam dole mu koma ina mukasan zamu? "
Mai mota yace sai sun bashi dari 1000 su biyu, da kyar aka laluba datti aka samo dari 500 cikin takaici suka barsu agun sukai gaba.
Datti kam duk ya rikice, shida yakesan suje gun Nafi wannan yaran ya d'an bashi kudi dan yaga da alama akwai kudi a jikinsa.
Maman hanne ta kalleshi tace " Yaya wlh ba karamin kuskure kai...... "
Tsawa ya daka mata dama yana takaicin bai samu wani kudin ba ga nashi ya kare uta ficika ba a d'auka nata ba yace "ke ni gafara bani guri, banza kanwar mai satan saniya duk ba yayarki bace taja duk abinda ya faru? Zaki wani bud'en baki kice wai nayi kuskure? Nayi kuskuren 'yarki ce? "
Maman Hanne tace "Allah ya baka hakuri.... "
Nima nace Ameen
*THE INNOCENT TEAM*
Toh faa... Su nafi an fara kishine? Ko shima ya fara sontane? Aneesa sokuwace fa
ReplyDeleteI don't understand the language.
DeleteDan boko ya shiga hannun kulawa en ga mahaipi mae kwadayin abin dunia
ReplyDeletewelldone ayusher,pls sign up in WATTPAD,all great writers like you(hausa and English writers) are there.pls it will be so fun to reads your novels on WATTPAD,U you can download it from play store,is free of charge.am not advertising it,but is the modern place were readers and writters interact with one another easyly,I searched for you I couldn't see you.
ReplyDeleteTnx, i will sign in.
ReplyDelete