Tuesday, 2 May 2017

ZUCIYA.....kowa da irin tasa 13

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

   *I Sincerely Dedicated This Page To All Masoyan Xuciya,  Nagode Kwarai da san da kuke mai.... *😍 *ILYSM*😍

1⃣3⃣

    Nafi tanannan zaund har Little ta fito ta kalli Nafi cikin takaici ganin tana murmushi ita kad'ai tace " Nafi bakiji haushin abinda su Umma sukai ba? "

   Cikin rashin kulawa da abin tace " name fa? "

  Little ta zauna a gaban madubi tace " kina gani sunzo sun dauki lace mai tsada da sunan wai aike akai? "

  Nafi ta kalleta tace " lalai Maryam meye abin jin haushi?  Kika sani ko da gaske suke? Sannan ko d'auka ma sukai ai sun isa ne naga ita zai aura? "

  Little tai d'an karamin tsaki tace "Wlh ba wani kayansu,  sannan dan ita zai aura sai akace tazo ta d'au abinda ba nata ba? "

   Nafi ta mike tace " kafin ki shirya bari na anso miki abinci. "

  Bata jira amsarta ba tai waje da sauri,  Little ta bita da kallo a fili tace " lalai wato dan indaina maganar shine zaki gudu? "

  Nafi kam tana fita tai murmushi  tace " ni da naga kaya daga sama?  Dan an d'au d'aya menene? "

  Kitchen ta wuce,  ta amso abincinsu kenan zata shiga bangarensu taji ance "Ke!"
Juyawa tai dan tasan Umma ce,  Umma tace " zo nan. "

   Ajiye tiren tai sannan ta karasa gunta,  Aneesa ta maka mata hararra tare da juya kai gefe.

   Nafi ta karasa tare da rusunawa tace "gani. "

  Umma ta mata wani kallo tace " munafuka kinje gun aikin ko kuwa? "
  Da sauri Nafi tace "Naje wlh. "
  Duk da dama Umman ta riga ta tambaya ankuma shaida mata taje amma sai cewa tai "in kika min karya na tambaya wlh kinji na fad'a miki jikinki sai ya fad'a miki. "

    Nafi tai kasa dakai ba tare da ta sake magana ba,  Umma ta kara kallanta sannan ta ce " me Little tace bayan mun fita? " dama wannan shine dalilin kiran wancan burga ne so take taji me akace bayan sun fita.

Nafi da mamaki ta kalleta tace " Bangane ba. "
Da kuwa Umma ta mata ta kara da kinci gidanku,  ni zaki kalla kicewa baki gane ba?

  Nafi tai kasa da kanta a hankali tace "kiyi hakuri. "

  Cikin takaici Aneesa tace "Dalla malama kara gaba. "
  Nafi wacce bata fahimci me ake nufi da kara gaba ba tace "Naam? "

   Cikin kuluwa Umma takaimata wani wawan mari wanda sai da Nafi tai baya tare da rike kuncinta.

   Umma ta nunata da yatsa tace " kin bar nan ko sai na karya ki? Shigeya wacce asalinta bashida tabbas. "

   Nafi ta juya ta fara tafiya sai dai tana tafe hawaye nabin kuncinta,  haka ta d'au tiren tare da goge hawayenta ta shiga.

   Little har tana shirin fita sai ga Nafi ta kalleta tace " lalai Nafi sannu da zaman hira. "

  Nafi tai murmushi kawai batace komai ba sai hanyar toilet data nufa.

  Tana shiga ta tsugunna sai kuka,  itakam Little abincinta taci ganin Nafi bata fito ba yasa taje bakin kofar toilet d'in tace " Nafi na tafi. "
  Da kyar ta daure tace "To. "

  Sai dataji alamun fitarta sannan ta dawo ciki,  ta dade kafin hawayen su tsagaita taci abinci sannan ta fara gyara d'akin.

