Wednesday, 17 May 2017

ZUCIYA.....kowa da irin tasa 24

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

*Hajja ce! I Sincerely Dedicate This Page to You... ILYSM😍*

*24*

    Tana nan a zaune jugum har ya fito daga wanka,  daga bakin kofa ya kalleta fuskar nan a had'e tam yace" me kikeyi har yanzu? "

  Mikewa tai ta d'anyi rau da ido tace " Haba Hubby na taya na ciwo kwalliya dan in birgeka zaka dinga wulakantani haka? Tunda kaga nazo ai kasan hakuri nazo in baka. "

   Ashraf ya wani saki murmushin rainin hankali sannan ya mata wani kallo wanda ita da akawa ita kadai tasan me yake nufi yace " Ko? "

  Tace " bangane ba? "

Ya d'an juya kai gefe yace " ke kina tunanin har kinkai matsayin da zaki tozartani a gaban mutane sannan ki biyo ta baya kice zaki ban hakuri? "

  Aneesa ta d'an canza fuska kad'an tace " Amma Yaya kasan dai ko waye dole yaji haushi,  ko bakasan na dinga kishin ka? "

  Kallanta yai sannan yad'an girgiza kai na takaici hanyar waje ya nuna mata da yatsarsa yace " yi nan. "

  Ta kare lagub'e fuska,  yace " kinfi karfi? "

  Juyawa tai a hankali tai waje tana fita yasama kofar makuli,  tare da jan tsaki.

  Nan ya shafa maganinsa sannan ya shiga kokawar sa kaya,  bayan yasa ma kwanciyarsa yai a kan gado.

    Itakam Aneesa tana fita Habib ya kalleta tare da guntse dariyar datake kokarin tahomai yace " Badai fada kukai ba? "

   Ta kalli Habib kamar zatai kuka sai kuma ta daure tace " a'a kaya zai sa. "

  Habib ya jinjina kai, zama tai a kan kujera shikuma ta mike yai waje, Aneesa ta dade a zaune tun tana irgaminti har ta dawo hour, ganin hour din Ashraf biyu a ciki gashi har bacci yana neman d'aukan ta yasa ta mike kamar ta kurma ihu.

  Abin haushi taje tana kwankwasa kofar Ashraf sai ga Habib ya shigo,  yana ganinta baisan sanda dariya ta zo mai ba.

Aneesa takalleshi cikin kuluwa tace " Abokin Ango meye hakan? "

  Habib ya had'e hannayensa biyu alamar ban hakuri yace " Tuba nake Amarya amma naga kamar fada kukai da Angon."

Aneesa wani takaici ya kara kamata ta kalli kofar Ashraf sannan ta kalli Habib dake juya kai yana d'an dariya haushi yakamata kawai ta tsugunna a gun tasa kukan shagwab'a.

  Kuka take sosai Habib ganin haka ya kara komawa waje.

Ashraf kam wanda kukan duk ya dameshi ya mike jiki a sanyaye ya bud'e kofar,  Aneesa tana jin ya bud'e ta kara sautin kuka.

   Ashraf ya tako a hankali,  ya tsugunna shima tare da sa hannu akan kafad'arta, kamar jira take dama ya tab'a ta kawai ta kankameshi tana kuka,  Ashraf ya shiga kokarin zare jikinsa amma ta kankameshi tamau sai kuka take.

   Ganin bata da niyyar sakinshi yasa ya mike da karfi,  Aneesa ta d'ago fuskarta wacce duk ta b'aci kaca kaca sakamakon kwalliyar datasha,  Ashraf ya dafata yace " Anie na fada miki ba sau d'aya ba kidaina kankameni haka."

  Ta turo baki tace " kai fa mijinane. "

  Ashraf yace " banzama ba tukunna,  sai an d'aura mana tukunna,  sau nawa ina sanar dake hakan? "

  Aneesa ta kara share hawaye tace " Yaya naji to zan daina amma d'an Allah kadaina wahalar da zuciyata. "

  Mikewa yai batare da ya amsa ba ya bud'e kofar d'akinsa yace " zo ki wanke fuskarki. "

  Ta turo baki tace " bakasan kwalliyar? "

  Kai ya girgiza alamar a'a yace " ki shiga kya gani "

  Ta mike zuciya ba dadi tai toilet.
  Tana shiga taga fuskarta a madubi kamar dodo,  da sauri ta matso liquid soap ta shiga wanke wa tana yi tanajin haushin ganinta a haka da Ashraf yai.

