Wednesday, 17 May 2017

ZUCIYA....kowa da irin tasa 27

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*Gaisuwa da jinjinar ban girma gareku masoyan arziki, soyayyarku daban take 'yan group d'ina na The Queen Bee da Ayusher Fan Club..... ILYSM💋*

{ *27*}

  Sun fara daga kan farkon karatu wato English Alphabet,Nafi ta zake sosai wajen ganin ta koyi abinda ake koya mata,  sai karfe 5 sannan wannan matar ta mike akan sai gobe a daidai wannan lokacin zasu sake haduwa.

  A galabaice ta dawo hostel yunwa duk ta isheta,  ba kowa a d'akin hakan yasa taji dadi, cornflakes ta had'a ta zauna tasha, jin cikinta ya d'auka yasa ta fito tai alwala tai sallar la'asar.

  Tana zaune a kan sallaya tana kara tisa karatunta a ranta sai gashi 'yan d'akin sun dawo.

  Nan suka mata wani kallo Ferry tace " ke kina nan wato mu muna can an samu wankin toilet ko? "

  Nafi ta kalleta tace " wlh bam sani ba. "

Wacce ta dafata d'azu yanzun ma ita tace " haba Ferry taya za'ayi yarinya tazo yau d'in nan amma kice tai aiki? "

  Ferryn ta kalleta cikin kuluwa tace " Ke Jibiya banasan salon iskanci, meye naki a ciki?  Ko dake nake magana? "

  Wacce aka kira da Jibiya itama cikin fad'a tace " badani kike ba amma hakki nane in fada miki gaskiya sannan ko yanzu kika kara abinda bai dace ba dole ne in fada miki gaskiya koda kuwa zakiji haushina."
Ta ja tsaki a karshen maganarta sannan tai waje a zuciye,  Ferry ta bita da harara tace " Yarinyar nan ta gama rainani wlh. "

  Itakam Nafi tana zaune duk jikinta yai sanyi,ba abinda ta tsana irin taga anyi fad'a a kanta.

  Mik'ewa tai ta kalli Ferry tace " D'an Allah kiyi hakuri." sannan tai waje inda taga waccan ta fita.

Ga mamakinta a zaune taganta cikin mutane suna ta hira da dariya.

  Nafi ta karasa inda take tare da musu sallama,  Jibiya ta d'ago ta kalleta sannan tace " new comer  ya akai? "

  Nafi ta d'an motsa baki alamar tana san magana,  ganin haka yasa ta mike taso kusa da ita,  Nafi ta kalleta tace " Banji dadi ba daga zuwana kuna fada akaina,  d'an Allah kiyi hakuri. "

  Jibiya tasa dariya sannan ta kama hannun Nafi suka zauna tace " Karki damu da wannan,  Ferry yayatace, ubanmu d'aya,  indai fad'a ne irin wannan mun saba. "

  Nafi ta kalleta cikin mamaki tace " Ayya bansani ba. "

  Hannu ta mika mata alamar suyi musabaha tare da cewa " Sunana Aisha Isma'il. "

  Nafi tai murmushi sannan ta mika mata hannu itama tace " Sunana Nafisa Abubakar. "

   Murmushi sukama juna,  Jibiya ta kalleta tace " a kano kike? "
Nafi ta d'aga kai alamar eh,  fara'arta ce ta kara bayyana tace nima haka. "

  Nafi tai murmushi, jibiya tace " Karki damu da Farida ko ince Ferry kamar yanda ake cemata, a ido ne take haka amma a zuciyarta sam mace ce mai saukin kai. "

  Nafi kam murmushi kawai tai,  suna nan a zaune Jibiya na janta da hira sama sama har magrib tayi.
Nam suka mike sukai alwala suka nufi massallaci.

   Washegari bayan sun shirya da safe suka fito aji dukansu 'yan d'akin,  Nafi an shiga cikin Uniform ba laifi tayi kyau dagwas da ita.
Sunshiga aji malamin Math ne ya fara shigowa,  itakam Nafi kawai iya kacinta kallon duk malamin daya shigo dan ko kad'an bata fahimtar kalma d'aya da take fahimta ba.

  Sai dai ta kalli Malami ta kuma kalli alo, haka malamai sukai ta fita wasu na shiga har aka tashi,  itadai tasan kawai dumama benci kawai takeyi.

   ¤¤¤¤¤¤¤¤

  Wani mugun kallo Ashraf ya ma wata kawar Aneesa da sauri ta kalli Aneesa a tsorace, Aneesa ta kalleshi tace "  Hubby me kake nufi?  Events d'in ne bakaso kome?"

  Ashraf ya kalleta yace " Anie kanki d'aya kuwa? Biki kwaya d'aya shine kike neman yin event kusan guda 10? Sannan kina san ni in hallarci guda 8? Akan me? "
  Aneesa ta kalleshi tace " bangane akan me ba?"
  Ya dan rufe ido kad'an sannan yace " tambayar ki ai nake akan me zanje? "

  Kawar Aneesa ta daure tace " Ashraf amma..... "kallan daya mata yasa tajs bakinta tai dif, Aneesa ta mike rai b'ace tace " Yaya meyasa kake min haka?"

