Wednesday, 24 May 2017

ZUCIYA.....kowa da irin tasa 32

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

©
*na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*Wattpad As_AyusherMohd*

{ *32*}

    Sun isa gida Habib ya gangara yai parking,  sannan suka fito,  Nafi ta rataya jakar bayanta uta kuma Little ta ja wo trolly d'in ta.
  Habib ne ya matso kusa da ita yace " Gimbiya Feena kawo in tayaki mana. "

  Ta kalleshi sannan ta kalli kanta tace " da me fa? "
  Nuna mata jakar bayanta yai,  tai murmushi sannan tace " ni ai ba kaya na d'auka ba Little ce mai kaya, da alama baka kula ba. " tana fad'a tai gaba.

  Habib ya bita da kallo,  gaskiya yarinyar nan tayi, shi dama tun tana yar kauyenta burgeshi takeyi.

   Little ce ta karaso tace " yaya mun gode."
  Ya rufe ido tare da yin mika yace " Princess na gaji. "

  Ta kalleshi cikin kulawa sannan tace " yaya kaje b'angaren su Asim ka kwanta. "
Kai ya girgiza mata yace " a'a gida zan wuce,  ai tunda Ashraf yai aure na daina kwana a nan gidan. "

  Kanta ta sunkuyar kasa alamar rashin jin dad'i ya matso tare da sa yatsar sa ya d'ago kanta yace " sai munyi waya."

  Kai ta d'agamai,  ya mika mata key yace " Ungo kiba Ashraf zan d'auki motata nai gaba nima."

  Ta d'agamai kai,  tana kallo ya koma ya shiga motarsa yai gaba.

  Nafi kam tana shiga d'akinsu tai wani ajiyar zuciya tace " Kai nayi Missing d'akin nan. "

  Kaya ta shiga cirewa ta d'aura karamin towel sannan ta fara ninke kayan makaranta.
Little ce ta shigo,  ta kalleta cikin shagwab'a tace " kina gani Feena har Ya Habib ya tafi? "

   Nafi ta karasa ninkewa sannan tasa agun kayan datti ta kalleta tace " Little wani irin so kikema Ya Habib? "

  Little tace " so mai yawa wanda yanzu ya zama jinin jikina."

  Nafi ta tab'e karamin bakinta tace " Shifa? "
Little ta fad'a kan gado,  ta d'an mirgina tace " Shifa haryanzu a kanwa ya d'auken."

   Nafi ta girgiza kai a ranta tace " Little nima matsalar dake damuna kenan,  gwara kema banaji kinajin rad'ad'in da nakeji in na tuna Ashraf fa mijina ne  sai dai yamin nisa. "

  Toilet kawai ta shige batare databa Little amsa ba tai wanka.
Ta dad'e tana gurza jikinta a cewarta dattin makaranta ya fita.

  Sannan ta fito,  bataga Little a d'akin ba hakan yasa ta zauna a gaban madubi ta fara goge fuskarta da cleanser.

   Hoda kawai tasa batai wani kwalliya ba, sai dai tayi kyau sosai,  ta mike kenan sai ga Little ta shigo ta tiren Abinci,  Nafi ta kalleta tace " Little ina kayana? "

  Little ta bud'e mata inda ta jera mata nata kayan,  Nafi tai murmushi ta sani sarai daba dan Little ba lalai da zaman gidan nan ya gagareta,  nan ta zab'o wata atamfa riga da siket, mamaki tayi dataga tana sa kayan da kyar,  Little tai dariya tace " ai dole kigafa dad'ewar da kikai bakizo ba,  ga yanzu kin kara girma bawai kiba ba ina nufin kin girma ta sama da kasa. "

  Nafi ta harareta tace " lokacin girman ne yazo,  da alama Little sai kin ban aran kayanki inyaso sai mukai a bud'amin nawa anjima. "

  Little tace " ki d'auka mana,  sannan kinsan fa yau da yamma zamu kamun Yusra sai ki gwada kayan ko da yake cewa nai a kiki daidai ni kawai dai karya kai nawa fad'i ne saboda nad'an fiki kiba. "

  Nafi ta saka wata doguwar rigar material sannan ta zauna suka zuba abinci suka faraci.

  Nafi ta kalleta tace " Little ya gunsu Amarya?"

  Little ta tab'e baki tace " hmm ke dai bari Nafi bayan kin tafi biki an gamashi lafiya sai dai a ranar da aka kaita sukai fad'a kaca kaca. "

  Cikin mamaki Nafi tace " fad'a kuma? "

  Little taja wani tsaki tace " Ita wai a dole a daren takesan ya bata wasiyyar mahaifinsa shikuma yace ba wanda ya isa ya sashi ya bada abinda baiyi niyya ba. "

  Nafi ta tab'e baki tace " ya suka kare to? "
"Hmm kedai bari Dady ne yaje da kansa ya sasanta yace Yaya yai hakuri gobe ya bata tunda dai hakkinta ne,  ita kuma karta kuskura ta sake tambayarsa. "

  Nafi ta d'an juya kai tace " Na d'auka tanasan shi dayawa, meye nata na damuwa da abinda baiyi niyyar bata ba?  Indai har tana gudun b'acin ransa? "

   Little tace " Zigata akai ya Asim da Umma."
Nafi ta d'anyi karamin tsaki tace " san da takemai baiyi nisa dayawa ba kenan indai har za'a zigata akan dukiyarsa."

  Little tai ajiyan zuciya,  Nafi tace " yanzu fa?  An bata ai nasan hankali ya kwanta. "

  Little tace "Hmm Yaya wai cewa yai wasiyyar dama mahaifinsa ne yace aba matar sa ta farko million d'aya ko ince wai ya ajiye kud'in a banki, to Yaya yabata kud'in sai dai Umma tace itakam gaskiya bata yarda wai kud'i kawai akace ba."

  Nafi ta had'e rai tace " shi kuma yayan me yace? "
"Uhm bai kulasu ba kinsan shi ai. "
Nafi ta kara tab'e baki tace " Allah ya sauwake. "

  Little ta amsa da Amin sannan ta d'aura da cewa " kigama muje ki gaida Mumy sannan kije kiga b'angaren Amarya. "

  "wa? Bada ni ba, inje in musu me? " sukasa dariya a tare.

¤¤¤¤¤¤¤¤

   A b'anagren Ashraf kuwa ya nemi aiki yanda kowa yake nema ya kuma samu ba babban aiki bane sai dai yanajin dad'in yanda yake fahimtar matsalolin ma'aikatansa tundaga kasa,  yana kuma fahimtar abinda ya cancanta da zai musu bayan ya amshi company d'in.
Sai dai su Asim da Kawu kam shar take a gunsu, Asim kam gani yake kamar saboda Aneesa ne ya hakura da mukaminsa,  sai dai shi kawu haryanzu yana tunanin da wani abu a kasa.

     Kamar kullum yau ma ya dawo gida daga gun aiki,  yana zuwa daidai saitin kofa yaji maganar mutane da karfe,  da alama ma musu sukeyi,  kai ya dafe cikin tsananin takaici sannan ya kwankwasa tare da murd'a kofar.
 
  Aneesa ce zaune cikin kawayenta su uku, sallama yai sannan suka kalli inda yake, Aneesa cikin kissa ta taso da sauri tazo ba kunyar mutane a falon ta rungumeshi tare da manna mai kiss a kunci,  Ashraf ya d'an zareta kad'an sannan yace " Bari in shiga ciki.."
  Hannunta ta sakala cikin nasa sannan suka fara tafiya,  shidai takaici ma hanashi magana yai.

  Yana shiga d'akinsa ya kwace hannunsa sannan ya kalli d'akin yanda ya tafi ya barshi haka dai ya dawo ya sameshi, ya kalleta cikin takaici yace " Anie mekenan?  Ba nace ki gyaramin d'aki na ba? "

   Ta shagwab'e tare da kwantowa jikinsa tace " kana fita su Laila suka zo ni ko tunawa ma banyi ba. "

  Ya kalleta cikin takaici yace "yau kwanan d'akin nan uku kenan a haka kullum da abinda kike cewa,  wasa wasa ma falo da mai aiki bata zuwa ta gyara haka nan zaki barshi da sunan kinada abinyi ko? "

   Aneesa ta kara shagwab'ewa tace " Hubby kayi hakuri zan gyara. "

  Wani mugun kallo ya mata yace " banaso fitarmin daga d'aki. "

  Zatai magana ya nuna mata kofa da yatsarsa sannan ya had'e rai sosai,  jiki a sanyaye ta fito,  sai dai dankar kawayenta su gane ta saki fuska.
Shikam tana fita ya sawa kofar makuli tare dajan wani tsaki yabi d'akin da kallo,  ko sanda yana shi kad'ai baya barin d'akinsa haka amma yanzu ji d'akisa?

Gadon ya gyrara sannan yai wanka ya kwanta a kai,  bai dade ba bacci ya d'aukeshi.
  Bacci yai sosai harya makara sallar la'asar sai karfe 5 ya tashi,  da saurinsa yai alwala ya fito masallaci.

  Sukam su Nafi ganin anyi sallar la'asar suka shiga yib kwalliya dan tafiya gidan biki,  saboda kawar Little ce sosai,  sunaso suje da wuri dan a gamama Amarya kwalliya su tafi da ita gun biki.

   Anko suka saka,  light purple d'in wani yadi ne,  shiba lace bane sannan ba material bane,  riga sukai da siket sannan sai head shima kalar kayan, sunyi kyau sosai da sosai, balle abin kan nasu Little ce ta d'aurama Nafi sannan ta d'aurana kanta,  Nafi tace " amma ankon yayi kyau. "

  Little tai murmushi tace " kawayenta ne kawai zasu sa wannan ragowar atamfa ce. "
Nafi ta jinjina kai sannan tace " Farin mayafi zamusa? "

  Little ta girgiza kai tace " a haka zamu. "

  Nafi ta kalli kanta sannan ta kalli Little tace " taya zamu fita a haka? "
Little tace " haka ake yi ai in ma mun d'au mayafin sai dai mu rike a hannu. "

  Nafi ta jin jina kai sannan ta zaro wani mayafinta karami golden color tace "ni dai da wannan zani. "

  Little tace " to. "
Sun fito abin sha'awa dan hatta takalminsu iri d'aya ne,  sai dai ba kyan kwalliya ba duk wanda ya kalli Nafi sai ta birgeshi,  kamar yanda nace Nafi ba fara bace can sai dai tana da kyau gashi batada jiki.

  Sun fito suka wuce gun Mumy dan amsar kud'in liki inji Little.

   A lokacin shi kuma Ashraf bayan ya idar da sallah yaga kiran Mumy hakan yasa ya karasa gunta,  yana zaune a kasa ta kawomai tiren abinci ya bud'e cikin mamaki ganin ba anan yake cin abinci ba.

  Ganin d'an wake yasa ya gane dalilin kiran,  zubawa yai yafara ci kenan,  Little tai sallama,  amsawa yai saidai bai d'ago ba,  lokacin Mumy ta tashi  daga falon,  wata sallama ya sakeji bayan ta little sai dai wannan muryar cikin sanyi take.

   Ya amsa sai dai yanasan juyawa kasancewar hali irin nasa yasa ya d'auke kai sai dai bai cigaba da cin abincin ba.

  Little ta karaso cikin murna tace " Yaya kaine anan? "

  Nafi ta kalleshi ta baya gabanta yai wani fad'uwa yaushe rabon data ganshi,  Ashraf ya kalli Little yace " ke wato kin girma ko? Sam bakya ma zuwa ganina sai dai inmun had'u a wani gun. "

  Ta rike hab'a tace ina na isa yaya?  Kana gani Yaya Neesa sam batasan muje mata wai muna takura muku nikuwa ina zaka ganni? "

  Baiyi magana ba, tace"Mumy fa? "
Ya ce tana ciki,  da sauri Little tai ciki.

  Nafi ta karaso jiki a sanyaye ta tsuguna daga ta bayansa tace " Yaya ina wuni? "

  Juyowa yai dan ganin mai magana,  kallan mamaki yake mata lalai yasan fuskarnan sai dai wacce ya sani inaa....  She can't be.
   Nafi ta mike ganin yaki amsawa sai wani kallo da yake mata,  tai hanyar waje,  dasauri yace  " Ke! "
  Ta tsaya sai dai bata juya ba, ya mike tsaye sannan yace " ke! "

  Nafi dai tana tsaye bata juyo ba,  a hankali ya tako zuwa inda take cikin fad'a yace " ba dake nake ba? "

Nafi ta juyo fuska  a had'e duk da tana shakkarsa amma ta daure tace " ganinai ba sunana kenan ba."

  "mene? "
Nafi tad'an burtso baki,  kallan mamaki ya mata yace " Ba Nafisa bace? "
Ta kara had'e rai ta kalleshi tace " au kama mantani? Ka d'aukoni daga garin mu amma kama manta da sunana? "

  Ta juya cikin takaici zata wuce,  da karfi ya fizgo hannunta ya jawota, kallan tsoro tamai,  tace " Yaya mai kake yi? "

  Kallanta ya karayi yace lalai itace ya fad'a a ransa,  a fili yace " ancemin kun kusa hutu ashe har kunyi. "
  Ta d'ago ta kalleshi sai dai batai magana ba,  yace " wato yanzu makaranta ta maidake mara kunya ko? "

  Tace " menai kuma? "yanda tai maganar yasa yace "Lalai yarinyar nan. "

  Kokarin kwace jikinta tai tace " ni ba yarinya bace. "
  Ya saketa tare da cewa " ke ya hanaki dawowa har kusan 2yrs. "

  Ta juya kanta gefe tace " nemana akeyi?"

  Ya koma ya zauna yace " ina zaku haka? "

  Biki zamuje.
Ya fara cin abincinsa, ya juyo da niyyar magana yaga batannan.

  Mama  ne ya kamashi yace " lalai yarinyar nan,  yaushe ta girma haka? Gaba d'aya tama canza kamar ba Nafin riga ba."

  Itakam tana fita tai d'akinsu,  a falo ta zauna ta matse hannayenta,  jikinta sai rawa yakeyi,  meyasa suka had'u?


*THE INNOCENT TEAM*

3 comments:

  1. Nice one .May almighty Allah continue to increase u in knowledge

    ReplyDelete
  2. Tnx a lot sis, Allah ya kara basira.

    ReplyDelete