      ¤¤¤¤¤¤

  Da yamma bayan little ta dawo Mumy ta sasu a mota suka fita shopping, sunyi siyayyar kayan abincinta sannan aka sai uniforms,  da house wear sannan suka wuce gun mai d'inki,  nan suka bashi sannan suka amshi ragowar sababbin d'inkunenta, wannan kuma akan gobe za'a mata tunda uniform ne bawai style za ai ba.

   Nafi kam kana kallanta zakasan tana cikin farin ciki dan little ma sai tsokanarta takeyi.

  Sun gama komai kafin su nufi hanyar gida,  Little ta kalli Nafi tace " Nafi kinsan Ice cream?"

   Kallan mumy tai wacce tai kamar batajinsu sannan ta kalli Little ta girgiza mata kai alamar a'a.

  Little ta zunguro kusa da Mumy tace " mumy asai mana Ice cream. "

  Murmushi Mumy tai tace " to. "

Nan suka karkata suka gangara 212, Little ta kama hannun Nafi suka shiga ciki, Nafi kam sai sadda kai kasa take,  dama Mumy bata bisu ba tana zaune cikin mota sai dai tabi Nafi da kallo wacce ta ke kula da nutsuwarta tunda suka fito.
Tana jinta sanda suna siyayya tana tab'a Little akan wai duk kayan na makaranta ne?  Ai sunyi yawa ina zata kaisu? Tanaji sai dai Little tai dariya tace "ke dai me ya dameki? "

  Mumy ta saki fuska tabi bayansu da kallo.

  Sukam suna shiga Little ta shiga zab'an abubuwan da zasu siya da yake duk sunayen da turanci take fada yasa Nafi kawai ta zura mata ido tanaji inama itama tasan ke ake cewa?
Sunyi siyayya sosai kafin su fito,  Nafi ta kalli Little tace " ku kam wani irin kud'i gareku?  Na ga sam bakwajin wahalar kashesu. "

  Little ta d'an harareta tace " Ke dai in an miki abu kawai kiyi godiya ki daina cewa ya miki yawa. "

  Nafi bata amsa ba sai dai ta bita da kallo,  nan suka koma mota.

   Mumy ta ja mota suka tafi,  sun isa gida mumy tai parking zasu fito Nafi tace " Mumy angode Allah ubangiji ya kara bud'i."
  Murmushi Mumy tai sannan ta amsa da Amin.

  Zasu fita sai ga Habib da sauri ya karaso,  shiya rike musu kofar motar,  Little kam wani shaukin farin ciki ne ya ziyarci zuciyarta tace " Ya Habib? "

  Yakwantar da kansa a jikin kofar kad'an yace " My Little Princess i really miss u"

   Little wacce zuciyarta ta kara yin haske ta juya fuska cikin shagwab'a tace " bayan yaya ya daina damuwa dani? "

  Habib ya kalli Nafi ba tare daya ba Little amsa ba yace " Nafisa ba magana? "

   Ina wuni ta fad'a cikin sanyin muryarta,  Ya amsa tare da kallan cikin motar yace " Mumy sannu. "

Mumy ta fito tare da cilamai makulli tace " akwai kaya a boot ka tayasu kwasa zuwa b'angarensu. "

  Ya chafe tare da yi mata salute yace " yes maa. "

  Mumy tai gaba,  Little ya kalla yace " Little Princess ba a huce bane? "

   Tace " Yaya Allah kuwa..... "

  Ya katseta tare da had'e hannayensa biyu alamar ban hakuri,  hakan yasa ta kasa karasawa,  itakam Nafi dama tad'an matsa nesa da su kad'an,  jitai Habib yace " To gimbiya sai ki matso mu kwashi kayanki ko? "

  Da mamaki ta juyo tace " Ba dai  nice Gimbiyar ba ko? "

  Habib yai dariya yace " me?  Bakyasan sunan? "

Zatai magana Little tace " Ni Princess ita Gimbiya?  Ya Habib to meye marabarsu? "

  Ya saki dariya yace " Princess ba dai tana kishi ba? "

  Da sauri tace " ni dai bance ba. "

  Nafi itakam ta karaso ta d'au ledoji manya manya ta nufi hanyar ciki,  Habib da sauri ya sha gabanta yace " ta ina mace yarinya kamarki zata iya d'aukan kayan nan? "

  Nafi ta kalleshi tace " zan iya,  kai dai kaba Maryam hakuri. "

   Ya kalli Little sannan ya juyo da niyyar yima Nafi magana sai dai can ya ganta tayi gaba,  ya saki murmushi tare da shafar keyarsa sannan ya koma gun Little.