     

     _A Company_

    Kawu zaune a kan kujerar dake tsakiyar dogon tabirin,  gefe da gefe mutane ne kowa zaune akan kujerar sa,  Wanda ke daga b'angaren hagu na kusa da kawu ya kalleshi yace " A gaskiya Chairman mun gaji da abinda Chief Director(Asim) yake mana,  a duk sanda muka bukaci sa hannunsa akan wani aiki ko meeting  a b'angaren mu ya dinga mana wala wala kenan,  sam baya yin aikinsa na Chief Director."

   Kawu ya kalli Asim wanda yaketa juyi a kujera cikin rashin damuwar abinda ake kararsa dashi, ran kawu ya kai koluluwar b'aci ya kallu wanda yai maganar yace " kar ka damu Director  idan har Asim bai canza halayensa ba nan da one month ni a matsayina na shugaban wannan company d'in zan saukeshi daga matsayinsa. "

  A zabure Asim ya kalli mahaifinsa wanda yana gama magana ya mike yai waje,  Asim cikin tsagali da raini ya kalli mutanen gun yace " ni kuka had'a da mahaifina? Lalai ran kowa in yayi dubu sai ya b'aci. " shima yabi bayan mahaifinsa.

  Office d'in kawu ya shiga,  yana shiga yaganshi a tsaye kusa dashi ya karasa yace "Abba.... "

   Littafin dake hannun kawu ya makamai iya karfinsa,  Asim ya fad'a kan kujera cikin tsoro yace " Yahkuri Abba amma sharri suke...... "

   Yatsa kawu ya nunamai idanunsa sunyi jaa yace "kai dakikin ina ne?  Meyasa sam kwakwalwarka bata aiki? "

  Yai wani hucci sannan ya cigaba "Company  d'in nan na Waye? Kana tunanin dan na rike shi na shekara ashirin yana nufin ya zama nawa? "

  Kai ya jijiga sannan ya cigaba " A'a, da zarar Ashraf yaso zai zo ya amshi matsayinsa ne babu kuma yanda zamuyi. "

  Asim cikin b'acin rai yace " ta ina zamu barshi? "
  Tsaki kawu yai yace " 50% d'in yaya(mahaifin Ashraf) gaba d'aya a gunsa yake,  kai kasan duk karshen wata kud'in dake shiga account d'insa ya ninka nawa mai 20%?"

   Asim wanda ya fara huccin takaici ya kalli Mahaifinsa,  kawu yacigaba "In baka rike matsayin ka ba ka nuna ma mutane zaka iya kana tunanin Ashraf mai taurin kai zai bakka ka cigaba da abinda kaga dama in har ya fara aiki anan? "

   Asim ya mike cikin takaici yace " shiyasa duk duniya ba wanda na tsana irin yaron nan,  mahaifinsa kaf arzikinshi sunan sa yasa,  kai daka wahala gurin taimakama uban sanda yana da rai bai ma kara ya barma ko da wannan companyn ba. "

   Kawu ya zauna kan kujera cikin b'acin rai shima ya kalli Asim yace " Ka kula sannan ka dinga kokarin b'oye tsanar da kakema Ashraf dan naga kamar kanka na rawa baka kunyar nuna mai. "

   Shiru Asim yai baice komai ba.......

     _A Gida_

      Nafi bayan ta gama komai tai wanka dama Little ta fito mata da kaya hakan yasa ta saka ta fito domin zuwa kitchen yin aiki.

   Ta d'anyi tafiya kad'an taji ance "Ina Zaki? "

    Tsayawa tai cak ta kasa juyowa,  shima bai sake magana ba hakan yasa ta daure ta juya a hankali,  daga gefe ta ganshi zaune akan d'aya daga cikin kujerun gun,  gani tai ba kallanta yake ba hakan yasa tad'an kuramai ido,  duk da bai kalleta ba jitai yace " Kallan fa? "

  Da sauri ta d'auke idanta tace " na fito ne kawai"

  Ya kalleta sannan ya mata alama da hannu akan tazo, a hankali ta karasa inda yake, ya kalleta yace " So nake kimin wani abu. "

   Cikin mamaki ta kalleshi tace " Me kakeso yaya? "

  Ya bud'e baki zai magana sai ga Aneesa ta karaso cikin salon tafiya da yanga,  tana zuwa ta shagwab'e murya tace " Cwt Yaya kaifa nake nema. "

  Ashraf ya kalli Nafi sannan ya kalleta yace  " Anie ya akai?"

