Thursday, 4 May 2017

ZUCIYA..... kowa da irin tasa 17

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

 

1⃣7⃣

     Kwanaki sun d'an tafi yau kwanar Nafi 10 sai dai abubuwa dayawa sun canza,  sam yanzu Ashraf yadaina mata magana tundaga wannan ranar ko gaisheshi tai kai kawai yake d'agawa,  tana zuwa gyaramai d'aki duk bayan kwana biyu sai dai daga ta shiga yake fitowa,  wannan abu na damun Nafi iya tsanani,  gida ya mata zafi ga Little yanzu suna jarabawa ba zaman gida take ba, sannan cikin gida kowa zancen biki ne a gabansa, shiyasa yanzu zamanta yafi yawa a kitchen,  sosai ta fara iya abinci dan yanzu tana nata iya kokarin.

   Kamar yanda ta saba yau ma a ka'ida zataje ta gyara b'angaren Ashraf suna gama aiki a kitchen tai wanka ta d'au abincinsa tai gaba,  ya bata makuli saboda wani sa'in in bayannan hakan yasa data kwankwasa taji shiru kawai tasa makuli ta bud'e,  karfe goma ne shiyasa kanta tsaye tai d'aki ta d'auka ya fita,  me zata gani?

  Ashraf ta gani kwance ya dukunkune jikinsa da bargo, lekawa tai cikin tsoro idanunsa a rufe suke hakan yasa ta karasa kusa dashi,  numfarfashi yake fitarwa sama sama,  Nafi ta tsuguna saitin fuskarsa,  hucin da yake fitowa daga bakinsa yasa tasan yanajin jiki, kuramai ido tai kawai hawaye ne suke zubo mata wanda ita kanta batasan tanayi ba,  a hankali yad'an bud'e ido ganin Nafi yasa ya ciro hannunsa da niyyar yi mata bayani,  itakam ganin yana miko hannu tai saurin rike hannun,  ya kara daurewa ya bud'e ido,  yayi mamakin ganin yanda take zubar da hawaye sai dai abinda yakeji yasa ya d'aure yace " rub zaki mikon."

  Mikewa tai da sauri ta shiga dube dube,  hannunsa ya sa ya nuna mata inda yake,  da sauri ta d'auko ta mikamai, nuna mata kafad'ar hagunsa yai ya d'aure da kyar yace shafamin anan. "

  Kallan mamaki tamai sai dai gani tai idanunsa a rufe suke, mikewa tai a hankali ta rasa ta ina zata fara,  ganin yanda yake hucci yasa ta d'aure a hankali ta d'an yaye bargon daga b'angaren sa na haggu.

    Vest ne a jikinshi shiyasa tana iya ganin gun,  mamaki ne ya kamata ganin gun ya kumbura,  da alama bigewa yai ko kuma wani abun lalai wannan ciwon ne ya sa mai zazzab'i,  kallansa tai cikin tsananin tausayi wanda bata tab'a ji ba,  yau ce rana ta farko da takeji inama ciwon ya dawo jikinta,  a hankali ta d'ebi rub d'in ta fara kokarin shafawa,  sai dai daga takai hannunta kan jikinsa sai tai sauri ta d'auke,  tasan magani ne da alama kuma yanda takeji maganin zafi zai mai.

   Cikin wani yanayi wanda Ita kanta bata sani ba tace " Yaya baka ganin zaiyi xafi? "

   A hankali yace " Nafeesa samin ba zaiyi ba. "

  Idanu ta rufe kamkam kamar ita za'a sawa a haka ta samai,  sam batasan hawayenta na d'iga akan gun ba,  Ashraf kam ido ya rufe dan akwai zafi sai dai jin hawayen nafi agun ciwon yasa jikinsa yai sanyi,  meyasa? Menene dalilinta? Wata zuciyar tace kasan Nafi da tausayi.

  

   Tana gamamai ta maida bargon ta rufe shi sannan ta share hawayenta wanda ita kanta tana mamakin yanda suke zuba haka, cikin sanyin murya tace " Yaya ka tashi ko wani abin kaci. "

  Kai ya girgiza mata alamar a'a,  idanunta suka kara cicikowa tace "Yaya dan Allah,  in kumaa da wani abu da kakeso sai in maka yanzu. "

   Idanu ya bud'e a hankali ya kakaro murmushi sannan yace " me kika iya?"

   Da sauri tace "duk abinda kakeso na iya kaji. "

  Ganin baiyi magana ba yasa tace "Dankali aka soyama da farfesun kayan ciki,  xaka iya ci? "

  Kallanta ya sakeyi sannan yace "eh"

Da sauri ta mike tai falo ta dan zubo a plate,  tazo kusa dashi,  kallanta yai baice komai ba.

