Tuesday, 2 May 2017

ZUCIYA.....kowa da irin tasa 12

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

1⃣2⃣

    Karfe hud'u Nafi ta bud'e idanunta kamar yanda ta saba,  shiru tai daga kwance tana tuno mahaifinta ta kalli little wacce take ta baccinta hakan yasa itama ta koma bacci.

    Har asuba tai Little ta tashi tai Sallah Nafi bata farka ba, ganin ta idar yasa tadan tab'a Nafi,  da karfi Nafi tace " Baffah kayi hakuri na tashi wallahi. "

   Ta fada tare da mikewa zaune da sauri, little tad'anyi dariya tace " Nafi nice!  Da alama Baffan nan bulala yake miki. "

  Ajiyar zuciya Nafi tai ta kalli Little tai murmushi kawai batace komai ba.

   Little tace " Tashi kiyi sallah. "
Nafi ta amsa da to tare da mikewa tsaye tace "kin tarar mi..... "
Katseta Little tai tace "Na tarar miki ke da bakya mantawa. "

   Nafi tai toilet tana murmushi.
Bayan tayi Sallah ne ta kalli Little wacce ke kwance kan gado da alama bacci zatai tace " Maryam  naga kin kwanta?"

   "Me zanyi to? Bayan sai karfe sha d'aya zan fita?"
Nafi tace" nima me zakiyi a kwancen nake tambaya. "
  Little ta zauna tare da kallan Nafi tace " Bacci mana. "

Idanu Nafi ta zaro tace" Bacci kuma?  Mu kwana muna kwanciya yanzu ma ki kwanta?  Tab di. "

Little tai dariya tace " Uhm hm i kam dai bacci zanyi. "tai maganar tare da kwanciya.

  Nafi ta kalleta tana mamakin wannan al'amari,  mutum ya kwana yana bacci sannan ya kara kwanciya da safe?  Shi ba ciwo yake ba?

Ganin tana ta zaune ga zaman ya fara isarta yasa ta mike  sanye da hijabin datai Sallah tai waje.

Ba kowa a wajen garin ya yi hasken gabanin asuba ta kalli katun gida a ranta tace" Masu gini sun sha aiki. "
   Kitchen ta nufa tana tafe tana kara kallan gidan mai cike da sha'awa,  sukam 'yan kitchen sunata hada hadar aiki,  ta gaishesu suka amsa cikin sakin fuska,  Matar jiyar nan ta kalleta tace " yanaga kinzo da wuri? "

  Nafi ta dan murmusa tace " in ma na zauna ba abinda zanyi shi yasa naga gwara na taho. "

   Kai ta jinjina,  Nafi ta kallesu tace " me zan fara? "
  Wata daga ciki ta kalli matar tace " Goggo me zatayi? "

   Goggo tai shiru can tace " ke wani bangare kika fiso? Akwai masu wanke wanke? Akwai masu bangaren dake dake da yanke yanke akwai masu bangaren girki. "

   Ba tare da dogon nazari ba Nafi tace  "Nafisan b'angaren masu abinci saboda inaso in iya irin abincin jiya. "

  Dariya suka sa mata,  Goggo  tace " Bangaren Abinci fa sunfi kowa wahala saboda da safe kowa da abinda yakeso a dafa mai,  wani sa'in da rana ko dare ma haka."

   Nafi tace " Bakomai."

  Nan ta zauna gun Goggo, takarda Goggo ta dauko ta shiga karanto abinda za'ama kowa yau,  sunyi sa'a wasu suna zuwa iri d'aya,  nan suka shiga aiki.

  Nafi dai sai dai juyawa dan ko sunan abubuwan bata sani ba bare ta dinga mikowa.
   An fara da masu fita karfe takwas, sai da aka gama dasu sannan aka fara ma 'yan gida su kuma nasu aka fita dashi.

  Nafi kam abin sai birgeta yake,  sai wajen karfe tara suka gama, Nafi ta musu sallama ta tafi.

    Har sanda ta dawo Little na ta uban bacci,  Nafi tanasan tai wanka gashi bata iya bud'e famfo ba, dole kawai ta samu guri ta zauna a kasa.

  Bacci ne yai gaba da ita,  wajen  9 da rabi sukaji ana kwankwasa kofa,  da sauri Nafi ta mike tare da bud'ewa,  Wasu yarane su biyu d'auke da ledoji suka kalli Nafi sukace " Dama Yaya ne yace mu kawo ma Yaya Little. "

Little dake zaune akan gado tace "Amra ku shigo mana. "

   Nan suka fara kokarin jan ledar,  Nafi ta amsa ta shiga dashi,  little ta kalli kayan tace " me yace?"

   Wacce ta kira da Amra tace  " cewa yai mukawo miki zai kiraki. "
Amra na rufe baki kuwa sai ga kiran Ashraf,  da sauri tai gyaran murya dan ya hanata wannan baccin,  tace "Yaya ina kwana? "

   Yace " kinga dama kin tashi? "

  Kallan Nafi tai sannan tace " Yaya ba bacci nai ba. "

  "Hmm ai inaji gaba ni da kaina zan dinga zuwa ina dubaki."

  Little ta d'an turo baki sannan tace " Yaya ga su Amra sun shigo da ledoji."