  Baki ta turo tace "ni dai banasan Anie kacemin Neesah na. "

  Kunne yad'an sosa sannan ya kalli Nafi wanda da alama zaman gun ya isheta yace " Nafeesa jeki kawai. "

  Wani kasalalen kallo tamai wanda ita kanta batasan ta iya ba,  so take ta tambayeshi me yakeso tamai?  Ga Aneesa agun ita kuma duk ta rasa mai zatace,  Aneesa ta maka mata harara sannan tace " Nafi yace kije zamuyi magana ne. "

   Kamar tai kuka haka ta juya ta fara tafiya,  me yake so?  Abinda ke mata yawo kenan.

  Itakam Aneesa zama tai ta shiga mai salo,  wani abun ya biyeta wani kuwa ya juya kai kawai.

   Nafi kam duk aiki take amma hankalinta nakan Ashraf har suka kammala girki,  nan Goggo tace "A d'au na Ashraf akai mai. "
Da sauri Nafi ta amshi tiren tace "bari na kaimai. "

  Goggo ta kalleta tace " kinsan b'angarensa ne? "

  Haka kawai tasamu kanta da yin karya tace na sani.

  Nan Goggo ta bata.

  Fitowa tai tana ta kalle kalle,  nan Allah ya had'ata da Amrah murmushi tai ta karasa gunta tace "Amra inane b'angaren Yaya? "

  Nan Amrah ta nuna mata,  karasawa tai tana tafe tana tunani da fatan Allah yasa yana nan.

    Knocking tai a hankali,  Ashraf dake kwance akan doguwar kujera yana kallo a falo yace "in abinci ne ajiye zan d'auka."

  Nafi ta kalli kofar kamar tai kuka har ta ajiye zata tafi sai kuma ta koma gefe ta zauna a kasa.

  Shikam ya dade kafin ya taso ya bud'e kofar,  mutum ya gane a zaune ya jingina da bango cikin mamaki yace "lafiya? "

  Da sauri Nafi ta mike ta kalleshi,  kallan mamaki ya mata yace " kece? "

  Kai ta d'aga kawai,  yace " D'auko abincin ki shigo. "
  D'auka tai sannan tabi bayansa,  tana shiga ta tsaya a bakin kofar,  ya karasa kan kujera yace " turamin kofar. "

  Rufe kofar tai sannan ta kalleshi,  da hannu ya mata alama akan ta ajiye abincin a dinning,  nan ta kai sannan ta kara tsayawa tana wasa da hannunta,  ya kwanta ba tare da yace mata komai ba,  itama shiru tai dan batasan me zatace ba.

    Shikam kwanciyarsa yai yana jiran tai magana,  sun dade sosai a haka shikam bacci ne yai gaba dashi.

  Nafi tana nan a tsaye jitai kafarta ta fara amsawa,  a hankali ta d'an matso kad'an cikin in ina tace "dama d'azu ne.... "

  Sai kuma tai shiru,  Jin shima baice komai ba yasa ta kara daurewa tace "naji kace zan ma abu? "

   Nan ma shiru,  lekashi tai kad'an,  gani tai bacci yake,  a hankali ta matso inda yake ta kuramai ido,  a ranta tace "na sashi yai bacci baici abinci ba. "

   Kallansa ta karayi,  itadai haka kawai tun sanda ta ganshi takesan taga tana kallanshi,  batasan sanda murmushi ya bayyana a fuskarta ba ta juya tai waje.




  *THE INNOCENT TEAM*

No comments:

Post a Comment