  Itama tsayawa tai rike da abinci batasan ya zatai ba.

  Suna nan a haka har bacci yai gaba dashi,  kuramai ido tai a hankali tace "Kayi bacci sau biyu kenan Ina tsaye. "

  Tai murmushi sannan tace "sai dai duk banajin haushin hakan. "

   Falo ta fito  ta maida abincin sannan ta shiga gyara,  har ta gama bai farka ba,  itakam zuciyarta na raya mata taje ta sanar da mumy halin da Ashraf ke ciki, sai dai tana tsoro dan kuwa tasan halinsa,  ta kuma kula kamar ba wani shakuwa sukai ba.

    Gashi ta gama aiki kuma sam batasan ta fita tabarshi shi kad'ai,  kuma tana tsoron kar azo a ganta matsala ta sake faruwa wanda ita kuma bataso.

   Haka tanaji tana gani tai waje tana waiwayen d'akin.

   _Kauye_

   Yau tun safe su maman Hanne suka shirya ita da Datti akan lalai yau ya kamata suje ganin muhalin Nafi saboda ai dama bai kamata suje daga farko ba.

   Sun fito suka tarar da D'an Litti a inda sukai zai jirasu,  Kowa ya kalli D'an litti  sai ya kara saboda tsananin gayun dayasha,  riga ce ta shadda mai dogon hannu yasa wando jeans ya tutura rigar a cikin wandan sannan ya kwama takalmi sau ciki ba safa,  ya kawo hula irin tamu ta hausa ya saka,  sannan ya kwama glass dinsa,  gefen aljihun wandon kuwa ya ajiye wata zargab'ebiyar wuka.

    Tsayawa yai ya wani karkace,  su Datti suka karasa, maman Hanne na rike da gari yai zafi,  wanda 'yan uwan Nafi suka harhad'a mata tarkace su fura ne,  kayan mata ne, gayayyaki na magani,  su daddawa ne,  kub'ewa busassa da sauransu.

    Datti ya kalli D'an litti  yace " kai amma wannan yaron kana burgeni,  ni kam dama kaine ka auri Nafi ba wannan ba. "

  Dan Litti ya juyo cikin gayunsa yace "Haba Malam ni ai nafi karfin Nafi sannan ni abinda yasa nake san zuwa rakiyar nan ba komai bane ila I want me to see Ashaf. "

  Datti ya juya kai tare da tab'e baki yace " mu tafi nikam ba turanci ne a gabana ba. "

  Sun isa Gwaram suka samu wata bus anata lodi masu zuwa kano nan suka shige,  Datti yai dariya yace " Ashe ma abin ba wuya."

    Me ruwa ne ta leko tana asai ruwa, Dan Litti ya kobare cikin salonsa yace " ke me ruwa Me too want water one. "

  Ta kalleshi tace " Dan boko banajin turanci. "

  Maman Hanne tace "Kayi mata da hausa D'an litti kasan ba iyawa tai ba "

  Yai murmushin kasaita yace " okay, bani ruwa d'aya. "

  Nan ta bashi, Datti yace "lalai yaro muna zaune dan rashin d'a'a sai ka sai ruwa kai kad'ai ba tare da ka sanmana ba? "

  Dan litti ya kara gyara zaman glass d'in sa yace "gatannan ka siya kaima."

      Datti ganin inya siya sai ya saima maman Hanne hakan yasa ya gwara shima ya hakura.

  Nan mota ta tashi suka fara tafiya..........

    _Gida_

   Kawu ne ya kalli Mumy wacce ke zaune cikin damuwa,  yace "Hajiya lafiya kuwa? "

   Kallansa tai cikin kulawa tace " Tunani nake yaushe ya kamata asa lawyer d'in mahaifin Ashraf ya kawo sakon wasiyyar nan? "

  Kawu ya mike zaune tare da dafata yace "Hajiya karki damu da wannan,  ai shima Yayan cewa yai abama wacce Ashraf ya fara aura,  sai mu bari sai anyi auren kenan ko? "

   Tai d'an dariya tace "I am really curious akan me ya ajiyema Matar Ashraf wanda ba wanda ya sani sai shi daya tafi. "

  Kawu yai dariya yace "nikaina na k'osa naga menene wannan, da yace lalai matar Ashraf ta farko ya umarta abama. "

  Nan suka shiga tattaunawa akan al'amarin wanda ba su kad'ai ba kowa ya kosa yaga menene wannan abun......

  To nima daban taba ji ba sai yau na k'osa na gani sai dai ina ta tambayar kaina,  Wacece matar Ashraf ta farko??????

*🗣🗣🗣🗣🗣🗣My Beely Badaru,  duk Amarcin ne🙈?*

*THE INNOCENT TEAM*

No comments:

Post a Comment