  Yace " Yanzu za'a kawo manyan,  naga su bazasu iya d'auka ba ko kuma turo Nafi ta dauka. "

  Little tace " to kana ina? "
Ina gun motor park,  Sai Amra ta rakota. "

  Little tace " to amma yaya kayan meye? "
Kayan Nafi ne so nake da yamma inkin dawo ki d'au driver ya rakaki gun mai d'inkinki sai a gwadata a mata. "

  Baki little ta bud'e to kawai tace tanaji ya kashe wayar.
Nafi ta kalla ta fadamata sakon sa tare da cewa kimai godiya daga nan duk ke ya siyowa kayan. "

  Cikin mamaki Nafi tace ni kuma? Little tace " eh mana ya san baki da kaya ga nawa sun d'an miki yawa. "

  Nafi tai shiru tana mamakin ledojin da aka kira da nata.
Little ta katseta "ki tashi dan Yaya baisan jira. "

  Nan suka mike itada Amra.

    Yana zaune cikin mota kafafuwansa na waje sannan hannunsa rike yake da waya yana dannawa.

   Nafi ta karasa inda yake ta tsugunna ta gaidashi,  kallanta yai kawai maimakon ya amsa sai yace " kema daga baccin kike? "

  Kai ta girgiza alamar a'a, yace " ki d'au kayan suna bayan mota."

   Nafi ta mike a hankali har ta je inda zata d'auka sai kuma ta dawo inda yake ta tsaya kyam tana wasa da 'yan yatsun hannunta, Ashraf ya kalleta yace " Nafeesa da wani abun ne? "

  Yawo ta had'iya sai dai ta kasa magana, ganin haka yasa ya cigaba da danna wayarsa baice mata komai ba shima.

   Nafi kam tayi tsuru ta kasa magana,  Amra kam tafiyarta tai ya rage saura su biyu, ta dade agun kafin ta daure tace " Yaya. "

Dasauri ya d'ago ya kalleta, tai saurin yin kasa da kanta dama abinda ta kasa fada kenan.
Kallan mamaki ya mata sai kuma ya maida kansa kan waya.

Ta kara daurewa tace " Yaya Na gode. "

    Tana fada ta juya zata d'au kaya,  jitai yace " Nafisa!! "

  Tsaya wa tai cak sannan ta juyo a hankali cikin tsoro,  ya kalleta kad'an sannan yace " Jiya me yasa kika rufemin kofa ina miki magana?"

    Kanta na kasa sai gabanta dayake fad'uwa,  Ashraf yace " meye dalili?  Ko raini ya fara shiga tsa...... "

  Katseshi tai da sauri da cewa " Wlh ba haka bane,  matsowar dakai kusa danine yasa gabana yaketa fad'uwa shiyasa na rufe. "

  Da mamaki yake kallanta yace " Nafisa yaushe kika koyi karya? "

  Idanu ta zaro cikin mamaki tace "Wlh ba karya nakeba Yaya. "

  Ya d'an kura mata ido hakan yasa  tai kasa da kanta,  a ransa yace " dole dan da alama namiji bai taba tsayawa kusa da ita haka ba. "
  Wani abu ya tuno ya d'auke kansa daga kanta a hankali yace " da alama sanda kika ciren riga gaban naki bai fad'i ba "

  Idanu ta zaro da sauri ta juya ta fara tafiya,  ya kalli yanda take sauri yace " kayan fa? "

  Idanu ta rufe,  cikin tsananin kunya ta shiga neman tahowa gun idanunta a rufe,  batasan har tazo inda yake ba,  jin tayi dan tun tube da kafa yasa ta bud'e ido da sauri,  Ashraf ya kalleta yace " Toh da alama gaban naki baya fad'uwa ko? "

  Tsugunnawa tai da sauri cikin tsoro tasa kanta a cikin cinyoyinta,  idanunta suka ciciko,  Ashraf ya mike tare da d'anyin murmushi,  ya matso saitin kunnenta yace " in kin gama kunyar sai ki rufemin mota. "

    Tanaji ya tafi,  ta dade kafin ta mik'e ta shiga bubuga kanta a hankali a jikin motar,  jin goshinta ya fara zafi yasa ta d'au kayan tare da rufemai mota tai gaba.

    Tana isa d'aki ta taradda Umma da Aneesa a zaune,  gefe kuma Little ce tsaye da towel da alama wanka zatai.

    A hankali cikin tsoro ta shiga d'akin,  tare da ajiye kayan, Umma tace " Yauwa Ke muga ledar nan. "

   Nafi ta mika ma Ummaa taja gefe ta tsaya,  Umma ta kalli Aneesa tace " wanene lace d'in? "

Aneesa ta ciro wani dankararen lace wanda kana ganinsa zakasan lalai mai tsada ne na gaske.

   Little ta kalli Umma tace " Umma nikam yaya fa bai fadamin ba?"

  Umma tai murmushi tace " Little kenan bakiji me nace ba?  Nice na aiki Aneesa ta fara siyomin kayan biki ita kuma ta manta ta bashi a cikin kayan wannan. "ta fada tana nuna Nafi.

  D'aukan lace din sukai suka tafi,  little ta shiga toilet ranta duk a b'ace.

   Nafi kam ko ajikinta dan batasan darajarsu ba,  itadai kunyar Ashraf ce ta kara kamata ya zatai inta ganshi?

   

   *THE INNOCENT TEAM*

No comments:

Post a Comment