Saturday, 13 May 2017

ZUCIYA.....kowa da irin tasa 22

*ZUCIYA*
       _ĸowa da ιrιn тaѕa_

© *na Ayυѕнer Mυнd*
    ayushermohd.blogspot.com

2⃣2⃣


      Mumy ta fito jiki a sanyaye kanta sai sara mata yake yi,  a waje ta hango Aneesa ta taho kamar zaki rike da wata zungureriyar waya tana tafe Umma na mata magana amma da alama bata ma jin me ake cemata,  Mumy tana tsaye a kofar su Little har Aneesa ta karaso,  idanunta sun canza.

   Da mamaki Mumy ta kalleta tace " Neesah meye hakan? "

  Aneesa wacce sai hucci take ta kasa magana sai neman cusa kanta ciki take,  Mumy tasa hannu ta riketa tace " Neesa meye hakan wai? "

  Umma ce ta karaso cikin kinibibi tace" Yauwa gwara da kika riketa wai Nafi zataje ta zane. "

  Mumy takaici ya kamata tace " in kuma Ashraf d'in yajiki kice me? "

  kallan Mumy tai kamar mai shirin kuka tace" Mumy amma kina ganin..... "

  Mumy tace " Laifinkine,  in har Nafi ta fiki sanin meke damun Ashraf, ke da zai zama mijinki amma ace ba kece ke kula da shi ba. "

   Umma tace " wace irin magana kikeyi haka?  Haba Amina ya zakisa yarinya a gaba wacce ranta yake a b'ace ki kara b'ata mata."

  Mumy ta kalli Umma sai dai takaicin abinda yake faruwa yasa ta kasa tanka mata.

  Umma ta juya kai tace " haba Amina _wace irin zuciya gareki?_ace ke kawai d'anki kika sani? "
  
  Mumy ta juya batare da ta sake magana ba.

  Aneesa ta kara zuwa wuya gani take kamar saboda Nafi itama Mumyn take mata haka.
Hannunta ta fizge daga gun Umma tai ciki a zuciye.

  Nafi kam ta d'auro alwala isha'i kenan,  ta zauna a bakin gado ta rasa abinda ke mata dadi,  taji an banko kofa da karfi kamar za'a b'ala,  da sauri ta kalli kofar.

  Little dake zaune akan kujera ma ta d'ago da sauri.

  Aneesa a zuciya ta shigo d'akin,  Nafi dake tsaye ta shiga kallanta cikin tsananin tsoro,  Little ta mike tace " Ya Neesa meye kuma hakan? "

Aneesa ta buga mata wata muguwar harara sannan ta nufi kan Nafi gadan gadan Umma kuma ko kunya tana tsaye a baya.

  Da karfi Little tace " Wlh Ya Neesa kika daketa sai na fadaki da Yaya. "

  Cikin kuluwa Aneesa ta wurga mata kallo,  Little ta kalleta tare da d'aukan wayarta tace " Wlh kika daketa yanzu zan kirashi."

   Aneesa kam ta kulu fam kamar zata fashe,  Umma ta matso ta gaurama Nafi mari iya karfinta sannan ta kalli Little tace" ni ki tabbatar kin fadamai inyaso ya zo ya rama mata. "

Tana kai nan ta fizgi hannun Aneesa tai gaba.

   Nafi kam ko kuka batai ba dan ganin zabgegiyar bulalar dake hannun Aneesa yasa batama ji zafin marin sosai ba.

   ¤¤¤¤¤

Mumy kam ana idar da sallah tai b'angaren Ashraf,  a hanya suka had'u da Mumy baice mata komai ba sai dai yasan gunsa tazo,  nan ya bud'e ya shiga tare da kunna kwan wuta.

  A bud'e ya bar kofar hakan yasa Mumy ta shiga.

  Shikam d'aki kawai ya wuce,  ya d'au ruwan da Nafi ta gasa mai gun ciwon ya zubar a toilett,  sannan ya matse towel d'in ya shanya sannan ya fito.

  Mumy na zaune hakan yasa yaje d'an nesa kadan da ita ya zauna a kasa,  Mumy ta kalleshi jiki a sanyaye tace " Ashraf abinda ya faru d'azu kayi hakuri....."

  D'agowa yai ya kalleta idanunsa sunyi jaa jikinta ya kara yin sanyi,  cikin wata irin murya wanda mai sauraro shi kad'ai zai fahimci abinda ke zuciyar me maganar Ashraf yace " Kin taba yadda dani Mumy?  Ko me aka fada a kaina tun ina karami kin taba yin bincike kafin kimin fada? "

   Mumy idanunta suka cicika da kwalla sai dai tsananin tausayin Ashraf dake yawo a ranta.