  Murmushi ya sakar mata sannan yace " me kuma nai yanzun? "

  Aneesa ta kafeshi da ido ranta duk ya gama b'aci ta daure tace " Ka tab'a ganin mijin daya ce ma matar da zai aura akan me zaije gun bikinsu? "

  Ashraf ya d'an daga kafad'a tare da d'aukan wayarsa ya fara dannawa sannan can yace " kowa da irin zuciyarsa,  sannan dama namiji aka sani dayin kyale kyalen biki ko mace? "

  Aneesa idanunta ns kansa ranta yakau kololuwa gun tashi,  ta bud'e baki zatai magana tags ya d'au waya ya kira wata number sanan taga yaa mike yai cikin d'aki.

  Idanu ta bishi da shi sannan tai waje fuuu,  kawarta ta mike ta biyo bayanta.

  D'akin Umma ta shiga da gudu ba ko sallama,  Umma na zaune tanacin abinci,  Aneesa ta fad'o kanta sannan ta saki kuka.

  Nan Umma duk ta rud'e ta shiga tambayarta abinda ke faruwa,  kawarta ce ta sanar ma Umma komai,  ran Umma ya b'aci sosaii ta kalli Aneesa rai a b'ace tace " Akan haka ne kike kuka?  Ai nasha fad'a miki ki cire san Ashraf aranki kiso kud'insa kawai ba wai shi ba amma nsga alama sam kin kasa fahimtata. "

  Aneesa cikin kuka tace " Umma ya zanyi?  Nafa fad'ama friends d'ina zancen events d'innnan. "

  Umma ya shafa kanta tare da kama hannunta sukai d'aki.

A bakin gado suka zauna,  Umma ta kalleta tace" ki rage events d'in daga goma zuwa bakwai,  a wannan lokacin kibar Ashraf ya sami duk abinda yakeso,  karki kuskura ki b'ata masa rai har zuwa lokacin da zai aureki ki amshi wasiyyar mahaifinsa. "

   Aneesa ta kalli Umma sai dai batace komai ba,  Umma ta cigaba "a sanda kika samu kansa kikasan ya gama mutuwa akanki lokacin ne zamu samu ya barma yayanki company d'insa."

  Aneesa da mamaki tace "Umma taya zanso mijina yabarma Yayana Company d'in mahaifinsa? "

  Umma tai wani tsaki na kulawar tace " Aneesa ke yarinyace bazaki tab'a fahimta ba,  alokacin da Ashraf ya amshi aikinsa,  dukiya da aiki suka fara mai yawa kina tunanin zai samu lokacin ki? "

  Aneesa ta girgiza kai,  Umma ta dafata tace " Aneesa kiyi tunani dakyau a haka ma mutumin da ba aiki yake ba baya ganin wani darajarki bare kunyi aure?  Yana ganin shi ke da iko dake? "

  Aneesa tai shiru sai dai Umma ta tabbatar kalamanta sun ratsa Aneesa sosai......

   Nan ta mike ta barta a d'akin,  shiru Aneesa tai tana tunani kalakala da wulakancin da Ashraf ke mata duk suna dawowa cikin zuciyarta, kwanciya tai akan gadon zuciyarta na mata sake sake kala kala......

¤¤¤¤¤¤

  Yau satin Nafi d'aya a makaranta,  har a wannan lokacin itadai bata fahimtar me ake a aji,  sai dai tana kokari sosai a gun karatun da ake koya mata.

  Yau aka kawo musu wani sabon malami na Computer bayan yayi introducing d'in kansa ne ya fara tashin mutane one by one dan tabbatar da abinda suka sani a gun waccan malamin nasu.

  "Ke tashi." abinda Nafi taji malamin ya fad'a kenan idanunsa ns kanta, a tsorace Nafi ta kalleshi sai da ya kara ce mata ta tashi kafin ta mike jikinta duk ya fara rawa,  Malamin ya kalleta yace "List 3 input of computer."

  Nafi ta zare ido cikin tsoro,  'yan aji kam gani sukau ba wanda ya samu saukin tambaya irin tata.

  Nafi tai shiru sai wasa da hannunta data shiga yi, zufa sai keto mata take a cikin jikinta.

  Ran malamin yakai kololuwa gun tashi gani yake kamar yamata tambayar yara taya za'ai wannan tambayar ta gagari 'yar Js 3?

  Ranshi ya b'aci yace " get out. " ya fad'a tare da nuna mata hanyar waje.

  Batasan me yace ba sai dai ganin ya nuna da hannu yasa ta had'a hannayenta biyu tashiga bashi hakuri.

Dariya 'yan aji suka saka mata,  ran Malam ya kara b'aci ganin taki fita, a zuciye ya d'au bulsla ya fara zuba mata,  Nafi kam ta daku sannan yace " ya bata nan da sati d'aya zai kirata a gaban class ya mata tambayoyi,  inta kuskura ta kasa to wlh ba shakka sai tayi dana sani mai tsanani."

Nafi kam zama kawai tai tana hawaye.......

Ni kaina ganin halin da Nafi take ciki sai dayasa hannuna ya fara rawa wanda na kasa cigaba da rubutun nan......


*LYSM MY FANS*😍😍😍😍

*THE INNOCENT TEAM*

1 comment: