Tuesday, 9 May 2017

Zuciya....kowa da irin tasa 19

Daga can b'angaren Little wacce ke kwance batajin dadi ta daga,  bayan tagaisheshi bai amsa ba kawai yace "little kizo yanzu. "

  Abinda ya fada kenan ya kashe,  little wacce da alama ciwon mara take ganin yanda take a durkushe sai dai ita batasan meke damunta ba,  ta kalli Nafi wacce ke xaune kusa da ita duk ta rikice kamar ita take ciwo.

   Tace "Nafi dan Allah jeki yayane ke kirana nikuma kinga cikina murd'amin yake. "

Nafi ta kalleta daa idanunta da sukai raurau tace " taya zan tafi in barki? "

   Little tace " naji muryar yayan ma kamar......"

   Ai Nafi da sauri ta mike batama jira karashen zancen ba tai waje da sauri, ganin saurin bai mata ba ga ba mutane agun yasa tadan sa gudu,  tabbas ciwonsa ne ya motsa abinda kawai tasa a ranta kenan.

   Sam bata kula da Asim ba wanda ke kokarin shawo kwana ita kuma zata mike,  dayake gudu takeyi iya karfinta kuwa ta bangaje shi,  Asim ya juyo cikin tsananin mamaki ganin wani kwararen ne?

  Nafi kam jikinta ya fara tsuma ta kalleshi a tsorace tace " Yahkuri yaya dan Allah. "

Asim ya d'ago da niyyar masifa,  sai dai me?  Can ya ganta ta mai nisa sai sauri take, ta sani bazai kyaleta ba sai dai yanzu abu d'aya ne a gabanta ba kuma taji akwai abinda zai tsayar da ita.

    Tana murd'a kofar tajishi a bud'e nan ta shiga ta fara sallama,  jin shiru cikin tsoro kawai ta dannu ciki,  baya falo hakan yasa ta wuce d'akin shi.

   A zaune yake a kasa ya kifa kansa akan gado, ba riga a jikinsa sai dogon wando hakan yasa Nafi ta juya baya da sauri,  a hankali tace "Yaya ga...... "

  Yanda yakeji yasa bai bari ta karasa ba ya katseta "Little yi sauri ki d'au roba a toilet ki taro ruwan zafi ki sa tsuma a ciki kizo ki dinga matsewa kina gasamin gun nan. "

   Nafi ta juyo a hankali tana san cemai ba little bace tace " Ya.... "

"Little wuce mana"

Jiki a sanyaye Nafi ta wuce toilet yanzu ta iya kunna famfo ta kuma san inda ruwan sanyi dana zafi yake,  nan ta tara a roba ta saka towel karami dake rataye a ban d'akin ta fito,  ganin yanda ya kifa kansa ko d'agowa baiyi ba yasa tasan yanajin zafin gurin,  kallan gun tai taga ya kara tashi ba kamar da safe ba,  idanunta ne suka fara cicikowa,  ta karasa a hankali tai kneel down ta bayansa ta fara matsewa tana gasa mai gun,  dun sanda tasa sai taga ya d'an motsa kad'an.
 

  Kamar a jikinta takejin ciwo nan,  intaga ya motsa sai ta runtse ido.

  Asim kam wanda ransa yakai kololuwar tashi ya tsaya ya d'auka yanzu zata dawo yaci mutuncinta, jin shiru yasa yabi bayanta a kufule.

   Bud'e kofar yai a zuciye yai ciki,  me zai gani????? Me kuma idanunsa suke gane mai??????? 
Tofah!  Babbar magana........

   ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤

A b'angaren su Datti kam haka sukai ta yawo suna neman taimako,  kayan da maman hanne tazo dasu suma sai siyarwa tai.

  Da kyar suka hada kudin mota suka koma Gwaram.....

  ¤¤¤¤¤¤¤

  Shikam d'an litti ya musu bayani har ya gaji amma ina... Sunce dole sai ya fada musu wanda ya sani yazo yayi bailing shi.

  D'an litti yace " ku nemo min Ashraf. "

Officer yace " Ashraf wa?  A ina yake?  Meye number wayarsa? "

To fa!  Da masifa D'an litti yace  " nidai ba na fada muku ba?  Sunanshi Ashraf a kuma kano yake. "

  Officer yace " me kake nufi to?  So kake mu shiga kano mu fara neman masu suna Ashraf ko me? "

   D'an litti takaici ya kamashi ya zauna a cell d'in kamar yasa ihu,  gashi sunce inya sake musu turancin nan nasa sai sun fasamai kai........

*THE INNOCENT TEAM*

No comments:

Post a Comment