  A falo Nafi ta tadda Aneesa da kawarta a zaune suna hira,  Nafi ta tsugunna ta gaidasu sannan ta nufi hanyar d'akinsu,  Aneesa ganin manyan ledoji yasa tace " ke zo nan."

  Nafi ta juyo ta kalleta sai dai bata karasa ba,  Aneesa tace " ke munafuka ba dake nake ba? "

  Nafi ta ajiye kayan a bakin kofa ta nufi gunta,  cikin masifa Aneesa tace " da ke da kayan nakesan ganinki. "

Nafi ta koma ta d'auko kayan ta karasa gunta, gyara zamanta tai sannan ta fizgi Ledar da karfinta ta shiga bincikewa,  Nafi kam yau ta kulu,  har ranta sai dataji haushin wannan abun,  tana kallon Aneesa ta juye ledar ma gaba d'aya akan carpet dai dai nan Little ta shigo falon,  mamaki ne ya kamata tace "me kenan? "

  Habib ya karaso shima ya kalli wannam cin mutuncin,  ga Nafi a gefe ta tsugunna,  Aneesa ta bugama Little harara idanta ya rufe ko Habib bata gani ba tace " Little wa aka saima kayan nan? "

  Little ta kalleta rai b'ace tace " Ya Neesa me ya dameki da wanda aka saiwa? "

   Aneesa ranta ya b'aci ga kawarta a zaune a kusa da ita,  tace " mene?"

  Little a zuciye ta karaso tace " Ya Neesa wai meke damunki ne? Taya zakiga kayan mutane kawai ki zubar a kasa? "

  Kawar Aneesa ta kalli Little tace " lalai Little yaushe kika zama mara kunya haka?  Aneesa ba yayarki bace?  Sannan yanzu da kika ganni anan tsara shirye shiryen da za'ai da bikinta da yayanki mukeyi ai ko bata zama matarsa ba ai yayarki ce bare an kusa. "

  Little ta kalleta a kule sai dai ta kasa magana ta kalli Nafi cikin takaici ta wani takure kanta a kasa zatai magana kawai sukaji ance "Tsugunna ki kwashe kayan da kika zubar. "

  Gaban Aneesa ne ya fad'i ta juyo a tsorace,  ba ita ba Little da Nafi ma kofa suka kalla haka ma kawar.

  Ashraf ne a tsaya kana ganinsa kasan ba wasa a fuskarsa,  Little ta kalli Habib wanda ke tsaye daga kofa,  a ranta tace " yaushe ya kira shi? "

  Aneesa ta kalleshi tace " Yaya.... "

  Wani kallo ya mata wanda yasa ta had'iye maganar ta cikin tsawa wacce ta razana kowa dake falon yace " Kowa ya fita."

  Nafi kam jikinta rawa ya kauri dashi,  bata tabajin yayi tsawa haka ba,  Little ta kamata sukai waje a sukwane itama kawar Aneesa da sauri tai waje ta nufi d'akin Umman Aneesa.

  Ya rage daga Aneesa sai Ashraf a d'akin,  ya kara kallanta yace " ba dake nake ba? "

  Idanunta na kansa kallan mamakin dizgata dayai take,  ta daure tace " Yaya ni zaka wulakanta akan Nafi? "

Shi baimasan a hannun Nafi aka anshi kayanba,  shidai Habib yace yazo akwai matsala a b'angaren su Little, da ya iso shine yake cemai Mumy ta siyo kaya Aneesa ta zubar.

   Ashraf ya kara kallanta,  idanunta suka ciciko tace " Yaya kana san ka nunamin ka fifita Nafi akaina kenan ko me? "

  Ashraf ya kalleta cikin tsananin takaici zaiyi magana kawai sai ga Asim da Umma sun shigo cikin masifa........



*THE INNOCENT TEAM*

No comments:

Post a Comment