*ZUCIYA*
_ĸowa da ιrιn тaѕa_
© *na Ayυѕнer Mυнd*
ayushermohd.blogspot.com
*Where are u Maman Shaheed, Jidda Samusa and Classic Feedoh? Ur page is here.... LYSM😍*
{ *26*}
Yau saura bikin Ashraf da Aneesa wata d'aya da kwana 10, a wannan ranar ce kuma Nafi ta shirya tsaf cikin uniform d'inta, Little tayi kokari wajen koya mata komai, Nafi ta fito fes da ita abin sha'awa ga kayan sunsha guga.
A wannan lokacin inba fad'ama akai ba ko hausarta kaji ba tabbas bazaka gane daga riga ta fito ba, Little ta jawo a kwatinta tana cewa " Zaki tafi ki barni ni kad'ai. "
Nafi tai murmushi a ranta tace da ina riga bana fita, yanzu nazo nan kuma shima gashi zan koma wani gun.
Little ta dafata tace " Muje Ya Habib na jiranmu. "
Nafi ta kalleta sannan ta d'anyi kasa da kanta tana wasa da hannunta tace " Maryam bazanje inma yaya sallama ba? "
Little ta d'anyi dariya sannan tace " kije mana, amma bada ni zaki ba, ni zanje gun Mumy inkin gama sai kizo can mu had'u. "
Nafi ta d'aga mata kai alamar eh sannan ta fito da saurinta, tana tafe tana tunanin me zata cemai, sam bata kula da Asim a zaune akan kujera ba, har ta wuceshi taji ance " ke dan kut**** baki iya gaisuwa ba? Ko dan zaki tafi wata kucakar makaranta kike tunanin kinfi kowa? "
Nafi wacce tsoro ya rufeta ta kalleshi a tsorace tace " yahkuri Ya Asim wlh ban kula bane. "
Ya girgiza kai sannan yace " da alama ma kayan sa miki akai. "
Nafi tai kasa da kanta kawai batace komai ba, ya tab'e baki sannan ya juya kai tare da cewa " sai aje ayi sallama da dadiron ki. "
Nafi kam bata fahimci me yake nufi sam da dadiro ba shiyasa ma bata damuba, ta juya ta cigaba da tafiyarta a ranta tana mamakin irin zuciya ta wannan mutumin.
B'angaren Ashraf tanufa, a hankali ta kwankwasa kofar, daga ciki Ashraf ya amsa da ashigo.
A hankali Nafi ta murd'a kofar sannan ta shiga ciki, yana zaune akan kujera rike da laptop da alama aiki yakeyi, bai d'ago ya kalleta ba bare tasa ran zai tanka mata.
A hankali take d'agowa tana kallansa sai dai ganin har yanzu hankalinsa nakan laptop d'in ga lokaci na tafiya yasa ta d'aure tace " Yaya zamu tafi. "
"To Nafisa Allah ya kiyaye. " abinda ya fada mata kenan har yanzu hankalinsa nakan abinda yakeyi, Nafi ta kalleshi jiki a sanyaye, makullin d'akinsa ta ciro sannan a hankali ta fara takawa har zuwa inda yake, mikamai makullan tai tace " gashi yaya."
D'agowa yai ya kalleta, idanunsu ne suka had'u gabanta yai wani irin fad'uwa da sauri tai kasa da ido, shikam har yanzu idanunsa na kanta bai kuma amshi makullin ba sai cewa yai "Sanda na baki cewa nai ki dawon da shi in zaki wani gun? "
Nafi ta d'ago a hankali ta kalleshi, idanunsa na kanta hakan yasa ta karayin kasa dakai tare da cewa " kafin in dawo kayi aure nasan kuma a lokacin baka bukatar aikina. "
Bai san sanda ya saki murmushi ba sannan ya maida kansa kan aikinsa tare da sa hannu ba tare da ya kalleta ba dan ya amsa, hannunsu ne suka had'u da juna, sai dai abin mamaki ya kasa d'auke hannunsa haka itama.
Ganin yanda take mutsu mutsu da baki yasa ya rike hannunta tare da makullin.
Yanaji sanda ta d'an zabura kad'an shi dariya ma taso bashi, ta d'ago tare da kafeshi da ido, mamaki ne ya kamata ganin hankalinsa ma baya kanta.
Idanunta na kansa sam ta kasa d'aukewa, jitai yace " kallan bai isa ba? "
Da sauri tai kasa da kanta, yace " ba jiranki ake ba? "
Kallansa tai da mamaki taya za'ai ta tafi bayan ya rike hannunta?
Ashraf ya kalleta cikin mamaki yace " So kike kuyi dare ko da wani abin da zaki fad'amin? "
Nafi ta d'an yi rau rau da ido tace " Yaya Hanuna fa? "
Yanda tai maganar ita kanta batasan ta iya ba, ya kalleta sannan ya kalli hannun, sakin hannun ta yai tare da zare makullin, ya kalleta yace "zan ajiye in ko in dawo sai kizo ki amsa. "
Ta kalleshi da mamakin kalamansa, ta daure kawaj sai cewa tai " Yaya nagode insha Allah bazan baka kunya ba. "
Ya mata wani kallo sannan yace " kada dai kije ki biyewa kawayen banza, sannan kar ki kuskura kiyi kuka da sunan wai kinyi rashin mahaifinki ko nan. "
Nafi ta d'aga kai jiki a sanyaye, nan tamai sallama ta juya a hankali take tafiya har ta fita daga kofar.
Tayiwa Mumy sallama nan Mumy ta bata dubu biyar wai kudin kashewa, itakam Nafi kin amsa tai sai da taga ran mumy ya b'aci tukunna, nan tai godiya suka fito, b'angaren Umma sukaje.