  Hannu yasa a bugi inda zuciyarsa take da karfinsa wanda kana iya juyo karar dukan ya cigaba " Kinsan ya nakeji a raina? A duk sanda kika zargeni da abinda banyi ba?....."

  Kasa karasa kalamansa yai saboda wani rad'ad'i da zuciyarsa take mai, Mumy wacce ganin yanayin d'anta da bata taba gani ba yasa hawayen datake b'oyewa suka zubo ta gefen idanta.

  Kallansa tai cikin dauriya tace " ba haka bane Ashraf. "

Ya kalleta sannan yai wani murmushin takaici yace " Nafi zata tafi makarantar kwana a satin nan insha Allah. "

Mumy bata d'auke ido a kanshi ba tace " amma naga kamar ba tada karatu? "
Ya sake yin wani murmushin wanda itakam mumy sam batasan taga yayi saboda bata sani me yake nufi yace "eh hanya za'a mata ta shiga Js ko 3 ne inyaso sai a dinga mata lesson kuma a makarantar. "

  Mumy ta jinjina kai tace " hakan yayi sai dai baka ganin karatun zai mata wahala? "

  Ashraf ya d'an tab'e baki yace " wannan kuma ruwanta. "

  Mumy tace " shikenan in makarantar ta fito sai ka fadamin sai muje a mata shopping Allah ya baka lada ya kuma yi albarka. "

  A cikin ransa yace Ameen,  ta mike tace " bari inje. "
Bai amsa ba ko ince tasan ma bazai amsa ba,  tana fita yabi bayanta da kallo sannan ya koma d'aki ya d'auko diary d'in mahaifin sa wanda wasiya ce kawai ya barmai.

  Shafin farko wanda a kullum sai ya karantashi yau ma shi ya karanta " _Ashraf kada ka kuskura kabar mutane susan abinda ke zuciyarka,_  _ka dinga kokarin b'oye bakin ciki ko farin cikin dake ranka, kar ka bari wani yasan sirrinka, wannan ita kadai ce hanyar da zaisa ka kare kanka...ko da kuwa 'yan uwanka ne na jini..._"

   Ashraf ya share zufar data keto mai duk da sanyin AC d'in da ke d'akin,  Murmushi yai wanda kana ganin kasan na bakin ciki ne a fili yace " Dad zan iya jure hakan kuwa?  I am really lonely."

   Ya kwantar da kansa kan gado,  kafad'ar sa na masa zugi sai dai zugin dake zuciyarsa tafi karfin wannan.......

 

    ¤¤¤¤¤¤

  Habib kam da kansa ya samu Abbansa ya mai bayani, Abban Habib na tsananin san Ashraf a lokacin ya kira wayar abokinsa ya sanar dashi, sunyi rashin sa'a matar tashi an mata transfer zuwa Rumfa Collage sai dai ya sanar dasu ai kanwarta ma principal ce ta FGC na kazaure,  nan ya sanar musu in suna san can d'in to a yanzu zai kira kanwar matar tasa ya fada mata.

  Nan Habib ya ma Abba alama da a yadda,  sunyi sallama akan zai kira anjima.

  Ba'a dade ba ya kira tare da sanar dasu ba matsala duk sanda suka shirya ko gobe ne su kaita.

   Nan Habib ya kira Ashraf yamai bayani.

¤¤¤¤¤

   A b'angaren D'an litti kuwa yan sanda sun gaji da ajiyarsa gashi abin haushi bashida alamar sanar dasu Inda Ashraf yake,  duk kuwa da dukan da sukamai,  hakan yasa haushi ya kamasu suka cilloshi waje tare da kwace wukar dake jikinsa.

  D'an litti ya sha kuka wiwi gashi ko ficika bashida shi, ga wunya datake damunsa.

  Dakyar ya mike ya dingisa ya shiga gari,  yayi sa'a ya sami wani mutum ya bashi naira d'ari.

  Nan ya gangara yasai wainar gero kan kace me ya cinye,  ta gumi ya baza yace " Oh Ni D'an litti haka rayuwata ta koma?  Daga boko sai a nemi halakani? Yanzu ni ina zan nufa in nemo Ashaf d'in? "

  Ya jingins kansa da bango zafin rana na damunsa.

  Nace wayyo🤦🏻‍♀

*THE INNOCENT TEAM*

7 comments:

  1. Interesting waiting for more plssss

    ReplyDelete
  2. Well done. Please NI da prince remaining

    ReplyDelete
  3. Please sis ki dan dinga posting mana a blog, sai muyi ta zaman jira ashe kina posting a Facebook bamu sani ba.

    ReplyDelete
    Replies
    1. Kuyi hakuri please wlh abubuwan ne dayawa, amma insha Allah zan dinga posting da zarar nagama...nagd.

      Delete
  4. Toh, Allah ya baki ikon yin hakan. Muna godiya sosai, Allah ya kara basira.

    ReplyDelete