Tana zaune a falo, Aneesa na gefe itada kawarta suna kallan wasu kaya, da kyar aka amsa sallamar ta, jiki a sanyaye ta shiga sannan ta tsuguna tagaida Umma sannan tagaida Aneesa da kyar suka amsa suna mata kallan uku saura kwata, Umma tace " ai anyi dabara da aka saki boarding dan na gaji da ganin yar rigar fulani tana yawo a gidan nan. "
Nafi batace komai ba, Aneesa ta harareta tace " Allah ya raka taki gona. "
Jiki a sanyaye Nafi ta fito daga b'angaren nan ta karasa kitchen tama su Goggo sallama.
A mota ta taradda Little zaune a gaban Mota kusa da Habib suna hira, tasa hannu ta goge fuskarta sannan ta karasa cikin mota.
Habib ya juyo ya kalleta yace " Gimbiya Nafeesa irin wannan jira da aka sani haka? "
Murmushi ta d'anyi sannan tace " Tuba nake, amma gimbiya ai Maryam ce bani ba. "
Habib ya kalli Little wacce taji dadin kalaman Nafi, yace " to me kike so indinga ce miki? "
"sunana mana. "
Habib yai dariya yace " ai ni bana fadan sunan mutum, kowa da sunan da nake cemai. "
Nafi ta kalli little tace " Little ki zabarmin to. "
Su dukansu dariya sukai, nan Habib ya tada mota, Nafi dama tana baya, ita kuna Little na gaba.
Sun fara tafiya Little ta juyo tace " Kinje kunyi sallama da yayan? "
Nafi tai murmushi tare da dg mata kai, Habib ya kalli Nafi yace " me yakeyi? "
Tace " na daiga yana danna abu irin na Little a falo. "
Suka sa mata dariya sannan Habib yace " Ashraf kenan, yanada kwakwalwa ga iya aiki amma har yanzu na rasa me yake hanashi yin aikinsa. "
Nafi ta kalli Habib da mamaki sai dai batasan me zata tambaya ba, jitai Little tace " anya ba abin da bane yake damunsa? "
Habib yai ajiyar zuciya yace " nima ina tunanin wannan, ai ko waye dole ne abin ya zamarmai Karma. "
Kai Little ta jinjina tace " Shiyasa bana ganin laifinsa in yana fada, itama Mumyn ai.... "
Sai kuma tai shiru.
Nafi kam ta kasa shiru ta kalli Little tace " Me ya sameshi dan Allah. "
Little tai ajiyan zuciya tace " Nafi ki bari sai kin dawo zan sanar dake."
Habib ya kalli Little baice komai ba.
Har suka isa makaranta zuciyar Nafi fal take da tunani kala kala menene ya faru da Ashraf? Ita kanta tana mamakin Mumy da ta auri kanin babansa kuma harda 'ya a tsakaninsu.
Sun shiga makaranta nan Principal ta hadata da wata Copper wacce zata dinga nata extra lessons, sunyi sallama Little ta shiga mota duk tausayin Nafi ya kamata.
Nafi kam sai data b'oye hawayenta, Habib ya mata alkawarin zuwa d'aukota shida Little in biki yazo, itakam batace komai ba dan bata wani damu taje bikin ba.
Tana nan a tsaye har suka shiga mota suka tafi, ta goge hawayenta sannan ta karasa gun House Captain dinsu da aka kira, nan ta kira yara yan Js 1 suka kwashi kayan Nafi.
¤¤¤¤¤
A gida kam har yanzu Ashraf bai sakema Aneesa kamar da ba, sai dai yanzu tana iya kokarinta wurin ganin ta farantamai rai, sosai take kula dashi, sai dai wannan ba damuwarsa bace in fact gani yakema ta takura mai bayan shi mutum ne dayakesan ya zauna shi kad'ai.
Mumy da ita da mahaifiyar Habib suka shiga kasuwan ni kala kala mall da sauransu, suka had'a lefe na gani na fad'a, sunso suje Dubai sai dai Ashraf ya hanasu, yace " shi baiga wani abu da za'a siya da har za'a rasashi anan kasar ba. "
Kaya kam anyishi, naira ta gurzu, sai dai wannan ba komai bane a kan irin dumbin kud'in da Ashraf yake dasu.
¤¤¤¤¤¤
An ba Nafi d'aki cikin 'yan ajinsu, gaishesu ta shiga yi dan ita a gunta hakan shine daidai.
Dariya sosai suka mata, jin hausarta yasa suka san bafulatana ce, d'aya daga cikinsu wacce kana ganinta kaga wayayyiya tana kwance saman up na gado, sanye da vest da wando ta zuro kai tace " lalai da alama mun sami yar kwana. "
Dariya suka kara kwashewa dashi wata tace " Ferry ashe kin gano? Da alama kan ba komai sai iyaye suka sami kud'in gomnati. " tafad'a tana kallan tulin kayan provision din Nafi.
Dariya suka kara sawa, Nafi tana nan tsaye idanunta suka fara neman kawo ruwa, watace ta dafata tace " ki shiga da kayanki, sai ki zauna a up gadan dake kallan na Ferry. "
Nafi ta d'aga kai alamar to, sannan ta shiga da kayan, daga ganin yanda suke mata kallan wulakanci yasa tasan bazataji dadin wannan zaman ba.
Sai dai ya zatai?????
Tana gama jera kayanta aka turo wata yarinya akan ta fito karatu karfe 2 tayi, Nafi tayi mamaki ganin ai yau tazo, sai dai ba yanda zatai sallah kawai tai tafita waje tanaji suna gulmar ta.
*THE INNOCENT TEAM*
No comments:
Post a Comment